Page 8
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆
For WhatsApp Channel 👇👇👇👇👇👇
***
***
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 8
FREE PAGE
Masarauta ce wacce ta amsa sunanta Masarauta, ko ta ina ka hanga iya kar ganinka dakaru ne zagaye da ita ,hannayensu d`auke da manya-mayan makamai masu tsoratarwa gami da firgita duk wanda ya d`ora idanunsa akan su,siffar Dakarun ta ban-banta da irin asalin sufar mutane,kallo d`aya za kai masu ka ji ba ka buk`atar sa ke d`ora idanunka a kan su.
Duk tarin damuwa da ke shinfid`e a saman fuskar Gimbiya Junainah, sai da ta fad`ad`a zuwa bayyanar farin ciki da annashuwa,yanayin Masarautar kad`ai in ka kalla ya kan d`ebe ma ta tarin d`unbin damuwar da ta ke cunkushe a cikin zuciya da rayuwarta,duk inda su ka ratsa bayi,hadimai,kuyangu har ma da Dakaru sune su ke zubewa har k`asa su na kwasar gaisuwa a gare su,ba tare da Gimbiya Junainah ko Tsohuwa Malikat Juwairiyya sun kula da su ba, ka sa hak`ura Gimbiya Junainah tai har sai da ta umarci hadiman da su ke d`auke da su bisi BIKAD da su dakata su a jiye ta ta sauka,ta ke su ka bi umarninta, har ta na had`awa da d`an gudunta ta fara zagaye harabar Masarautar, ba ta zame ko ina ba sai k`ofar da zata sadata da d`akin Kawunta Ishmal,turus ta ja ta tsaya sakamakon ganin k`ofar ta sa a rufe, rasa wa zata tambaya ta yi sakamakon rashin giftawar wani a wurin ,kusan a hargitse ta juyo da nufin komawa baya domin ta samu damar da za ta tambayi wani ko wata ko da daga cikin bayi ne me ya ke faruwa,dakatawa ta yi sakamakon kusan cin karo da ta yi da Kuyanga Jazila ,da sauri ta zube k`asa ta na mai hurwa da ban hak`uri, "Ki gafarce ni ya ke Uwar d`akina kuma Uwar Gijiyata,na tuba ki yafe ni,tsananin murna da d`okin jin labarin kin dawo ne ya sa ni zakwad`i har da kaiwa ga aikata wannan d`anyen kuskuren ,amma ina mai rok`on afuwa da ga wajen ki"," Duk ba wannan ba Kuyanga Jazila na zo da zinmata gami da saran tare da son ganin Kawuna Ishmal, amma kuma sai na ci karo da k`ofarsa a rufe abinda a tarihi da rayuwata ban ta`ba ji da gani ba,bugu da k`ari ga alamomi da dama da su ke nuni da cewar Sashen na sa ya dad`e a rufe,me ya ke faruwa kuma sannan ina ya je?".
"Ki gafarce ni ya ke Uwar Gijiyata domin ba na da zarafi ko ikon da zan amsa ma ki wad`annan tarin tambayoyin na ki,hakan ya fi k`arfina,hakan ba zai yiwu gare ni ba,a matsayina na Kuyanga kuma baiwa"," Ban ga ne me ki ke son cewa da ni ba ,ko dai ki na son ki ce da ni Kawuna Ishmal ya na cikin tashin hankali ko munmunan yanayi ?","Kusan haka ne Uwar Gijiyata, amma na bi Allah na bi ki,da kar ki sa sunana a cikin wannan lamarin kuma ki daina tambayata komi hakanan,ban san wacce irin jarfa ko masifa zan fad`a a ciki ba".
Wata lafiyayyar Shak`a Gimbiya Junainah ta kaima Kuyanga Jazila, idanuwanta su ka firfito waje ta ke ta fara yunk`uri da kakari,numfashinta ya na kai kawo sai faman sama da k`asa ya ke,ita kuwa Gimbiya Junainah tuni launin idanunta sun canja sun rikid`e zuwa asalin idanun Macijiya, cikin k`araji da d`aga murya ta ke tambayata ,"Ina Kawuna Ishmal ya ke,kuma me ya same shi a iya tsawon kwanakin da su ka shud`e,waye ya ke da sa hannu a cikin duk abinda ya faru da shi ?",firgici,rud`u gami da shiga tashin hankali, shine ya ziyarci Malikat Juwairiyya da tawagarta a yayin da su ka k`araso wurin,su ka yi tozali da abinda ke faruwa, k`araji mai k`arfi Gimbiya Junainah ta cigaba da sa ki daga bisani tai wurgi da Kuyanga Jazila can gefe guda ta na mai fatali da duk abinda ya shige ma ta gaba,daga k`arshe ta silale k`asa sumammiya,da dabara Malika Juwairiya ta sa su Kuyanga Jazila su k`a mik`a ta zuwa `bangaren Malikat Juwairiyya d`in.
Lokaci guda labarin dawowar Gimbiya Junainah ta karad`e gami da zagaye Masarautar BAIBAH,da kuma mutanen da su ke rayuwa a cikinta da gefanta ma gabad`aya
Zaune ta ke bisa lallausar kilisarta wacce ta sha mabanbantan a do da kwalliyar,a ta kowacce fuska.sai da ta gyara zaman ta sannan ta ce da shi,"Basiru ba zan kyale ka ba matuk`ar na bincika na samu akasin abinda ka fad`a min ko ka zo da shi".
Sai da ya Kai hannaye da k`afafunsa k`asa kana ya d`ora da cewa,"Na rantse ma ki da girman *KARAGAR MULKI* da ki ke zaune a kanta a koyaushe zancen da na fad`a ma ki gaskiya ne,ban zo ma ki da wannan batun ba har sai dà na bincika iya bincikawa na tabbatar da sahihanci gami da inganci sa,sannan na tunkare ki da shi ,kuma a yanzu haka gabad`aya mutanen Garin BIHINAR na can hankalin su a tashe da sa rai gami da tunanin za ku iya kai ma su hari a kodayaushe,kuma sun san da cewa Yariman su ya na tare da ku a cikin wad`annan mutanen da ku ka tsare".
Wani k`ayataccen murmushi ne ya bayyana a saman fuskar Sarauniya Junayyah mai d`auke da ma'anoni daban-daban,"Sarkin Yak`i ka sa a kaisa Gidansa sannan a had`a ma sa shatara ta arzik`i ,idan ya huta zan nemesa domin ya amshi ladan lek`en asirin da ya yi,wannan ai shine a na zaton wuta a mak`era sai ga ta a masak`a,amma kafin nan ka tabbar da ka je ya nuna ma ka shi Yariman ka gansa da kanka","An gama Ranki ya dad`e, yanzu za a aikata kamar yanda ki ka umarta,fad`a ta ki cikawa ta mu",cikin rawar murya Dakaren ya bud`e bakinsa ya na mai cewa,"Ki gafarce ni ya ke Uwar Gijiyata bazan iya nuna mi ki d`aya daga cikinsu a matsayin ko da nufin shine Yariman k`asar BIHINAR ba,domin ban ta`ba ganin sa ba,hasalima ba ya shiga duk wani abu ko harkar da ya, danganci Masarauta da sarautar ƙasar sa gabaki d`aya,wannan shine abinda ya ke min k`aik`ayi gami da d`ar-d`ar a cikin zuciyata tun kafin in kai ga k`arasowa gabanki",Sai da ta mik`e tsaye fuskarta a had`e ta na mai bayyanar da tsanani fushi da `bacin rai,"Kai wanne irin shashashan mutum ne mai cike da wauta da shirme,ta ya haka za ta kasance,a ina ka ta`ba jin irin haka ta faru,ace Yarima sunkutun da guda kuma na babbar k`asa kamar BIHINAR ace ba a san shi ba ,sai kace k`aramin yaro,Kai ko da yaro ne ai ya kamata gami da can-cantar ace ka san shi",da rarrafe gami da had`i da jan ciki Dakaren ya iso gabanta ya na mai kama k`afafuwanta ya rik`e ya na mai cewa,"Na rantse ma ki da wanda raina ya ke hannunsa iya abinda na fad`a ma ki shine gaskiya, ba ma ni kad`ai ba hatta wasu da ga cikin mutanen k`asar ba su san shi ba kuma ba su ta`ba ganin sa ba,Na ji ta bakin majiya mai k`arfi cewa ko a cikin Masarautar ba a cika ganinsa ba,idan ko har ka gan shi to ba shakka magana ce ta fita Yak`i ko farauta,duk wata k`asaita girma,tak`ama da d`aukaka da aka san d`an Sarki na da ita to shi baya amfani da ita kuma na ji cewa,".........,"Ka ga wannan surutun na ka ya ishe ni,Shamaki ku ta fi da shi masaukin sa zan sake neman sa a nan gaba in da buk`atar hakan,", Da hanzari ta nufi d`akin sirrinta ta jawo wani tangamemen madubinta har kashe Ido ya ke,girmansa da zubi da tsarinsa kad`ai abun kallo da al'ajabi ne,ga wanda ya ke kallonsa sai ya shagala ba tare da ya sa ni ko ya fuskanta ba.wasu munanan kalamai ne su ke fita daga bakinta,wanda za su iya zama silar kurumta ga wanda ya ke sauraren su,yare ne marar dad`in ji da saurare,bayyanar fuskar wani munmunar halitta a cikin madubin ya sa ta dakata da jero d`alamisan da su ke a bisan bakinnata.
"Abira lafiya ki kuwa, mene ne dàlilin da ya sa ki ke yimin irin wannan kiran gaggawar bayan Kinsan ina can na himmantu wajen had`a tsimin gagarabadau wanda zai taimaka ma na mu kai ga cin nasara tare da cikar burika da muradanmu,bayan kuma kin san hakan had`ari ne kuma babban kuskure a gare ki da nima ba ki d`aya ?"," Fatsar da muka jefa a cikin ruwa ce tai babban kamu, muna zaton za mu kamo kifi sai ga shi mun kamo tarwad`a , wanda hakan ne ya sa na kasa hak`uri har sai na lasa ma ka zumar da na lasa a bakinka kai ma ka ji d`and`anonta"....."ki dakatar da duk wani tsegumi da ke bakin ki ki jirani ina nan zuwa nan da cikar wasu makonni",ya da katar da ita,"Ba Zan iya ba ne har sai na tsegunta ma ka","Yi maza to ki hanzarta ina sauraranki,ko kuma ki zama sanadiyar da za mu fad`a a kogin danasani","Yanzu haka maganar da na ke ma ka,Yariman k`asar BIHINAR ya na hannunmu a matsayin fursuna","Me.....me..me me ki ka ce ?","Eh abinda kunnenka ya ji haka na fad`a Yarima Haisam d`an Sarkin BIHINAR yana hannunmu","Waaaaa iiiihuhu sai ni Boka Dürsäås ,jikan Gulmar d`a gurin Nazab,tatta`ba kunnen Harzam",ya saki wani ihuya na mai k`arawa da cewa," aiki ya yi kyau muna gab da d`aukar fansar rayukar jinanen iyaye da y`an'uwanmu da su ka zubar mana da su","Dama na san haka zata faru,shiyasa ma na kasa iya hak`ura har sai na fad`a ma ka,don haka ina son ka tak`aita aikin da ka ke domin ka samu damar isowa cikin k`ank`anin lokaci k`asar BAIBAH na marhabin da isowar ka,kafin ka zo zan san yadda zan yi in tsamosa ko ince in nemosa tunda ba wanda ya san shi,daga cikin `yan'uwansa in ware ma sa d`akin da ya ke,tunda a yanzu ya na tare da fursunonin da aka kama su gabad`aya ","Ban gane ba ki na nufin baki San shi ba ne ko me,ko kuma ba dagaske ne ya na hannunku ?","A'a ya na tare da mu kawai dai fuskarsa ce ba wanda ya santa,sai ina mai tabbatar ma ka ko ta halin k`ak`a sai na zak`ulo shi walau cikin ruwan sanyi da lumana ko akasin haka " ,"Ana wata sai ga wata amma ba komi maza ki aikata hakan gani nan zuwa nan da cikar wani wa'adi",da wannan su ka rabu da juna.