Page 10
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
***
***
BOOK 1
PAGE 10 ❤🔥
FREE PAGE
"Yauwa Yarona d`an Albarka Na gode sosai, in sha Allah za kai albarka".
Sai da ya washe bakin sa alamun yaji dad`in Addu'ar da tai mai kafin ya ce da ita," Momynah na k`agara in ga kin haihu,na ga d`an k`anina da za ki haifi min mai kama da ni".ya kai zancen ya na mai cigaba da matsa mata k`afafunta.
Sai da Hibba ta zaro idanunta waje kafin ta ce,"Kai Muhammad Jaheed Namiji kuma ka ke son in haifa,ina laifin ka ce in haifa maka yar Mace,wacce za ka rik`a kama hannunta ku je makaranta, wacce za ka rik`a tayawa Home work, wacce kuma za ka tsaya kai da fata wajen ganin tayi ilimin Addini da na zamani,ka zama bango kuma gatanta,ka cike mata sauran gurbin Ahali da ta rasa",ta kai k`arshen zancen muryarta a raunane.
Duk da k`arancin shekaru na Jaheed sai da maganganun Hibba kuma Momynsa suka sa jikinsa yai sanyi,"Shikenan Momynah da ga yau zan rik`a Addu'a Allah ya sa ki haifo mana Baby girl,zan kama hannunta mu tafi ko ina,duk inda zani tare da ita zani,ba zan bari wani Namiji ya shiga cikin rayuwar ta ba balle har yasa ta Kuka,zan kasance mai aikata komi dumin ita,kuma ni zan za`ba mata suna",ya d`an yi shiru kafin ya cigaba da cewa,"Amma fa dole ta rik`a ce min Yayah ko tunda na girme ta ko?".ya kai k`arshen batun cikin sigar yarinta.
Sai da Hibba tai dariya kafin ta bashi amsa,"Ba dolenta ba Jaheed, ai dole ta Kira ka da Yayanta,kasan akwai tazara ta wajen shekara Goma a tsakanin ku,ka kenan dole ta girmama ka".
"Yehhhhhh Na ji dad`i tunda nima na kusa zama Babba".
" Yau to bar k`afar haka naji ta yi min sauk`i yanzu taho mu ci abincin da ka kawo min","A'a ki ci naki ne ni na ci nawa,kuma ni bana jin yuwa"....."Shhhhhh rufa min baki,sai ka ci shi,ki baka ga abincin da yawa bane ba ai nasan irin Cin abincin naka dan haka ha bud`e bakin ka".
Sai da Jaheed ya saki murmushi kafin ya bud`e baki ta fara sanya mashi abincin a baki,a cikin Zuciya da Idanunsa kuma ta na k`ara samun k`ima da matsayin mai girma ya rasa wanne irin so,k`auna da kulawa ta ke ba shi,a lokacin da tai Aure ba sa tare ba k`aramin kewa da rashin ta yai ba,ta kan ba shi muhimmanci fiye da dukkan wani abu ko kuma ita kanta,takan `bata lokaci mai tarin yawa don ganin kawai ya yi farin ciki ko nishad`i,ta fi kowa sanin shi da kuma fahimtar halayen shi,ko wannan abincin yasan za ta iya cinye shi har ma ta nemi k`ari amma saboda yana tare da ita ba zata iya cin shi ita kad`ai ba,dole sai sun ci tare,haka ta koma yanzu bunu-bunu ta nemi abinci,ba su wani d`au lokaci wurin cin abincin ba ya mik`e ya ce mata ya k`oshi.
"A'a ba ka isaba dawo zauna sai mun cinye shi tare".
" A'a ni kam ba zan dawo ba na k`oshi,wannan abinci ai sai dai ke ni yafi k`arfina in ba so kike nan gaba kad`an a kasa banbance ni da ke in zama Orobo kamar ke".
Yanayin yanda ya ga ta zaro idanu waje ne yasa ya fara dariya gami da k`ok`arin barin wajen da gudu,"Au guduwa za kai to wallahi Inanan ina jiranka za ka dawo ka same ni ba dai ni kake kira da Orobo ba,zamu had`u ai,inna kama ka za ka basu labari".ta na zancen da fara'a kwance akan saman fuskarta.
"Ah aha,su Hibba ne zaune anan Ana hutawa?", Cewar Baba Asabe cikin yanayin izgili da k`arasowarta wurin kenan.
Murmushin yak`e Hibba ta saki kafin ta bata amsa da uhm.
Bayan ta samu wuri ta zauna ne ta ce da ita," Ananan Ana ta zuba ma ciki lodi ko,ni na rasa wanne irin Aure ne wannan ki ka yi, kin tafi kamar ba ki tafi ba kullum kina cikin Gidannan, wai me ye matsayin da ma'anar wannan Auren,shin mijin na ki gajiya yai da ke ne ya maido ki Gidan ku ko ko sakin ki yayi,ko dai ya kasa d`aukar nauyin d`awainiyar ki ne da ta ke abinda ya ke cikin ki,domin na ga alama shi kan shi da za a bashi dama da cikin Gidannan zai dawo ya tare,shin ahalin su ba su da Zuciya ne komi?"...
Kamar an jeho Ummie Maryam haka ta shigo cikin Parlourn tana mai fuskantar ta da cewa,"Haba Baba Asabe wannan wacce irin magana ce,ta ya za ki zo gabanta ki titsitsiye ta da irin wannan zafafan tambayoyin,ai hakan bai dace ba kuma bai kamata ba".
"A kamarya bai dace ba,a tunanin ku Dan ku kun Gaza gaya mata gaskiya sai muma mu taru mu zuba mata ido,dole ne mu gaya mata gaskiya, taya mace da Gidan Mijin ta zata dawo zama Gidan iyayenta,gabad`aya ci da shanta har ma dana Wanda ta ke ikirarin Mijin ta ne yana cikin Gidannan,me hakan yake nufi shin ta zama sakakkiya ne ko kuma ya nuna gazawarsa akan ta ne a fili,kullum tana zaune k`ark`ashin bishiya bata aikin fari balle na `baki daga ta ci sai tai kashi,ko da yake duk wanda ya k`i cin biri ya ci dila,haka kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho,ayi dai mu gani domin tafi-tafi takardar sakinta za ku ga ta biyo baya ,ko kuma wata rana ku wayi gari ya gudu ya barta"....
''Wa ya gaya ma ki haka zata kasance da ita,ko angaya maki kowa ke da bak`ar k`addara irin ta ki Asabe", Cewar Mama Hadiza da fitowar kenan daga sashen ta hannunta d`auke da jik`on maganin da take baiwa Hibba Dan samun sauk`in nak`uda.
A kid`ime Baba Asabe ta waigo jikin ta har yana rawa," Hadiza me kike nufi da wannan kalaman naki a gare ni ?''.
"Oh baki gane ba,to bari in yi maki dallah-dallah yanda zaki gane shin kin manta nan Gidan ba Gidan Mijinki ba ne ba Kema Gidan iyayenki ne,Gidan da ki ke zaune tsawon shekaru Ashirin da wani abu tun `yar ki da kuma d`an ki na da `yan shekaru,shin ko kin manta da hakan ne,ke yara biyu ki ka zo da su ,Na rasa me ma tsare mi ki a cikin Gidannan Asabe, shin nayi maki wani abu ne wanda na can-canci wannan cin kashin da ki ke min,ba ki da wani abu sai dai son ki ka ga kin bak`anta min da ni da `ya`yana me na tsare miki dan Allah ?".
Hawaye Baba Asabe ta sharce muryarta Na fidda sautin kuka ," Yanzu daga na zo fad`a ma `yarki gaskiya sai ki bi bayana da sharri da kuma gori"....
"A'a Asabe k`aryar kike ba gaskiya ki ka zo faɗa mata ba,kin zo ne ki yi abinda kika saba sai kuma reshe ya juye da mujiya".
" Mama dan Allah ki k`yaleta ki zo mu tafi,ki bar kula ta ",Cewar Hibba hawaye ma zuba daga idonta.
" Babu inda zani don banga dalilin da zai sa in barta ta cigabada da cin kashi a kaina ba,iya Wanda tai a baya ma ya Isa".
"Aiko dai maganar ki gaskiya ce Yaya ai Baba Asabe bai kamata ace ita ce ke furta irin wannan laffuzan ba,ita ma Hibba matsayin `ya take a wurinta bai kamata ta fad`i munanan kalamai akanta ba", Cewar Umma Jamila.
Umma Hafsat ce ta amshe zancen da cewa" Anya kuwa kun fahimci lamarinnan dai-dai kuwa,ni a tunani na gaskiya Baba Asabe ta fad`a, shin mene ne aibun zancenta anan,ku duba fa ku gani kaf Gidannan ba wata d`iyar da aka haifa a cikin Gidannan da tazo tai irin wannan zaman da take"....
Umma Maimuna ce ta matso tana mai gyara d`aurin zanin jikinta tana mai cewa"A'a a'a Kema kin so rashin gaskiya tun farko Yaronnan sai da ya baku uzirinsa,wacce ta ke matsayin mahaifiyarsa ce bata da lafiya,kuma ba a wannan Garin take ba,ita kuma Hibba tana buk`atar kulawa,ta na buk`atar wani a kusa da ita,shi kuma ba shi da kowa anan kuma ba mazauni ne ba,ko kun fi so ya barmu `yar ku ita kad`ai a Gida duk abinda zai same ta ya same ta,shin haka ne manufarmu ku ko wani abu na daban ?".
"Bar su kawai su fad`i duk abinda suke so ,amma ina so su kwana da sani Hibba ba inda zata har sai bayan ta haihu, maganarsu kuma ba abinda zata sa ko ta hana", Cewar Mama Hadiza ran ta a `bace.
Ummie Maryam ce ta matso kusa da ita tana mai cewa," Dan Allah Mama ku bar wannan maganar haka a barta ta wuce,babu dad`i ace a Gidannan ake wannan hayaniyar, bai kamata ba",
Tunda su ka fara wannan hayaniya Hibba ba ta iya cewa komi ba sai faman zubar da hawaye kawai ta ke,ita kanta ta rasa me tayi ma Baba Asabe da har ta tsane ta haka ko dai don rashin Auren d`anta da ba tayi ba ne ba oho.
Shigowar Baba Malam ne yasa rikincin ya kwantawa bayan ya ba Baba Asabe rashin gaskiyar abinda ta aikata, kana ya sallami kowa ya bar gun,Ummie Maryam ce ta tafi da Hibba d`akinta tana lallashin,gami da janta da hira ko da wasa ba ta bar ta ita kad`ai ba balle har ta samu damar tuna abinda ya faru ko barin shi a ranta.
*Bayan wasu kwanaki*
"Gaskiya wannan tafiyar ta ka ta yau tayi sauri ka iso da wuri".
"Na ta so da wuri ne,saboda ina son in yi shearing d`in happiness d`in da na samo tare da ke"," Masha Allah na ta ya ka murna tun kafin inji me muka samu".
"Grandma ta samu sauk`i an sallameta yanzu haka suna Gida ita da Cecelia ,tana tafiya da k`afafunta ba tare da taimakon k`arafa ba", ya kai zancen fuskarsa na washewa da mad`aukakin farin ciki.
" Kai Alhmdllh Masha Allah wannan labarin yayi dad`i,ko ba komi hankalin mu gabad`aya zai kwanta tunda Grandma ta samu sauk`i komi zai koma normal ".
" Sosai ma wani k`arin abun farin cikin na yi magana da Mahaifin Samuel wanda zai Auri Cecelia mun sasanta yanzu ya yarda za ai bikin su nan da wani lokaci".
"Ikon Allah wannan shi ake kira da dad`i kan dad`i ga Grandma ta warke kuma ga shi za ai Auren Cecelia ba abinda zamu ce da Allah sai Godiya mara adadi domin hakan duk kad`an daga cikin iko,buwaya,k`udira da kuma izininsa".
" Haka ne my wife nasani shi kad`ai ke da iko gami da izinin aikata abinda ba kai zato da tsanmani ba,domin a cikin mu babu Wanda yai zaton Grandma zata sake taka k`afafunta, haka kuma babu wanda ya sa ran Mahaifin Samuel zai sauko ya yarda ayi Auren d`ansa da Cecelia kasancewar sa mai tsananin lafiya akan duk abinda ya ce,amma sai gashi Allah ya tankwasar da Zuciyarsa har ya amince da za ai Auren ".
" Haka ne gaskiya domin ni kaina yanda kake bani labarin yanayin yanda yake behaving in ka je masa da maganar dai-dai to a tsakanin ku abun har tsoro yake bani".
"Wallahi kam,hakan ba k`aramin imani ya k`aramin min ba"," Ai haka ake so,duk abinda ya faru da kai a rayuwa ba hakanan banza ya je zuwa ya tafi ba, dole akwai wani darasi da ake so ka amfana da shi,walau darasi mai kyau ko kuma akasin sa".
"Amm na kwaso gajiya ya kamata in zo in tafi, 9pm kar dare yai min sosai"," To shikenan my darling husband Allah ya tsare min kai ".
"Amen amma kin san me ?", ya cigaba batare da ya tsaya ba," Ji nake kamar kada in tafi ko dai zaki shirya mu tafi can Gidan mu mu kwana tunda kin ga Gobe Sunday,in ya so sai in dawo da ke ranar Monday early in the morning".
Zazzaro Ido waje Hibba tai kafin ta ce da shi,"Ni dai babu ruwana ,ko ka manta Kaine ka kawo ni ka ce sai bayan na haihu zamu koma","To mene ne Dan kin je kin kwana d`aya ko biyu kin dawo Gidan ki ne fa can inda zamu".
"Wannan ai rashin kunya ce taya ma zan iya fuskantar Mama da irin wannan Maganar kai ko Ummien Jaheed ba zan iya tunkara da irin wannan zancen ba".
`Bata fuska yai alamun bai ji dad`in abinda ta ce ba ya ɗora da cewa," To shikenan na hak`ura tunda haka ki ka ce ya zanyi, I don't have anything to say tunda haka Macen da nake kira da My Woman ta za`ba min".
Sai da Hibba ta kama hannunsa ta rik`a kafin ta fara bashi hak`uri, "Bayanda zan yi ne abun na da nauyi ne sosai fiye da yanda za kai tunani,ko ka manta we are Hausa Fulani people an sanmu da kunya fa".
Murmushin gefan baki yai kafin ya ce," one day it may kill you,this shame ba hmmmmmmmm it may kill you,in dai zaki cigaba da biye ma wannan k`ananun abubuwan na ku".
"Hhhhhh ba abinda zai same mu, ai halayya da d`abi'u ne masu kyawun gaske".
" Raba ni da su,ba gasu a ta dalilin su ba ,za ki bar Mijin ki cikin kewa da kad`aice ba,kuma alhalin ko ke nasan kina son Mijin ki tunda gashi na gani a idon ki".
"Lah...lah..lah ni dai ban ce ba,yaushe ma na fad`i haka?"," Kin fad`a mana ni naji da kunnuwana","Na fad`a kuma a yaushe ?"," Kin fad`a mana","Ni dai wallahi ban fad`a ba","kin fad`a mana","A'a ban fad`a ba".
Rau-rau tayi da idanunta ganin dagaske yake,"Kin ga I'm sorry da wasa nake maki ba ki fad`a ba ni ne na fad`a",Sai da ta kai mashi duka kafin ta ce da shi ni ba ruwana sa kai tunda haka ka koma ",ta kai zancen tana mai mik`ewa tsaye.
" Haba Haba ke kaman taya za ai kice baza ki yafe min ba kefa Mace ta Gari ce fa","Hmmmmmm Na gano ka dad`in baki ko, to ba za ai hak`urin ba","Haba ni ne fa kuma ina wani laifi don Miji yayi ma Matarsa dad`in baki ?".
"Hhhhhh shikenan naji sarkin wayo Na hak`ura mu je in raka ka kar da kayi dare"," To mu je tunda kora na ki ke.
Sai da Hibba ta ja gefe guda kafin ta ce,"Ya Salam wai yaushe ka koma haka ni ban sani ba".
"Afuwan kar ki ce kin fasa raka ni,mu je na tuba".
Kamar ta ce da shi wani abu kuma sai ta fasa ,amma sai dai me ko da wasa ta kasa iya d`aga k`afarta guda.
Yanayin yanda ta fara yamutsa fuskarta ne ya sa ya tambayeta,",lafiya me yake damun ki,ko kina jin wani ciwo ne".
Kafin ka ce me tuni Zufa ta rufeta da k`yar ta iya sanar da shi abinda yake damun ta," K`afata,marata Na kasa ita tafiya".
"Innalillahi, mai ki ke so,me zan miki, da me zan iya taimaka miki",gaba ki d`aya duk ya rud`e.
Ka kira min Ummie Maryam ko Mama kai ni ko wa ma zaka Kira ka kiramin "..
A ruɗe gami da sauri ya fito,Allah ya tai make shi ya na fitowa ya hango Ummie Maryam ta taso k`eyar Jaheed daga wajen Mama Hadiza, tun d`azu take neman shi ya zo ya kwanta ashe yana can ya addabi Mama Hadiza.
" Lafiya nagan ka a cikin irin wannan yanayin ","ba lafiya ba Hibba ce....Hibba ce ban dan meke damun ta ba".
Kafin ya k`arasa magana tuni Ummie Maryam ta kai cikin d`akin,sanda zau shigo d`akin har ta kamo ta jikinta,"Ka ga maza je ka fiddo motor Haihuwa za tai,dama tun ɗazu na kula da ita,sai faman yamutsa fuska ta ke,amma da na tambaye ta sai ta ce min ba komi".
Ko da ya fita daburcewa yai kamar Wanda ya manta hanyar fita Gidan,inda Allah ya taimake su ,tun kafin su je ko ina nak`udar tai tsamari bayan wani lokaci ta haihu a cikin Gida ba tare da sun je asibiti ba,ta haifi `yarta mace,zo ka ga murna bakin mutanen Gidan,karma Muhammad Jaheed da gani yake kamar shi kad`ai akai ma haihuwar.
Sai washe gari sannan Abbakar ya samu damar ganin Babynsa sosai da sosai, sosai ya zuba ma ta idanu sosai yake jin sonta na k`aruwa a cikin Zuciyarsa shi har wata ajiyar Zuciya yake.
"Lafiya na ji kana ajiyar Zuciya sai ka ce wanda bai ta`ba d`aukar Baby ba "," Na ta`ba d`aukar Baby mana amma irin wannan ce ban ta`ba d`auka ba,idan na tuna wannan `yata ce sai inji kamar ba wani wanda ya kai ni samun kyauta mai girma ,wacce ta can-canci alfari a duniya sama da ni,Na kan k`ara gode ma Allah game da bani wannan kyautar da yai wacce ba kowa ya ke baiwa ba".
Hibba kam ba abinda ta ke sai binshi da kallo fuskarta d`auke da murmushi,"Kin ga matso mu gani cikin ni da ke da wa take kama".
"Hmmmm wannan d`iyar taka na rasa da wa taje kama ga dai mutum nan amma ban san da wa take kama ba,Na ga dai hancin ta kamar irin naka ne","Uhmmm haka ne idanuwanta ta kuma irin na ki ba".
Dariya Hibba tai kafin ta tambaye shi da gaske ya ke," Da gaske na ke, k`ara kallon ta ki gani,kin gani shape d`in sa iri d`aya ne",cikin murna Hibba ta sake zuba mata Ido kafin ta ce,"Lah wallahi haka kuwa,to bakin ta kuma na waye ?",su duka biyun suka sura mata ido don son gano bakinta kuma irin Na waye.
Hibba ce tai zaraf ta ce,"Irin Na Cecelia ne",sosai Abbakar ya zaro idanun sa waje tare da ambaton Cecelia kuma? "Eh mana kalla ka gani".
" Ta`b indai haka ne kina da aiki tun wuri ki mata nasiha kar ta biyo halin Cecelia because she so disturbant, bata jin magana ga tsiwar tsiya".
"Ai Kaine zaka ji da ita in ta tashi tsiwar ta ta"," I'm out babu ruwana a ciki","Hmmmm da ruwanka kai ba ma ruwa ba har ma da tsakinka akwai,kasan me ?".
" A'a sai kin fad`a","Jaheed na rok`on alfamar ka bar shi ya za`ba mata suna","Wannan ai ba wani abu ba ne ba,ya za`ba mata in ya so sai ai mata hud`uba da shi ".
" Kai amma na ji dad`i Na gode sosai ban San da wanne baki zan iya nuna maka irin yanda na ji dad`in wannan alfamar ba, domin jiya da ya zo ya iske ana mata wanka ya ga tawada a tsakiyar babban yatsanta na k`afarta ta dama murna yai tayi wai da shi take kama tunda shima yana da tawadar".
Dariya Abbakar yai yana mai cewa,"Kin can-canci fiye da haka a gare ni shikuma Muhammad Jaheed wannan Babyn tashi ce,in yace ba mai ta`bata sai shi ai ta zauna,tunda na ga kusan tare da shi akai d`awainiyar da cikinta shima ya zama babban Yaya ".
Haka dai suka cigaba hirarrakin su Wanda rabi duk akan Babyn ne da kuma shieye-shiryen ranar sunanta .
Sosai Hibba da Babynta su ke samun kulawa daga wajen kishiyoyin Mahaifiyarta da kuma Ummie Maryam hatta da matan yayyanta ba a barsu ba,hatta da Yayanta Nasir wanda daga shi sai ita,da ke karatu a Kaduna sai da ya zo ganin baby.
Ranar suna Baby ta ci suna *JADEEDA*,lokacin da aka kai Babyn ayi mata askin suna ne Baba Asabe ta bi su ta sa Wazamin yai mata tsagar Gidan ta rumanci wato eleven eleven,sanda aka dawo da ita sai faman canyara kuka take.
"Hibba na ga Babynnan kamar anyi mata tsaga ?", Cewar Anty Na'ima Matar Yah Mustapha ta biyu.
" Tsaga kuma akan me za ai mata tsaga in ba neman fitina da tashin hankali ba,to wai wama yasa akai mata tsagar,tsagar da tun-tuni Baba Malam ya hana ya ce haramun ce".Cewar Yayah Hanne ta na mai tambayar Jidda da ta shigo da ita.
"Ni dai babu ruwana Baba Asabe ce ta sa ayi mata wai ai ba ta da dangin Uba gara a rufa mata asiri a yi mata tsaga hakan zai sa a rik`a zaton ko `yar wannan ahalin ce".
"Mene!? aiko yau ba zan kyake Baba Asabe ba,don naga abun nata k`ara cigaba yake,ta ya meye had`in ita wannan Yarinya da wata tsaga,ba fa Mahaifinta aka haifa a cikin Gidannan ba Mahaifiyarta aka haifa fa,yanzu me ki ke tunanin zai faru idan Abbakar d`in ya gani nasan ran shi ba zai so ba".
" Kin ga Yayah Hanne dan Allah ki k`yaleta tsaga dai an riga da anyita,ba kuma zata gogu ba,ko kun manta haka ce ta faru a lokacin da Ummie Maryam ta haifi Jaheed duk da Baba Malam ya hana tsaga sai da ta sa akai mashi,wanne irin tashin hankali ne ba ayi ba a ranar,kawai ku barta so take bikin sunan ya watse,kun ga ita ba ruwanta mu ke da asara da bak`in ciki, kuma dama burinta kenan ace ba a tashi lafiya ba,in dai don tsaga ce na samu Zuma mai kyau in rik`a shafa mata har ta `bace".
"Kuma da gaskiyar ki Hibba, abinda take so kenan ayi fitina din haka k`yaleta shine mafi a'ala ban manta yanda dangina suka tafi da `bacin rai a ranar sunan Jaheed ba kuma duk saboda ita ba", Cewar Ummie Maryam.
" Shikenan tunda haka kuka ce amma wallahi taci bashi kuma sai ta biya shi,in ba dan Mahaifin Yarinyarnan yana da hankali da natsuwa ba ai da bamu san ina wannan abun zai tsaya ba ".
Haka dai su ka dunga tausar Yaya Hanne har Allah ya sa aka tashi taron lafiya ba tare da wata hayaniya ba.
Sai bayan da su Hibba su kai Arba',in sannan suka koma a lokacin tare da Muhammad Jaheed suka tafi.