KARAGAR MULKI

Page 5

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*
     (Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
    
***
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆

For WhatsApp Channel 👇👇👇👇👇👇

***
STORY & WRITTEN BY 
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
   And now...*KARAGAR MULKI*

BOOK 1 

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 5
      
"Ni Altine yau na shug uku kuma na ga takaina,wannan wacce irin musiba da bala'i ne su ka tunkaro mu,da har ta kai Mai Gida ka shigo cikin Gidannan Rawani,Hula,Takalmi kai har ma da babbar rigarka a hannu?", ko ta kan ta bai bi ba ya wuce tamkar iska za ta ɗauke shi,shirun da ya biyo bayan wannan magana da Altine ta jiMe Gidanta ya yi ya sa hankalinta k`ara tashi,ba ta sake shiga mak`ura kuma k`ololuwar tashin hankali ba har sai da ta ga ya zauna da`bas a k`asa kuma a gabanta idaniyarsa na zubar da kwalla,duk nauyi da kuma girman cikin da ke jikinta bai hana ta tashi zumbur da ga inda  ta ke zaune ba a cikin d`akin ta nufi zuwa inda ya ke,cikin tashin hankali rud`u gami da firgici, duk hanyar da za ta bi domin ganin ta lallashe shi ko ta sa mu makamar ko masaniyar da ta jefa shi cikin wannan munmunan lamarin amma ina ,k`arshema kusan mutum mutumi ya zama a gareta," Kai wannan lamarin abun rikitarwa ne kum abun dubawa ,ta ya babban mutum kamar Hakimi zai shiga cikin irin wannan halin harma kuma ace ya na zubar da kwalla a saman idonsa ,Kai! Gaskiya da sa ke,wai an ba mai kaza kai da k`afafu don haka ba zan kyale ba,kuma ban ga ta Zama ba wai an saci d`an `barawo",da gama fad`in haka ta bazama zuwa cikin asalin Gidan su Hakimi domin ta sanar da Mahaifinsa abinda ya ke faruwa,sai dai kash ta tayi rashin sa'a da nasara domin Mahaifin Hakimin ba ya nan Mahaifiyarsa kuma ba ta cikin halin da za ta iya ji ko sauraren wannan zancen,kasancewar ta na fama da jinyar rashin lafiya na tsawon wani dogon lokaci, da sauri Altine ta sa ke fitowa gami da bazama wajen ganin ta sami wanda zai kawo ma ta d`auki a cikin wannan sark`ak`k`en al'amarin da ta riski kanta a ciki,kasancewar yau itace Ranar da kasuwar Garin ta ke ci ne ya sa ko da ta fito ba ta samu damar ganin kowa ba,haka ta cigaba da zagaye layi da anguwar ta su.
Cin karo ta yi da wani mutumi wanda ya ke tafiya cikin natsuwa haiba da dattako,a kallo d`aya da za kai masa za ka shaida hakan ,domin hakan a bayya ne ya ke a gare sa duk da yawanci mutanen Garin su na ma sa kallon k`ask`anci da wulak`antarwa ne,wasu har kallon mahaukaci su ke ma sa ma,domin yawan kiransu da ya ke bisa tafarkin gaskiya ,tafarkin tsira duniya da lahira, tafarkin *ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM* tafarkin ALLAH UBANGIJIN SAMA DA K`ASA mai rumfa ba tokara mai saukar da ruwan sama mai ikon sawa da hanawa,a kullum burin sa shi ne subar biye ma bokaye da `yan tsibbu,kuma su bar yin shirka da ALLAH.
Za ka sha mamakin in ka ji cewar mutanen k`asar BAIBAH musulmai ne sai dai duk wani hukunci ko dokokin addinin musuluncin ba sa binsa ,Kai ko da lokacin sallah ne yai baifi ka ga mutum goma sha biyar ko k`asa da haka ba a a cikin Masallaci da nufin bin jam'in sallah ba,su ma ba tare da bin dokoki ko sharud`d`anta ba,haka su ke rayuwarsa a bai-bai duk da cewa a baya ba haka su ke ba.
"Bawan Allah na rok`e ka da ka tsaya ka saurare ni",Kasa tsayawa ya yi gani ya ke kamar za ta tozarta shi gami da wulak`anta shi kamar yanda su ka saba," Na had`a ka da wanda ka ke fad`akarwa gami da wa'azantarwa domin sa da ka tsaya ka saurari abinda na nufo ka da shi,ba wai na zo ne domin in tozarta ko in wulak`antaka ba,hasalima taimakon ka na ke nema",Waigowa yai ya na mai tsayawa a inda ya ke ba tare da ya ko d`ago ya kalleta ba",ina jin ki ,fad`i abinda ke tafe da ke,Ubangijina ya sa ina da hanya ko damar da zan iya taimaka ma ki",ya ce da ita cikin natsuwa.
"Na dad`e da sanin ko kai waye,tun ina `yar k`ank`anuwata kai d`in malamin addini ne wad`anda aka fi yi maku lak`abi da mutane ma su hikama da basira kuma ALLAH yai ma ku baiwa gami da nasibin magance dukkan wa su matsaloli da su ka tunkaro al'umma,na rok`eka da ka biyoni ka ga halin da mijina ya ke a ciki wala'allah ba za ka rasa wani taimakon da za ka ba shi ba",sai da yai shiru na wani lokaci kafin ya ba ta amsa da cewa," Ki yi hak`uri amma ba zan iya bin ki zuwa gidan ki ba,domin addinina bai yarje min akan aikata hakan ba"......da sauri ta dakatar da shi,ta na mai cewa,"A'a na rok`e ka da kar ka ce haka,domin ni ba na nufin ka da shari ko wani abu makamancin haka,kai akan haka ma zan iya rantse ma ka da Ubangijin da ka ke bautawa kuma ka ke fad`i ta shi akan a bauta ma sa shi kad`ai dare da rans",Shikenan na amince zan bi ki,bisa dogara gami da sakankancewa da Ubangiji na zai kare ni daga sharri da kuma kaidin ki da ki ke bi na da shi in akwaisa,don haka muje"," Na gode kuma na ji dad`in wannan karamci da halacci da ka nuna min ,yanzu bari in yi gaba sai ka biyo ni in kai ka i zuwa gidan nawa","A'a sai dai ni in yi gaba ,ki bi ni a baya domin Addininmu bai yarje min akan haka ba","to ta ya haka za ta kasance alhalin kai ba ka san Gidan nawa ba","Ba damuwa za ki iya yi min kwatance a halin yanzu ko kuma in muna tafiyar",sai da Altine ta girgiza kan ta sannan tace,"Lalle Kai ka kasance mai taka tsan-tsan gami da bin dokokin Ubangijinmu,wata k`ila hakan ne ma ya sa ka zama na daban a cikinmu,sa`banin mu da a kullum mu ke cikin zullumi gami da tarin matsaloli da damuwa a kowacce safiya da marece",daganan tai ma sa kwatance hanyar da za su bi ta kai su zuwa Gidan na ta.
A yanayin halin da Altine ta bar Hakimi a ciki a haka su ka riske shi ba tare da ya ko motsa ba, a kallo d`aya da Malam Musa yai ma sa ya fahimci asalin abinda ya ke damunsa, ba komi ba ne face tarin firgici,tsoro gami da damuwa.
Sai da ya d`an matsa gaba garesa kad`an sannan ya ce da shi,"Ya kai wannan bawan Allah mene ne yai tsamari ko yai zafi da har ya jefa ka cikin irin wannan munmunan yanayin, ko ka manta ka na da Ahali ko ince iyalin da za su shiga damuwa a saboda kai ne?","Zan fi so ace na gan su ,su na kururuwa gami da ihun mutuwata ne fiye da in cigaba da rayuwa a cikin irin wannan halin "....da sauri M.Musa ya dakatar da shi ta hanyar cewa," Subahanallahi wannan furucin bai kamace ka ba,duba da girma,hankali da kuma yawan shekarun ka","Malam ka ke ko?,ko ma ya ne sunanka na san ka sanni da irin aikin ko muk`amin da na ke a rik`e da shi cikin wannan Masarautar,kuma ka ga abinda ya wakana a fada a safiyar yau d`innan,ka ga irin mulkin kama karya,fin k`arfi,kwace gami da zalincin da aka gudanar a cikin wannan fadar  duk hakan ya faru ne da  taimako na ,ta d`aura min nauyin kamo ma su irin wannan laifin a kaina alhalin bazan iya d`aukar wannan nauyin ba ,ya yi ma zuciya da gangar jikina girma da nauyi,ba zan iya cigaba da kawo mutane ta na cigaba da zaluntar su ba,a haka fa na rage yawan mutanen da su ka can-canci in gabatar a gabanta, domin adadindin su ya kusa kaiwa Hamsin,ta ya zuciyata za ta iya d`aukar ganin ta na hukunta wa'inan tarin mutanen,akan haka dai na gwammaci in fad`i in mutu kai ko mushe ne na gwammaci da  inyi da in cigaba da taimaka mata ta na ha'intar mutane ".
Sujudi Shukuri M.Musa ya kabbara ya d`ago ya na mai kwarara yabo da Godiya ga Mai duka ,sai da ya d`auki wani tsawon lokaci a cikin wannan halin kana ya dakata ya na mai cewa,"Yau burina ya cika na samu wani mutum guda d`aya a Garinnan kuma a Masarautar BAIBAH da ya ke kyama halin MULKI da zaluncin Sarauniya Junayyah, tabbas alamace da ke tunkarowa gami da nuni da cewa k`aryarta ta zo kusa da zuwa k`arshe,tabbas kai mutumin kirki ne kuma na musanman, had`uwata da kai alkairi ne kuma ALLAH ne ya tsara hakan ,zan so ka amince da ni mu had`a hannu da hannu wajen sauke nauyin da ya rataya a kan mu"," Nauyi kuma,wanne irin nauyi haka ?,Ni gaba d`aya ban gane me ka ke son cewa ba ?","Ina nufin da ni da kai mu had`a hannu wajen ceto mutanen k`asar BAIBAH daga cikin mugun ramin da su ka afka wanda ya ke d`auke da zurfi,fad`i,duhu tare da mugayen majizai da kunamu a cikin sa","Kamar in na fahimceka ka na nufin in d`aura d`amarar yak`i ko yin fito na fito da Sarauniya Junayyah ko?","Tabbas ka fahimce ni dai-dai abinda na ke nufi kenan ta hanyar hakan ne kawai zamu",........"Ka ga M.Musa ya Isa haka dan Allah, ni ba nufi na kenan ba,kuma ba haka ba ne abinda ya ke a cikin zuciyata ba ,ban shirya cilla rayuwata da ta iyalinna a cikin halaka ba,tuni na yanke shawarar zan d`auki Matata mu bar wannan k`asar da zama baki d`aya, mu tafi can wani wurin da ba a sanmu ba mu cigaba da Rayuwarmu abinmu shikenan  abinda na tsara".
"Wannan babban kuskure ne da za kai danasanin aikata sa a rayuwarka,meye ribarka idan har ka tafi ka bar k`asar ka da `yan'uwanka a cikin munmunan yanayi alhalin ka na da damar da za ka iya ceton su ?", da sauri Altine da ke sauraronsu tun d`azu ba tare da ta ce komi ba ta tsoma bakin ta a cikin lamarin,muryarta har ta na rawa ,kai har tsallaken kalma ta ke tamkar wani zai rigata ta hanyar cewa, " A'a Mai Gida kar ka amince da shi,domin ni ban yarda da shi ba ina tsoran kar ya  je ya jefa rayuwar mu cikin munmunan had`arin da ba mu ta`ba zato ko tsammani ba ","Ko d`aya ko da wasa,ba haka na ke nufi ba kuma ba manufata a gare ku kenan ba,hasalima ni gaba d`aya rayuwar mutanen k`asar BAIBAH na ke son saitawa gami da gyarwa gaba ki d`ayansu"," Ta`b sannu da k`ok`ari  ,Na gaishe ka ,ba dan duba da dattako da kamalar da na ke gani kwance a saman fuskarka ba da tuni na dad`e da kiran ka da mahaukaci, Anya kuwa kasan fad`i da girman k`asar BAIBAH kuwa ?,da har ka ke ikirarin saita ta da hannun ka  wai ina k`udan ya ke balle romansa ,","Na san k`asar BAIBAH ciki da waje ,tamkar yunwar cikina,kai hasalima sanin da nai mata shine ya sa na zo ma ka da wannan batun "......ya dakatar da shi da sauri ya na cewa.
" Malam ka yi hak`uri in dai wannan itace buk`atar ka to ba za ka samu ba,domin kaf a cikin Ahalina da na Matata mu biyu kad`ai mu Kai saura ,ba na da kowa ita ma kuma haka ba ta da kowa,cikin jikinta kawai mu ke da shi dan haka ba zan iya saka rayuwarta da ta abinda ke cikinta a had`ari ba","Na rantse ma ku da Allah wanda na ke bautawa ba na nufin ku da wani sharri, asalin gaskiyata kawai na ke fad`amaku,kuma ai me cinikin duhu shi ya saba da lalube","wacce gaskiya ce da kai a cikin wannan shaci fad`in zancen na ka ?".
"Zan fad`a ma ka abinda ya ke binne a cikin zuciyata, amma sai dai in har ka yarda ka amince za ka da duk zancen da na zo ma ka da shi madamar hakan ya can-canci ka amince d`in"," Na yarda ina sauraranka fad`i in ji",M.Musa bai iya ya ce da shi komi ba har sai da ya matso kusa da shi sosai da sosai yanda ba wanda zai iya jin wani abu da zai fad`a,ko da Hakimi ya ji batun da M.Musa ya zo ma sa sai da ya tafi taga-taga zai fad`i sakamakon jin wani rikitaccen al'amari da ya yi",Kasa cewa Komi ya yi har sai da ya d`auki wani dogon lokaci mai tsawo kafin ya dawo cikin hayyacinsa,har sai daga k`arshe ya iya cira bakinsa ya ce da shi,"Ta ya ka iya cigaba da rayuwa bayan ka san wannan sirrin mai cike da rikitarwa, rud`u da ban al'ajabi,ko dai hakan ne ya sa duk wata doka da hukunci na wannan Masarautar ba sa hawa kan ka ,ta bar ka ka yi duk abinda ka ke so ?","Wannan dogon labari ne shima mai zaman kansa,zan sanar da Kai shi in sha Allah anan gaba ","Zuciyata rawa ta ke Ina jin tsoron amincewa ka kai,tunda bayan ni da kai ba na tunanin da akwai wani da zai iya yarda da wannan lamarin a kaf mutanen k`asar BAIBAH, ni kaina ina d`ard`ar da zancen a cikin Zuciyata,ban San kuma me ka ta ka da har ka ke tunanin za ka yi nasara a wannan tafiyar ba"," Bawai ina nufin mu tak`ali Sarauniya Junayyah da yak`i ba ne ba,A'a domin ita d`in maciji ce ba ta ramin kanta,ita d`in hawainiya ce mai saurin rikid`a izuwa launi-launi,tsintarciyar mage ce ba ta mage,ita d`in tamkar kaska ce mai mak`alewa a jikin dabba don ta sha jininta ta cutar da ita,ita d`in Kura ce mai lullu`be da fatar akuya,shimfid`ar fuskarta kuwa tamkar kwanciyar mage ce mai d`aukar rai,don haka  zamu nemi zaman sulhu ne da ita ,idan kuma ta bijira hakan sai muyi amfani da Hatimi wajen juyata ta k`arfi da yaji ko ta so ko ba ta so ba","Hatimi kuma ?","Eh Hatimi dai wanda ka sa ni,wanda a shekarun baya,ake amfani da shi,duk me shi shi  ya ke da k`arfi da iko fad`a a ji a Masarautar BAIBAH, wanda ake la'akari da girmansa ko k`ank`antarsa,kuma kowacce k`abila a cikin k`asar su na da irin na su ","To ai ni Hatimi na K`arami ne ba wani babba ba ba ne ba,kuma k`abilata d`aya da Matata"," Ni kuma nawa babba ne da na gaje shi a wajen kakana na hud`u "," To ta ya Hatimi guda biyu zai Zama sanadiya ko jagorar yin nasarar mu",Hakimi ya sake jeho ma M.Musa wata tambayar a karo na ba adadi.
"Muna da wani mutum d`aya da ba zamu sha wahala wajen jansa cikin wannan tafiyar ta mu ba"," Shi kuma wannan mutumin waye shi","Ishmal yaya a wurin Sarauniya Junayyah kuma wanda su ka fito ciki d`aya da ita,wanda ya ke rufe a can gidan yari na tsawon watanni shidda"."Da alama dai tsananin burin da ke d`anfare a cikin ruhinka ya fara zautar da kai a ta ya Yarima Ishmal ya juta ma `yar'uwarsa da su ka fito ciki d`aya ba ya abin da kamar wuya kam","Kwace goruba a hannun kuturu ba abu ne mai wahala ba,inda har ka shirya ma hakan ",Cewar Malam Musa
Hakimi rasa me zai ce ya yi ,sai zuba ma sa ido da ya yi,sai shine da kansa ya ce da shi,"Kar ka da mu ya kai Hakimi domin na dad`e da shiryawa gami da tsara duk abinda ya kamata dama kawai na ke jira sai yau Allah ya kawo min ita ta hanyar ka".
"Me ka shirya game da Mai Girma Ishmal"," Zan bi duk hanyar da zan bi domin in ga na fito da shi ,kuma zan yi komi a bisa taka tsan-tsan gami da kula ba tare da ko da sunan ka ya fito ba ,kawai abinda na ke so da kai ka tsaya a saman maganar ka da alk`warinka har zuwa sanda za mu yi amfani da Hatiminka","Na yi ma ka alk`awari da d`an da ke kwance cikin cikin matata zan kasance mai cika alk`awari a gare ka muddin ina da rai kuma ruhina na doran k`asa",da sauri M.Musa ya furta Kalmar subahanallahi gami da yi mishi dogon bayani akan bai kamata mutum ya rantse da wani abu mai rai ko mara rai ba ,Da Allah kawai ake rantsuwa shima hakan in ta kama,kuma da dalili kwakwkwara,sun d`auki lokaci mai tsawo akan haka ya na mai bayani