Page 12
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 12
"Ranki ya dad`e,barkan ki da hutawa"," Barka dai Kuyanga Jazila "," Dama zuwa nai inji labarin Gimbiya Junainah shin ta farka ne ko har yanzu ta na cikin munmunan halin da ta ke a ciki ?","Hmmmmm Kuyanga Jazila kenan ai lamarin Gimbiya Junainah ya fara tsoratarwar gami da firgita ni,na rasa Makama ko madogarar da zan kama har in samu tsinin da zan rik`a balle har in kai ga kamo bakin zaren lamarin".
"To fa wannan shine gaba kura baya siyaki,to da wanne `bangaren ya kamata ki ji da shi ya ke Uwargijiyata,da lalurar da ke samun Gimbiya Junainah,ko matsalar da ke tsakanin Gimbiya Junainah da Sarauniya Junayyah koko da matsalar da ke tsakanin Sarauniya Junayyah da d`an'uwanta Yarima Ishmal ,cikin ukunnan da wacce za ki fara ?"," Jazila dukkanin su abin dubawa ne ,na farko Gimbiya Junainah ba za ta ta`ba samun lafiya ba matuk`ar ba muryar Kawunta Ishmal ta ji a kusa da ita ba,dad`in dad`awa ina tsoran kar ciwonnan na ta ya birkice ya koma ciwon da ke addabar rayuwarta,mu bani mu lalace tunda ba musan wanne irin taimako za mu bata ba,kuma zuciyata na yawan hasaso yanda zamu kaya tsakanina da Sarauniya Junayyah idan har na furta kalmar ta sake Ishmal daga d`aurin zaton da ta yi ma sa,wannan shine abubuwa guda uku da suka tsaya min a rai kuma su ka hanani sukuni,sukan soki zuciyata ,suka mai tsanani da zafi ","Allah ya k`ara mi ki yawan rai ai ita Gimbiya Junainah bai kamata a barta ta cigaba da zama a cikin irin wannan yanayin ba,duba da komi ka iya faruwa da ita a saboda hakan","Na San da haka Kuyanga Jazila amma taurin Kai da kafiya na Sarauniya Junayyah shine abinda ke dakatar da ni a duk sanda nai yunk`urin tunkararta da zancen,","Ya shugabata ki gafarce in abinda zan fad`a laifi ne ko kuskure ,amma nasan abinda zan fad`a gaskiya ne,ke ce macen da ta fara zama a kan KARAGAR MULKIn da Sarauniya Junayyah ta ke tak`ama gami da nuna isa da iko a kanta ,kin zauna akanta na tsawon shekaru da dama,bai kamata ki cire idanunki a kan duk wani hukunce-hukuncen da zata rik`a yankewa ba,idan har buk`atar hakan ta taso,kamar dai a irin wannan matsalar da ta taso ta Gimbiya Junainah da Kawunta Ishmal, ki na da damar da za ki yanke kowanne irin hukunci akan lamarin su ,domin a samu maslaha da kwanciyar hankali ,domin ina jiye mi ki tsoran kar wata rana a haife mi ki d`a mara ido,ko kuma a zo ana ga irintanan "."Na ji dad`in wannan batun na ki Kuyanga Jazila zan zauna in sake duba batun da izinin Allah"," Na gode sosai da sosai Ranki ya dad`e da amsar abinda na zo ma ki da shi da hannu bibiyu "," Kar ki damu Jazila kin can-canci fiye da hakan ma ,a kullum kuma a koda yaushe ina ma ki addu'ah da Allah ya albarkaci rayuwarki ,kin kasance ki na ta wahala tsawon lokaci da Gimbiya Junainah, tun tasowar ki ,kin rabu da Mahaifiyar ki kin za`bi Zama da ita aduk girman Lamarin da take fuskanta ko tsananin da tsaurin da ta ke a ciki muna Godiya akan hakan ".
" Kar ki ce haka Malikat Juwairiyya domin ni a gare ni ina kallon Gimbiya Junainah a matsayin mahaifina ko Uwar da tai sanadin zuwana wannan duniyar ne ,ta yi min abinda su suka kasa yi min shi,ta Cece rayukanmu ni da su a lokacin da ba muyi zato ko tsammani ba,badan ita ba da yanzu ba ma raye,tausayi da tausayawarta a gare mu ya wuce gaban kwatance,ko kin manta ita ce ta dakatar da hukunci Sarauniya Junayyah a kan mu da badan haka da da yanzu an k`one mahaifiyata da ranta a tsakiyar kasuwa gaban tarin mutane,akan d`an k`ank`anin laifin da ba muji ba bamu gani ba,hakan ya sa na ke ganin yafimin in zauna da ità ,in mata bauta tare da biyayya kuma in bada raina fansa a gareta ,wata k`ila hakan zai iya zama matsayin Godiya bisa halacci da karamcin da ta yi ma na".
"Kin ga Kuyanga Jazila zo ki je ki kwanta dare ya fara yi,ki daina yawan dawo da abinda ya riga da ya wuce,kin sa da idonta biyu ba zata bar ki ki idasa wannan zancen da ki ke ba ,ki bar ni zan cigaba da kulawa da ita,domin wannan lamarin na Gimbiya Junainah abu ne na k`addara da ba zai yiwu a same shi a yanda ake so ba,Kinsan ita k`addara wani rubutu ne ko zane daga Ubangijin sammai bakwai,kuma yakan rubuta shi akan wanda ya so kuma a sanda ya ga dama"," Zan so ace ki bar ni in kasance da ita,kamar hakan zai fi bani kwanciyar hankali da kuma natsuwar ruhi","A'a yau d`aya na yafe mi ki gami da d`auke ma ki wannan nauyin ki je ke ma ki kwanta ki huta kamar kowanne mutum,zuwa da safe sai ki dawo","shikenan ya shugabata bazan iya jayayya da ke ba,zan tafi amma da garin Allah ya fara haske zan dawo",sai da Malikat Juwairiyya ta saki murmushi sannan ta ce ba komi sai kin dawo ,fatana a kan ku duka biyun Allah ya albarkace ku ya sa ku cigaba da rayuwa a tare".
Na yi duk me yiwuwa, na wahaltar gami da azabtar da su amma a cikin su ba wanda ya yarda ya amsa shine Yariman k`asar BIHINAR,tamkar sun had`a bakinsu wuri d`aya ne",Sarauniya Junayyah ta k`are zancenta cikin alamun sarewa gami da gajiya bisa lamarin da ga can `bangaren d`an duk`urk`ushi kuma munmunan mutumin cikin amon sauti mara dad`i ya fara magana ransa a matuk`ar `bace,"Kin ba ni mamaki da kunya ace wa'inan jariran yaran da ba su kai ko su Ashirin ba ace wai kin kasa ji da su,kin kasa tsamo mutum d`aya acikinsu tamkar an baki aikin da ya fi kowanne aiki girma da hawala a duniya,Kai ko ba tare da amfani da tsafi ba ai ya ci a ce kin tsamo mana shi daga cikin sauran Dakarun "," Na rantse ma ka da kushewar mahaifinmu har da tsafin na yi amfani amma ban samu wata makamar da zan rik`a ba,idan na tunkaresa ma sa sai inga ya rikid`e ya koma min dodo mai barazanar fizgar raina ta k`arfi da yaji".....da hargagi wanda ya ke d`auke da fushi a cikinsa ya dakatar da ita,"Ki rufe min bakin ki anan domin wannan dogon bayanin na ki ba abinda zai amfana min da shi,face ya sake hassala ni","Ka yafe ni ya kai d`an'uwan Mahaifina ba wai na ba ka wannan labarin ne dan Ranka ya `baci ba a'a na fad`a ne don sa ran zamu samu maslaha akan hakan daga gare ka,in ma da yiwuwar kabar duk abinda ka ke anan ka taho sai mu jida lamarin a tare ni da jai",sai da ya sa ke murtuke yank`wanenniyar fuskarsa mai kamar a taka fura sannan ya ce,"Wannan lamarin da ki ka zo da shi ba mai yiwuwa ba ne,domin aikin da na ke aikatawa ba k`aramin muhimanci ne da shi ba,yanzu zan fad`a mi ki abinda za ki aikata da kai tsaye zai bayyanar da kan sa ba tare da an k`ara shan wata wuya ba","Na ji matuk`ar dad`i da jin wannan batun na ka,na dad`e da sanin Kai gugar k`arfe ne sha kwaramniya,dole a ganka a barka indai a fagen tsafi ne ka ci dubu sai ceto ,amma me ya sa tun farko ba kasanar da ni dabarar da zan yi amfani da ita ba,sai yanzu da muka d`auki tsawon lokaci "," Na so ganin irin gogewar da ki ke da ita a fanni abinda na ke koyar da ke ne shiyasa, sai dai na yi kuskure da na yi zato gami da tsammani kin kai wani mataki da na ke mafarki ashe duk ba haka ba ne ba","Na tuba ka yafe ni ya kai d`an'uwan Mahaifina kuma abun tunk`ahona,na yi ma ka alk`awari daga Rana irin ta yau ba za ka k`ara samuna da irin wannan sakarcin ba","da hakan ya fi ma ki domin duk fad`i tashin da na ke a kan ki ne kawai na ke yin su ,ki je d`akina za ki ga wani tulu ya na d`auke da tsumin tsafi a cikinsa ki d`auko shi sannan ki samu kashin dokin da Yarima Ishmal ke hawa ,da kuma yankin alk`yabar da ya ke sawa,ki had`a su wuri guda ki k`ona ki had`a da wannan tsumin,sai kije ki watsa ma su shi a jikinsu ,su duka daganan duk abinda ya biyo baya kya ne me ni daga baya,ki sanar da ni",ya na kaiwa nan ta dena ganinsa a jikin madubin tsafin nata,kusan har jikinta na rawa ta mik`e tsaye ta nufi bargar dawa kin domin samo mahad`in maganinnata,sai dai me hankalinta ya dugunzuma ya tashi sakamakon rashin ganin dokin Yarima Ishmal da ta yi a jerin dawakin da ke bargar,da mad`aukakiyar murya ta fara kiran sunan Tanimu Dakaren da ke kula da dawakin,kamar zai kifa haka ya k`araso gabanta sai faman haki ya ke,ko tsayawa sauraren gaisuwar da ya ke ma ta ba tai ba ,sai jefo ma sa da tambaya da ta yi,"Ina dokin da d`an'uwana Ishmal ya ke hawa ya ke na ga ban ganshi anan ba ?"da sauri ya ba ta amsa da cewa,"kwana biyu da su ka wuce ya yi rashin lafiya ne ,to shiyasa a ka ke`be shi, shi kad`ai domin ba shi kulawa da kuma gudun kar ya shafa ma wani daga cikin dawakan",sai da Sarauniya Junayyah ta sa ki wata ajiyar zuciya mai k`arfi har sai da wannan bawan ya d`ago ya na kallonta,share shi ta yi ba tare da ta nuna ta san kallonta ya ke ba ta ce da shi"Ba damuwa ina son ganinsa ne ko za ka iya yi min jagoranci zuwa inda ya ke","Da guduma kuwa Ranki ya dad`e ai ko da cewa ki kai in sa`bo shi bisan wuyana in kawo shi gaban ki yanzu zan aikata hakan bare kuma yi miki jagora zuwa inda ya ke ai ya fi komi sauk`i a gare ni","ka ga dakatar da wannan surutun na ka ka wuce mu je domin ba ni da lokacin `batawa a nan ",bai k`ara cewa komi ba har su ka Isa gurin,sai dai su na isa ta aikesa da nufin ya je ya d`ebo ko ya k`aro ma dokin karmami duk da ga tarin abincinnan a gaban dokin har ya tafi sai wata zuciyar taraya ma sa anya ba wani mugun abun ta ke da nufin aikatawa ba shi ya sa ta aike sa,wurin da ba za ta iya ganinsa ba ya samu ya lafe a cikinsa amma shi kuma zai iya ganinta,bai sha mamaki ba har sai da ya ga ta duk`a ta d`ebi kashin dokin,ta zuba a cikin alkyabbarta ba k`aramin tashi hankalinsa yai ba zuciyarsa ba inda ta karkata sai tunani ko wani mugun abun zata aikata ma d`an'uwanta Yarima Ishmal ,ganin ta na shirin jiyowa ne ya sa shi saurin k`ara shigewa can cikin yayin da ya ke a cikinsa don gudun karta gan shi, ya na mai dafe saitin zuciyarsa da ta ke bugawa da sauri dasauri,sai da ya tabbatar da ta isa barin bargar sannan ya fito ,ga tsegumi iya tsegumi ya na cin bakinsa amma ba shi da wanda zai tseguntawa,ya sa ni muddin wannan labarin ya fita a bakin ransa domin da ga shi sai ita su ka san ta zo cikin barganan don haka ba zai yi wuyar kamuwa ba,rashin hak`uri da kuma rashin iya rik`e kai ta kai sa har ya na sai da ya furta cewa,"Kai jama'a in Banda abin Sarauniya Junayyah me za tai da kashin doki, in ba neman duniya kuma ta sa a gaba ba,ga dukiya,ga MULKI da duk wani abu na more rayuwa, amma duk da haka a yanzu wani mugun abun ta ke son kullawa wani ,dama ance duk wani mugun abu da za a kulla ta hanyar asiri,tsafi ko tsubbace-tsubbace to da k`azanta ake had`a sa in ba haka me zatai da kashin doki fisabilillah ",da haka dai ya cigaba da surutunsa na banza na wofi,wanda ba zai amfana ma sa da Komi tunda ba wanda ya ke jinsa .