JADEEDA

Page 7

by @cwtsumiey19988

*JADEEDAH*

         (It's a story of two love birds who are so different from each other ) 
STORY & WRITTEN BY :
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
        MENE NE ABIN YI ?
        KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*

***
***


BOOK 1 



PAGE 7 ❤🔥
       FREE PAGE

"Why are you disturbing me Cecelia, in this early morning, kin kira kin kira na ki d`agawa ba sai ki kyale ni ba haba dan Allah, yau fa Sunday ce,yauce ranar guda kawai da make samun hutu".....
    "Deborah ce ba Ceceliar da ka raina ba", Grandma ta katse shi cikin d`aga murya.
    Cikin in'ina da kuma rud`ewar da yai sakamakon jin muryarta da yayi,"Grandma", ya ambaci sunanta tare da d`orawa da cewa,"Kiyi hak`uri ban san ke bace ba shiyasa  ban d`aga da wuri ba".
    " Oh kayi tunanin marainiyar wayon taka ce ko, to ba ita ba ce nice,Anya Daniel, ba akwai wani abu da kake `boyemin ba wannan sauyin naka ya fara bani tsoro,let me ask you kana ma zuwa Church kuwa?".
   Wani zazzafan gumi ne ya fara keto mi shi tare da sanyi a lokaci guda,har sai da Grandma ta sake tambayarsa tare da cewa,"Wai ko ba ka jin abinda nake cewa ne?".
    Shiru Abubakar yai hankalin shi yai matuk`ar tashi hakan ya sa ya kasa iya sarrafa harshen shi.
    "Na shiga uku ni Deborah, me nake shirin ji haka daga gare ka,Yesu Almasihu ka kawo min d`auki,yanzu Daniel so kake kace min ka daina zuwa Church wanne rud`un duniya ne ya same ka,ko so kake ka  ta`bewa ta samu wurin zama a cikin rayuwar ka,me kake so ka zama ?", ta tambaye shi cikin tsananin tashin hankali.
    "Amm mmm...uhmmm.....Grandma ki yi hak`uri ki saurare ni,you know ranar Sunday ita kad`aice ranar da nake samun hutu,shiyasa nake yawan tashi a makare", muryar shi ta raunana sakamakon k`aryar da zai mata ya ciga da cewa," Amm...ammm...amma fa ina zuwa time to time ".
    " k`aryar ka ke Daniel, you are a liar ba ka zuwa Church muryarka ta tona maka asiri,Na shiga uku na ni Deborah, Anya ba sauya min kai a kai ba,haka fa nai ta fama da kai ka zo muyi Merry Christmas tare da kai k`iri-k`iri ka k`i zuwa,har happy new year mu kad`ai muka gudanar da shagulgulan bikinta,,wai meke damunka mene ne ya sa kasauya,me kake son kazama da har ya sauya d`abi'un ka har haka,Daniel ka gayamin asalin gaskiyar da ke faruwa anan ?",ta kai k`arshen Maganar da sigar tambaya cikin nuna tashin hankali da kuma fushin da ta ke a ciki.
      Sai da Abubakar yai da gaske kafin gwarin gwuiwa gami da dakiyar Zuciya ya ce da ita,"I swear ni ba abinda ya canza ni,inayin bauta iyakar iyawata ina zuwa wurin bauta gami da tsarkake ko neman kariyar kaina daga dukkanin wani abun k`i ba lalle sai ranar Sunday ba duk ranar da na samu sassaucin aiki ina kai ziyara zuwa Church ".
    " Hah Daniel ban yarda da kai ba I'm not believing you,you are a big liar,ka kawo min wata hujja guda ɗaya da za ta iya sawa in amince da kai ".
     "Grandma i swear ina zuwa Church, mai zai sa in bar asalina,in bar koyarwa da tarbiyar da ki ka bani ba".
   " To in har haka ne ka tashi  a yanzu ka nufi Church d`in da kake attainding ka had`a ni da wani Pastor ko Reberal to fa sannana ne zan gasgata abinda kake cewa".
    "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un",shine abinda Abubakar ke ta yawan mai-maitawa,yau ya tabbata sharri ko illah da k`aryar ke dashi,a yau ya k`ara tsanar k`aryar da yake mata tun bayyan musulumtar shi,bai san dalilin da yasa yake tsoro da shakar gaya masu ya musulumta ba,ko dan tsoran kar yarasa su  amatsayin su na dangi kuma ahalin da yake da da su akaf fad`in rayuwar sa.
    Idanuwansa da suka rine sukai jajajur ya sauke akan Hibba da tun farkawar ta a barci taga bashi a cikin bedroom d`in ta biyo sa Parlourn, yanayin da ya gani akan fuskarta yasa shi yai saurin d`auke idanunsa akanta.
    Ammon muryar Grandma da ya sake karad`e masa kunnensa ya fargar da shi gami da dawowa hankalin shi akanta," I  repeat it ka tashi ka je ka had`a ni da Pastor d`in Church d`in da ka ke zuwa ko wani wanda zai gamsar da ni in yarda".
   "Shikenan Grandma......shikenan zan je yanzu amma ki sani duk abinda ya faru da ni it's your fault, because i'm felling sick, na dad`e kwance bana da lafiya,I spend almost two weeks bana da lafiya,sai jiya aka sallame ni, na dawo Gida".
    "Jesus Christ amma kuma Daniel shine baka gaya min ba,me yasa kake haka,mai yasa zurfin cikinka yayi yawa,ka ga fad`a min mene ne matakin lafiyar taka a yanzu,ina fatan dai kana samun sauk`i,ka Na dai taking medicine naka akan lokaci ko ?".ta fad`a cikin rud`u
    " Ina samun lafiya in sha Allah tomorrow zan yi resuming a bakin aikina"....
    "In sha Allah kuma Daniel, Na ji kamar haka ka ce ko dai kunne na ne ke jiye min ba dai-dai ba ?".
    A diririce ya ce da ita"I'm sorry ba haka na ke nufi ba,I mean by the grace of God".
    ."A'a Daniel there are something wrong don haka,....hello.... hello".....ta kasa k`arasawa sakamakon mutuwa da wayarta ta yi a dalilin rashin charge.
    Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar ya fad`a gami da kai hannunsa saman kan shi ya rik`e alamun alamun jin zafi ko ciwon da yake ji,cikin sauri ya sake bin layin nata amma kuma yaji wayar a kashe.
   " Ya Salam Allah ka sa ba wani abun sabo Grandma ta ke shirin aikatawa ba da har ya sa ta kashe wayar gabad`aya",shine abinda ya fara fad`a bayan gama kirannata.
"Me ye zai sa ba zaka fad`a ma su ba,ka sanar ma su da Cewar ka Musulumta a bar wannan `boye-`boyen da kuma shiga cikin irin wannan tashin hankalin".Cewar Hibba bayan ta k`araso kusa da shi game da mik`a mi shi Glass Cup na ruwa mai sanyi.
   Bayan ya sha ruwan ne ya bata amsa da cewa," Ina jin tsoro Hibba, ina jin tsoran abinda zai biyo baya, idan har suka san gaskiya zan iya rasa su su duka ban san dalilin da yasa na ke jin  bugun Zuciya a duk lokacin da nai tunanin ko yunk`urin aikata hakan ba,Cecelia k`aramar Yarinya ce,ita kuma Grandma ta tsufa ga shi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba,ina jin tsoran halin da za su shiga idan suka samu wannan labarin".
   "Abu mafi a'ala ka sanar da su sai ka fi samun kwanciyar hankali fiye da ka cigabada da `boye wannan lamarin mai girma a cikin Zuciyarka,ka sani kana tare da Allah, ka Sani dogaro da shi kad`ai ya Isar ma akan komi".
    " Kar ki damu in sha Allah zan yi k`ok`arin aikata hakan,amma yanzu ya jikin naki,ko dai zamu je hospital ne a sake duba jikin ki da na Babyn gudun faruwar wata matsalar ?".
    "A'a kar ka damu na samu lafiya,Doctorn da ya duba ni jiya ma ya isa I'm feeling better now".
    "Anya kuwa na yarda,karda fa unborn d`ina ya samu matsala ",ya kai zancen yana mai d`ora hannunsa a saman cikinta d`an kimanin watannin biyar.
    Yalwataccen murmushi ta saki gami da cewa," Au ta Unborn d`inka kawai ka ke bayan kuma jiya shine ya hana mu samun wadataccen barci ".
    "Shikenan tunda na ga abun naka akwai selfish a ciki,tashi mu je in had`a maka ruwan wanka kafin ka fito na gama had`a mana breakfast tunda Garin ya riga da ya waye"," okay to mu je ".
    Acan `bangaren Grandma hankalin ta a tashe ta kai dubanta kan Cecelia da ke zaune ,ta ca`ba adonta da k`ananan kaya as usual, ta jawo attached d`inta ta d`ora asaman kanta .
    "Cecelia akwai matsala there is a problem, something happened","Matsala kuma Grandma,which kind of problem, shin ko wani abu ya samu Brox Daniel d`in ne ban sani ba ?".
    "Ban sani ba Ceceliar, Something wrong ya faru,gabad`aya Daniel ya janca na rasa gane kan shi ko ku ma a abinda ya ke cikin Zuciyarsa".ta kai zancen muryarta na raunana.
    Kusa da ita Cecelia ta matsa gami da jawota jikinta ta fara lallashin ta da cewa,", It's okay mana,ki bar tashin hankalin ki haka,kin ga ba wata isasshiyar lafiya ce da ke ba kar ciwon ki ya motsa, in Jesus name komi zai dai-daita kin ji".
    " Ameen Cecelia, ta shi mu je Church d`in nan domin so nake in sa ayimin dogon Addu'o'i akan Daniel lamarin sa ya fara bani tsoro,amma ina mai tabbata maki in har bikin Easter ya zo Daniel bai shigo Garinnan ba ni da kaina zan shirya in je har can Kanon Inga halin da yake a ciki,domin ba na tare da natsuwa ko kwanciyar hankali a game da shi".
    "Hakan ma yayi dai-dai, da zaran anfara yi mashi addu'a komi zai dawo Normal.
    Tunda ga wannan lokacin Grandma ba ta sake zama ba kullum cikin yawaita bauta da yin sadaka take akan Jesus Christ ya sa hankalin Daniel ya dawo gare su tayi addu'ar da kanta sannan tasa Pastor ko Reberal yayi,Cecelia ma na iyakar iyawarta.
    Yau Sunday Cecelia ce zaune a k`ark`ashin wata bishi sun fito cin abinci,ta rafka tagumi da duka hannayenta,,k`arasowar Gloria k`awarta ta sa hannunta ta cire mata tagumin kafin ta fara yi mata fad`a da cewa " Haba Cecelia me yake damun ki,what happen,ko kina son ki cutar da kan ki ne ta ya tun kina `yar Yarinyar za ki rik`a jefa kan ki cikin irin wannan dogon tunanin,kin San how long nake tsaye anan ina maki magana amma ko motsin kirki  ba ki ba ?".
    Sai da Cecelia ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita kafin ta fara ce da ita,"Ki yi hak`uri Besty ina cikin damuwane lamarin Brox Daniel kullum k`ara worth yake,kullum K`ara yin nisa daga gare mu yake,yanda kika san Wanda akai masa asiri haka ya koma,ga Maganar Aurena da Samuel sai matsowa take yanzu haka ya kusa six months bai zo inda muke ba".
    A firgice  Gloria ta mik`e tsaye kafin ta ce,"what kina nufin Brox Daniel Wanda na sani ko kuma wani daban ki ke nufi".
    "My friend I'm sorry, da `boye miki wannan lamarin da na yi,Na san halin ki ne za ki tashi hankalinmu, saboda tsananin son da ki ke mashi,Na bari komi ya dai-daita sai in sanar da ke"....
    " It can not be possible, ba zai yiwu ba, I will find him,zan nemo shi a duk inda yake,kawai ki bani address nasa zan je in ga halin da yake a ciki".
    "Kin gani ko dama abinda na guda kenan shiyasa tun da faru ban sanar da ke abinda ke faruwa ba,but please ina so ki kwantar da hankalin ki domin da akwai shirin da muke shiryawa ni da Grandma,by the grace of God komi zai dawo Normal".
    " No no Cecelia bazan iya hak`uri ba kawai ki bani address d`in in je in gani halin da yake a ciki".....
    K`arasowar Grandma cikin hanzari da kuma fushi shine ya dakatar da Gloria game da san amsar address d`in Daniel a gurin Cecelia da ta ke, hannun Cecelia kawai Grandma ta fara ja tana mai bin hanyar da zata kai su Gida, a firgice Cecelia ke binta sai faman tambayarta me ke faruwa take amma ta kasa sanar mata har sai da su ka isa Gida.
    "Wai Grandma me yake faruwa haka naga duk kin tashi hankalin ki, nima kuma kin tashi nawa?".
    Sai da ta fitar da isaka daga bakinta kafin ta sanar da ita abinda ke faruwa da cewa," Yau Pastor ya sanar da ni wani abu game da Daniel wanda ya tashi hankalina,don haka yau ba zan iya rintsawa ba har sai na sa Daniel a cikin idanuna,ba zan runtsaba har sai nayi tozali da shi in my own eyes ".
    " A'a Grandma ma haka ma ba zai yiwu ba, kin san ko k`arfe nawa kuwa yanzu,zamu yi tafiya dare fa kenan? ".
    " Yo meye matsalan a cikin ba dai zamu ruski Garin da ya ke a ciki ba komi dare,mu tafi kawai".
    "A'a ba za ai haka ba gaskiya kin manta k`asarnan yanzu bata da tsaro,taya zamu jajibi tafiya cikin dare alhakin ko inda zamu ba mu sani ba kuma ba mu ta`ba zuwa ba,ga ra dai mu bari sai zuwa gobe early in the morning sai mu tafi".
    " Ina ni ban aminta da wannan tsarin na ki ba a yau zamu tafi ba sai gobe ba","Haba Grandma taya idon ki zai rufe ga gaskiya ina fad`a maki amma kin k`i amincewa,taya garin gyaran wata `barnar zamu jefa kan mu cikin wani halin na had`ari,Na roƙe ki da suansn Yesu mai cetonmu ki bar tafiyatnan sai gobe,in har ba so ki ke wani abun kuma na daban ya same mu ba",da k`yar Cecelia ta samu tai convincing d`in Grandma ta bar tafiyar sai da safe amma ba ta barta ta huta ba har sai da ta had`a masu duk wani abu da ta san zasu buk`ata kafin ya kyaleta,Ai ko Gari na wayewa ko breakfast bata,bar su sunyi ba su ka d`auki hanya sar Garin Kano don sugano me ya ke faruwa da Daniel d`in su.