Page 5
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
***
***
BOOK 1
PAGE 5 ❤🔥
Tsawar da ya daka itace ta dakatar da Hibba daga tunkarowa inda yake,hannunta rik`e da robar ruwa mai sanyi da cup,har ruwan dake cikin cup d`in sai da ya zube k`asa alamar ta ji tsoro, dawowar shi kenan daga office yana k`ok`arin shigowa cikin Gidan.
"Na gaya maki Cecelia zan zo", ya fad`a cikin d`aga murya," Na gaya maki zan zo,ina da aiyuka dayawa ne anan,nauyi ne ya k`aru a kaina da bazan iya tahowa in barsu ba,that's why ki ka ga na d`au wannan long time d`in ban shigo ba,amma ba hakan na nufin na manta da ku ba".
"Oh wani abun mai mahimmanci ka ke da shi shine ne har ya tsare ka,kuma har muhimmancin sa ya kai ka manta da mu,rayuwar ka kawai ka ke kai kad`ai ka manta da mu da dukkanin wani abu da ya shafe mu in ya wuce ka tura ma na da kud`i,ba ruwanka da mu ,har Grandma ta k`araci ciwonta ta warke ba ka zo ka ganta ba,ko an gaya maka kud`i sune kawai matsalar mu,muna buk`atar ganin ka a kusa da mu"...
" I said shut up Cecelia are you out of you sense, ba kya cikin hankalin ki ne,ta ya za ki tasa ni gaba kina fad`ar duk abinda ya zo maki a bakin ki,ko ni sa'an wasan ki ne,don haka ki shiga taitayin ki,ki fita a harkata kawai ki zuba min ido in kuma ba haka ba".......
"In kuma ba haka ba fa,uhm me za ka aikata,Na ce me za ka aikata Daniel".
" I'm sorry Grandma ba wai wani na ke nufi da hakan ba ne ba,kawai dai jin yanda take magana da ni ne ta `batan mun rai har na fad`i irin wannan munanan kalam a kanta amma dan Allah ki yi hak`uri ".
" Ka rik`e hak`urin ka ba na so Daniel,ba na son hak`urin na ka,amma ina son ka sani, I swear to the God idan har ba ka zo Gida mun yi bikin murnar Christmas a tare da kai ba sai na tako k`afata har nan cikin Garin Kanon in ga abinda ka ke `boyewa da har ya zama katanga ko shamaki a tsakanin mu".
Cikin rawar murya Abbakar ya ce da ita,"Bbbbb.....ba sai kin zo ba Grandma ni da kaina ma zan zo in sha Allah "," Daniel you said what ?".
Cikin yanayin kama kan shi ya ce da ita,"Ina nufin by the grace of God zan zo har Jos ɗin kafin bikin Christmas zan zo".
Shiru Grandma tai na wani d`an lokaci kafin ta ce da shi cikin kwantar da murya "Daniel me yake damun ka,dole akwai wani abu da yake damun ka,ba haka na san ka ba,dole akwai wani abu da ke damun ka ko kuma ka ke `boye min shi".
" A'a Grandma ni ba abinda ya ke damun kawai pressure d`in office ce yanzu ma haka dawowata daga office kenan ko cikin Gidan ban shiga ba".
"Shikenan Yarona Na yarda da abinda ka ce,ka kula da kanka ka ji,kuma kayi k`ok`ari ka zo da Christmas tunda nasan ana bada hutu a lokacin".
" Kar ki damu Grandma zan zo","OK shikenan bye take care of yourself I will call letter yanzu ka samu ka huta",
A hankali kamar mai yin samd`a haka ta k`araso kusa da shi,hannunta ta kai kan wuyan shi gami da idasa cire masa neck tie din da ya fara cirewa tun shigowar shi, kujerar da ke kusa da shi ta zaunar da shi,ta cire mashi takalmi da sock d`in da ke k`afarsa,sannan ta ba shi ruwa mai sanyin da ta zo da shi.
Kan hannun kujerar da yake ta zauna gami da tallafo kan shi ta d`ora a saman k`irjin ta ,tare da cewa da shi,"I'm so sorry kaji my husband, in sha Allah everything will be ok,kar ka manta muna tare da Allah ba zai ta`ba bari wani abu mara dad`i ya same mu ba ",haka dai ta cigaba da fad`a masa dad`ad`an kalmomi har ya saki ranshi ba wai dan ya manta da abinda ya faru ba".
"Na gama had`a abincin tun d`azu ,ka zo kafara watsa ruwa sai mu ci abincin"," Mu watsa ruwa dai bak`in ya ke I'm tied bazan iya wanka ni kad`ai ba".
"A'a wallahi na fa yi wanka tun d`azu, kuma fa kalli har kwalliya nai maka ko cewa na yi kyau ba kai ba,kuma sai ace in sake wani wankan a'a gaskiya".
Ta k`asan ido ya fara kallonta tare da cewa," Ai haba ai ni ban gani ba,kuma ma ai kwalliyar mai sanyi ki kai, Ni kuma kin san nafi son zazzafa,don haka dole a sake min wata sabuwa".
Bakinta ta bud`e gami da fiddo da dara-daran idanunta waje ta tana mai cewa,"Allah wannan wayo ne nasan na yi kyau na, kuma kwalliyar ta zazzafa ce,kawai dai kawai",ta na maganar ta na ja da baya daga kusa da shi.
Bai fi taku biyu lafiyayyu ya yi ba ya cimmata,tamkar `yar tsana haka ya rabata da k`asa ya nufi bathroom da ita,ba tare da ta yi zato ba ya sakar masu ruwan sanyi akan su,k`ara sosai ta saki tana mai ruk`unk`ume shi,tare da cewa ,"Me ya sa ka aikata haka,kafa san bana son ruwan sanyi",Tai Maganar ta na mai kai mashi duka a k`irjinsa.
Zuwa lokacin tuni sun gama jik`ewa sharkaf,kayan su sun man-manne a jikin su sai da,ya raba jikinta da na shi kafin ya bata amsa da cewa,"Ni kuma kin ga ina son ruwan sanyi,kuma da ruwan sanyi ya bige ki sai kwalliyar ki ta zama zazzafa".
Dubanta ta kai jikin ta ,matsananciyar kuyan ce ta kamata wanda har hakan sai da ya sa ta shige jikin shi tana mai `boye fuskarta a k`irjinsa.
Hannunsa ya kai yana tattare mata gashin kanta da ya barbazu a saman fuskarta tare shafa gurbin tsagarta eleven eleven tsagar rumawa,"Da gaske na ke komi na ki birge ni ya ke,duk wani abu da za ki ko ki ka yi k`arasawa in so ki na ke,ina son ki ina son in k`are rayuwata da ke,ba zan so in rasa ki ba ko da na dak`ik`a ne domin hakan zai zame min babbar illah da kuma silar cutuwa a gare ni"......
Hannunta ta kai saman bakin sa ta rufe,tare da cewa," Ba abinda zai same ka domin na maka alk`awari ba zan ta`ba yin wata rayuwa in har ba da kai ba,zan rayu da kai a kowanne irin yanayi na dad`i ko akasin haka".
Sai da ya rankwafo ya had`a kan shi da na ta kafin ya ce da ita,"Thanks, thanks a lot,Thanks yuo for being my wife ina farin ciki da samun ki a rayuwata kuma a matsayin matata".
₹₹₹₹₹₹
A k`agauce ya ke shiryawa yana yi yana na cewa,"Yau na makara sosai na yi late,kuma muna da manyan bak`i da zamu yi meeting da su ban san har Gari ya waye haka ba",ya kai zancen ya na mai maida hankalin sa akanta,matsawa kusa da ita yai ya zauna har ya zauna ba ta san ya zauna ba,sai da ya kai hannu ya cire tagumin da tayi da hannu bibbiyu,Wanda hakan ya sa ta firgita ganin shine ya sa ta saki ajiyar Zuciyar mai k`arfi
"Lafiya me ya same ki,ban saba ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba,ko dai kina son komawa makarantar ki ne ki gama tare da k`awayen ki?",.
Da sauri ta girgiza ma shi kai tare da cewa ," A'a ni bani sha'awar komawa waccan makarantar,hasalima ta fita a raina,photo na na da naka ba inda ba su karad`e ba a cikin makarantar,kuma da labari mara dad`i don haka na hak`ura da ita bana da burin sa ke komawa cikinta".
"Ko kin san cewa ba kowanne lokaci ka ke yarda ka bar abinda ka ke so don saboda maganganun wasu muta ne na daban akan ka ba, a lukutta da dama mutanen mu ba su fiye yayata abun alkairin mu ba,sai dai su yayata sharrinmu,kuma ma wai me muka aikata,shin son da muka nuna ma juna mu sa`bo ne ko-ko mun ta`ba aikata wani Zunubi ne?"....
Muryarta na rawa ta dakatar da shi da cewa,"A'a aa ni ba haka na ke nufi ba,saboda ata dalilin sa har yau iyayena ke fushi da ni,don haka bana son shi,idan harma zan cigaba da karatun to sai dai in sake wani `bangaren in koma kamar health line haka".
"An gama ranki ya dad`e daga yau ki fara kallon kan ki a matsayin malamar lafiya,mafarkin ki zai cika wanne `bangarrn ki ke so ki karanta?".
"Ammmm.....Nursing ina son in zama Malamar jinya".
"Daga yau ki fara counting d`in kan ki a cikin jerin Malaman jinyar da mu ke da su a cikin Garinnan, I promise za ki karanci Nursing za ki Kira kan ki da wannan sunan da izinin Allah".
Cikin yanayin farin ciki ta rungume shi bakinta ya k`i rufuwa,sai faman bin shi da kyawawan Addu'o'i take,"Kar ki damu responsibility na ne naga na wadata ki da duk wani abu da ki ka buk`ata,tunda har na iya rabo ki da iyayen ki,bayan shi kuma da akwai abinda ki ke so".
Rau-rau tai da idanun jin ya ambaci iyayenta,", Me kuma ya faru ya Habibaty?",ya tambayeta a k`agauce.
" Ban san me zan yi masu su yafe min ba,ina son su ina son in rik`a zuwa inda su ke amma ka na ganin wancan time d`in da mu ka je Baba K`arami ya koroni ko cikin Gidan bai bari na shiga ba,na kasa iya jurewa ko mantawa da wannan rana".
"Ki shirya mu tafi zan kai ki da kaina ni da kaina zan kai ki cikin Gidan ki ga duk wanda ki ke son gani", bata san sanda murmushi ya ku`bce ma ta ba alamun taji dad`in abinda ya ce.
" A'a ka tafi wurin aikinka kawai ka makara tuntuni,indai ka bar ni sai in tafi ni kad`ai, idan ka dawo sai ka biya ka d`auko ni".
"A'a ki dai bari in kai ki da kaina kamar hakan zai fi"," Kar ka damu yau in sha Allah ba abinda zai faru ka taya ni da addu'a kasan fa yau kana da meeting kuma mai muhimmanci ka ga bai kamata in tsaida ka ba".....
"Kema kina da muhimmanci mai tarin yawan gaske a gare ni,kin ga kenan bai kamata in bar ki kiyi tafiya irin wannan ke kad`ai ba".
" Kar ka damu in sha Allah ba abinda zai faru da ni zan je in dawo lafiya, ka ga ni zan iya kai kaina can Gidan na mu har ma in dawo amma kuma can Companyn ba abinda zai tafi yanda ku ka tsara in har ba ka,ka ga kenan da buk`atar ka tafi can,kuma ka ga ni ban ma shirya ba balle har mu tafi,kayi tafiyar ka kawai da zaran na Isa Gidan zan Kira ka in sanar ma ka",da haka dai ta samu har ta shawo kan shi ya yarda tya tafi ya barta ita kuma ta shirya a tsana ke kafin ta tafi na su Gidan itama.
Cikin shiga ta kamala ta nufi Gidan na su,tun Isar ta k`ofar Gidan fuskarta ta yalwata da mad`aukakin murmushi,a lokacin su Baba Malam suna majalisi
Da karad`i a muryarta ta shiga cikin Gidan tana kiran sunayen duk wanda ya zo mata a baki,"Ummie Maryam, Umma Jamila, Umma Hafsat, ku fito ga ni na zo,ina Yarona Jaheed ya ke",Ba iya sunayen wad`anda ta ambata ba har da su Lami Matar Alaranma Sama'ila da ta zo,hatta da sauran matan `ya`yan Gidan sai da su ka fiffito,nan fa kowa ya fara murnar ganinta da yai ta dad`e anan tsakar Gida kafin Ummie Maryam ta ja ta su shiga ciki.
"Yanzu ke Hibba idon ki kenan ace sai yanzu za ki waiwayo Gidannan tun tafiyar ku,kar ki so ki ga yanda Baba Asabe ke yada maganganu akan rashin zuwan ki".
Rau-rau tai da idanu,hawaye na shirin zubo mata kafin ta ce,", Allah Ummien Jaheed ba laifin na ne ba,har k`ofar Gidannan na zo amma Baba K`arami ya kora ni,badan na so ba ina ji ina gani na hak`ura na koma badan na so ba",
Waige-waige Ummie Maryam ta fara yi alamun rashin gaskiya kafin ta fara kwakkwafarta da cewa," To kar ki yarda ki sanar da Mama wannan labarin don ba zai mata dad`i ba kuma hankalin ta zai ta shi".
Da to ta amsa mata gami da k`ok`arin mai da hawayen da suke son zubowa daga idanun ta.
"Ki yi hak`uri kin ji,kar ki damu da wani abu da ya ke faruwa kin ji wata rana sai labari,ince dai kuna zaune lafiya da mijin na ki,kuma ya na kula da ke yanda ya kamata?".
Sai da fuskar Hibba ta fad`ad`a kafin ta bata amsa da gyad`awa mata kai.
" Yauwa na ji dad`in jin hakan yanzu maza ki je gurin Mama nasan tana can ta tsumayin ki".
"To Ummie Maryam bari inje,amma ina Yarona ya ke ko yana makaranta ne ?".
"Yayah yau bai je makaranta ba yana can d`akina kwance ba lafiya".
" Ayya bari in je Inga Mama sai inzo in duba shi","To shikenan sai kin biyo".
Da sassarfa ta idasa shiga cikin d`akin Mahaifiyarta,a tsaye a bakin window ta hango ta da alama jiranta ta ke kamar yanda Ummie Maryam ta ce.
Ambaton sunan ta tai cikin yanayin kewa da kuma rashin ganin ta.
"To me ye haka, daga zuwa kuma sai kuka,ko kin manta yanzu kin girma".
" Mamana na yi kewanki,ban ta`ba d`aukar irin wannan dogon lokacin ba tare da ke ba,Na yi kewanki ki sosai".
"To ba gashi yanzu kin ganni ba,don haka kukan ya Isa haka,ya mai Gidan na ki yana nan lafiya dai ko ?",
Sai da Hibba ta duk`ar da kanta k`asa alamun ta ji kunyar tambayar da akai mata kafin ta ba ta amsa da cewa" Yana nan lafiya ya ce in gaishe ki anjima ma zai zo sai ya ku gaisa".
Haka Mama Hadiza ta cigaba da yi mata `yan tambayoyin,Wanda za su sa ta fahimci wanne irin zama su ke gudanarwa ita da Mijin na ta,sun d`auki lokaci mai tsawo a tare kafin Hibban ta ce zata je ta gano jikin Jaheed da aka ce ma ta ba shi da lafiya.
Sosai hankalin Hibba ya tashi ganin yanda jikin Jaheed yai tsamari,kamar tai ma shi kuka,rungume shi tai sosai a jikinta sai faman lallashin da ban baki ta ke.
Shigowar Baba K`arami ne ya sa ta d`an dakata,cikin ladabi da kwantar da murya ta fara gaishe da shi,amma ina ko da wasa bai amsa ba,tun kallon farko da tai ma shi ta sha jinin jikin ta Zuciyarta ta fara kai kawo da tunanin me zai biyo baya.
"Ke waye ya baki izinin sake taka k`afar ki a cikin Gidannan ba na hane ki game da hakan ba?".
"Baba K`arami kayi hak`uri wallahi Allah ba zan iya rayuwa ba tare da ku ba,na tuba dan Allah ka yafe ni"....
"Yi min shiru mara kunyar banza mara kunyar wofi,ki sani kin riga da Kin `bata rawar ki da tsalle a wurina tun ba yanzu ba,abu na k`arshe da zan umarce ki da shi kija `yan k`afafuwanki ki bar Gidannan tun kafin dare yai miki".
Har k`asa ta duk`a tana mai had`e hannayenta wuri guda ta na ba shi hak`uri tare da cewa,"Na rantsa maka duk abinda ka ji muta ne na fad`a akan mu sharri ne babu wani abu na `batanci ko na rashin dacewa da ya ta`ba shiga tsakanin mu,sharri ne kawai".
" Ba na son jin komi daga gare ki kawai ki tashi ki ba ni wuri",shine abinda ya ce da ita yana mai nuna mata hanyar fita daga na shi `bangaren,ko motsin kirki kasawa Hibba tai,wai yau Yayanta da ya ji da ita acikin kaf ahalin Gidan su yau shine ke kyararta shike korarta ya na fad`in baya san ganin ta,wanne irin Zunubi ne ita kuwa ta aikata da har ta can-canci irin wannan hakuncin.
Ganin da gaske ba zata fita ba kamar yanda ya ya ke so yasa da kan shi ya fizge Jaheed dake rungume a jikinta ya ja hannunta a tsiyace bai sake ta ba har sai da ya kai ta tsakar Gida sannan ya jefar da ita har yunk`urin fad`uwa k`asa tai.
Tun kafin ya ce komi Baba Asabe dashigiwar ta Gidan kenan ta fara sallallami gami da cewa,"A aha wa idona je gani kamar Hibba, sai yau mu ke ganin ki `yar dad`i Miji ?",Salatin da ta saki ne ya janyo hankalin sauran mutanen Gidan
"Ban damu da ki cigabada da zuwa cikin Gidannan ba ko ki daina ba amma da ga rana irin ta yau na haramta maki shigowa cikin nawa sashen,Na yafe ki bani ba ke,ki fita harka ta kiyi taki harka ki aikata duk abinda ki ka so,Na cire hannuna a cikin dukkanin lamuran ki"......
" To sai me idan ka cire hannunka a cikin lamarin ta shin zata mutu ne ko wani abun na daban da babu shi a cikin littafin k`addarar zai same ta?".Cewar Mama Hadiza da fitowar ta kenan
"Ki gafarce ni Mama amma wallahi Hibba ta kunyata ni,gabad`aya ta fita a raina taje can ta yi rayuwar da taza`ba ma kanta amma ba shakka wata rana za ta fahimci ta aikata kuskure,a lokacin da ba lailai ne ta iya gyara shi ba"...
"Kar ka kuskura ka yima `ya ta baki ,domin ba kai ne ka haifar min ita ba,idan kuma ka sake sai na wanka maka Mari a fuskar ka", Ba shi K`aramin da aka ce za a mara ba ilahirin mutanen Gidan da suke tsaye a wurin sai da suka sha jinin jikin su
Cikin sauri,in'ina had`i da sheshshekar kuka Hibba ta shiga tsakanin su ta na mai cewa,"A'a Mama haka ba za ta faru ba,in dai akai na ne bazan yarda ki d`ora hannunki a jikinsa da sunan hukunci ba,zan tafi zan daina zuwa har sai sanda shi da kan shi ya gaiyato ni cikin Gidannan,zan jure zafi,rad`ad`i da kuma kewarku da zan yi har zuwa sanda zai yafe min laifin da yake zargin na aikata,ko kuma ranar da gaskiya za tai halin ta".
" A'a Hibba ba inda za ki ,Kema `yace haifaffiya a cikin Gidannan don haka ba inda za ki".
"A'a Mama ko da ni ke `ya a cikin Gidannan ban kasance mai yi maku biyayya ba, ko mai sanya ku cikin farin ciki ba,danvhaka tafiya zan yi",ta na kaiwa nan ta juya ta nufi hanyar fita daga cikin Gidan ba tare da ta bi ta kan haka ko wayarta da ke d`akin Mama Hadiza ba.
Tana fita kuwa tai sa'a ta ci karo da mai a dai-daita ta shiga,sai da su kai nisa sannan ta tuna da ta baro waya da Jakarta a can,mai a dai-daita d`in ta rok`o ya bata aron wata ta Kira Abbakar.
Yana jin muryarta hankalin shi ya tashi , fitowar shi kenan daga meeting d`in nan take yai handling d`in komi a wurin assistant managern sa yayi Gida hankali a tashe.