Page 13
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 13
Tsakar dare ne wanda yai dai-dai da Sulusin dare,ko ina ka sanya kadarar mujiyarka za ka sauke ganinka ne a saman fitilun k`asa ma su d`auke da Auduga da Man gyad`a a cikin su,su na a sagale a ko ina,hasken su ya wadata zuwa lungu da sak`on Masarautar,haske tamkar wata d`an daren kwana Goma sha biyu,Gari ya yi tsit ba hayaniyar komi,sai kukan tsintsaye da na karnuka,yanayin yanda iska ke k`adawa kad`ai ya Isa ya k`ara shagalar da Mutanen Garin gami da k`ara samun damar jin dad`in barcin da su ke.
A guje ta fito daga d`akin Gimbiya Junainah, mayafinta a hannu k`afafuwanta ko takalmi Babu ta nufi d`akin Malikat Juwairiyya cike da firgici da rud`u, ita kanta Malikat Juwairiyya sai da ta kusan fad`owa daga bisa Gadon katako da ta ke kwance wanda ya sha shimfid`u na alfarma da k`awa .
"Kuyanga Jazila Anya kuwa lafiya za ki fad`o min cikin d`aki a wannan talatainin dare tamkar wani abun tsoro ya biyo ki ,ko dai jikin Gimbiya Junainah ne ya motsa ?", kasa iya ce ma ta komi tai sai faman bud`e baki ta ke gami da nuna ma ta hanyar d`akin Gimbiya Junainah da ke kwance cikin mawuyacin hali,tsakanin mutuwa da rayuwa,ba tare da da Malikat Juwairiyya ta tsaya sa ke tambayarta wani abu ba ta nufi hanyar da da za ta sadata da d`akin Gimbiya Junainahn domin San ganin ainihin abinda ke faruwa, sai da tai danasanin shigar ta d`akin dan da fari so tai ta juya da baya,kwata-kwata batai tsanmanin ganin abinda ta riska ba,abun ya zarce hankali da tunaninta,tunda Allah ya halicce ta ,har kawo tsawon shekarun da ta yi a duniya da kuma wanda ta yi ta na mulkin k`asar BAIBAH ba ta ta`ba cin karo da iftila'i,masiba ko bala'in da ya kai kwatankwacin irin wannan ba,Gimbiya Junainah ce kwance a saman na ta Gadon cikin mawuyacin hali, fatar jikinta ta gama rikid`ewa ta koma zallar fatar macijiya, sai faman ihu da k`araji ta ke,sai ka yi da gaske za ka gane hakan domin sautin hakan ba ya fita,ko da ko su Malikat Juwairiyya ba sa jinsa sai dai sun fahimci hakan ne daga yanayin da ita Gimbiya Junainah ta ke nunawa iyakacin ita kad`ai ce tasan irin rad`ad`i da azabar da ta ke fuskanta ,ganin jarabta da halin k`ak`anikayi da ta ke ciki ya sa Malikat Juwairiyya k`arasowa kusa da ita ta na mai d`ora kanta saman ciyarta ,domin son ba ta taimakon gaggawa daga saman kan Gimbiya Junainah kuwa wani Jan hayak`i ne tare da bak`i ke ta faman kokowa dole d`aya ke son ya rinjayi d`aya ya shiga jikin ta,kusan k`arfinsu ya zo d`aya hakan ne ya hana wani daga cikin su ya samu nasara.
"Wannan wanne irin bala'i ne, wacce irin musiba ce ke bibiyarki ki na `yar k`aramar ki ,wanne mugun ne ,wanne azzalumin ne ya had`a rayuwarki da wannan munmunar k`addara?", Cewar Malikat Juwairiyya cikin sheshshekar kuka wanda ya ke fallasa sirrin zuciyar wanda ya ke yinsa tare da karya zuciyar mai saurare don muryarta d`auke ta ke ko cike ta ke fal da rauni,gazawa,tausayi had`i da rashin sanin madafa akan lamarin.
" Tsoro na ke Malikat Juwairiyya kar da Uwar Gijiyata ta rasa ranta a sanadiyar wannan halin da take a ciki,dubi fa yanda su ke wahalar da ita ,ba ki tunanin za mu nemi taimako ko daga wajen Sarauniya Junayyah ne","Ke ni gabad`aya hankalina da tunanina sun gushe na manta da wani abu kalmar taimako ina sauran magungunanta da su ke ajiye a cikin d`akinnan ?","Na duba su tun kafin halin da ta ke aciki yai tsamari amma Babu su,hasalima Ragayar da ki ke zuba irin wannan ajiye-ajiyen babu ita ta `bace bat babu ita babu labarinta tamkarma bata ta`ba wanzu a wurin ba","Na shiga uku ni Juwairiyya ga shi Bokanya Azizah sai nan da wasu kwanaki wa'adin zuwanta cikin k`asarnan da ta d`iba zai cika ban san ya zan yi ba ina tsoro kar Gimbiya Junainah ta illata ,laifin hakan duk a kaina zai rataya domin ni na tilastamata sai ta dawo da zama cikin Masarautar nan ta k`arfi da yaji"......Malikat Juwairiyya wannan duk ba shi ne abu mai ma'ana da muhimanci ba mu nemo wanda zai iya taimaka mata ko da kuwa Sarauniya Junayyah ce","A'a A'a kar ki soma aikata haka,bad`i ba rai kenan aikata hakan babban kuskure ne idan har Sarauniya Junayyah ta zo nan ba na tunanin Gimbiya Junainah za ta k`ara dak`ik`a d`aya a doran duniya da ranta ,sai dai mu yi zancen wata amma ba dai ita ba ",cikin yanayin karayar zuciya da sarewar jiki Kuyanga Jazila tace," To in Banda ita wa ki ke tunani za mu kira ya kawo ma d`auki da taimako cikin gaggawa ? "Cikin San yi jiki ta ba ta amsa da cewa,"Ba ni da shi,ba ni da shi Jazila kawai sai dai in ta ambato Innalillahi wa'inna ilaihirraju'una³,la'ilaha illallah anta subahanaka inni kuntu minal zalim,Rabbi inni Lima anzalta ilayyamin kairin fak`ir, ba ya ga haka ban san abinda zan yi ba", fad`in wannan kalmar ke da wuya daga bakin Malikat Juwairiyya sai ga wani farin haske ya zo ya doke ja da bak`in hayak`in ,shi kuma ya samu damar ya shiga jikinta,d`aya ya bigi bangon yamma d`ayan kuma ya nufi na arewa, ta ke Komi na jikinta ya sa ki bugun numfashinta ya k`ara k`arfin gudunsa, ita kanta Malikat Juwairiyya ta man ta rabonta da ta fad`i waccan kalmar da ta ambata a yanzu,gaba d`ayansu mamaki kusan kashe su a zaune yai,har ta kai Malikat Juwairiyya ta ka sa iya jurewa har sai da ta magantu ta hanyar cewa," Wai Kuyanga Jazila kin ga abinda idanuwana su ka gani kuwa a yanzu ko ko tsufa ne ya fara sa ni gane-gane ko d`imuwa da tashin hankali da na ke a ciki ne su ka sa na rud`e har na kai matakin fara zaucewa ,gami da fara gane-ganen abinda bai faru ba?","Na rantse mi ki har da Allah na gani","To ke kuwa me ki ka ji na ambata da har ya ke da tsananin k`arfi da ya fi na wa'inna shed`anun,ƙarfin iko ?","Wannan kuma fa d`aya domin ni ba zan iya tantance me ki ka ce ko wanne irin yare ne ki kai ba,har gara ma zan iya cewa ya yi kala da irin yaran wad`ancan masu jajanyen kunnuwan da su ke shigowa wannan k`asar fatauci,in kuma ba haka ba ne ba sai dai in ce ko wasu d`alamisai ne irin Bokanya Azizah ta aiko mi ki da su da taimakon tsafin ta"....."Kai tir da wannan lafazi na ki na k`arshe",ta katseta da sauri,"Ina Bokanya Azizah ina wannan k`arfin ikon sai da in da akwai wani abu wanda ya ke tafe tare da ban al'ajabi k'unshe da sabon darasi da kuma k`addara domin dai na san"..... Kasa k`arasawa tai sakamakon abinda ta ga ya na faruwa,Gimbiya Junainah ce ta fara motsawa ,sai da ta d`auki wani dogon lokaci ta na motse-motse tamkar za ta ta shi sama ,sai ga wannan hasken da ya shiga cikin jikinta d`azu ya fita da jikinta,fit tamkar an zarosa ta k`arfi amma sak da irin kamanninta hatta da tufafin da ke jikinta iri d`aya ne,yana gama fita daga jinkin nata ya nufi bangon gabas da ke d`akin ya ratsa ta ciki ya `bace,ita kuma nan ta ke numfashin jikinta ya tsaya bugun zuciyarta ya dakata,da Alama ruhin jikinta ne ya fita ya bar gangar jikinta anan kwance.
"Na shiga uku Ni Juwairiyya me na ke shirin gani haka kaddai a ce min Gimbiya Junainah ta mutu har an d`auke ruhinta zuwa barzahu,ni inanan sa ke da baki a banza da wofi ?", wani irin ihu Kuyanga Jazila ta sa ki tana mai Kai raramu a jikin Gimbiya Junainah ta na mai girgiza ta gami da rok`on ta ta shi kar ta tafi ta barta,in ta mutu ba ta san ina za ta je ba bare har ta samu wata in gantacciyar rayuwar ba,Hankalin Malikat Juwairiyya ya kai k`ololuwar ta shi har ta kai tunaninta ya toshe ta rasa sanin me ye Makama da madafar da za ta rik`a,akan wannan lamarin.
Sun d`au lokaci mai tsawoa haka ba tare da wani cikinsu ya tsagaita ko ya samu damar fita da ga halin da su ke a ciki ba,har da ga k`arshe Malikat Juwairiyya ta d`ora kanta saman gangar jikinta gami da kama hannunta ta rik`e,zunbur ta mik`e gami da sanya d`ayan hannunta ta kuma rik`e hannun Gimbiya Junainah, yanayin yanda ta ji jinin jikinta ya na gudana ya yi matuk`ar k`ara jefata cikin wani tashin hankalin gami da firgici, sosai ta ke jin yanda jininta ke gudana,kusan an ri`banya shi da wajen kaso uku akan yanda ya ke gudana a baya,Kasa iya cewa komi ta yi sai sa hannu ta yafito Kuyanga Jazila da nufin ta zo inda ta ke ta ji itama wacce ta na can gefe sai faman gurshek`en kuka ta ke ,hannunta kawai ta kama ta d`ora a saman na Gimbiya Junainah, cikin hanzari ta zare na ta,ta na mai ja da baya, muryarta na rawar har ta na had`awa da in'ina duk da ba hali da d`abi'arta ba ce ba,"M..mmm..Malikat kin ji abinda na ji kuwa me hakan ke nufi kuma","Na ji mana Jazila ai hakan ne ya sa na kira ki ke ma don ki ji,abu d`aya na fahimta shine Gimbiya Junainah ta na raye ,har yanzu da sauran ranta".....da sauri ta katseta da cewa,"Bayan duk abinda mu ka gani a yanzu a gaban mu kuma sai ki ce ta na raye,anan fa kuma yanzu-yanzu mu ka ga ruhinta ya fita daga cikin jikinta kai tsaye ya nufi barzahu kuma sai ki ce ta na raye,ta ya haka za ta faru kuma a ina ki ka ta`ba jin haka ta kasance ko dai kin shiga d`imuwa da firgici ne a saboda halin da mu ka riski kan kan mu a ciki?","Ni ma ban sani ba Jazila,wata k`ila ma na haukace ne shiyasa na ke fad`in haka duk da dai"........kasa k`arasawa tai sakamakon wata irin girgiza da Gimbiya Junainah ta yi ,"Lah kin ganin Malikat Juwairiyya ta motsa da gaske dai ta na da rai,sai dai kamar ta dena motsin gaba d`aya ,to hakan me kuma ya ke nufi ?","Ta ya zan iya sani Kuyanga Jazila nima fa anan na ke zaune tare da ke",ta fad`a a d`an zafafe,ta na mai d`orawa da cewa,"Ba zai wuce kawai mu zauna mu zubama sarautar Allah Ido mu ga abinda zai faru domin ba mu da tsimi da dabara akan wannan lamarin",