Page 10
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 10
"Na rantse har da Abinda zai kashe ni ban d`aukar mai kaya ba,ban d`aukar ma sa komi ba", Hydar ya ce cikin firgici da rud`un da ya shiga sakamakon jin da yai ance za a saka shi a mari," Amma ai ka shigar ma sa d`aki na shiga ban d`auka ba ai ba bata fidda `barawo kawai ka fiddo ma sa da kayansa ko jikin ka ya gaya ma ka",Cewar Sarauniya Mufida, cikin kakkausar murya Sarauniya Mubina ta ce"Kar ki sa ke cewa da d`ana `barawo in kuwa ba haka ba na rantse",...."Dan Allah ku yi ma na shiru haka,kubar mai alhakin yanke hukunci ya yanke mana, Haba duk kunbi kun addabi mutane da hayaniya sai ka ce ku ne kawai ma su `ya`ya a duniya, ku dai ba ku ta`ba iya zama wuri guda sai kun raba hali Haba,kowa fa da ku ka gani a wurinnan ya na da abinda ya ke ya bari ya zo nan ba wai ya zo sauraren rigima da tashin hankalin ku ba ne ba",Cewar Sarauniya Murjanatu,"Bas su bas su su cigaba da nuna min, su d`in asalin su waye,su tabbar min ni ba abakin kowa na ke a wurin su ba,matsayina,girmana da k`imata ba abakin komi su ke ba ba su ganinta ko da ko kad`an","Ka gafarce mu ya Me Martaba, domin ba hakan ne buri ko fatana ba",Cewar ,Sarauniya Mufida,tana mai k`ask`antar da kanta cikin ladabi da biyayya ita kuma Sarauniya Mubina sai faman cika da batsewa ta ke,ko ta kan su bai bi ba ya ce da Hydar,"Ka mai da mashi kud`in sa hankalin kowa ya kwanta domin wallahi na gaji da irin tashin hankali da damuwar da ku ke d`ora min da wanne zan ji da zund`en da mutanen Gari su ke min akan ku,ko da ciwon zuciyar da kuke k`ok`arin d`ura min ku da iyayen ku Mata, a kaf cikin ku ba mai halin kwarai ko na za`ba,daga mai shaye-shaye, sai mai sata,sai d`an daba da kuma d`an daudu duk ga kunan taron tsintsiya ba shara duk haka ku ke ba na za`ba a cikin ku,In na fita mutane suna ganin k`ima da darajata amma cikin Gidana babu wannan,wani lokacin har sa`bo ni ke a saboda ku ,ina tunanin wanne zunubi na aikata da har Ubangiji ya jarabce ni da ku a matsayin Ahalina....me na yi....me na Aikata ",Muryarsa ta fara rawa wanda har fuskarsa sai da ta nuna tsananin jin zafin abinda ya ke fad`a, da rarrafe Hydar ya Isa wurin da Me Martaba ya ke fuskarsa na zubar da hawaye ya ce da shi," Mahaifina ka ya fe ni,da na zama silar jefaka cikin wannan halin,amma wallahi na rantse ma ka ban d`aukar ma sa komi ba,kuma ma ni ai ba a ta`ba kamani da makamancin irin wannan laifin na sata ba, nasan dai na shiga d`akin da nufin in yana da abinci a d`akin sa ya bani in ci tun safe ban ci komi ba sakamakon zazzafan zazza`bin da na kwana da shi,na je can madafi babu wanda yai saura sun mik`asa shashin Bayi kamar yanda su ka saba,kuma ba su gama na rana ba,har Jakadiya na tambaya na sanar da ita yanda akai ta ce in bari a dafamin wani abun ma na ,na ce da ita ta barshi mai yiwuwa ba zan rasa abinda zan ci a d`akin sa ba",kusan kowa da ke wurin sai da zuciyarsa tai sanyi sakamakon jin abinda ya ce,kar ma shi Hashim da abun ya fi bugun zuciyarsa,cikin muryarshi wacce mai ita ya ji jiki ya d`ora da cewa,"Dagaske na ke wallahi ban d`aukar ma ka Kud`i ko kaya ba,ko Hanan ga ta nan ka tambaye ta,tunda ku san tare mu ka fito da ita a cikin d`akin ",Hannat ce tai saurin cewa," Hanan kuma ,ka tabbata ta shiga cikin d`akin ?",ita kanta Hanan d`in sai da gabanta ya fad`i sakamakon jin an anbace ta a cikin wannan hargitsin,cikin inda-inda ta ce,"Meye na sa ni a cikin wannan lamarin k`ar ku ja min sharri".....Hannat ta katse ta da cewa,"Sharri kuma ai ke kin san na fi k`arfin in tsaya `bata ma kaina lokaci akan haka,kuma kin san ai na ganki a inda ki ka je ki kai kayan","Wai me ya ke faruwa ne,me ku ke son cewa sai faman wasu maganganun ku ke ba tare da nasan asalin abinda ku ke cewa ba",Cewar Sarauniya Madina wacce tunda a ka zauna da ita sai yanzu ta yi magana,Idanuwan Hannat a tsaitsaye ta sa ke bud`e ba ki ta ce,"Ba abinda ya ke faruwa kawai dai k`aik`ayi ne ya koma kan mashek`iya,duk wannan ta da hankali da hana zaune tsayen da ake k`anwarshi Hanan itace ta d`auki kud`in da kuma kayan dan ni da kai na na ganta wajen Hauwa Dillaliya ta kai mata kaya ta siya,har mita na iske ta na yi wai ita ba ta saba siyan irin wannan kayan ba,tunda ba ta cika hud`d`a da maza ba,duk da dai ban ga kayan ba da idanuna tunda ta na ganin na ta ce ta sallama,a bata kud`in amma tabbas itace ta d`auke su",Wani dogon salati da sallallami Sarauniya Mubina ta sa ki ta na mai tattafa hannayenta,"Yanzu duk wannan duka da d`aukar alhakin da ku ka yi ma wannan yaron ba bisa hak`in sa ba ne Ashe kai da `yar'uwarka ne ku ka had`a kai ku ka jamishi sharri dan kun tsane sa ko?", duka da Sarauniya Mufidata kai ma Hannat tai saurin gocewa ta na cewa,"K`aryar ta ke Munafuka so ki ke kawai ki wanke d`an'uwanki da ga zargi shiyasa ki ka ja ma Hanan sharri yarinyar da tun safe ta bar Gida","To ai nima da safen ne mu ka had`u da ita a Gidan Hauwa Dillaliyar",Hannat ta sa ke ba ta amsa,"Za ki rufa min ba ki anan ko kuwa,idan sata ce a kaf Gidannan waye ya kai ki ko a tunanin ki kowa ma irin ki ne?",....."Wai ke me ya ke damunki ne,meye ya shiga tsakanina da ke,dole sai kin ja ma `ya`yana sharri dole sai kin nuna ma duniya su d`in ba mutanen kirki ba ne ba alhalin kema da kallar na ki gembon a jikin ki","Cewar Sarauniya Mubina,"Amma ba dai irin na ki ba ko don kuwa kin san duk lalacewar yarana sun fi na ki nagarta da kuma halin kwarai", ta tari numfashinta "Kunga dan Allah ya Isa haka ku barmu mu samu maslahar wannan lamarin da me za mu ji sai ka ce k`ananan yara haba dan Allah mana",Tari ne ya sark`e Me Martaba, wanda tun ya na yin sa a hankali har abun ya fara cin tura numfashinsa ya fara wahalal shak`a mik`ewa ya fara niyar yi ya tafi taga-taga zai fad`i da sauri Hafsat tai kan sa za ta taro sa ya d`aga mata hannu gami da karkad`a ma ta yatsa alamun kar ta kuskura ta ta`ba shi,amma duk da haka ba ta iya ta barshi ba sai da ta bi bayan shi har ya ida sa shiga turakar sa,kusan kowa kasa tashi yai daga wurin sai Hanan da ta ke ta faman motse-motse, Sarauniya Murjanatu ce tai k`arfin hali ta ce da Hanan," Ke Hanna ki ji tsoran Allah, ki fad`i gaskiyar abinda ya faru kin ga dai abinda ya faru yanzu a gaban ki,in kuma so ki ke bak`in cikin ku ya kashe Me Martaba sai ku cigaba da duk abinda ku ka ga dama",kasa cewa Komi tai sai motse-motse da soshe-soshen da ta fara ta na tutturo bakin ta gaba,hakan ne ya fara `bata ran Sarauniya Murjanatu ta daka mata tsawa ta na mai cewa,"Za ki fad`a min gaskiya ne ko sai na k`araso inda ki ke na d`ora hannuna a jikin ki,kin san ni bana shiga harkar kowa kuma ba na d`aukar raini ko wargi",Gaban Sarauniya Mufida sai bugawa ya ke cikin ranta sai fata da addu'ah ta ke ya sa kar ta ce ita ce ta d`auko, wacce irin kunya da nauyi ne za su mamayeta in haka ta kasance, tasan dai Hanan na shan tabar ganye amma ai ba ta ta`ba kamata da laifin sata ba.
"Nnnn...nnnni ni ce na d`auka", ta bada amsar cikin rarrabuwar harshe,hayaniya ce ta fara tashi a cikin zauren kowa sai tofa albakacin bakin sa ya ke kar ma dai Sarauniya Mubina da ta sa ke baki sai habaici ta ke jefa mu su,takaici da bak`in ciki ya sa Sarauniya ta kama hannun Hanan ta ja domin su bar wurin da sauri Sarauniya Mubina ta bi bayanta ta na cewa,"As Allah ya raka taki gona gayayyar arna a idi ku tafi can da bak`in halinku da mugun abun ku,dama can mun san garin banza a farau-farau d`in wofi ya ke k`arewa,Ta Allah ba ta ku ba in sha Allah duk wani k`ullunboto da mugun abinda ku ke shiryawa a kan ku zai k`are",
Da haka kowa ya watse ya nufi `bangarensa,Hydar kuma ya bi bayan Sarauniya Mubina domin ta gasa masa jikin sa saboda ba k`aramin duka ya sha a hannun Hisham ba.
Zama Sarauniya Murjanatu ta yi ta na mai sauke wani dogon numfashi wanda ya ke nuna tsan-tsan bak`in ciki ko damuwar halin da ta ke a ciki," Ba ni ruwa in sha",ta ce da Jakadiya Azima da ke kusa da ita cikin sauri da azama ta kawo ma ta ruwan cikin sabuwar tasa sai k`yalli da walwali ta ke.,"Ya Shugabata ki na lafiya kuwa na ga fuskarki ta nuna tamkar kina cikin damuwa ?",Jakadiya Azima ta tambaye ta,bayan ta gama shan ruwan,sai da ta sa ke nisawa a karo na biyu ka na ta ce da ita,"Lamarin Gidannan ne Jakadiya,Lamarinnan ya dame ni a kullum k`ara hargitsewa komi ya ke ba ga matan Gidan ba ba ga `ya`yan Gidan ba ,komi sai k`ara lalacewar da ta`bar`barewa ta ke "," Subahanallahi wani abun ne eta sake faruwa, ban da rikicin da ya faruwa a tsakanin Sarauniya Mubina da Sarauniya Mufida ?","Bawai zan ce lamarin sauran mutanen Gidan ba ya damuna ba amma dai hankalina da tunanina ya fi karkata wajen Me Martaba ne,ina tsoran kar wani abun ya same shi koma ya je wata cutar can daban ta same shi duk a saboda haukan mutanen Gidannan, yanzu haka fa dafe da k`irjinsa ya bar babban zaure ba tare da an gama zaman da a ka Kira mu domin sa ba,numfashin sai faman hawa da sauka ya ke",sai da Jakadiya ta d`an firgita sakamakon jin abinda ya fito daga bakin Sarauniya Murjanatu har ta na cewa,"Na shiga uku ko dai in je in kira ma sa Ɗan Magorin Masarauta ne kar abun yai nisa da tsamari ?","A'a kar ki je domin kin san halin Me Martaba a yanzu a halin da ake ciki bawanda zai saurara komin girma da matsayin sa kuwa,ki bari zuwa d`an anjima zan je in ga halin da ya ke a ciki inda buk`atar a kira Ɗan Magorin Masarautar sai a kirasa","To shikenan Ranki ya dad`e yanda ki ka ce haka za ai",har Jakadiya Azima ta d`an yi shiru sai kuma ta matso tana mai k`ank`antar da muryarta ta ce,"Idan ranki ba zai `baci ba ya shugabata da akwai maganar da na ke son muyi da ke game da al'amuran da su ke faruwa a cikin Gidannan ",sai da Sarauniya Murjanatu ta gyara zamanta kana ta ce da ita," Uhm mu je,fad`a kan ki tsaye ina sauraren ki fatana dai komi za ki fad`a ya kasance alkairi ne kuma mafita a bisa tarin matsalolin da mu ke fuskanta a cikin wannan Masarautar ne "," Kusan haka ne dai ko kuma kai tsaye in ce wani haske ne,ni ke son in haskaka a cikin lilli`ba`ben sirrin da ke binne a cikin wannan Masarautar, shin tunda ki ke a rayuwar ki kin ta`ba cin karo da wani Sarki da ya ke da tarin matsaloli irin na Sarki Abdullah ko kuma ya ke da fand`arrun `ya`ya marasa ji,marasa natsuwa da hankali kamar Sarki Abdullah? ",ta tambaye ta ta na mai tsayawa don ta ji me za ta ce,da sauri Sarauniya Murjanatu ta girgiza ma ta kai alamun a'a ba ta ta`ba gani ba,ta d`ora da cewa" `Ya`ya fa bakwai Allah ya albarkaci Me Martaba da su hud`u maza uku mata amma kaf a cikin su in ki ka cire Hafsat ba wanda bai da mugun tabo a tattare da shi,shin me hakan ke nufi,wanne sirri ne ya ke binne a k`asa game da hakan?","Ban sa ni ba,ban sa ni ba Jakadiya","Kamar ya ba ki sa ni ba,ke fa jinin Sarauta ce gaba da bayan ki kin yi gadonta ta ko ina , kamata yai ace ko wani a cikin Gidannan ko a waje bai yi irin wannan tunanin ba ya kasance ke kin yi sa,Babban d`an sa fa,Haisam yana tattare da mugayen Aljanu da su ke sawa ya juye ko ya rikid`a launi-launi ko ya yajuye ya zuwa mabanbanta fuskoki,Hashim ya kasance k`asurgumin d`an daba,Hashim gashi Namiji cikakke amma d`abi'a da halayya d`insa kaf na Mata ne,tamkar d`an daudu haka ya ke,Hydar kuma kullum cikin bin Mata ya ke,tamkar d`an bunsuru haka ya ke ,A mata kuma Hannat sata ko `beran masallaci ya rufa mata asiri ,ita kuma Hanan Shaye-shaye, Hafsat ce kawai za ka bigi k`irji ka ce ba abinda ta ke aikatawa,kin ga kenan akwai lauje cikin nad`i a wannan lamarin ta ya haka za ta kasance, don haka ki yi tunani ki zauna ki natsu ki zurfafa tunanin ki kuma a ciki ki yi amfani da dabara,basira, har ma da hangen nesa wata k`ila ki hango hasken fitilar da na ke son ki hango,don haka na bar ki lafiya zan tafi in kin ba ni izini ",sa ke baki Sarauniya Murjanatu tai ta na bin bayan Jakadiya Azima har ta `bace ma ganin ta ba tare da ta iya cewa da ita komi ba....