Page 3
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
***
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆
For WhatsApp Channel 👇👇👇👇👇👇
***
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 3
FREE PAGE
"Mai Gida Lafiya kuwa ?,na ga jikinka duk ya yi sanyi ,kamar wanda aka zare ma lakka ,ko dai ba ka da lafiya ne ?,domin na san rashin lafiya ne kad`ai za ta zama silar yin jinkiri ko lattin zuwan ka fada ","Hmmmmm ke dai bari ,yau zuwa fadar ne duk ba shi a cikin raina duk jikina ma a ma ce ya ke",da k`yar ta iya duk`awa ta ajiye k`waryar da ta ke hannunta sakamakon tsohon cikin da ke a jikinta haihuwa yau ko gobe," To ko dai marke ko garahunii zan jik`a ma ka ka sha ,zuwa wani d`an lokaci jikinka zai warware","Ke ni ba wani jik`o da zan sha domin ni ba shi ne matsalata ba hankalina da tunani duk su na can wajen haikacen abinda ka iya afkuwa a fada ne,shi ne mak`asudin shigata cikin wannan halin",sai da Altine ta dafe saitin k`irjinta,ta na mai cewa,"Na shiga uku na ni Altine,in ce dai ba wani sabon iftila'i ko masiba ce ta sake kunno mana a cikin k`asarnan ta mu ba?","Ko d`aya ba haka ba ne ba,kawai dai matsalolin da su ka saba ne kawai su ka sake d`aukar zafi a duk tsakiyar mako na wannan Masarauta".
"Waiyo Allahnah har hankalina ya d`an kwanta domin ni a firgice na ke rayuwa a cikin wannan garin ,domin ni da fari har na yi tunanin ko labarin dawowar Boka Dürsäås cikin Garinnan ka ji","ana babbakar Giwa waye zai jiyo k`aurin zomo Ke na ga alama tunanin kanki gajere ne,duk da dai nasan kowaye Boka Dürsäås fiye da yanda ki ka san shi da duk munanan d`abi'u da halayansa,sai dai ni a yanzu ba shine abinda ya da me ni ba,wannan mulkin kama karyar da Sarauniya Junayyah ta ke ne ya fi damuna da tsayamin a raina","To fa ikon Allah to ai wannan ya riga da ya zama ruwan dare,kusan kowa ya riga da ya saba da irin wannan rayuwar a cikin wannan Masarautar na zalinci,fin k`arfi da kuma rashin imani, sai dai mu yi fatan Allah ya kawo mana ranar ganin k`arshenta","Hmmmmm ke raba ni da wannan dogon zancen na ki ,bari in hanzarta Isa Masarautar kafin hukunci ya sauka a kaina,tunda dama ance kaza me `ya`ya ita ce ke tsoran shurwa,kema kuma ya kamata ki d`aure ki lek`a a wannan makon kar fa Sarauniya ta ga ne kin daina halarta zaman fada","Ayyya me gida ,nima ina son inje wannan cikin ne ke hanani gami da takura min duk ya yi min nauyi amma bari in gani ko zan iya zuwa sai in taho","Da dai ya fi domin ance zama lafiya ya fi zama d`an Sarki" haka ya kakka`be babbar tagguwar da ke jikinsa ya fita.
Zaune ta ke bisa katafariyar *KARAGAR MULKINTA* wacce ta sha mabanbantan ado da kwalliyar,a ta kowacce fuska,bayi guda buyi maza na tsaye daga gefanta su na yi mata fifita da kyawawan mafitai,idan kai duba ya zuwa gabanka gefan hannun dama da na hagu mutane ne fululu iyakar iya ganinka,duk ranar tsakiyar mako,rana ce da ake zaman fada a Masarautar BAIBAH, duk in har shekarunka sun kai matakin da za a kiraka da ak`ili to halartar zaman fada a wannan ranar ya zaman ma ka wajibi,duk wani mai rawani a cikinta ,hadimi ko hadima ,talakawan gari,ma su kud`in gari,mata da maza,Kai ko wacce ta ke saman gwuiwa ba a cireta a sahu ba. Kai kowa da kowa sai ya halarta akasin hakan kuma munmunan ko tsatstsauran horo ne zai biyo baya,domin a irin wannan ranar ne ta ke yanke duk wani hukuncin zalincin da ta so,sosai hakan ke k`ara d`arsar da tsoro,rud`u gami da firgici ga mutanen Garin, a gaban kowa za a hukunta Mama,Baba ,`ya`ya ,k`ani,`yarka ko wani mafi kusanci a gare ka ba tare da iya aikata Komi ba, sai da ta gyara zaman ta sannan ta fuskanci inda Hakimi ya ke zaune da nufin ya yi mata bayanin abinda ya ke tafe da shi.
Da sauri ya matso ya na mai fad`uwa a gaban ta ya ce da ita,"Allah ya ja da tsawon Ranki ya shugabata, ya kuma d`ora ki a kan mak`iyanki ki yi nasara a kan su,ke d`in inuwar bagaruwa ce ga sanyi ga k`aya,`yar kunama ba a wawarki,sabon labari kowa ya ganki ya tuna Allah,`yar masara ana goyanki kina fidda gemu,duniya mai Ido d`aya a tsakar ka ba kya ganin gabanki sai da bayan ki",ya d`an tsagaita bai cigaba da cewa komi sai da ya ya maida ganinsa akan mutanen da ya zo da su sana ya d`ora da cewa
"wad`annan sune talakawanki mak`ask`anta da su ke yunk`uri gami da k'ok'arin fatali da duk dokar da ki ka sanya a cikin wannan k`asa ta ki,ta hanyar k`in bin umarninki...",ya dakata a nan ta hanya umarnin d`aga hannu da tai ma sa,wani Murmushi k`eta Sarauniya Junayyah ta sa ki kafin daga bisani ta ce," Kafin in saurari laifi ko zunubin da su ka aikata ina Sarkin Bulala ya ke?",kamar wanda iska ta jefo haka ya fad`i gabanta hannaye da gwuiwowinsa na zube a k`asa jikinsa har rawa ya ke,ya ce da ita,"Gani gabanki ya ke Uwargijiyata,fad`i umarninki kai tsaye ,komi girma ko k`ank`antar sa,kai ko da kuwa rai na ki ke son ki ke da bak`ata,take yanke zan fisgo mi ki shi daga gangar jikina, balle kuma na wani"."Wa'innan k`ask`antu mutanen ni keson ka fara saukewa haddin bulala Hamsin-Hamsin kafin in saurari irin kalar zunubin da suka aikata,tunda na ga alama a cikin k`asarnan har yanzu da akwai sauran mutanen da buri ke sa su sauka daga kan tsandauri su koma kan yashi ko ta`bo "," An gama Ranki ya dad`e ",da sauri wani tsoho daga cikin su wanda zai kai kimanin shekara saba'in da biyu ya fad`i a gabanta ya na mai neman afuwa,sassauci da rangwame, amma ba wanda ya kula shi daga k`arshe ma ta kansa Sarkin Bulala ya fara,sanda zai gama tuni ya fita daga haiyacinsa domin har kusan suma ya yi.
Sai da Sarkin Bulala ya gama hukunta duka mutane Goman da Hakimi ya zo da su kana tace da shi ," Ina jinka Hakimi",nufinta ya ida sa mata zance.
"Wad`annan mutane guda hud`u su na da mabanbanta laifi ne,wannan da ki ke gani", ya nuna wannan tsohon da yai magana da fari da yatsa," Shine wanda ya shuka k`atuwar Gonarnan ta barkono wacce ke kan hanyar kubyim sai dai munyi-munyi da ya fitda kason masarauta amma ya k`i ,suna can ya `boye su a cikin Gidansa ,har hukunta sa munyi amma kafiya da taurin zuciya irin na wannan tsohon ya k`i yarda da ya fito da su ya bayar",da rarrafe had`i da jan ciki haka d`an tsohon ya k`araso gabanta har ya na dafa k`afafunta ya ce,"Na rantse da ke da kuma KARAGAR da ki ke zaune a kanta ba haka ba ne ba,kin san sha'anin noma sai hak`uri,kar ma barkono da ba ka ta`ba kwashe shi gabad`aya a lokaci guda, kuma bana ba a samu amfanin gona na kirki ba,hakan ya sa ban bada mudu ko adadin abinda na ke badawa duk shekara ba,kuma ban manta ranar da su ka zo da niyar in bada adadin barkonon da na ke badawa na basu hak`uri tare da cewa su bari in kwashe shi duka gabad`aya sai in fidda hak`in Masarauta, domin ina jin tsoran faruwar wani abu in aka ga bai kai yawan wanda na saba badawa ba sai su ke tunanin ko bayarwa ne bazan ba,alhalin na yi iyakar bakin k`ok`arina wajen ganin na fahimtar da su hakan amma sun gagara fahimta",duk ya na wannan zancen ne sa'ilin da jikinsa ke mak`yark`ata gami da zubar da hawayen azabar da ya sha.
"Ina Sarkin Dogarai ya ke ?", Sarauniya Junayyah ta tambaya cikin kakkausar murya,da hanzari sa ya zo ya zube a gabanta ya na mai amsa kiran na ta"Ka tafi tare da shi tare da wasu Dakarun ku kwaso duk sauran barkonon da ke cikin Gidansa sauran wanda ya ke a Gonarsa ku banka masa wuta,wata k`ila hakan zai sa sauran `yan Uwanka manoma su san duk abinda randa ta samo albarkacin mod`a ne", wani ihu wannan tsohon ya sa ki mai d`auke da zallan tausayi gami da kashe zuciyar duk wanda ya saurare sa ,har had`awa da mirgina-mirgina a k`asa ya ke da saran ko Sarauniya za ta ji tausayin sa amma ina daga k`arshe sai cewa tai," Ku d`auke min shi daga gabana domin na tsani ji da ganinsa,talakan banza talakan wofi da wata munmunar halitta ta sa",A firgici Hakimi ya matso ya na mai nuna mutum na biyu wanda su kan su tun kafin a zo kansu tuni hantar cikin su ta d`uri ruwa d`aya daga cikin su ma har fitsari ya fara saki saboda rud`u tare da firgici hukuncin da za a yanke masa,"Allah ya taimake ki Wannan shi kuma d`an kasuwa ne kamashon da ake fitarwa da sunan Masarauta duk k`arshen mako shi ya dai na bayarwa saboda wani k`aramin dalili na sa",da sauri Attajiri Sadi ya bud`e baki da nufin cewa wa ni abu ta dakatar da shi ta hanyar daka ma sa wata munmunar tsawa,dole ya had`iye maganar da ta ke k`unshe a bakinsa ya na mai duk`ar da kansa k`asa,"Ku je ku kwashe duk abinda ya mallaka,tun daga cikin shagon na sa,har zuwa cikin Gidansa,kama daga kan kayan abinci dukiya ko kadara ku samin su a cikin ma'ajin Masarauta, su kuma kud`in a kai mansu Baitul mali,sannan shi kuma ku gana masa azaba ta tsawon adadin kwanakin da ya d`auka bai bada kamashon ba","Ki gafarce ni ya shugabata amma wallahi na rantse in ki ka aikata haka gare ni mutuwa zan yi daga ni har Ahalina,mun Kai mu wajen talatin amma nauyin ci,sha,biyan harajin su,Kai duk kulawansu a Kai na ta ke,muddin Babu ni rayuwarsa salwanta za tai,kuma maganar gaskiya kud`ina ne su ka mak`ale da na tura yarana fatauci,har yanzu ba su dawo ba ,da zaran sun dawo na yi alk`awarin Zan biya in ma k`ari ake son inyi na jinkirin biyan da nai,na rantse da KARAGAR ki zan yi,ki tausaya min ,ki tausaya ma Ahalina,kuma ki jik`anmu ki yafe mana,na rantse ma ki ko da yunwa kad`ai a ka barmu sai ta zama silar ajalin mu".
"Oh ka Na nufin ba ni da tausayi ne da har na iya yanke ma ka wannan hukuncin ne ko mi?", a firgice Attajiri Sadi ya d`ago da kansa daga duk`en da ya ke ,ya Kasa cewa Komi sai zuba idanuwansa a kanta da ya yi kamar me san gano wani sirri da ya ke `boye a tattare da ita,wanda hakan babban laifi ne,domin ya na daga cikin manya-mayan dokokin Sarauniya Junayyah na ba a had`a Ido da ita,wani murmushi mai d`auke da tarin zalinci, mugunta da rashin imani ta sa ki,tare da cewa," Ku tafi da shi Zan buk`aci ganinsa a nan gaba",tun kafin ta rufe baki Sallama ya cukwuikuye Attajiri Sadi da wa su daga cikin Dogarai su Kai waje da shi,Hakimi kam yau ya ga takansa domin sai da ya sharce tarin zufar da ke tsatstsafo ma sa daga goshinsa sannan ya nuna mutum na gaba ,ba wai iya murya ko gangar jikinsa ba hatta zuciyarsa,da `yan hanjin cikinsa in aka ce ma sa su na rawa yarda zai tare da cewa,"Allah ya huci zuciyarki shi kuma wannan haraji ne ya dai na biya ",Kasa iya cewa Komi wanda a ka nuna ya yi dama can ya shiga rud`u da firgici tun d`azu shi ne ma ya saki fitsari tunda farko ,gabad`aya lamarin ya gama firgita shi ya fita acikin kwakwalwarsa da tunaninsa,jira kawai ya ke ya ga irin rashin imani da tausayin da za ta nuna a kan sa domin ya na da yak`inin hukuncin da zata yanke a kan sa ba mai dad`i ne ba.
Sai da ta k`are ma sa kallo tunda ga saman kansa har zuwa babban yatsan k`afarsa,yamutsa fuska ta fara yi harta kai ga ta fara tsirtar da miyau da ga bisani sai ga yunk`urin amai na biyu baya da hanzari ta mik`e tsaye ta na mai kauda ganinta a kansa ta ce,"Kai tur Allah yai wadaranka kai kuwu kana kallon kanka kuwa?,sai ka ce wani jemage,ji bi kan ka,wani k`ato da shi,cikin ka kuwa kamar an shimfid`a tabarma,k`afafuwanka kuwa iwa na jaririn kwad`o ,anya kuwa kai ba dabba a kaso ayi ba ,ka yi taurin kai aka barka a haka ?,ga yunwa ta yi ma ka katutu da kanta a cikin jikin ka,ta ya ka yarda hakan ta kasance,ko kai lusari ne da ba za ka iya fafutukar ka nemo ma kan ka arzik`i a duk inda ya ke a fad`in duniyarnan ba ?, hankalina ya tashi wai ance da rago sha fura mu tafi gona da na gan ka, ka ga magana da kai ma hatsari ce a gare ni,domin ina tsoran kar ka shafa min annobar da ta ke tattare da kai ,ku yi hanzarin kauda min shi daga gabana Kai ba ma a gabana kad`ai ba har k`asata ba na buk`atar ganin sa,Kai ba ma shi kad`ai ba har da iyalinsa ku had`asu sannan ku bincika a kaf k`asar BAIBAH idan har da me irin siffa ko halitta irin ta sa ku kore shi daga cikin k`asata ba sai kun kawo shi gabana ba,ba zan iya sauraren sauran masu laifin ba domin wannan tsohon banza gabad'aya ya gama`bata min ranata ,sai zuwa zaman fada na gaba,ke kuma Jakadiya",ta mai da kallonta saitin da Jakadiyar ta ke tsaye,jikinta har `bari ya ke ta iso gabanta,"Ki yi hanzari ki sa a kawo min burkutu da farfesun naman zabo",tana kawowa nan tai gaba abin ta,sauran bayi da hadimanta su ka mara ma ta baya , batare da ta sa ke bi ta kan mutanen da su ke wurin ba,k'af fadawanta ba wanda yai zarrar mik`ewa da nufin barin wurin,ballantana kuma mutanen gari talakawa, har sai da tai wasu dak`ik`ai da barin fadar sannan su ka fara tashi jiki duk yai sanyi tamkar wad`anda aka zarema lakka,Hakimi shi ne mutum na k`arshe fita daga fadar kusan duk laifin abinda ya faru akansa ya ke d`ora laifi ko zunubin abun ji ya ke dama bai kawo su ba,amma kuma wani lokacin sai ya rik`a tunanin in da ace bai kawo su ba da bai san wacce irin masifa hakan za ta haifar ma sa ba,mai yiwuwa ta sadaukar da naman sa da jinin sa ga Dodonta .