KARAGAR MULKI

Page 4

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*
            (Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
    
***
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆
STORY & WRITTEN BY :
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
   And now...*KARAGAR MULKI*

BOOK 1 
 
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 4
       FREE PAGE
"Ki gafar ce ni ya shugabata, amma wannan shi ne iyakar abinda na ji game da wannan lamarin, bayan shi ban san Komi ba",Sai da Sarauniya Mufida ta saki wata naunauyar ajiyar zuciya gami da gyara zamanta kan tattausar kilisar da take a kanta kana tace," Ina son a yau ba sai gobe ba, ki bi duk hanyar da za ki bi ,ki nema min iso wajen Me Martaba,domin ina da buk'atar in gana da shi,ban ta`ba ganin inda barewa ta yi gudu  d`anta ya rarrafa ba,ta ya akai Me Martaba Sarki Abdullah zai yanke wannan d`anyan hukuncin ?",da sauri Jakadiya Azima ta sake duk`ar da kanta jikinta na mai cigaba da rawa,a tun sanda ta ji umarnin Sarauniya Mufida.
"Ki gafarce ni amma ina jin tsoran aikata hakan, domin `yar'uwar zaman ki ko ince abokiyar takun sak`ar ki Sarauniya Mubina ta tunkari Me Martaba Sarki Abdullah da irin wannan manufar,kar ki so ki ga yanda ta kaya a tsakanin su kuma  ba ta sami nasara game da abinda ta je da shi ba,ban kuma san me zai sake faruwa ba idan wa ni ya sake zuwar ma sa da makamancin irin wannan buƙatar,ina tsoran abinda ya faru a baya,tunda duk mun san shi d`in Zaki ne rurinsa mai rura dabbobin dawa ne,",shigowar zarah a kid`ime ya zama sanadin dakatawarsu daga zancen da su ke,har sai da ta kai Sarauniya Mufida ta ta shi ta zauna bisa kan kilisar da ta ke zaune ta na mai cewa," Zarah lafiya me ya ke damunki za ki fad`o mana tamkar wacce abun tsoro Kura ko Zaki su ka biyo bayanta?",sharce hawayen da su ke kwaranya a saman fuskarta ta yi kana ta zube a gabanta tare da cewa,"Ki yafe ni ya shugabata a rikice na ke ne shi yasa ,hakan ne ya sa ba na iya tantance dai-dai da ba dai-dai ba,amma ki gafarce ni "," Ba komi amma mene ne ya firgita ki,gami da jefa ki cikin wannan halin ?","Yanzu Galadima ya dawo Gida, sai dai labarin da ya zo mana da shi bai mana dad`i ba,wai ya ce Me Martaba ya cire hannunsa game da lamarin su Yarima Haisam daga k`arshema cewa yai mutanen k`asar BAIBAH su yanke ma su duk hukuncin da su ka ga dama,ba abinda ya damesa,ba sa hannunsu game da lamarin su","Na samu wannan labarin, don haka ki kwantar da hankalin ki yanzu haka ma maganar da ki ka iske mu  muna yi kenan, za muyi duk me yiwuwa wajen ganin an sauya wannan hukuncin,duk da dai nasan tunkarar Me Martaba Sarki Abdullah tamkar tunkarar tsangayar Kura ne,wacce ba a ba k'are dillancinta","Ranki ya dad`e ki na ganin hakan zai yiwu kuwa,kin fa san halin Me Martaba zai yi wuya ya canja daga hukuncin da ya yanke,kin fa sani tun farko shi ba mutum ne mai magana biyu ba,to ta ya hakan zai kasance ?,halin mutum ai sabulun wankansa",sai da Sarauniya Mufida ta sauke wata k`yak`yawar ajiyar zuciya sannan tace,"Mai sulken yak`i bai jin tsoran ko kuma d`aukar wargi,duk da ni kai na ina girmama hakan sai dai in nai duba da girman lamarin sai in ga tunkarar Me Martaba ba komi ba ce,Babu yanda za ai mu bar Yarima Sadauki a cikin wannan munmunan yanayin ,amma za mu yi iyakar bakin k`ok`arinmu ba tare da mun nuna gajiwaya ko jin tsoran mu ba ,ke ko da ta k`ark`ashin k`asa ne zamu bi har sai mun ga mun ceto su sannan zamu sarara,in da alk`awari ruwa ba zai dafa kifi ba,domin Yarima Haisam ba k`ashin yadawa ba ne a Masarautarnan".
"Allah ya k`ara mi ki nisan kwana, na ji dad`in wannan furucin na ki,haka kuma ina mai alk`awarta mi ki da zan bada tawa gudunmuwar a cikin duk abinda ya taso ta ko wanne irin hali,Zan so in Zama dutsan d`anawa wajen ganin an cimma nasara a wannan al'amarin "." Ba damuwa in har da buk`atar hakan Zarah zan nemeki,amma ina son in sanar da ke da ki kwantar da hankalin ba abinda zai faru da Yarima Haisam da izinin Allah "," Na gode da dad`ad`en kalaman ki gare ni ,sai dai in ba za ki damu ba zan so in tambaye ki wani abu guda d`aya da ya shige min a duhu tun tsawon tasowata","Ke ko wacce tambaya ce da ki ke da ta tsaya mi ki a cikin k`ok`on ran ki da har ki ke son ni in amsa mi ki ita ?","Game da lamarin Me Martaba ne da Yarima Haisam, Wai wacce irin gaba ko matsala ce a tsakanin su ,tunda na ta so nasan ba a ga maciji a tsakanin su,ba su shiri ko kad`an hasalima ba sa zaman inuwa d`aya a tare,mene ne dalilin haka ,mene ne musabbabin wannan rashin fahimtar ?,ina son in sa ni ,zuciyata ta kasa iya cinyewa ko had`iye wannan batun".
"Tabbas kin zo da lamari me girma,ba na tunanin tunda abun ya faru da akwai wani ko wata da ya ta`ba ta da wannan labarin,idan har ki na son ganin k`ololuwar `bacin rai da tashin hankalin Me Martaba to ki yi k`ok`arin tada wannan maganar,ko da wasa ba wani mai zarrar da zai ce da ke zai iya tunkarar Me Martaba a wannan lokacin"," Ikon Allah, ki ce lamarin babba ne fiye da yanda na ke zato da tunani,amma duk da haka  na k`wad`aitu da son sanin asalin abinda ya faru a lokacin bayan"cewar Zarah.
"Allah Sarki har kin sa hawaye sun fara k`ok`arin kwaronyowa daga cikin idaniyata,kinsan wani abu Zarah?",ta tambayeta,"A'a Ranki ya dad`e, sai kin sanar da ni"," da akwai tarin darussa a cikin wannan labarin,Allah na yin duk abinda ya so a kuma sanda ya gadama kuma ko a cikin Rak`uma Allah ke fidda Amale, Giwar Masarauta Maimunatu ita ce mace ta farko a wurin Me Martaba Sarki Abdullah,wacce ya nuna ya na so sai dai abin ya zo ma su da tangard`a gami da gargada sakamakon kasancewarta na baiwa,an sha daga kafin a shawo kansa ya yarda zai yi Aure domin shi a nashi son samun ya `yantar da ita sannan ya Aure ta,ya na yi ma ta son so ne me yankan shakku,Mahaifinsa da Mahaifiyar sa ba sa son alak`ar su ,sai da aka kwada`ai ta ma sa da in ya amince da burin mahaifinsa za a bashi ita a matsayin baiwa daganan sai yai sad`aka da ita,sana ya amince ya yarda,wani abun ikon Allah a ranar da aka d`aura ma sa Aure da ni da Sarauniya Murjanatu a ranar ya mai da Maimunatu sad`akar sa ya kuma tare da ita ba tare da ya kula d`aya daga cikinmu ba duk da kasancewar mu `ya`yan sarakuna ,a lokacin da haka ta faru Sarki Abbas Mahaifinsa ransa ya `baci sosai matuk`a da fari ya so yai masa magana amma daga bisani ya fasa sakamakon shi mutum ne mai kawaici ,cikin k`udira da buwaya ta Allah sai ga ciki ya `bullo a jikin Maimunatu daganan ta tsallake ko barranta daga sauran bayi,da akwai abu uku da ba za su ta`ba faruwa da ita ba na d`aya ba a bada aronta,na biyu ba a sayar da ita,na uku ba a cin gadonta tunda ta Zama Ummu waladun har Allah ya sa ta haifi Yarima Sadauki kuma shi ne babban d`a a wurin Sarki Abdullah,daganan ta Zama Giwar Masarautar tunda ita ce ta fara haifuwar jikan Sarki sai da Yarima Haisam ya shekara kusan Goma sannan Allah ya sa Giwar Masarautar Maimunatu ta sa ke haifo d`iyarta mace mai suna Lailat,duk da mu ma Allah ya albarkace mu da namu `ya`yan ,a wannan tsakin ne Allah ya jarabci shi Yarima Haisam d`in da wata lalura,wacce sai da k`yar mu ka iya gane asalin abinda ya ke damunsa,maganganun sun rabu kashi-kashi a wannan lokacin wasu suna cewa jifa ne wasu kuma suna cewa ko wani kuskure ne da aka ta`ba aikatawa a cikin masarautar ne ya koma akan sa,wato k`aik`ayi koma kan mashek`iya har kusan hatsaniya ce ta kusa tashi a lokacin".
Zarah ce ta sa ke zak`uwa da son jin zancen har ta kai ga cewa," wannan wacce irin lalura ce kuwa haka da har take k`ok`arin rarraba kan ahalin gida da masarautar ma gabad`aya?".
"Cutar iskokai ko in ce ma ki cutar Aljanu kai tsaye,ita ce takama shi, su ka  addabe shi gami da hana sa sukuni da zaman lafiya"." Yah Allah cutar iskoki kuma wacce na sa ni dai ?",cewar Zarah,"A'a ba irin wacce ki ka sa ni ba ce ba,wacce tafi k`arfin hankali da tunanin ki ce,ke ba na tunanin ki ba,bana tunani a kaf rayuwar ki kin ta`ba cin karo da mai irin lalura irin ta sa ,a iya  tsawon shekaruna a duniya ba ma a Gidan Sarauta ba ban ta`ba ganin ko cin karo da irin munmunan tashin hankali ko in ce munmunar k`addara irin ta Yarima Haisam ba,na zubar da hawaye fiye da yanda zan iya ba ki labari,ke ba ma ni kad`ai ba duk wani wanda ya kwana ya tashi a cikin masarautar nan sai da hankalin sa ya tashi kuma ya zubar da hawaye".
"A da da farko iya shi kad`ai abun ya sha fa,idan sun tashi zai sha wahalarsa da azabarsa har daga bisani ya wartsake da kan sa,A wannan lokacin Malaman addini,Bokaye,`Yan tsibbu,Masu rauhanai,`yan duba ke har ma da `yan bori kasuwanninsu su ka bud`e a cikin wannan Masarautar,duk hakan ta faru ne domin k`ok`arin wajen ganin Yarima Haisam ya sa mu lafiya,amma hakan ya ci tura ya kuma gagara,domin ba wanda ya ci nasara a kan haka,daga k`arshe sai abun ya bunk`asa ya gawurta fiye da yanda zan yi ma ki bayani,kusan ma sai su ka k`ara rikitawa gami da lalata ma sa tunani,kusan sai in ce ma ki kamar sun k`ara ma sa wasu Aljanun ne".
Sai da Zarah ta gyara zamanta sannan ta ce," Innalillahi wa'ina ilaihirraju'una, kenan zuwan su bai yi wani amfani ba,tunda ba su iya yi ma sa magani ba ?","Haka ne gaskiya domin ba wanda yai nasara  a,cikin su daga k`arshe sai Aljanun su ka fara shafar duk wanda su ka fi kusa da shi,duk wanda tsautsayi ya sa ya na ku sa da Yarima Haisam Aljanun sa su ka tashi to zai wahala ka iya tsira daga kaidin su,domin Aljanun na sa sukan zo da yanayi kala-kala, Mahaifiyar sa Giwar Masarautar ita su ka fara addaba,suna wahalal da ita har kusan haukata ta su ka yi ,ke har yawo tsirara su ka rink`a sa ta,a duk sanda hakan zata faru za ki ganshi ya na biye da ita ya na k`yalk`yala wata mahaukaciyar dariya mai cike da zallar k`eta da mugunta,hakan ba k`aramin rikici da sa`bani ya kawo ba a tsakanin Yarima Haisam da Me Martaba ba, gani ya ke kamar iskanci ne ko kuma Yarima Haisam ya na sa ne a kan duk abinda ya ke faruwa,daga k`arshe sai aka raba ma su muhalli ko wa da sashen ko `bangaren da ya ke rayuwa,a tunanin Me Martaba ko hakan zai zama hanyar maslaha".
"Ranar da ta fi ko wacce rana tsanani da muni ga duk wani d`an Masarautarnan ita ce,ranar da tsakar dare Iskokin na sa su ka motsa ba wanda zai iya cewa ga hanyar da Yarima Haisam ya bi ya shiga cikin Sashen Giwar Masarautar, saboda ance k`addara ba ta jin magani,sai ganin wuta na tashi daga cikin na ta d`akin akai,sai kuma kawa da ihunta da su ka karad`e kunnuwan mutanen gidan,k`arin wani tashin hankali,da Yarima Haisam ya zo ya tsaya bakin k`ofar shiga d`akin duk wanda ya zo da niyar shiga cikin d`akin ko k`ok`arin taimakon ta bugu d`aya zai ma sa sai dai gyatumarsa ta haifi wani,da k`yar da ji`bin goshi a ka samu damar janye sa daga wurin,shi ma sai da a ka d`ad`d`auresa da sark`ok`i sannan aka ci wannan nasara,kuma har aka ci aka k`are yana wannan dariyar ta sa mai k`ona zuciya mai sauraren sa,cike da zalinci da k`eta,  sai dai me sanda za su shiga ciki tuni rai yai halin sa ,Giwar Masarauta a ranar ta bak`unci lahira,ke ba ita ba harta k`ananun yara abokansa cutar da su ya ke,kaf k`asarnan sai da ta girgiza, anyi zama ya fi sau a k`irga a fada da fadawa domin san Samo hanyar da za a shawo kan wannan matsalar,amma ina hakan ya ci tura kuma ya gagara,,tunda haka ta faru aka mai da sa Sashen sa aka rufe,shi k`adai,ba tare da wani ya sake zuwa inda ya ke ba,sai da ya kwashe lokaci mai tsawo sannan a ka fara bud`e sa, a ranar da ya fito k`aramar k`anwarsa ta hango shi ta yo kan sa da murnarta ta rungume sa,saboda kewa da ta addabeta ga rashin uwa mahaifiya ga shi shi ma ya yi nesa da ita,sai da za ki sha mamaki In ki ka ji abinda ya faru "," Ya shugabata me ya faru",ta tambaya cikin d`okantuwa da zak`uwa da lamarin. "A ranar sai gawarta aka `ban`bare a jikin sa domin wata irin shak`a yai mata wacce ta zama sanadiyar fitar ran ta daga gangar jikinta gabad`aya,sannan ya mai da hannayen sa saman wuyan sa,da nufin sai ya ra ba kan sa da rayuwar sa shima,ansha fad`i tashi a wannan lokacin, k`arshe k`aramar k`oramar da ke bayan Masarautarnan ya fad`a,sai da yai kwana uku  ya na rayuwa a cikin ta,da zaran an fiddo sa  zai koma sai dai a d`auresa idan kuma ya kwance ya koma,sai bayan kwana ukun sannan Waziri ya nemo wani hatsabibin masunci,ya fito da shi ,inda ya na fitowa Me Martaba ya bada umarnin a fitar masa da shi daga cikin Masarautar sa ba ya buk`atar sa ke ganinsa a cikin ta,wannan hukuncin ba k`aramin k`ara hargitsa Masarautar yai ba,amma funfurinfus Me Martaba ya sha fa ma idansa toka yak`i sauraren kowa,wasu na ganin hakan kamar shi ne abinda ya kamata Me Martaba ya aikata tun da farko,wasu kuma  suna ganin hannunka bai ta`ba ru`bewa ace za ka yanke ka yar,Madaki shi ne wanda ya ja shi a jikin sa ya Kai sa gidan sa ya cigaba da zama da shi,bai ta`ba hutawa ba a kullum cikin nemo masa magani yake amma kullum abun k`ara girmama ya ke ,wannan shi ne asalin k`iyayya da gabar da ta ke a tsakanin Me Martaba da Yarima Haisam ,a ta sanadin sa ne Matar da ya fi so ta rasa ranta,da kuma k`aramar d`iyarta".
  Tun kafin ta kai ƙarshen labarin Zara ta je sharɓar hawaye,"Ranki ya dad`e wannan labarin ya girgiza ni ta ya d`a zai iya kashe Mahaifiyar da tai sanadin kawo sa duniya,anya ba akwai lauje cikin nad`i ba ?", cewar Zarah
" Maganar ki  dutse ,sai dai ina son in sanar da ke a kaf duniya ba wata halitta da Yarima Haisam ya ke so Sama da Giwar Masarautar Mahaifiyar da ta kawo sa duniya,sai Mahaifinsa Me Martaba Sarki Abdullah, a `bangaren  shak`uwa kuwa ba a magana tsakanin sa da `yar'uwarsa Gimbiya Lailah,amma kuma a kaf duniya Babu wad`anda su ka fi shan wahalar da cutarwasa kamarsu tunda har sanadin rayuwar su ya zama","Tab wannan lamarin akwai rikita tunani da kwakwalwa,ga kuma tarin ko d`unbin tausayi da alhini a cikin sa","Ba ki san Alhini da tausayi ba sai kin ga lokacin da Yarima Haisam ya dawo cikin hayyinsa da tunaninsa,ya kula da irin `barna da kuskuren da ya aikata, yai kuka ,yai kawa,ya jima kan sa tarin raunika,ke har yunk`urin kashe kan sa yai,dole ki zubar da hawaye ki ji tausayi imanin ki ya k`ara k`aruwa,ki girmama buwaya da d`aukakar buwayi gagara misali,ke har jinya sai da ya kwanta na tsawon wani lokaci".
"Ya shugabata jin labarin  ko waye Yarima Sadauki ya sa na k`ara k`aimi wajen son yin rayuwa da shi da kuma ganin na taimaka ma sa ta kowanne `bangare da izinin mai sama".
"Zan ji dad`i in har ki ka kasance kamar yanda ki ka ce", Wannan alk`awari ne a gare ni zan cika sa komi wuya da tsanani, da haka na ke son in yi ma ki sallama in kin ba ni dama ya shugabata kuma uwar d`akina?"," Za ki iya tafiya sauran bayani za ki ji daga bakin Jakadiya Azima "....