Page 9
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1
PAGE 9 ❤🔥
"Hankalin ka ya kwanta sai ka zuba ruwa a k`asa ka sha don murna,tun jiya da muka dawo Grandma ba ta iya magana,k`arshe mun tashi ko motsin kirki ba ta iyawa,sannan ina mai sanar da kai an dakatar da maganar Aurena sakamakon jin Cewar ka bar Addinin Crista, don haka kayi farinci ,amma ina so ka sani,ban damu da fasa Aurena da akayi ba amma muddin har wani abu ya samu Grandma ba zan yafe maka ba",tana kaiwa nan ta yanke wayar.
Sosai jikin Abbakar ya fara rawa,bai san sanda ya kai zaune kan kujerarsa ba,kan shi ya d`ora kan desk sai faman buga kan shi akai yake yana fad`in," It's my fault, ni ne na janyo mata shiga cikin wannan halin".
"Ya Salam Manager kana lafiya kuwa,ko wani abun na damun ka ne?".Cewar Abbas Acounter da shigowar shi kenan, kasa iya cewa da shi komi yai,amma tuni idanuwansa sun sauya kala.
"Amm...Amm....ba komi amma ina so zan je Gida,kace ma Buhari Isa ya kirani zan bar mashi sallahu", yana kaiwa nan ya zari car key d`in sa ya fita,cikin k`ank`anin lokaci ya isa Gida,yanayin da ta ganshi kad`ai ya tabbatar mata da ba lafiya ba,da k`yar ta yunk`ura ta tashi tsaye.
"Lafiya na gan ka yanzu,nasan lokacin tashin ka bai ba,kuma kamar kana cikin damuwa ko dai wani abun ya sake faruwa ne ?".
"Grandma ce tun bayan komawar su ba lafiya so shine fa na ke son inje in dubo halin da take a ciki".
" Amma ba kai zai driving ba ko?",har ya juya zai tafi Maganar ta ta dakatar da shi.
Murmushi yak`e ne kwance akan fuskar shi,kafin ya ce da ita,",Kar ki damu I will be fine,zan je in dawo lafiya lau,ki Kira Ummiey Maryam ta sa a kawo maki Jaheed ya taya ki zama ko da zan iya kaiwa dare".
Da to ta amsa mi shi,har bakin gate sai da ta raka shi,tana ji tana gani ya tafi ba dan ranta ya so ba,ta so ko da motar haya ne ya hauwa amma ina bai amince da hakan ba,haka ta ja k`afafunta ta koma cikin Gidan tana mai nemo wayarta ta Kira Ummie Maryam domin ta sa a kawo mata Muhammad Jaheed d`in domin ba zata ji dad`in zama Gidan ita kad`ai ba.
Cecelia kuwa hospital takai Grandma, bayan an admitting d`inta an yi mata duk abinda ya kamata ta dawo ta tasa ta sai faman kuka ta ke, tsoranta d`aya kar Grandma ta mutu ko ta samu wata matsalar,domin in hakan ta kasance bata san ina zata sa rayuwar ta ba,duk da kasancewar suna rayuwa tamkar `yan'uwa da `yan unguwarsu da kuma mutanen da suke halartar Church guda d`aya, amma ba ta da kamar Grandma da kuma Broth Daniel,duk da Cewar shi ma ba ya tare da ita,''Broth Daniel ka cuce ni idan har ka zama sanadin faruwar wani abu ga Grandma to ba zan ta`ba yafe maka ma".
Motsin shigowa cikin room d`in da ta ji ne ya sa ta saurin d`ago da kanta ,Gloria ta gani hakan ya sa ta ƙara k`arfafa kukanta,da sauri ta k`araso ta na mai lallashin ta,"I'm so sorry my friend na ji abun bak`in cikin da ya same mu ki yi hak`uri ki bar kuka haka kar wani ciwon ya same ki''.
"Gloria ki barni dole ne in yi kuka,Samuel ya guje ni,tun bayan dawowar mu a jiya da mutane suka samu labarin abinda ya faru,Mahaifin shi da kan shi ya kira shi ya dakatar da shi,wai tunda d`an'uwana ya bar Addini ni ma wata rana zai iya rinjayata in bar Addini don haka ni ba Matar da ta dace ya aura ba ce,tunda Grandma ta ji wannan labarin bata k`ara cewa uffan ba,zuwa da safe ko motsin kirki ba ta iya yi".ta kai k`arshe zancen ta na mai sake fashewa da kuka.
"Na samu labarin komi Cecelia shiyasa ma na zonan,nayi kaico kuma nayi mamakin abinda Broth Daniel ya aikata unfortunately ban ta`ba tsanmanin haka daga gare shi ba,Dan haka ki yi hak`uri,komi da ki ka ga ya faru it's about destiny,kafin in zo nan mun yi magana da Daddy na yace in baki hak`uri zai zauna da Dadyn Samuel sannan ya na son ki had`a shi da Broth Daniel d`in zai yi mashi wa'azi ko da za a samu ya dawo cikin hankalin da natsuwarsa".
" Kai..kai ...Gloria I'm so happy Na ji dad`in wannan magana taki ,thank you ban dan da wanne irin baki zan gode maki ba".
"Kar ki damu Cecelia wannan ai duk yi ma kai ne,kin san fa irin yanda na ke son Broth Daniel, Na kwallafa raina akan shi,ba na jin zan iya rayuwa ba tare da shi ba,zan yi iya yina na ga mun dawo da shi kan haya madaidaiciya".Nam fa Gloria ta cigaba da lallashin ta har ta samu ta ci wani abu cikin abincin da ta zo da shi.
Shi kuwa Abbakar sai wajen Magaribha ya iso Jos sai da ya tsaya ya sauke sallolin da su ke akan shi sannan yai sai duk abinda ya ke ganin zasu buk`ace shi sannan ya Isa hospital d`in da ya ke tunanin ko tabbacin can Cecelia zata kai Grandma, san da ya Isa bai sha wahala ba a ka kai shi d`akin da a ka kwantar da su,Cecelia ya iske ta d`ora kanta kan gadon da Grandma take, barci ya kwashe ta a haka hannunta d`aya na rik`e da da hannu Grandma,kamar mai jin tsoran wani zai kwace mata ita,sosai ta ba shi tausayi ,gefe guda ya samu ya zauna ba tare da ya yi wani motsin da zai tashe su ba,ganin da gaske barcin ta ke ita kuma Grandma an sama mata drift yasa ya shigar da duk abinda ya zo da shi ya nufi office d`in Doctorn Dan yasan me yake damun Grandma d`in da har ta shiga cikin wannan halin.
Sosai ya samu kwanciyar hankali bayan ya samu gamsasshen bayani daga bakin Doctor d`in ,"Kar ka damu stress ne ya jefa ta a cikin irin wannan halin amma za ta samu lafiya da izinin Allah,zamu sake dubata zuwa gobe daganan sai mu ba ku sakamakon na k`arshe ",wannan shine batun da Doctor yai masa na ƙarshe.
Bai sake komawa Room d`in ba har sai da ya gabatar da Sallahr magariba, lokacin Cecelia ta farka daga nannauyan barcin da ya sace ta,sosai ta rink`a mamaki kayan da ta gani an shigo da su,ganin Abbakar ya shigo cikin d`akina yasa ta d`aure fuskarta gami da kauda kanta gefe alamun bata ma son ganin shi.
" Me ya sake dawowa da kai ,ko ka zo ne k`arasata kamar yanda ka d`auko hanya ne ?".
"Shut up Cecelia na gaji bana son wad`annan k`ananun zancen , ki bar komi ya wuce,I have my own right to do any religion that I want,don haka ki bar ni,Na zo nan ne domin Grandma ta samu lafiya Dan haka bana buk`atar wani sabon tashin hankalin".
Ganin da gaske yake yasa ta ja bakin ta tai shiru,suka cigabada da zaman kurame,shi ya cigaba da yi ma Grandma duk abinda akace ayi mata,duk bayan wani lokaci zasu rik`a motsa mata hannu da k`afafunta don gudun paralysis ya same ta.
" Ki tashi ki tafi Gidan su Gloria ki kwana ni zan kwana da ita anan",shine abinda Abbakar ya ce da ita, ta so tayi ma sa musu amma ganin ba fuska ya sa dole ta hak`ura,ta d`ebi kayan abincin da Glorian ta zo da su ta tafi da su.
Lokacin da ta Isa Gidan su Gloria ta sanar da ita zuwan Daniel ba k`arami Murnar da mamaki ta yi ba, har Allah Allah take Gari ya waye su je hospital d`in ta gan shi,ta sanya shi a idonta ko ta samu sauk`in daga irin nauyin da Zuciyarta ta ke yi mata akan son shi.
Sai dai kash tun kafin su tashi a barci Mahaifiyarta ta yi masu knocking akan su tashi.
" Lafiya Mom za ki tashe mu tun yanzu ?", Gloria ta tambaya da alamar barci akan fuskarta,"Surprise Dadyn ki ya shirya maki".
Sai da Gloria ta `bata fuska kafin ta ce,"Surprise kuma wanne irin surprise ? ",.
My daughter ya Na ga fuskar ki haka kamar ba ki farin ciki da abinda ma fad`a maki ba ?".
" Ba haka bane ba Mom kawai da akwai inda na ke son zuwa early in the morning d`innan that's why ".
" Ayyah my dear hakan ba zai yiwu ba domin yanzu haka Mota na waje na jiran mu,go back and fack your thing zamu bar Garin Jos yanzu"...."What!....za mu bar gari mu je ina,yaushe aka yanke wannan hukuncin?".
"Oh ki kwantar da hankalin ki,domin Mahaifinki ne ta samu matsayin Pastorn a wani Babban Church d`in da suka gama Ginawa yanzu haka yau za a gudanar da bikin bud`e Church d`in shi yasa ya aiko da Mota a d`auke mu a kai mu Airport domin mu samu Isa Lagos d`in don mu samu halarta bikin".
"A'a Mom.. No ....hakan ba mai yiwuwa bane ba,ni babu inda zanje,ina da wanda nake son gani a yau ba zan biki ba"....
"Kema kin san baki isaba babu inda za ni ba tare da ke ba,koma meye ki bar shi sai wani lokacin ,idan kuma kin musa,min a haka da sleeping dresse d`in zamu tafi da ke".
Hankalin Gloria ya yi matuk`ar tashi yai ba, ba shiri ta nufi inda Cecelia take zaune ta rabka uban tagumi ta ce da ita," I'm so sorry, Na so ace tare da ni zamu yi fighting d`in wannan battle d`in da ya tun karo ki sai dai kash hakan ba mai yiwuwa bane ba, ina mai baki hak`uri akan haka,tafiyar gaggawa da ta kamani zuwa Lagos mun koma can da zama gabad`aya da family na,sai dai ki sani a ko ina nake ina tare da ke,zan baki goyon baya hundred percent akan mu dawo da Broth Daniel kan hanyar da ta kamata,zan tafi ba dan na so ba".
Haka suka tashi jiki kowa a cikin su a sanyaye ,Cecelia ba ta tafi hospital ba har sai da taga tashin su Gloria kana ta juya ta tafi tana mai share hawayen kewar k`awa ta Gari da tai yi,k`asa hak`uri Gloria tayi har sun fara tafiya ta dakatar da driver d`in da gudunta ta dawo baya tana mai kwalama Cecelia kira,cike da mamaki ta juya tana mai tambayarta.
"Lafiya Gloria na ga kin dawo?",Gloria na mai da hakin gudun da ta yi ta bata amsa da cewa," Komi lafiya ina son in baki sak`o wajen Broth Daniel ki fad`a masa har yau har gobe ina son shi,ina jin shi a cikin raina, Zuciyata ba zata samu salama ba har sai na ganni a matsayin Matar shi,ba zan huta ba har sai na ga hakan ta kasance,I promise I will be back soon zan dawo saboda Soyayyar shi,shi shi kad`ai ki gaya mashi hakan".tana kai wa nan a zancenta ta juya da d`an gudun ta ta koma motar su ka tafi Mahaifiyarta ma ta yi mata mitar tsaida sun da tayi amma ita ko a jikinta.
Ba k`aramin mutuwa jikin Cecelia yai ba sakamakon jin abinda Gloria tace,wannan wacce irin Soyayya ce,da har za ta bari ta makantar da ita har haka shin ko ta manta yanzu ba addinin su d`aya da Broth Daniel ba ne ba ko me?",abubuwa da dama suka cigaba da kai kawo a cikin rai da Zuciyarta kafin daga bisa ni ta watsar da su ta cigaba da tafiyata zuwa hospital d`in da Grandma take kwance.
Sanda ta Isa duk wani abu da ya kamata ayi ma Grandma anyi mata hatta da wanka yasa Nurse d`in asibitin sun yi mata,nan haka suka cigaba da jinyar Grandma har na tsawon kwana biyar tun Cecelia Na jin haushin shi har ta fara ragewa,domin ba abinda ya rage daga kulawar da yake ba su sai ma abinda ya k`aru,kuma zaman shi a tare da su bai sa ya daina ko rage na shi Addinin ba,har mamakin k`arfin halin shi take,tsakanin shi da Hibba kuwa sai dai waya tuni an kawo mata Muhammad Jaheed shi ke taya ta hira.
Ranar da suka cika one weak ranar Grandma ta farka,ita kanta ta yi mamakin ganin shi tsaye akan duk lamarin ta ,duk wani abu da ake so ko za a buk`ata shi ake tambaya, ba musu kuwa zai je ya kawo shi,da kallon mamaki kawai ta ke bin shi da shi har daga k`arshe ta ce da shi,"Daniel ina cikin mamaki na sha canja Addini da kai zai sa ka guje mu ka wofintar da dukkan lamarin mu ashe ba haka bane ba, kawai Zuciya da tunanina ne su ke ba ni hakan".Grandma ta fad`a cikin muryarta ta marasa lafiya.
"Haba Grandma ta ya za ai in aikata hakan ba fa ni da wasu ahali da ya wuce ku, me zai sa in guje ku,ina son ku ba zan iya barin ku ba ,kamar yarda na ke son Addini na ba zan iya barin sa ba".
"Shikenan Daniel indai haka ne na yarda ka cigaba da bin Addinin da,kake so amma Na rok`e ka kar ka barmu,kar ka sauya mu a matsayin ahalin ka.
"In Sha Allah ba zan aikata hakan ba,ni ban k`i ba ma ku shirya mu koma can Kanon da ku,mu yi rayuwar mu a tare a can"...
Ta katse shi da da cewa," A'a ni babu inda zani nafi son in k`arasa `yar sauran rayuwata a cikin wannan Garin tare da `yan sauran k`awayena da suke Raye,muna daga nan zan dunga yi maka addu'a da ga kai har Matar ta ka".
"Dan Allah Grandma ki daina fad`ar mutuwar nan ba yanzu ba ina son har `ya`yana da na Cecelia sai kin gani".
" Kayya dai d`annan a haka ma ai mun sha miya,sai dai mu jira mutuwa kawai yanzu,damuwata d`aya a yanzu shine bazan ta`ba iya kama hannun d`anka in tafi Church tare da shi ba,ba za ka ta`ba iya haihuwar `ya`ya kasa sunan mamarka,ni ko babanka ka ba shine kawai damuwata.
Cecelia ce tai saurin amshe batun da cewa,"Kar ki damu Grandma ni inna haifi yarana zan sa sunan ki har da ma sunan su Dad".
"Kai na ji dad`in haka my dear Allah yasa in ga `ya`yan naku gabad`aya".
''Yauwa Grandma ki K`ara kwantar da hankalin ki hatta da Maganar bikin Cecelia zan yi k`ok`ari in ga na dai-daita ta kafin intafi,kin ga Doctor ya ce ba zai sallame mu ba har sai ya ga kin samu lafiya sosai da sosai".
"Kar ka damu Yarona indai don wannan ne komi zai koma normal",haka Abbakar ya cigaba da jinyar Grandma sai da yai kwana goma kafin ya koma Kano, gaba d`aya ya raba hankalin shi Gida biyu yau ba shi Kano gobe ba shi Jos,sosai ya fita cikin hayyacinsa har Rama sai da ya fara ,bayanda za ai ya bar ma Cecelia jinyar Grandma ita kad`ai hakan ya sa dole yake go and come d`in ,ya kan yi aikin shi a system ko da yana can Jos d`in ,Grandma tafi wata kwance a asibitin hakan ya sa ya maida Hibba Gida ganin Month d`in Edd ta ya kusa shi kuma ba mazauni ne ba, sosai jikin Grandma d`in take samun sauk`i hatta fara tafiya amma da taimakon k`arafa hakan ya fara sa hankalin su ya kwanta ita kanta Grandma d`in har tausa Abbakar d`in take gani irin fad`i tashin da yake duk akan su.