Page 2
*KARAGAR MULKI*
(A historical, fictional,magical,heart touching love story, with confusion ,destiny and betrayal )
***
For WhatsApp groupππππππ
For WhatsApp Channel ππππππ
***
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
β€ Wannan page naku ne massoya na β€ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘
PAGE 2
FREE PAGE
"Ranka ya dad`e a sake duba wannan lamarin duba da yawan rayukan mutanen da su ke a hannun mugayen kuma azzalumai mutanen nan"....." Ya Isa haka Madaki fad`uwar girma ne ga rak`umi ya shanye ruwan d`an tsako don na riga da na gama yanke hukuncina,Babu ta yanda za ai saboda `yan tsurarun rayukan da ba su fi a k`irga su ba,in sa K`asata da Al'ummata cikin tashin hankali da musiba, da masifa ba na jin zan iya aikata hakan,Bazan ta`ba yarda wad`annan tsirarun Dakarun su zame min hayak`i fidda na kogo ba ,ko ka manta ne yanzu ku ka kawo min koken halin da mutanen k`asar nan suke a cikinsa,sake mai-maita min inji "," Allah ya gafarce ka ya kuma huci zuciyarka na yi wannan maganar ne".....tsawa mai k`arfi Me Martaba Sarki Abdullah ya daka masa tare da cewa, "Mai-maita min abinda ka fad`a"," Tuba na ke Ranka ya dad`e na tuba na bi Allah na bika cewa nayi 'Talakawanka sun shiga cikin firgici gami da rud`u a yayin da suka sami labarin cewa jirgin ruwa na wannan k`asar ya fad`a hannun mujusawa mutanen can wato mutanen k`asar BAIBAH,`yan kasuwarmu masu fita fatauci sun kasa fita fataucin su,hakama ma su shigowa su kawo ko su sari kayanmu a wannan k`asar sun dakata da zuwa ,Kai ko da daga cikin Gidajenmu ba kowa ke da zarrar iya fita yai wani sharafi ko wani uzuri na saba,hatta da matanmu ma su zuwa dauji su d`ebo magunguna ko lallen da su ke k`unsa ma hannayensu da kuma itace da su je Ζonawa duk sun firgita gami da dai na zuwa domin jin tsoran abinda ka iya riskar su a saman hanyar su ta zuwa,marasa lafiyarmu kuwa na cikin halin rad`ad`i da azaba sakamakon babu maganin da za a ba su su sami sauk`i ko sassauci,Allah ya ja zamaninka wannan Shine abinda na ce da kai".
"Amma a irin haka kake so in jefa rayuwar su a cikin halaka da kuma halin k`ak`anikayi,sun fa yarda da ni sun aminta da cewa zan iya kare rayuwa da dukiyoyinsu ,taya zan Kasa cika masu wad`annan mafarkan na su,ko ka manta ko da mage ta tsofe gashin bakinta ya fi k`arfin zuwa bakin `bera ,ko mutum d`aya Babu a cikin fadarnan da ya amince da irin abinda kace ko da irin su Dagaci ko Hakimi ne,ta ya zan amince ma?",
" Ni ma abinda na gani kenan ya mai girma Ranka ya dad`e ",cewar Waziri ya k`ara da cewa," Ai ba yanda za ai saboda wasu `yantsirarun rayuka mu jefa d`unbi ko in ce milyoyin Mutanenmu cikin tashin hankali ba ,idan mu ka aikata hakan kenan sun zame mana dutsan d`anawa wajen rusa daula da iyaye da kakannin mu su ka sha fama gami da zubar da jinanen su wajen ginawa".
Makama ne ya kar`be zance da cewa ,"Gaskiyar ka Waziri domin hakan ma ba mai yiwuwa ba ne,ina da tabbacin in har aka bari a kayi wannan yak`in ba abinda zamu samu face k`asarmu ta jik`a gami da kwaranya da jinanenmu da na `yan'uwanmu,matanmu,`ya`yanmu,iyayenmu Kai har da k`ananan yara da ma mu kanmu, kaga mun bada damar da zamu kashe kanmu da kanmu kenan,duk da dai ance abin sa'a da nasara ne a tsinci matar d`an garuwa da cikin tulu kuma har ta haifeshi lafiya",ya k`are zance ya na mai ya mutsa bakinsa da fuskar sa"Yauwa Makama ka fad`i maganar da ta dace anan, ina Tafida da Galadima duk ku fito ku tofa albarkacin bakin ku mana,in ba haka ba za ai mana sagegeduwa a yi mana sakiyar da ba ruwa,tunda ni dai na dad`e da sanin cewa kifi da kaska ba sa ta`ba Zama wuri guda,kamar yanda suka turo Maga takardarsu da takarda a juya bayan takardar a rubuta masu cewa mu ba mu da wata Alak`a da su ba ma mu san su ba,dan haka suna da damar da za su yanke masu duk hukuncin da suka gadama, to fa hakan zai ba mutanen k`asarnan ta komoBIHINAR salama a zukatansu su fito su cigaba da duk hud`d`od`i da hidimunsu,idan kuwa ba a aikata hakan ba nan gaba kad`an mak`abartar Garinnan za ta fara amsar bak`i daga haka kuma sai ai batun cika, domin yunwa da k`ishi za su fara hallaka mutanen mu ,kar ma a kai duba ya zuwa marasa lafiyar mu a tsaya a yunwa da k`ishir ruwa kawai ",Cewar Waziri,nan fa hayaniya ta `barke a cikin fadar kowa na fad`in abinda ke bakin sa.
Sai da shi da kansa Me Martaba Sarki Abdullah ya tsawatar masu kana su ka natsu
"Da sauran kallo wai anci gumba an hana maye ,duk ina hankalin ku ya ke ne ko kun manta cewa har da Yarima Haisam a cikin wad`annan Dakarun, kuma ku ke cewa a kyale su rayukansu su salwanta,ba me k'ara, kawaici ko hangen nesan da zai iya hango hakan a kaf cikin ku,ko da ya ke ban yi mamakin ba tunda garin banza a farau-farau d`in wofi ya ke k`arewa kuma ma dai buri ke sa mutum ya sauka da kan tsandauri ya koma bisa yashi ko ta`bo", cewar Madaki
Galadima ne ya matso ya na cewa," A'a Madaki wannan kalami ,furci ko zance bai kamace ka ba,domin ka san ko Goma ta lalace ai ta fi biyar albarka,ka ga kenan bai kamata ka danganta mu da wannan maganar ba kuma ai duk jirgi d`aya ya kwaso mu da ga mu har kai d`in",Nan fa wata sabuwar hayaniyar ta sa ke `barkewa har ana k`ok`arin cire mayan riguna
A wannan karon ma Me Martaba Sarki Abdullah ne ya k`ara natsar da su ya d`ora da cewa," Kamar yanda Waziri ya ce za ai haka d`in don dama mun zauna nan don mu samu matsaya ne,da zata bamu maslaha ne ba wai mu yanke hukuncin da zamu dawo muna kuka da shi ba,duba da ganin d`aukacin fadawan da muke da su sun nuna da a janye game da maganar yin fito na fito ko yak`i tsakanin mu da mutanen k`asar BAIBAH, to hakan shine matsayarmu dan haka Maga takarda ya aikata abinda Waziri ya ce domin mu samu zaman lafiya a k`asarmu,sannan dad`in dad`awa ina son a isar da sak'o ga duk wani wanda d`ansa ko d`an'uwansa da ke cikin wad`anda wannan iftila'i ya ratsa da su ,to zamu bada diyya,duk mutum d`aya zamu bada Dirhami Hamsin ,Dinare d`ari da kuma rak`umi wanda ya ke d`auke da kayan abinci,a matsayin diyyar rayukan su".
" Fak`at an kawo k`arshen wannan zance hakan da ka aikata shine mafita da salama a gabaki d`ayanmu",cewar Waziri alamun abin yayi masa dad`i ya na mai watsa hannayensa sama kamar yanda ya saba.
Sai da Sarki Abdullah ya had`iye wani abu da ya zo ya tokare masa a mak`okwaronsa kana ya ce,"Kowa zai iya tafiya na sallame ku,tunda mun kawo k`arshen wannan lamarin",cewar Me Martaba Sarki Abdullah ,kusan kowa daga cikinsu da tseguminsa k`unshe a bakinsa su mai hanyar waje,Madaki kusan shi ne na k`arshen fita,daga bisani ma kasa cigaba yayi da tafiya ya tsaya ba tare da ya fita ba kuma shi bai shigo ba,ganin hakan da Me Martaba Sarki Abdullah ya yi ne ya sa a ka kira ma sa shi,ko da ya zo tsaye ya yi ba tare da ya iya cewa da shi komi ba,hannu Me Martaba Sarki Abdullah ya kai yana mai cire rawanin da ke d`aure a saman kansa,shima Madaki cire na sa rawani yai tare da samun wuri ya zauna gefa dashi,suna cire rawaninsu ne idan har za su tattauna maganar da ta shafi ahalin su ba wai Sarauta ba,shi Madaki k`ani ne a wurin Sarki Abdullah.
" Kayi hak`uri Yaya ba ni da yadda zan yi ne har sai na nuna ainihin gaskiyar da ke binne a cikin zuciyata,domin lamarin ya zame min gaba kura baya siyaki"......"Duk da kana da yak`inin hakan ba zai amfana ko canja komi ba ?",Me Martaba Sarki Abdullah ya katseshi ta sigar tambaya
"Hmmmmmmmm kar ka aro mayafi ka yafa a saman harshen ka domin yunk`urin ko k`ok`arin lilli`be wani abu da ya ke a zahiri,ka sa ni nima kuma na sa ni,ko a k`asar arna k'are ba ya biyayya kuma na san da biyu wai an jefi biri da rani saboda Yarima Sadauki ya na cikin wannan tawagar ne ka yanke wannan tsatsauran hukuncin akansu, amma da ba shi a ciki nasan za kai iya me yiwuwa wajen ganin ka ceto wad`an cen Dakarun,duk hasken fitila bai kai ya na wata ba,duk fa wanda za ka jawo jikin ka bai kai ya shi ba,na rasa gane wacce irin zazzafar k`addara ce da musiba ta gifta a tsakanin ku kai da shi?".
" Shi ya za`bi da yai irin wannan rayuwar,Madaki idris duk abinda ka ga ya ke faruwa da shi daga gare sa ne,Ni ba ni da hannu ko wata alak`a a cikin hakan,kuma a saboda rayuwarsa shi kad`ai ba zan aikata babban kuskuren da zan zo in yi dana sa ni ba,ko ka manta ko shi waye ? ,ba fa ya d`aya daga cikin yaran da ake alfahari da su ko jin dad`in da farin cikin zuwan su duniya,ba shi da albarka kuma bai kasance d`a na gari ko na kirki ba, ko kusa ko kad`an shi d`in tamkar d`an Allah ba ni ne shi d`in yaro ne da ke tafe da munmunar k`addarar da ke rusa ahali,gami da tarwatsa shi"....da sauri Madaki ya katsesa sakamakon jin d`atatan lafuzan da su ke fitowa da ga bakin sa"Duk irin fad`i tashin da yake akan ganin ya wanke laifin sa a gare ka,ta dalilin haka ne fa ya sadaukantar da rayuwarsa ya shiga cikin jerin Dakarun da suke ba k`asar ka kariya, ya zamanto Babu wani Jarumin Sadauki da ya kai sa kwazo,juriya da kaifin basira in har a fagen yak`i da dabarunsa ne,shine mutum d`aya,sadauki kuma Jarumi wanda ya ke iya fuskantar runduna komi yawa da had`arinta,kuma yai nasara,da ba dan shi ba da yanzu ba ka san a wanne mataki k`asar da ka ke fifitawa fiye da shi ta ke ba,shi d`in dai shi ne Jarumi kuma Sadauki d`aya da d`aya da ka ke da shi kuma ka ke tak`ama da shi ,duk ya aikata hakan ne domin sa rai da kwad`ayin wata rana zaka ja shi a jiki kuma ka yafe masa laifin da cutarwar da ya aikata maka".
"Ba na tunanin da akwai wani abu da zai aikata komi girmansa da zai iya kankare bak`in tabon ko kuma in ce bak`in fentin da ya gogama zuciya,ruhi da gangar jikina,ni a gare ni duk d`aya mamaci ya karye da zamansa anan da kuma can duk d`aya su ke".
" Na rok`e ka ka dubi girman Allah ka yafe ma Yarima Haisam laifin da ya aikata maka shi ma ba akan san ransa haka ta faru ba,ko ka manta ko a cikin rak`uma Allah ke fidda amale, ka sa baki a cikin lamarinnan kuma ka bi duk hanyar da zaka bi kasa a dawo da Dakarunnan cikin k`asarsu domin suma suna da hak`k`i a kan ka"."K`anina Idrisa ka yi hak`uri amma na gama maganata,ba zan ta`ba canja wa daga hakan ba,shine matsayata "," A'a kar ce haka kana da hanyoyi mabanbanta da za ka bi domin ceton su"......."Me Martaba Sarki Abdullah ya dakatar da shi ya na mai cewa,"Idan har wannan shine rok`on ka kad`ai a gare ni za ka iya tafiya"."Wannan shine hukunci kuma matsayar da ka yanke?",Ba tare da ya bashi damar amsa tambayar da ya yi masa ba ya d`ora da cewa,"To in har haka ne ni ma na shirya gami da d`aura d`amarar tare da d`anbar yak`i da yin fito na fito da kai har sai na samu hanyar da zan ku`buto da Yarima Haisam ,ko da hakan na nufin sauke wannan rawanin da ke d`aure a bisan kai na,a tak`aice ina nufin dole gyada ta fidda mai in tak`ita ta sha matsa",yana kaiwanan ya mik`e tsaye yana mai kakka`be babbar rigar da ke jikinsa ,ba tare da ya kuma sauraren wata kalma daga Me Martaba da ya ke cewa da shi ba yai tafiyarsu.