8: Tuhuma
by @mbello38
A gajiya a wahale gashi an daddaure hannayenta, adeela ce a keji. Bakin ciki da takaici sun cikata gashi batada wata hujjanda zesa a yadda da batunta gameda tashera. Bugu da kari ga amshe ruwan rakenda tashera tayi.
Babban cikinsuma shine shairin data kulla mata na sanadiyan rasa rayukan kiyashinda suka fita tare. Koranta daga tudu za'ayi har abada. Kudurinta ya tashi aiki kenan? Ta zama korarriya kenan? Ba tudu, ba 'yan uwa, ba kowa?
Kai baze yiwuba. Amma muddin tashera ta kaima sarauniya ruwan zaki adeela ta tashi aiki. Zata yarda da duk karyayyakinta. Oh ita adeela shikenan rayuwanta tazo karshe. Dama tayi zamanta a tudun fira at least su suna bukatarta.
Seji tayi an bude keji, tashera ta tako ta daga haban adeela. "Kin tashi aiki. Gumza, katseta ki tafi da ita!"
Haka aka kawo adeela dakin sarauniya aka jibge a gabanta.
"Wannan itace adeela sarauniyata. Itace me laifin." Tashera tace cikin zumudi.
Wani mugun kallo sarauniya tayima adeela cikin takaici. "Wato kece kikayi sanadiyan rasa rayukan kwari don shegen rashin jinki ko?! Kuma har kinada kwarin gwiwan dawowa nan tudun!! Bayan wannan mummunan laifinda kika aikata!!!"
Adeela ta dago a gajiye ta kalla sarauniyar. Ta kalla sauran manyan kwarin dake wurin sannan ta kalla tashera ta nunata.
"Ita ta bada shawaran abi katanganda jangwale yake harya biyomu. Ita ta biyo hanyata lokacin da nake boyema jangwalen donya biyoni ya cinyeni. Ita ta amshe kwallon ruwan raken dana samo ta kawo miki. Ita kuma ta amshe kafan faran dana samo ta kai dakin ma'adinai. Tashera ta shahara wurin amshe duk abinda na samo."
Yaran kwari uku suka shigo dakin tareda sintura suka tsaya gefe suna kallon adeela. Gaban sintura ya yanke ya fadi tana mamakin yanda taga adeela. Meya faru da kawarta?
"Aw haba? Ina amshe abinda kika samo kamanme? Ko akwai wanda ya ganta da kafan fara?"
"Kece kika kawo kafan fara dakin ma'adinai." Dumu ta tabbatar da hakan.
"Amma aiba ita ta samoshiba, amshewa tayi daga wurina."
Sintura ta kallo tashera. Haba itade tasan kawarta bazata taba yin abinda ake tuhumarta dayiba.
"Haba? Wa yaga lokacinda dana tura miki jangwale? Wa yaga lokacinda dana amshe ruwan rake? Duk hujjojinki na iskane donko karya kikeyi! Sarauniyata, a hukuntata daidai da dokan tudun adama!"
Harma seda tashera ta tuna dan guzurin jakan abincinda adeela ta watsar a kasan katanga wanda ita tasheran ta cinye a hanyan dawowanta tudu.
Shugaban sojoji, para ta kallo adeela. Ta bude baki seme?
"Mu munga lokacinda kika kwace kwallon ruwan rake daga adeela." Jafu ya maida bayani.
"Kika nausheta." Bilba ta kara.
"Kikasa gumza da wasu mata su uku suka matseta kika kwace kwallon ruwan rake daga bakinta." Jafu ya karasa labarin.
Kallo ya koma kan tashera, ta sankare. Ya akayi wadannan yaran suka san abinda tayima adeela? Kenan suna wurin lokacinda ta kwace ruwan raken?
"Sarauniyata, da an kawo miki ruwan rakenda yafi haka yawa, amma wannan matan ta jawo kiyashi suka rasa ransu. Ki koreta kawai!"
Sarauniya hubba ta gyada kai cikin amincewa da batun tashera. Gaban sintura se bugawa yakeyi don in sarauniya taji maganar tashera, to kawarta ta kade.
Adeela ta kalla tashera cikin tsana. Wato itade ta dage seta sa sarauniya ta koreta a bisa laifin da bata aikataba! Ji tayi kaman ta shaketa.
"Amma adeela kawarmuce." Bilba ta koka. Haka kawai za'a koran musu kawa me cetonsu daga hatsari!
Idanun adeela suka sauka kan bilba. Ta gane sune yaran data ceto daga cikin gidan gona. Allah sarki, ashe akwai masu sonta.
"Ita ta cecemu daga gizo da rina lokacinda suka biyomu." Rijami ya bayyana.
"Babba Adeela nada kirki sarauniyarmu, karki koreta." Jafu ya koka.
"Da gangan ta jawo jangwale ya cinye sauran kiyashin, kirkin kenan?" Gumza ta bayyana.
Kai! Adeela ta koka. In kanada makiya, ka guje shairinsu. Ta yaya za'ayi ta bada shaida akan abinda bata ganiba?!
"Ke baki wurin lokacinda abin ya faru, ta yaya akayi kika tabbatar ita adeela ta jawo jangwalen?" Jaguwa ta tambaya gumza.
Shiru. Can ta kalla tashera. "Tashera sojace me kulada rayukan kiyashi. Akan me zata mata karya?"
Sarauniya ta kara gyada kai cikin yarda da kalaman gumza.
Tunda adeela taga haka ta san shikenan kashinta ya bushe. Za'a koreta akan abinda batayiba. Me laifi zata kubuta.
"Kaman yanda dokan tudun adama take, ke adeela, zaki tara inaki inaki kibar......."
"Dakata sarauniyata!"
Kowa ya kallo kofan dakin. Wata kiyashi ta shigo a jigace, a wahale, tana dingishi kafarta daya an cire, antenna daya babu, ta iso ta tsaya gaban sarauniya.
Kallon adeela tayi, Aiko adeela ta sankare. Tasah ta mutu! "Paipai!!!"
Shikenan karya yazo karshe. Paipai zata tona ma tashera asiri. Yau karshenta yazo. Tashera najin sunan tasan karyanta ya kare ta kalla gumza. Para ta kalle paipai cikeda mamaki. Daga gani taga rayuwa.
Sarauniya nata kallonta da yanayin data shiga. "Paipai, meya sameki?"
Bayan bada muguwan shawaran da tashera tayi, lokacinda jangwale ya biyosu, paipai da wasu kwari uku suka ruga a guje donsu tsereme amma inaaa, jangwalen bade huduba ga iya tsalle. Dirowa yayi kan duka kwarin ukun suka mutu ya cinyesu.
Paipai ta tsira amma ya cire mata kafa daya da antenna daya. Ta ruga ta boye a cikin wani shuka. Se ganin tayi jangwalen yabi tashera da adeela. Abinda yaba paipai mamaki shine, tashera zata iya boyeme ba tareda ya san inda takebama amma seta fito tabi hanyanda adeela ta boye sukayita gudu.
Abindama yafi bata mamaki shine, lokacinda tashera tabar gudu ta fuskanci jangwalen. Paipai tasha shikenan za'a cinyeta amma seme, wani jangwalen ne ya bayyana suka hau fada dana farkon.
Ita kuma tashera ta koma hanyan tudun bayan ta cigabada da tafiya samo raken. Paipai ta kai har yamma kafin ta iya dawowa tudu amma seme? Daga tudun mitsili ita da wasu kwarin tudun suka hango su tashera suna bugun adeela suna amshe kwallon ruwan rake.
"Karya takeyi! Ya za'ayi in bada wannan shawaran a matsayina name kulada rai da lafiyan kwari?!!" Tashera ta musa.
Paipai ta kalla tashera cikin takaici. "Kawata....kauya, a idona aka taketa ta mutu kuma aka cinyeta. Duk akan muguwan shawaran ki!"
Kowa yayi shiru yana tunani. Dumu tace aiko labarin yara ya tabbata na amshe ruwan rakenda tashera tayi. Kulada lafiyan kwarin kenen? Ga duka ga amshe wahalan wata? Watanma ta kasa da ita?!
Lampura tace tasan paipai nada gaskiya da rikon amana. Bata taba karyaba kuma a yanda taji jiki haka, wane karyane zata iyayi akan tashera?
"Inma tana kulada rayukan kwari, banda nawa. Nasha wuya a hannunta." Adeela ta fadi a sanyaye.
Shiru ana jimamin wannan rikitaccen al'amari. Aikin soja shine kulada rai da lafiyan kwari. In har soja zata iya cin amananda aka bata, to be cancanta ta zama sojaba don zata iya kawo karshe kwari. Ta zama karyarriyar soja.