Page 9
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
***
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆
For WhatsApp Channel 👇👇👇👇👇👇
***
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Page 9
"Uban waye kai, kuma da me ka ke tak`ama da har za ka shiga har cikin d`akina ka d`aukar mi kayan sawaa,wa ya baka izini ko ya tsaya ma ka da za kai min satan eyehh?"Ya k`are zancen ya na mai kai ma sa duka a karo na ba adadi,bugun shi ya ke bugu irin na fitar hankali ba tare da ya duba ina ne ya dace ya buga ko kar ya buga a jikinsa ba,daga baya Hashim gani yai dukansa da hannu da ya ke bai kai ma sa yanda ya ke so , ya rarimi wata kujera da ke kusa dashi ya fara buga ma sa ita a ka,sosai Hydar ya fara kururuwar neman d`auki da taimako,domin k`arfin sa da na Hashim ba d`aya ba,duk yanda Ciroman Dawaki,Sarkin Dogarai da Baraya su ka so su shiga tsakanin su amma sun Kasa abun ya faskara,dole sai da su ka kai ga kiran iyayensu Mata,a matuk`ar hargitse Sarauniya Mubina ta k`araso wurin,hankalin ta ya k`ara tashi fiye da yanda ta fito daga `bangarenta sakamakon yanda ta ga Hydar d`anta na kuwwa gami da neman taimako har zubar da jini ya ke amma ba wanda ya iya kai ma sa d`auki a kaf cikin Masarautar ba wanda yazo domin ya ce-ce shi,da wani irin k`arfi ta shiga tsakanin su ta na mai `ban`bare Hashim daga jikin Hydar ba tare da ta tsaya jiran komi ba ta fara yarfa mishi Mari a ko wanne `bangare na kuncinsa,ba k`aramin firgici da gigicewa Hashim yai ba a sanda marin ya sauka a kuncin sa ba, domin kwata-kwata bai yi zato da tsammani faruwar hakan ba,a fusace ya d`ago ya na cewa,cikin yanayin sa na `yan daba"Kai³..uban waye ya ke da zarrar aikata hakan a gare ni ko shi d`an uban waye?".....Ya kasa idasawa sakamakon tozali da yai da ita,"To d`an daba mara tarbiya wanda bai gaji natsuwa da hankali ba, ni ce na mare ka ko za ka rama ne?",Cewar Sarauniya Mubina, "Hattara dai Allah wallahi, dan in ba d`an mutuncin ki da na ke ganin `bishi-`bishin sa ba da Wallahi na rantse tsaf zan iya ramawa,in d`aga nawa hannun in shararawa tsohuwa Mari a fuskarta don fuska ai ba fin fuska tai ba"," Shakka ba bu tsaf na san za ka iya tunda ba ka gaji arzik`i da mutumci ba,ba a gada a wurin Uwale ba,bata koya ma ka sanin darajar na gaba da kai ba,bare har ka girmama shi bari in k`ara marin na ka sai in gani ko dagaske kana da zarrar da za ka rama d`in",ta kai k`arshe maganar ta na mai sa ke d`aga hannunta a karo na biyu don ta mare shi,daga bayan ta a ka rik`e hannun a na cewa,"Ahir d`in ki na hane ki da ki sa ke d`ora wannan k`azamin hannun na ki a jikin d`ana tunda shi d`in ba sabon bawa ba ne da aka siyo a ka girke mi ki ,dan ki ta jibga ba ",ta yarfar da hannun bayan ta gama bayanin da za tai,har sai da Sarauniya Mubina ta sa ki wata k`ara sakamakon zafin da ya ratsata har cikin kwanyar kanta,Cewar Sarauniya Mufida da ta k`araso wurin yanzu,"Dama na sani wani aikin sai amale, haka kuma barewa ba tai gudu d`anta yai rarrafe ba,me ake tsammani ga wanda ya ke da Uwa kamar ki,ai sai dai ya kasance kamar wannan, d`an daba mai satar kajin mutane da agwagi", wata gajeriyar dariya Sarauniya Mufida tai ta na mai d`orawa da cewa,"."Hehehe wannan shine hauragiya,an bar jaki an `bige da bugun taiki,kuma dama bahaushe ya ce mai cinikin duhu shi ya saba da lalube, wai na Masai ne ke cewa da na waje ya taka kashi, Idan har maganar sata ake a nan wurin to sai ince ke ce ki kai wannan nak`udar, d`ana kuma da ki ke magana ya riga da ya yi gaba ya bar sauran `yan baya da kwasar k`ura".....,"Rufaa mana baki anan,da dai ace ba mu san asalin ungulu ba ne sai tace daga masar ta ke,kuma da ki ke wannan zancen banzar,na san kin san hasken fitila ba d`aya ya ke da na wata ba,haka kuma sama ta yi ma yaro nisa sai gani ko hange daga nesa,d`ana yafi gaban ki had`a shi da wancan shashan yaron na ki ko kin manta waye d`ana kuma a ta ya na haife shi,shi cikkaken d`ane ba shi da gaurayen ko sirkin komi ko kin man ta ko shi waye?,"."A'a ban manta ba kamar yanda kema na san ba ki manta da yanda na haifi nawa d`an ba,na haife shi a lokacin da Ina Sad`akar Me Martaba, wato ina matsayin baiwarsa ina alfahari da hakan,domin a lokacin ina kan mataki ko k`adami mafi k`ask`anci da rashin gata amma hakan naja hankalin me Martaba fiye da matan da ya ke Aure,duk da su d`in sun kasance `ya`yan Sarakuna ne ,ban sani ba ko sun gaza ne har idanuwansa su ka sauka a kai na ba oho","Ke ki iya bakin ki kar ki ce za ki zagar min mahaifiya anan don ba zan iya d`aukar hakan ba"Cewar Hydar cikin yanayin jin jiki,"In an zage ta wata Uwar za ka iya aikatawa ko ba duk kai ne ka jawo komi da ya farun ba uban wa ya sa ka satar min kayana?","Sata kuma da ma kan sata ne ka lakad`a ma sa wannan Uban dukan za ka kashe sa,kamar ka samu dabba ko jaki,bayan ku indai sata ce tamkar `beran masallaci haka ku ke","Au abun `yar yarfe ce kenan to ai nima nasan asalin na ki kuma dad`in abun ni dai sai mutum ya kira ni da baiwa ko kuma yai min k`azafi ko k`aharu,amma ke waye bai san sunan da Masarautar ku ta yi ba da irin mulkin kama karyar da ake gudanarwa a cikin ta har fa .....Sarauniyar Mubina ta dakatar da ita da cewa,"Kar ki soma aibata mana ahali domin duk kyan tafarnuwa ba tai yi ya albasa ba,kuma ko jimina ta nutsa kanta a ta`bo ba za a kirata da kaza ba,haka kuma ruwa ba tsaran kwando ne ba",a d`an zafafe da lamarin Sarauniya Mufida ta mai da mata da martani,"Ai koma dai mene ne ke ce ki ka fara kuma d`an ki shine yai ma d`ana sata don haka dole ne ya amshi zunubi ko hukuncin hakan","Hukunci kuma ,to a taya wacce hujja ko makama ce da da za ta tabbatar mi ki da shine ya d`auki duk abinda ki ka lissafo? "Sarauniya Mubina ta tambayeta," Hujja ai ba a buk`atar hujja ga wanda aka san shi farin sani a har yai shura a `bangaren sata",Cikin tsananin fushi Sarauniya Mubina ta kai ma Sarauniya Mufida wani bugu a saitin bakinta ta kuwa yi sa'a ta same ta a dai-dai wanda hakan ne ya sa ke hautsina wurin da kuma k`arin zuwan su Hisham da Hannan ,wanda kusan a kan idon su su ka ga bugun da Sarauniya Mubina ta kaiwa Sarauniya Mufida mahaifiyarsu,babban burin su su duka su Isa gurin da ta ke su ramama Uwar su bugun da ta yi ma ta domin cikin k`ank`anin lokaci bakin ta ya suntuma yai k`ato,in ba dan d`ai-d`ai kun Hadiman da su ke wurin sun shiga tsakiya ba,da tuni anyi `batatta
......Tsawar da aka da ka nasu daga can baya ta dakatar da su,me Martaba Sarki Abdullah ne da kansa cikin Isa da da tak`amarsa da su ka zame masa jiki ,a kallo d`aya da za kai ma sa sai ka sha jinin jikinka duk da fuskarsa ba ta nuna halin da ya ke a ciki,ba ka iya gane fushi ko `bacin ransa indai a kan fuskarsa neya ce da su,"Da alama dai taron dabbobi na tara a cikin wannan Masarautar ba mutane ba",kowa da ke wajen sai da jikin sa yai sanyi ba tare da sun iya koda kyakyawan motsi ba,kallon sa ya mai da kan Sallamarsa ya ce da shi,"Ka sanar da su, su taru a Baban zaure gaba ki d`ansu har da ma wad`anda ba sa nan ,idan wani ya so kar ya je,ya ga abinda zai biyo baya",Yana kaiwa nan ya juya zai bar gurin ,da sauri Hanan ta ja baya ta na mai takure kanta wuri guda sakamakon kusan cin karo da Mai Martaba da tai,muryarta na rawa ta ce da shi,"Ka gafarce ni ya Mai Martaba wallahi ban san ka taho ba kuma a rud`e na ke".....da hannunsa kawai yai mata alama da ta dakata ya ra`ba ta ya wuce ,ganin ya bar gurin ne ya sa ta k`ara kwasawa da gudu ta je inda Mahaifiyarta Sarauniya Mubina ta ke tana tambayar ta, "Kiyi hak`uri a kid`ime na ke,yanzu labarin ya riske ni wai dagaske ne abinda na ji koko "......." Dallah tafi can ba ni wuri sakaryar banza sakaryar wofi duk abinda ke faruwa tun d`azu sai yanzu za ki wani zubo da gudu sai ka ce gaske,ai da kin sani ba ki zo ba in ya so zuwa anjima sai ki zo ki d`auki gawar mu da ga ni har d`an uwan na ki",Ba tare da ta sa ke bi ta kanta ba ta nufi hanyar barin wurin ,ba wanda ya sake kuma kula wani a cikin sai dai faman harar juna da suke haka su nufi Babban zaure domin amsa kiran Mai Martaba.