Page 11
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Page 11
"Da biyu wai an jefi biri da rani,dama ni na san haka za ta kasance tun bayan da na ga sun kawo mu wannan d`akin, na san da akwai wani abinda ke shirin faruwa,ba hakanan banza ba,duk da dama su d`in azzalumai ne na k`arshen bugawa", cewar Jamal cikin yanayin azabtarwa da wahalalwar da ya ke a ciki.
Sai da Salim ya ja numfashi mai d`an tsawo wanda ya ke cike da rauni da nuna zallar gajiya da wahalarwa ga wanda ya yi sa,sannan ya ce ," Ni kai na ina mamakin yanda hakan ta kasance ,ya akai wani ya san da cewa muna tare da Yarima Haisam a cikin wannan tawagar ta mu,kuma a cikin wannan k`asar ta BAIBAH ko dai hakan na nufin akwai d`an lek`en asiri da ya ke rayuwa a cikinmu ko a Masarautar BIHINAR ne ?",Kamal ya amshe zancen ya na daga can gefe kishingid`e ya na faman d`aure cikinsa wanda ya ke fitar da jini ,"Ai ba sai ka wahalar da kan ka wajen dogon tunani da son gano abinda ke binne ba, alhalin ya na a bud`e a sarari ,ko tantama ba na yi wannan haka ya ke,da akwai d`an lek`en asiri ko dai a cikinmu nan ko kuma a can Fadar BIHINAR d`ayan biyu dole akwai wanda ya ke gaskiya a ciki"," Maganarka dotse Kamal sai dai ina da ko kokonto akan batunka na cewa da akwai d`an lek`en asiri a cikinmu,mun tashi a tare tun yarinta zai wuya wani cikinmu ya cutar da wani a cikinmu kai da haka ta kasance gara shi ya cutu,to in dai har haka ne ta ya za a samu wanda zai iya fallasa sirrin da ke tsakanin mu",cewar Habib.
"Duk ba wannan ba ,kuture zance ko batun ta ya mutanen k`asar BAIBAH su ka san muna tare da Yariman k`asar BIHINAR, mu nemo hanyar ko matsayar da za mu tsaya a kan ta,a ganina kamar hakan ne abinda ya fi mu maida hankali a kan sa fiye da mai-maita abinda dukkanin mu mu ka san da shi","Ka yi gaskiya Ayub,sai dai wannan hukuncin Yarima Haisam ne,shi ke da damar ko ikon yanke shi,domin mu d`in duka bayinsa ne kuma a k`ark`ashin sa mu ke,dad`in dad`awa shine jagoran wannan tafiyar ta mu,duba da hakan ya sa na ke ganin shi ya fi can-canta da ya yanke ma na matsayar da ya kamata mu bi,duk da dai wannan sabuwar matsalar kacokan ta `bullo ne daga `bangarensa"," Haka ne Jamal ,amma ni dai ina mai rok`on Yarima Sadauki akan cewa ya yanke hukunci dai-dai yanda ya ke ji a cikin zuciyarsa,kar yai duba da halin cutuwar da mu ke a cikinta,domin ina da yak`inin akan dukanmu rayukanmu fansa ne a kansa,za mu iya juriya gami da fuskantar ko wacce irin wahala ko musiba akan ssa,domin ni dai na san idon da ya juri ganin Sarki ba zai ta`ba gazawa ko kasawa da jin tsoro da shakku ganin Galadima ba,"Haka ne Jamal dukkanmu mun yarda kuma mun bi gami da yin mubayi'a akan abinda ka ce,rayukanmu duka fansa ne akan ka Yarima Sadauki, hukunci na gare ka a yanzu",ya na kaiwa nan a zancensa yai shiru kusan su duka ba wanda ya k`ara yunk`urin cewa komi a cikin su.
Yarima Haisam kyakyawan gaske ne , fari kal da shi me zubin larabawa,shid`in ya na sanye da wandon da riga mai d`auke da sulken yak`i a samanta , k`afar shi na sanye cikin wani takalmi,sau ciki na fata bakake su ma , ya had`u mak`ura yanda kasan shi d`in ba ba afurke ba ne ba,fuskarsa na d`auke da dara-daran Idanu farare k`al da su ,kwayar cikin idon tamkar an d`iga masa zaiba-zaiba a cikinsa , ya na da dogon hanci da dan karamin baki,mai d`auke da ja a jikinsa,tamkar wanda ya shafa Jan baki a jikinsa , ga wani kontancen saje a gefe da gefen fuskar shi , gashin kan shi bak`ik`k`irin da shi ya zubo,yanda kasan ya na samun gyara na musanman, gaba ki d`aya ya tara shi a bayan k`eyarsa sai wasu sirarren da su ka zubo mishi a gaban goshi , ya na da tsayi ga murɗaɗen jiki kamar dan dambe , damtsen shi a murde su ke kamar za su fasa hannun rigar da ke jikinsa, ga wani kyakyawan gashi kwance luff saman hannayensa da ma fatar jikinsa gabad`aya ,Tabbas ya amsa su nan nasa na Yarima Sadauki,ko a yanayin tafiyarsa,maganarsa,cin abincin sa ,Kai da kome da kome na sa rayuwarsa da yanda ya ke tafiyar da su za ka ga natsuwa,kamala,kwarjin tare da dattako a ciki,mutum ne mai tsantseni gami da taka tsan-tsan da rayuwa,bai fiye hayani da surutu ba ,idan har ka ji doguwar maganar sa to da d`ayan mutum biyu ne Nurain ko Madaki,su ne kawai ma su sanyawa ya tsawaita maganarsa a fad`in rayuwarsa su ya ke kiran da duniyarsa kuma rayuwarsa.
Jingine ya ke jikin bango kansa duk`e a k`asa sai faman wasa da tsinken hannunsa ya ke ya jima kafin ya ce da su wani abu, don kusan wasu daga cikin su ma har sun fidda ran zai ce da su wani abu,cikin yanayin yanda ya saba magana d`auke da natsuwa,fitar sauti muryarsa kad`ai zai iya shagalar da mai sauraren ta har barci ya fara barazanar d`auke sa ya ce da su,"Ina mai ba ku hak`uri a bisa yanayin da na jefa ku a ciki ,amma ina so ku sa ni,ko kuma in yi ma ku tuni akan abinda kun riga da kun San shi,Ni d`innan ban za mo Yaro Nagari mai albarka kamar ku d`innan ba,Mahaifina da Mahaifiyata ba wani a cikin su da ke alfari da haihuwata,Babu wani mutum a ahalina da ke jin dad`in danganta kansa a da ni a matsayin jininsa ko d`an'uwansa,ban kai matsayi ko girman da zan amsa sunan d`an Me Martaba Sarki Abdullah ba,ni wofintacce kuma korarre d`a a gare sa ne, ba na tunanin da akwai wata Rana da za ta zo komi nisa ko tsaurin da za ta zo da shi da Me Martaba zai iya alak`anta ko danganta kan sa da ni ,Sanin hakan da na yi ne ya sa ba zan ta`ba yin ganganci ko kuskuren aikata hakan ba,domin ina jin tsoran abinda hakan zai haifar,babban burina a rayuwa bai wuce in aikata wani abu ta kowacce fuska da zai sa ya ji dad`i ko yai alfahari da haihuwata da ya yi ba,ko da ko hakan zai sa in cutu ko in rasa raina,Na san a yanzu kuma a halin da ake ciki,hankali da tunanin sa ba a kaina ya ke ba,don haka ba zan zama sanadiyar da zan kawo ma sa wata matsala,tasgaro ko rud`anin da bai zato da tunani ba,muddin Me Martaba Sarki Abdullah ba zai iya fitowa duniya yai ikirari tare da alfarin cewa ni d`an sa ne kuma gudan jininsa na cikin sa ne ba,To tabbas ba makawa ni ma ba zan iya amsa sunan shi a matsayin Mahaifina ba,ba zan iya alfahari ko fankamar da shi ba,idan da a yanzu zai fito ya ce da duniya ya yafe min laifin da na aikata ma sa,ya amshe ni a matsayin d`ansa ,kuma ya sa ni a cikin jerin `ya`yan da ya haifa da ba shakka babu wani dalili da zai sa ban amsa hakan ba,ni ma zan yi alfahari da shi kuma in alak`anta sunana da na sa,ko da hakan zai zama silar jan numfashina na k`arshe a rayuwa da duniyata,Sai dai kash! hakan ba mai yiwuwa ba ne,ko da kuwa a mafarki ne,don haka ina mai shawartar ku gami da Baku umarni da cewa kar ku kuskura ku jefa kan ku ko d`ayanku a cikin wannan wasan ku wakilta wani daga cikin ku da ya nuna ni a matsayin jinin Me Martaba Sarki Abdullah, amma ba a matsayin d`an sa ba,domin ni ba zan iya aikata hakan ba,kun ga daganan sai ku yi tafiyarku ku koma wancan kurkukun da zama har Allah ya kawo ranar da za ta zama ta k`arshe a wajen ku, ko ku koma gida a raye gaban `yan'uwa da ahalinku ko kuma wani abun ya same ku na daban".
Jiki a sanyaye Ayub ya matso kusa da shi ya na mai cewa,"Haba Yarima Sadauki me ye zai sa ka rink`a fad`ar haka,ko ka manta a tsakanin mu mu duka da akwai alk`awari mai k`arfi wanda igiyar k`arfe ta sark`afe gami da d`auresa".
"Sanin hakan da na yi ne ya sa,ba zan ta`ba iya ganin ku cikin halin k`unci da wahalalwa ba"........Habib ne ya katse shi da sauri ta hanyar cewa,"Ban ji dad`in wannan batun da ya fito daga bakin ka ba,domin ni na yi tunanin da zaton duk mun riga da mun zama d`aya Babu wani abu da zai raba mu duk tsauri da tsanani sa,sai gashi kai da karankanka ka na furta irin wannan zance,ba tare da ka yi la'akari da irin rayuwar da mu ka gudanar a baya ba"," Habib ka yi magana mai kyau domin ina da tabbacin ba abinda za su iya yi mana,sai dai ko su wahalal ko cutar da mu,ba za su iya kashe d`aya daga cikinmu ba ,saboda kokonto ko tsoran rashin sanin tak`amaimai waye Yarima Sadauki a cikin mu kun ga kenan koma me zai zo, zai zo mana da sauk`i", wannan furcin ba k`aramin dad`in sa su ka ji ba har ta kai ga gabad`ayansu kowa sai da ya tofa albarkacin bakinsa da kuma nuna rashin jin dad`in irin hukuncin da ya yanke tare da tabbatar da su na tare da shi duk wuya duk runtsi,sun yarda za su fad`i tare su ta shi a tare ko da kuwa za su rasa ransu gabad`aya ne.