KULSOOM

NINE

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

   CHAPTER NINE

      A duk in da Khaldun yake a halin yanzu ba shi da wani tunanin da ya wuce ƙannensa guda biyu wato Ayusha da Meerah. Zuciyarsa bata da wani sukuni kullum cikin taraddadin a ina suke? Mi suke aikatawa? Dawa suke abota a matsayin ƙawayensu? Ya san ƙannensa ko su waye su to amma yana jin tsoron zamanin nan mai saurin juya mutum farat ɗaya. Shiyasa duk irin yanda yake kulawa da su yanzu sai abin ya ƙara ƙamari domin baya cikakken hour uku bai kira su ba.

Ko yanzu a mota yake ya fito daga bakin kasuwa wurin wani abokinsa ya nufi store ɗinsa na shinkafa. Bayan yayi parking ya ciro wayarsa ya kira Ayusha sai da ta katse ya sake kira sannan ta ɗaga cikin nutsuwa tace.

“Assalamu alaikum Yayanmu”

“Wa'alaikissalam... Ayusha kuna lafiya?”

Murmushi tayi mai sauti har yana jiyo ta sannan tace.

“Uhm! Yayanmu dai, ko ɗazu fa ba'a daɗe ba ka kira..”

“Ayusha sai a kace don na kira ɗazu kada in sake kira kuma?”

“A'a Yayanmu kayi haƙuri tambaya ce”

“OK to, where are you now? Dawa ki ke tare?”

“Huh! Yayanmu Ina Harami fa, ina zan kasance yanzu,kuma ina tare da Meerah da kuma Ayaa”

A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan yace.

“Ya kukayi da barrister Kabeer? Ina nufin zancen auren ku, ina fata sun shirya?”

Yanzu kam dariya ta yi tana  girgiza kai sannan tace.

“Yayanmu sun sani yau sauran 3weeks and some days Ko”

“Hakane, Allah ya nuna mana, duk abinda kuke so dan Allah ku zaɓa kin ji ko Ayusha ki zaɓawa Meerah, ki zaɓawa Meerah da kanki kin san halin ta...”

Muryar Meerah ya tsinta tana faɗin.

“Toh Yayanmu ina fa jinka, Anty Ayusha ce ta fini sanin abin ƙwarai? Lallai ma.....”

Murmushi ya yi yace.

“Ayusha bata waya”

Karɓar wayar tayi tana dariya tace.

“Yi haƙuri Yayanmu wasa nike...”

“Meerah kin kai ƙarshe da zaɓinki kuwa?”

Zaro ido tayi har tana sarƙewa domin bottle ɗin lemu ne a hannunta, tana cikin tari tace.

“Haba Yayanmu wurin ibadar ne zan tsaya kula wani saurayi? Ka yi haƙuri sai na dawo mana..”

“To shi kenan Allah ya nuna mana kun dawo lafiya, ina Sa'ad?..”

“Yah Sa'adu tun ɗazu muka rabu da shi yace sai dare idan yazo”

“OK to, ba Ayusha waya”

Karɓar wayar Ayusha tayi tace.

“Ina ji Yayanmu...”

“Ayusha ki kula da Hajiya da Meerah sosai kin kin ji ko. Kiyi addu'a Allah ya haɗa hankalinki da ke da mijin ki...”

“Kai ma Yayanmu muna nan muna yi maka addu'a Allah ya baka mata ta gari mai albarka, Ayaa ma har da wannan a cikin addu'arta  ba dare ba rana”

Cikin jindaɗin maganar ta yace.

“Na gode Ayusha, Ina Hajiya?”

Waigawa tayi ta na kallon ina zata ga mahaifiyar tasu amma bata hango ta ba.

“Yayanmu bata kusa fa.”

“Ok to ki gaishe ta”

Daga haka suka yanke wayar.

********

      Sai da na kwashe tsawon sati uku cur! Kamar yadda aka gindayamin sharaɗi ko ƙofar gida ban leƙa ba. Duk wata wahalar gidan nan ga kaina ta yanke cibi, ga wayata wadda sai da na sha wahala sannan na samu wayar nan amma sanadiyyar dukan da Yah Naziru yayi min na yasar da ita taci screen,bata nuna komai sai haske. Mama na sa ne ta ƙyaleni da duniyar da ne da tuni an canza min wata  ko an sanyo min screen ɗin. Abu goma da ashirin ya ga me mini. Kowa ya hanani ɗaukar wayarsa hatta Innani mai rakani kashi,daman Khadija bata da waya bata damu da ita ba. Sai na yi da gaske cikin dabara nike satar wayar Innani in saka layina text ne nike gani sai kuma in kira wanda ni ke son kira idan na gama in mayar mata. Ina ganin messages ɗin Maimu na ban haƙuri amma bana kula ta. Sau biyu tana zuwa ina ji ana ce mata bana nan ban kuma damu ba domin ita ma ɗin ba ƙaunata take ba shiyasa na fita a harkar ta. Na kuma ɗaukarwa kaina alƙawarin ba zan sake aikata abin da ba'a so ba kuma duk ƙawayena na yanke hulɗa da su in sha Allah.

   Ina zaune ina ɗan rage gajiya bayan na gama niƙar waken awara da aka kawo. Naji Muryar Mama a kaina.

“Yanzu Kulsum haka na yi miki? Duk wanda yazo sai Kice ba ki son sa kina da wanda kike so.....”

Baki na zumɓuro na ce.

“Ni dai gaskiya Mama duk bana son su babu wanda ya mini...”

Duka ta kaiwa baki na wanda sai da ta ɗan same ni kaɗan duk da na doje tana faɗin.

“Don ubanki ke har wata zinariya ce da kike ganin kin fi ƙarfin kowa. In duk ba ki son sauran to shi Idirisa miye laifin sa?...”

Zabura nayi na miƙe tsaye tuni har hawaye sun ciko a  ido na ina faɗin.

“Mama wane irin Idirisa kuma daga sunan ma an samu matsala, wallahi ni ban son shi  ban ƙaunar shi. Kuma dan Allah Mama ki daina ma zancen shi kada Yah Naziru da Baba su hau su zauna a kai....”

Butar da ke hannunta ta rafka mini a gadon baya wanda yasa ni rugawa na faɗa ɗaki ba shiri ina rusa kuka ina faɗin.

“To wallahi ni a daina  yi min zancen wani Idirisa a cikin gidan nan don ni wallahi ko sunan sa naji wani irin baƙin ciki ne ke zuwa yana danne min ƙahon zuciyata...”

“To Idirisa kaf dangina da na ubanki babu wanda yayi wayewarsa da ilminsa, domin degree gare shi ga ilmin addini sannan yayi gininsa na zamani ya gama domin yana da zafin nema sannan kuma ga mu maƙota musamman waye shi suma iyayensa sun san wacece ke...”

Ƙara fashewa nayi da kuka ina faɗin.

“wallahi ko mutuwa zan yi ba zan aure sa ba sai dai ku aura masa Khadija amma ni dai ban komi da Idirisa wallahi. Mugu azzalumi mai baƙar fuska yana can hankalinsa kwance ni kuma ina nan ya haɗani da iyayena ni dai Allah ya isa wallahi”

Ina jin tahowar Mama na yi sauri naje na rufe ƙofa na saka sakata domin idan har ta ritsa dani babu abinda zai hana ta naɗamin na jaki.

********

Maimu ta rasa yanda zatayi ta shawo kan Kulsum tun da suke da ita bata taɓa yin fushi da ita irin wannan ba ita abin har mamaki ya ke bata. Domin duk yadda zata ja ta su je wurin shiriritar su duk dukan da za'a yi mata ba zai hana gobe ta sa ke neman ta ba. Amma wannan karon abin  ya canza, tayi duk yadda zatayi taƙi ta kula ta. Yanzu kuma da ake batun auren wata ƙawar su Azima nan take ta tunanin yadda zatayi taga sun shirya da ita.

Tana zaune tana tsaka da tunani sai ga wani saurayin Kulsum ya kira ta. Ba ɓata lokaci ta ɗaga tace.

“Maina Manya!”

Dariya yayi yace.

“ku ne manya, in kuna ga wuri wane mu”

“haka dai ka ce..”

“Haka ɗin ne ma. To ya kike? Ina Kulsum? Kin dai hana ta ta so ni...”

Dariya Maimu tayi ta ce.

“Dan Allah ka daina faɗin haka. Kulsum ɗin ce dai 'ƴar renin wayo gani ta ke tafi ƙarfin ajinka shiyasa, kuma ita ba 'ƴar kowa ba....”

“Na ji Maimu. Miyasa bana samun ta a waya sannan na daina ganin ta a online ko ina tamkar anyi ruwa an ɗauke”

Taɓe baki tayi tace.

“Oho! Waya sani may be an sayar da wayar an sai garin masara tsoffi su samu abinda suka kore ma bakin su ƙuda”

Dariya yayi yace.

“To shi kenan ni dai dan Allah ki binciko min ita ya kamata mu haɗu idan waya ce zan saya mata wata”

“A'a Maina za dai ka saya mana ba ita kaɗai ba”

“To shi kenan naji, daman ai baki taɓa yi wa mutum abu dan Allah ba. Ki nemo ta sai mu haɗu”

“ok to, bye”

   

               OUM AMEER