KULSOOM

EIGHT

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

      CHAPTER EIGHT

       Wani irin matsiyacin kallo na watsawa Maimu da ke ta yimin masifa wai akan miyasa ban jira mun tsaya mun tambayi masu gadin cewa yaushe mahafiyar Khaldun zata dawo ba.

Rai a matuƙar ɓace.

“Na fasa manufa ta ne sai me to?”

Da matuƙar mamaki Maimu ta kalleni tace.

“What? Kin fasa me?”

“Na fasa manufata nace ko akwai  mai sakani dole?”

Taɓe baki tayi tace.

“Eh to, no one will force you but kinyi loosing mafarkin Ki Kulsum har abada kenan...”

Cike da mamaki na kalle ta nace.

“To hell with the dream Maimu. Mutunci madara ne idan ya zube ba zai kwasu ba, kamar yadda yake Yayan su Ayusha haka nima nike da Yaya Naziru idan har wata mace tazo gidanmu gaban mahaifiyata da irin wannan zancen ya zamu ji? Tabbas ba zamu ji daɗi ba ko da kuwa da wasa take. Saboda haka na fasa aikata hakan. Sannan da yake ke makira ce shine kika tsabbace gefe kika ce wai ni kika rako. Gaskiya kin  bani mamaki Maimu, i thought duk abinda zai farmana zamu tare shi tare da ke, amma ba komai duk da haka na gode...”

Har na wuce gaba sai kuma na dawo ina kallon ta kamar yadda itama take kallo na nace.

“Sannan kuma Maimu rabon mutum duk inda yake idan Allah ya nufa zai samesa sai kiga ya samu,saboda haka ban cire rai ba, zan je in yi ta gayawa Allah shi zai mini maganin komai”

Daga haka na wuce ban bata damar furta ko kalma ɗaya zuwa gare ni ba na tare mashin na haye abina zuwa gida.

  Mai mashin na dire ni ƙofar gidanmu take naji 'yan hanjin cikina sun hautsina saboda ban san mai zan shiga in tarar ba.

Cikin sanɗa na shiga cikin gidan ina mai leƙe ko wane lungu da saƙo na gidan da kallo. Cike da murmushin nasara na shige ganin ba kowa a tsakar gidan. Madafa na nufa na fara dubawa, yadda na bar komai haka na dawo na samesa. Ɗaki na wuce abina ina mai hamdala domin ba wanda kenan yayi noticing cewa bana gidan. Sai da na kwashe tsawon minti talatin sannan na fito bayan naji motsi a tsakar gidan.  layin ƙarya na fara tamkar wadda ta shafe hour biyar tana sharar bacci. Sai da shiga toilet na fito sannan na hau sauran aikace aikacen da bari ɗazu. Inna dai haka tayi banza dani kamar bana gidan. Ni kuma da na san cewa fushi take hakan yasa ban matse mata ba,a haka naje ɗakin Yaya Naziru na duba amma sai naga ba jakar sa hakan ya tabbatar min cewa ya koma Zaria da yamman nan, hakan sai ya ƙara kwantar mini da hankali na.

Sai da na gama duk abinda nake nayi shirin kwanciya na kwanta ina chart. Khadija kam ta daɗe da yin  bacci jiki duk ya gaji,S.S 3 take suna shirye shiryen rubuta waec ga ɗan banzar zuwa lesson ɗin da ya saka su gaba, shiyasa da ta dawo ta gaji nan da nan take yin bacci.

Chart ɗina da Maimu na duba message ɗin da ta turomin wai nayi haƙuri da abinda ya faru ita ba haka take nufi ba.

Tsaki naja tare da fitowa cikin chart ɗinta ina mai ƙara jin haushin ta game da abinda tayimin. IG na shige ina ta kallon Abubuwan da Ayusha take ɗorawa. Wato duk iskancinka duk  ƙaryar ka duk jiji da kanka dole sai ka samu wanda ya wuce ka ta ko wane fanni,har gwanda masu kuɗi in sunyi suna da dalili kai fa? Kai ba kowa ba ɗan Galadiman ragga.... Ba laifi duk inda suke ita ƙanwar su Meerah babu in da suke da shigar banza most of the Pic ma sun fi saka Abaya amma masu maiƙo.

  Na shagala sosai da kallon su kawai ba zato ba tsammani naji saukar bel a gadon bayana wanda sai na yi wurgi da wayata ba tare da na sani ba. Wata irin gigitacciyar ƙara na saki tare miƙewa ba shiri sai dai ban gama miƙewa na sake jin wani bel ɗin a cinya ta.... Duk yanda na so na kasa ƙwatar kaina Yah Naziru sai jibgata yake tamkar ya haɗu da riƙaƙƙen maƙiyinsa....cikin ikon Allah na samu wani ƙarfin tura shi yayi gefe da gudu na ranci na Kare sai ɗakin Innani amma ina! Na makara domin Innani tuni ta garƙame ɗakinta, da gudu  na juya zuwa ɗakin Inna itama ta rufe na Baba ma haka. Hakan ya tabbatar min da cewa haɗin baki ne suna sane da dukan da Yah Naziru zai yimin. Duk yadda nike tunanin muguntar Yah Naziru ya wuce nan mugu ne wanda babu ɗigon tausayi ko kaɗan a zuciyar sa domin wannan daren sai da ya ga yayimin liƙis sannan ya ƙyale ni. Nayi kuka nayi kiran Innani da Inna da kuma baba tamkar rai na zai fita ba wanda ya kula ni hatta Khadija da azaba tayi azaba sai da na kira ta, baiwar Allah haka take ta kuka tana roƙon Yah Naziru akan ya ƙyaleni amma bai saurare ta ba ƙarshe da ta shigo tsakanin mu don zalunci haka Yah Naziru ya watsa nata bel sai da ta gudu itama bata Shirya ba.

Yadda naga rana haka naga dare ko kaɗan ban samu na runtsa ba. Haka na kwana ina darzar kuka tamkar wadda aka ƙarshenta yazo.

Da ƙyar na rarrafa na yo alwalar asuba domin duk jikina ciwo yake min ga shi duk wani wuri ya fashe musamman bayana ga wani irin mugun zazzaɓi da ya rufe ni lokaci ɗaya.

Ina kan sallaya Mama ta shigo. Ko kallon ta banyi ba sai ma ƙara kawar da fuska ta gefe da nayi ina mai sheshshekar kuka a hankali domin sai daren jiya na tabbatar cewa duk wanda yake gidan ba ƙaunata yake ba.

Saukar muryarta naji tana faɗin.

“Nasan cewa duka ba shine maganin shiriya ba Kulsum amma gwanda kiji a jikinki kamar yadda kike sani ɓacin rai. Ina miki addu'a Allah ubangiji ya shiryar da ke ya baki miji nagari, in sha Allah yadda na wahala da ke da gumina ina kare miki mutuncinki har abada nasan Allah ba zai barni haka ba. Daga yau kada ki sake fita gidan nan ko nan da ƙofar gida idan kuma kika sake fita Allah ya isa ban yafe miki ba. Kuma in gunduwa-gunduwa Naziru zai yi da namanki babu abinda ya shafe ni, kuma ki tashi  daga yanzu aikin gidan nan komai ya dawo hannun ki domin kin ga Khadija batun jarabawa suke... ”

Wani Sabon kukan na sake fashewa da shi Ina faɗin.

“Wallahi ni Mama bani da lafiya, duk jikina ciwo yake, zazzaɓi nike ji.. Dubi yadda jikina ya fashe Mama....”

Kuka nake ina nuna mata duk inda ya jimin ciwo, ko ina kuma ga shacin bel amma Mama ko kallona bata sake yi ba tayi waje abin ta tana cewa ita ba ruwanta in mutu ma idan zan iya.

Haka na sha kukana ƙarshe na je na duba magani Paracetamol na sha sannan na sake dunƙulewa kan katifa ta.

 

Ƙarfe goma na safe Baba ya shigo ɗakin mu yana kiran Suna na amma ko dogon motsi bana iya yi sanadiyyar zazzafan zazzaɓin da ya rufe. Matsowa yayi ya yaye bargon da na lulluɓa ya taɓa jiki na yaji yayi gaɗau da zafi. Da taimakon shi na shirya muka je wani chemist aka bani magunguna na dawo gida shi kuma ya wuce kasuwa.

                OUM AMEER