KARAGAR MULKI

Page 6

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*
   (Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
    
       
***
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆

For WhatsApp Channel 👇👇👇👇👇👇

***

STORY & WRITTEN BY 
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
   And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever 

BOOK 1 

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 6


A fusace ya shigo cikin harabar Sashen na sa,sai da abinda ya ci karo da shi ne ya d`an dakatar da shi gami da k`ara kashe ma sa jiki da zuciya,Nurain ne ya gani a harabar Gidan, sai faman Kai komo ya ke,a kallo d`aya da za kai ma sa ka fahimci ya na cikin tashin hankali da damuwa,jiki a sanyaye Madaki ya nufi inda ya ke ya na mai dafa kafad`arsa,cikin hanzari Nurain ya waigo  domin san ganin waye a bayansa,cikin muryarsa mai d`auke da rauni ya furta kalmar,"Babana","Na'am Nurain,ya naganka a cikin wannan yanayin, me ya ke faruwa,tamkar hawaye na ga su na zuba a saman fuskarka ?","Baba d`an'uwana,d`an'uwana na ke tunani zuciyata bazata iya d`aukar rashinsa a tare da ni ba,ban san a wanne hali ya ke a ciki ba,ina jin zafi da k`una a cikin rai da gangar jikina ina jin tamkar zuciyata zata rabe gida biyu","Dama na sa ni Nurain baza ka iya rayuwa ko jin dad`in rayuwar ba matuk`ar ba ka tare da Yarima Haisam, d`ayanku ba zai ta`ba iya jure rashin d`an'uwansa ba,mu je zuwa d`akina da akwai magana mai matuk`ar muhimanci da na ke son mu tattauna da kai".da to kawai ya iya amsa ma sa su na mai nufar hanyar d`akin Madakin,har su ka isa cikin d`akin su ka zauna ba wanda ya sa ke iya cewa komi na wani lokaci.
"Baba yanzu wacce matsaya Me Martaba ya yanke game da wannan rikitaccen al'amarin ?"," Yak`i sahalcewa ko sa hannu a kan wannan lamarin,daga k`arshe ma cewa yai su yanke ma su duk hukuncin da su ka gadama"......da sauri Nurain ya dakatar da shi ya na cewa,"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'una Baba ta ya za ai ya yanke wannan d`anyan hukuncin, mai ya sa zai aikata hakan,ko tsana da rashin k`aunar da ya ke ma sa ce ta sa ya yanke ma sa wannan hukuncin ?","Nima abinda na fahimta kenan sai dai yai hak`uri ba zan iya amincewa ko yi ma sa biyayya a wannan karon ba ".
Da d`an sauri Nurain ya ce "Ina sauraronka Mahaifina, wanne irin mataki ka yanke,ina son inji domin kuma in san wacce irin gudunmuwa zan bayar a cikinta,rayuwata da raina fansa ne ga Yarima Haisam, matuk`ar akwai hanyar da ake tunanin za a bi domin a ku`butar da su a shirye na ke da in tunkareta komi tsanani da kuma had`arin da ke a cikinta"." Zan had`a ma ka tawaga cikin sirri kuma a `boye ku shiga har cikin k`asar BAIBAH ku yi duk me yiwuwa ku ceto Yarima Haisam, a cikin wannan tafiyar da za ku yi da akwai dokoki guda biyu a cikinta,na farko ban damu da rayuwar kowa ba a cikin su,ko da ko Jamal ne da ya ke d`ana kuma k`ani a wurinka ,don haka ku mai da hankali da tunaninku a kan Yarima Haisam kawai,shi kad`ai ne alhaki da nauyin cetonsa ya ke a hannunku,kuma ya rataya a wuyan ku,ban damu da rayuwar sauran ba ko kad`an ko su rayu ko su mutu ba na da damuwa a kan haka,duk d`aya wai an yi ma tuwo `barin miya,hakama duk d`aya mamaci ya karye a wuya  ,na biyu kar ku yarda ko kusa ko da wasa ku baro k`asar BAIBAH ba tare da Yarima Sadauki ba,wannan shine dokar,har gobe har jibi Yarima Sadauki a wuri na tamkar `Dawisu ne ko da tsintsaye ko ba su namansa sai Sarki, ".
" Rayuwata fansa ce ga d`an'uwana Yarima Haisam, don haka na amince zan yi wannan tafiyar ko da hakan na nufin kowo hanyar ko silar zuwan k`arshen rayuwata,ko da hakan na nufin zan riski kaina a cikin mugun ramin ko halin k`ak`anikayi da za a iya cewa Gaba Kura baya siyaki","Na ji dad`in jin haka da ga gare ka ,gama da ma hakan na yi tsammani daga gare ka ,tuni da ma na fara k`ok`arin had`a rundunar da za su yi ma ka rakiya a tafiyar",.....,wani bawa ne ya shigo cikin d`akin cikin sauri fuskarsa na bayyanar da rud`u gami da firgici, yanayin yanda ya shigo ne ya sa Madaki da Nurain dakatawa da ga zancen da su ke,cikin fushi Nurain ya ce da shi,"Me ya ke damunka ne Sallama ko ba ka cikin hayyacin da hankalin ka ne,me ye yai zafi da tsanani da har zaka fad`o ma na cikin d`akin a irin wannan halin sai ka ce wanda Kura ta biyo ?",cikin yanayin girmamawa,mutuntawa gami da k`ank`an da kai Bafad`en ya fara ce"Ka gafarce ni ya kai k`aramin mai gidana ba wai na aikata hakan da gangan ba ne,A'a ko kusa ko kad`an ba haka ba ne ,na ga abinda ya rikita ni ne har ya zama linzamin da ya jefa ni cikin wannan halin "," Ka ga ka dakatar da duk wani dogon zancen da tsegumi ka tafi kai tsaye ka fad`a min me ya ke faruwa ,domin na k`agauta da inji me ka ke tafe da shi","Me Martaba Sarki Abdullah ya na tafe ma'ana ya na bisa kan hanyarsa ta zuwa wannan d`akin domin ya gana da kai ya shugabana kuma na ji ai ance zai zo ne domin ya samu labarin ka na k`ok`arin shirya wata runduna domin aikata can zuw k`asar BAIBAH, had`i dada,.........ya kasa k`arasawa sakamakon shigowar Sarki Abdullah ba tare da sun yi zaton hakan da gaggawa ba, 
"Ranka ya dad`e lafiya ka zo da kan ka,ai da sai ka aika in zo da kaina ba sai ka zo ba",........" Ka ga ka dakata da wannan shiriritar da shashancin domin ni ba shine ya kawo ni ba na zo ne domin in gargad`eka gami da ja ma ka kunne".......,"Mai Martaba me na yi kuma ,me kuma aka ce da Kai na aikata a yanzu kuma","Ka dakatar da k`ok`ari ko shirin tura tawaga zuwa k`asar BAIBAH,aikata hakan babban kuskure ne, ban shirya salwantar da rayukan jama'ar k`asata akan wad`ancan `yan tsirarun rayuwar wasu mutane da su ke a hannunsu ba"."Oh dama kan wannan maganar ce ta sa ka har kai tattaki ka zo nan ?,to idan dan haka ne ina mai ba ka hak`uri da bazan iya yi ma ka biyayya akan hakan ba",A hassale Me Martaba  ya d`ago ya na mai sauke kadarar mujiyarsa a kan k`aninnasa ,kasancewar yau ce rana  tafarko da hakan ta faru a tsakaninsu,jikinsa har rawa ya ke ya fara magana,"Me ka ke son cewa ,ko ka na nufin ban isa in sa ka abu ka yi ba,koko me ka ke nufi ?","A'a ka Isa har ka yi yawa ma sai dai Maganar gaskiya indai akan lamarin Yarima Haisam ne,ba zan iya ba, domin ni bazan iya wofintar gami da watsar da lamarinsa kamar yanda kai ka aikata ba,ni a wurina har gobe shi d`in cikakken jinina ne ,d`ana kuma na har abada,ba zan ta`ba iya hukuntasa da laifin da ba shi ya aikata ba,Ni ba na d`aya daga cikin mutanen da su ke butulce ma Allah akan jarrabawar ko k`addarar da su ka riske su,Ni ba irin ka ba ne,ina da banbanci da kai,zuciyata ba a kangare ta ke ba kamar yanda ta ka ta ke a bushe "....... Kasa k`arasawa yai sakamakon saukar marin da ya sauka a saman kuncin sa hagu da dama,cikin yanayi fushi da hassala ya d`ora da cewa," Har yau har gobe inanan a matsayin da ka sanni da shi ,ko Babu sauratar k`asarnan a kaina ni Sama da kai na ke ,tsayayyen mutum na ke ba sakarai na ke ba,kuma kar ka manta idan kura tai kuka ma su akuya ne ke jin tsoro su d`auresu,kuma ko jimina ta nutsa kanta a ta`bo tafi k`arfin a kirata da kaza don haka ka shiga cikin taitayinka kuma ka iya harshenka kasan furci ko kalamin da zai fito daga bakinka har ka tunkare ni da shi, in kuma ba haka ba yanzu hukunci mai cike da danasani zai biyo bayan abinda ka aikata","Ka yi hak`uri Me Martaba amma ba abinda ka ke zato na ke nufi ba ,kawai dai zuciyata ce a cunkushe ga rud`u da damuwa da suka dabaibaye min rayuwata,kaina har wani tafarfasa da turiri ya ke min ,ban San me zan yi ba na rasa makamar da Zan kama akan hakan, na rasa madafa da makama akan lamarin gabad`aya "," Kabar komi a hannuna Idris,zan yi abinda ya dace kar ka je wajen azar`ba`bi da gaggawarka  ka ja ma k`asata wani bala'in da masifar da ban yi zato ba balle tsammani,ka bar su kawai acan ,k`adarar su ce ta kai su can kar hakan ya zama sanadin da zamu hak`ura da su kar garin ceton su muyi  babban danasani",ya kai k`arshen maganarsa ya na mai sanyaya muryarsa da nufin ya lallashi Madaki Idris ya amshi zancensa da hannu bibbiyu,duk`ar da kai k`asa Madaki yai ya na mai nuna ladabi da biyayya ga Me Martaba Sarki Abdullah, cikin k`ank`antar da kai ya ce da shi,"Idan  har ka na nufin in kyale rayuwar Yarima Sadauki ta salwanta shine abinda ya dace to ina me ba ka hak`uri akan ba zan iya yi ma ka biyayya ba,na yarda in fuskanci ko wanne irin hukunci ne ko da kuwa ta `bangarenka ne na shirya ma hakan,kai ko da hakan na nufin ni ma zan salwantar da tawa rayuwar ne",cikin k`osawa gami da gajiya da sauraren kalamin da ke fita daga bakin Madaki Idris Me Martaba ya dakatar da shi,"Shikenan mu tafi a haka,amma ina son ka sani in Gafiya tak`i fitowa daga rami hayak`i a ke mata ,Ni kuma na yi ma ka alk`awarin zan nuna ma ka asalin ko ni waye da kuma matsayina a cikin k`asar BIHINAR, mu zuba ni da kai mu gani,mu ga waye zai yi nasara,zan toshe duk wata kafa da za ka bi domin yin nasara,kai ko damar da za ku fita daga cikin k`asar nan kai da tawagar ta ka ba zan ba ku ba,wannan shine alk`awarin da zan yi ma ka kuma maganata ta k`arshe da kai in har akan wannan lamarin ne",ya na kaiwa nan a zancensa ya fita daga d`akin cikin hanzari da sauri har iskar babbar alkyabba da ke jikinsa ta na komawa fuskokinku su.
Jiki ba kwari Madaki Idris ya Kai zaune tamkar wanda aka turesa ya na mai fad`i jagwab,sai da ya d`auki wani lokaci mai tsawo sannan ya iya bud`e baki ya ce,"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'una wannan wacce irin musiba ce da tashin hankali, har sai yaushe za ta zo k`arshe,yaushe ne za mu samu damar ganin iyakarta,a duk sanda irin haka ta zo kaina rud`ewa ya ke tunani na ya dakata,na rasa MENE NE ABIN YI ?,kaina ya fara tafarfasa, tunanina da hankalina duk su gushe,kwakwalwata ta dakata da aiki gami da toshewa na tsawan lokaci,Babu abinda na ke ji da gani face Yarima Haisam, ba na damuwa da kowa face shi,shi kad`ai d`insa Kai ko ni karankaina ba na ji da ganin kaina,na yarda na amince Yarima Sadauki na daga abinda na fi so ,kuma ya kasance jarabta da k`addara a gare ni".
"Ya Kai Mahaifina ina mai ba ka hak`uri abisa abinda ya wakana a yanzu ,sannan ina yi ma ka albishir tare da alk`awari akan cewa ko ni kad`ai ne zan shiga cikin k`asar BAIBAH in fito lafiya tare da Yarima Haisam a raye,in mai do ma ka da yaronka kuma d`anka a har cikin wannan k`asar ta BIHINAR cikin k`oshin lafiya", da hanzari tamkar Madaki zai kifa haka ya k`araso inda Nurain ya ke,muryarsa har rawa ta ke ya na mai cewa," Dagaske Nurain za ka sa ka rayuwarka a tsaka mai wuya,kuma ka jefa ta a bigiren da za ka iya rasata domin ka ceci d`an'uwanka na jini?","Kwarai kuwa dagaske na ke na shirya tarar aradu da ka matuk`ar hakan zai sa Yarima Sadauki ya dawo k`asarsa cikin k`oshin lafiya","To ta ya hakan za ta kasance bayan yanzu kuma a gabanka Me Martaba Sarki Abdullah ya tabbatar da bazai ta`ba barin hakan ta faru ba matuk`ar ya na da rai","Ni kad`ai zan tafi in tunkari k`asar BAIBAH, ba tare da wani mutum ko d`aya ba,nasan zai yiwuya Me Martaba Sarki Abdullah ya tunanin hakan a ransa domin babbar kasada ce kuma kuskure,ba duka me hankali ne zai yarda ya d`auka ko ya aikata hakan ba matuk`ar ya na cikin hankali da tunaninsa","Kai Masha Allah na gode ma Allah da ya azurta ni da samun d`a mai kaifin hankali ,basira,kwazo da kuma hankali, kamar kai tabbas zan had`a ma ka duk kalan guziri da kuma abinda za ka buk`ata a halin wannan tafiyar ta ka,tare da duk wata gudunmuwa da za ka so kuma ka buk`ata","Na gode sosai Mahaifina da ka amince da wannan batun nawa,domin ni ba kowa ba ne in har ba Yarima Haisam d`an'uwana kuma abokina aminina ",daga nan su ka fara tsara yanda komi zai kasance a cikin tafiyar .