KULSOOM

SEVEN

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

CHAPTER SEVEN

        Kallo ɗaya Maimu tayimin tace.

“Are you sick?”

Ƙara ɓata rai nayi nace.

“I'm not in the mood. Komai ma damu na yake. Gidan su Khaldun zaki kaini”

Cike da mamaki tace.

“What!... Are you kidding me Kulsum?”

Gyaɗa kai na nayi nace.

“I'm damn serious... I met with him yesterday ya gurzamin abinda ba zan iya yafe masa ba...”

Cikin zaƙuwa tace.

“Kice wallahi. Where did you guys meet?”

Harara na maka mata nace.

“Ba dan ina so ki rakani ba wallahi kema da bazan nemeki ba. Duk kece ai kika ja min, kika barni ina ta jiranki ganin baki fito ba yasa na wuto titi ina taron lipt na haɗu da shi da wani....”

“But who's the second guy”

Taɓe baki nayi nace.

“How would I know him, daga haɗuwa a titi. Sai da ya gurzamin sannan ya bari suke kaini Lalan”

Ɓata rai Maimu tayi tace.

“Amma dai kin cuceni wallahi da baki kirani a waya ba....”

Wucewa nayi gaba tare da jan tsaki nace.

“Ni da kika bari nan ina jiranki nayi ta kira baki ɗaga ba zaki wani zo min da zancen renin hankali”

Bayana ta biyo da sauri itama tana faɗin.

“Wait! Kulsum kin ma kalli kanki kuwa? Ba wanka ba komai ji hijab ɗin da ke jikin ki..”

Hararar ta nayi nace.

“That's how I supposed to dress mana. Ke dai mu tafi kawai”

Tunda muka shiga napep Maimu ke zubamin hirar family ɗin Khaldun take naji son shi ya ƙara huda dukkan gaɓɓan jikina. Wayarta ta ciro ta hau nuna min hotunan Ayusha da Meerah  da kuma Sa'ad sai mahaifiyarsu Hajiya Amamatu. Sosai suka burgeni suka kuma shiga raina duk yawancin hotunan su Ayusha a ƙasar waje ne sun sha kyau har sun gaji. A  raina nake addu'ar Allah ubangiji ya mallakamin Khaldun.

**********

Duk yadda Khaldun ya so ya zillewa maganar da Jodan ke masa ya kasa. Tun da Jodan ɗin ya shigo office ɗinsa ya fara masa maganar ya share sa.

Laptop ɗinda ke gaban sa Jodan yaje ya janye ya rufe tare da faɗin.

“Zurmi dole sai munyi wannan maganar fa. Mahaifiyarka ta sharɗanta maka lokaci you have to be serious about it...”

Kallonsa Khaldun ɗin yayi yace.

“Then what should I do?”

Girgiza kai Jodan yayi yace.

“Khaldun please sit down and think. Matan zamanin nan kai ka zaɓo da kanka aka yi auren ya aka ƙare ballantana kace duk wadda aka samo maka....”

Murmushi mai sauti yayi sannan ya kira sunan Jodan.

“Jodan..”

Kallonsa yayi shima yana murmushi yace.

“Na'am Zurmi...”

“Jodan ina ƙaunar iyayena fiye da yadda baka zato, haka ƙannena. Iyayena sun wahala dani ba kamar mahaifiyata. Tayi wankakau tayi surfafau wurin ganin na samu karatu. Sun jure wahala sun hana cikinsu abinci duk wata walwala sun hana kansu sun  ɗaure taro da sisi sun bani wurin ganin na haɗa degree. Ni Kuma daga nan na bazama kasuwa cikin wahala da daɗi, ruwa da iska na jure har na tako wannan matsayin da taimakonsu da kuma ɗumbin addu'o'insu zuwa gare ni... Allah ya ƙara jaddada rahamarsa ga mahaifina, duk abinda ubangiji yayi daidai ne shine Ahad-Assamad wanda baya taɓa kuskure amma gani nake mahaifina ya tafi bai gama jin daɗin dukiya ta ba yadda ya kamata.. Astagfirullah!”

Cikin tausayawa Jodan yace.

“Don't ever say that again.. Allah yasa can ya fiye masa nan”

Gyaɗa kansa yayi yace.

“You are right Jodan. Amin na gode. To be sincere Mahaifiyata ta gama min komai kuma duk duniya tafi kowa sanin ciwo na,ko ni na tabbatar banson kaina kamar yadda take so na saboda tasan in da muka fito, she will never choose a wrong woman to me. Na fawwalawa Allah al'amari na sannan na bawa Hajiya dama ta zaɓomin mata duk wadda ta yarda da ita nasan in sha Allah zanyi farin ciki da haka har abada”

Cike da gamsuwa da bayanin sa Jodan yace.

“Masha Allah. I wish you all the best abokina. Ni dai I eager in ga wacece wannan amaryar...”

Dariya yayi yace.

“Duk mune ai Nima tunda bansan ko wacece ba. I'm eager too in wacece abokiyar rayuwar tawa”

“Hmmm! Ni dai baki na da goro...”

“Look Jodan,ni fa na faɗa ba kai ba, saboda haka ba goro ne a bakinka ba ko duwatsu ne kai ka sani. Yanzu dai ka bani wuri in ci gaba da aiki na”

Miƙewa yayi yana dariya yace.

“Na tafi to,but zan wuce Sokoto kada kace ban sanar maka ba”

“ Alright, Allah ya tsare hanya, Sai munyi magana”

Daga haka Jodan ya fice shi kuma yaci gaba da aikin sa.

********

  Tunda mai napep ya ajiyemu ƙofar wani katafaren babban gini zuciyata ta shiga bugawa da ƙarfi kamar zata fito daga ƙirjina.

Kallon Maimu nayi ina zare ido nace.

“Maimu nan ne gidan?”

Gyaɗa kanta tayi tana murmushi tace.

“Ai duk Layin nan ba gida irin wannan rankatakab! Kinga gidan su ƙawata can wadda nace miki ɗinnan”

Kallon direction ɗinda take nunamin nayi ina mai jinjina kai domin shima ya haɗu iya haɗuwa duk da bai kai na su Khaldun ɗin girma da tsaruwa ba, daga waje ma kawai, to ina ga mutum ya shiga ciki.

Hannu na taja ganin na shantake ina ciyar da ido na abinci.

Muna kaiwa ƙofar gate wasu ƙarti suka taso guda biyu masu kakin Police ɗayan yace.

“Malamai Lafiya? Wa kuke nema?”

Ganin yadda suka ɓata fuska babu sauƙi yasa Maimu cikin sarƙewar murya tace.

“Hajiya.... Hajiya muke nema...”

Kallonmu suka yi daga sama har ƙasa sannan ɗayan ya sake cewa.

“Wacce Hajiya..?”

Saurin nuna musu ni tayi tana zare ido tace.

“Wannan ce na rako tana da magana wurin Hajiya Amamatu...”

Da mugun mamaki na kalle ta nace.

“Na zo ko dai muka zo malama?”

Girgiza kai tayi tace.

“A'a rakoki nayi gaskiya...”

Kallonmu police ɗin yayi yace.

“what so ever dai, duk iyalan gidan basa nan sun tafi wurin Umrah sai mai gida kawai”

Ban san lokacin da na sauke sassanyar ajiyar zuciya ba ina mai hamdala a cikin raina. Domin sai yanzu na gane cewa ƙaryar iskanci na ke domin wallahi ba zan iya ba.

Hannun Maimu na janyo wadda ta dake tana tambayar su yaushe zasu dawo. Ban tsaya jin ta ba mukayi gaba sai mita take min.......

               OUM AMEER