TEN
💝 KULSUM 💝
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
CHAPTER TEN
Duƙe ni ke ina ɗauraye wurin da na gama tiƙar wanke-wanke. Amo na ji tamkar na Azima Shu'aibu tana kwaɗa sallama. Miƙewa nayi da tsintsiya a hannuna na kalli ƙofar da ke yi wa mutum iso zuwa cikin gidan namu. Ai ko sai mukayi ido huɗu da ita. Cikin tsantsar mamaki na ke kallon ta na ce.
“Azima.. Is that you?”
Murmushi ta sakar min tace.
“Tabbas ni ce. Muje ciki”
Tsintsiyar na jingine a gefe na nufi ɗakinmu tana biye dani. Har na shiga ban dai na mamakin ganin ta ba domin nafi shekara biyu rabona da ita, tun wani faɗa da mukayi wurin bukin Birthday party ɗinta saboda kawai wani abokin ta yace yana so na ƙarara ya nuna son lalata dani na wanka masa mari gaban mutane shine itama ta mare ni akan sa dalilin haka ne yasa mukayi baran-baran.
Tsaye nayi ina kallon ta kamar yadda itama ta ke kallona. Fuska ba yabo ba fallasa nace.
“Azima Shu'aibu I hope all is well....”
Girgiza kai tayi tace.
“But I think you will offer me a seat before asking me anything..”
Zaunawa nayi gefen katifar khadija tare da nuna mata gefen katifata muna kallon juna nace mata.
“Ke tauraruwa ce mai wutsiya wadda ganin ta ba alheri ba. But ga wuri nan ki zauna”
Murmushin yaƙe tayi wanda kana gani kasan magana ta bata yi mata daɗi ba. Zaunawa tayi sannan ta kalleni tace.
“Ke san miyasa nike ƙara son ki? Saboda baki shakkar faɗin duk maganar da tazo miki a rai, bakin gaskiyar ki kike furzo zance...”
Cikin ƙulewa nace.
“Azima mi ya kawo ki gidan mu, ke da kika ce kin fi ƙarfina ke ɗiyar masu arziki ce kinyi gadon arziki gaba da baya ni kuma ɗiyar matsiyata nayi gadon talauci gaba da baya, mi kike gidan da babu tyles da sai siminti da yashi....”
Murya ƙasasa cike da nadama tace.
“Please Kulsum I'm so sorry, I'm really sorry for everything that had happened, sharrin shaiɗan ne da kuma zuciya. Wallahi duk abinda na gaya miki ba har zuciyata ba ne, kawai ɓacin rai ne.....”
“Ɓacin rai? Akan wani ƙaton banza wanda babu haɗin Iya ko na Baba a tsakanin ku ki mare ni kuma akan gaskiyata sannan ki ce ɓacin rai ne...”
“Kulsum please ki daina ɗaga murya, kiyi haƙuri, tunda har kika ga na zo gidanku ai komai ki ke ji ya ci ace kin sauke shi. Katin gayyata ne na kawo miki...”
Taɓe baki nayi ba tare da na bari ta ƙara sa sauke maganar ta ba nace.
“Allah ya shiryar dani, na daina zuwa Birthday party ɗin Ko wace ƙatuwa...”
“Kulsum ba birthday ba ne. Is my wedding Invitation......”
Matsowa tayi ta riƙe hannuna cikin magiya tace.
“Kulsum please ki bar komai ya wuce ina roƙon ki, nima na daina komai na shiryu wallahi. Remain three weeks to my wedding that's why na zo kawo miki kati. Naje gidan su Maimuna nace tazo ta rakani ta faɗamin kina gaba da ita....”
“Ba gaba ni ke da Maimuna ba alaƙar mu na yanke wadda naga ci gaba da yinta ba zai haifamin ɗa mai ido ba domin so ta ke ta kai ni ta baro”
“Kulsum ga yadda ta faɗamin kun samu rashin fahimta ne kawai...”
Wani irin ɓacin rai naji ya turnuƙomin rai ɓace nace.
“Wadda ta tura ni inje ga zina abinda har na koma ga Allah ba zan manta shi ba,sannan ta tura ni in yi ƙaryar cikin Shege in tayarwa da iyayena da kuma iyayen Khaldun zaki ce wai rashin fahimta ne? Haka take haɗani da samari na banza wanda ni nasan Allah ne kawai yake kare ni ba iyawa ta ba. Maimu ba Allah a ranta har 'ƴan less ta sha kai ni wai zan samu kuɗi zan fantama.....”
“She made a big mistake but on behalf of her Ina baki haƙuri. Tayi nadama sosai tabbas ba ta kyau ta miki ba. Tayi alƙawari a wannan karon duk wani abu ya sake faruwa duk hukuncin da kika ga dama ki ɗauka...please ki bata last chance dan Allah. Maimu ta riga da ta shaƙu dake wanda a dalilin haka har zazzaɓi ta kwanta, please kiyi haƙuri ki zo muyi hidimar bikin nan tare kin san bani da wasu ƙawayen da suka fi ku”
Shiru nayi ina sauraren ta, daga ƙarshe na sauke numfashi na ce.
“Shike nan. Allah ya kaimu idan na tambayi Inna gobe zan shigo”
Rungume ni tayi cike da murna tace.
“Thank you so much friend. Allah ya kaimu ɗin”
Nace amin.
Daga nan ta tashi ta wuce wai ana jiranta.
*******
Tare suka shigo farlourn Hajiyar ta su shi da Sa'ad a dalilin kiran da tayi musu.
Ko da suka shiga Ayusha ce kawai da Hajiyar a farlour. A ƙasa Khaldun yayi masauki yayin da Sa'ad ya zauna gefen sa. Gaishe ta yayi cikin ladabi ta amsa. Itama Ayusha saukowa tayi daga kan cushion ta ce.
“Yayanmu barka da warhaka, ya office?”
Murmushi yayi yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah Ayusha ya shirye-shirye?”
Dariya tayi tare da miƙewa tsaye tace.
“Yayanmu dai...”
Sai kuma ta kalli Sa'adu tace.
“Yah Sa'adu ina wuni”
“Lafiya lau amarya Ayusha.”
“Yah Sa'adu har da kai ko? Yayi kyau. Ayaa bari in je in ga Meerah mi take har yanzu a kitchen yunwa tamkar zata halaka mu”
Kallonta Hajiyar tayi tace.
“Yawwa je ki duba ta dan Allah, tunɗazu kamar an aiki bawa garin su yanzu haka tana can tana latse-latsen waya”
Sai kuma ta mayar da Kallonta gun Sa'ad tace.
“Sa'adu ka gama fentin gidan naka ne?”
Sosa kai Yayi yana murmushi ci ke da tsantsar so na haƙiƙa ya kalli Khaldun yace.
“Ayaa Yayanmu shi yayi fenti komai ya gama yi min. Duk da ina da halin da zanyi wani abin bai bari nayi ba...”
Hajiya kallon Khaldun ɗin tayi tace.
“Ba na ce ka bar shi yayi fenti ba tunda ka yi mishi mai wuyar?”
Cikin ladabi yace.
“Hajiya lokacin da zai yi lalura zai zo ba komai. Saboda kuma lefen da zai yi na ɗauke masa yin fentin, ba wanda zai saya mashi ko allura komai ya saye da kansa. In dai akwai hali babu abinda ba zan yi musu ba.”
“Yanzu haka ma abokina na jirana zamu je Kano abinda babu sai mu cika...”
Sallamar Baba Mu'azu ce ta katse shi wanda ya shigo direct ya zauna.
Miƙewa Sa'adu yayi ya fita ya ba su wuri bayan sun gaisa, daman ana jiran shi a waje.
Kallon Khaldun Hajiya tayi tace.
“Alhaji Mu'azu ga shi nan ka ƙara ji daga bakin sa, ta ya mutum irin sa shi ba ƙaramin yaro ba yace ya bada zaɓi a zaɓo masa mata”
Gyaɗa kai Baba Mu'azu yayi cikin mamaki yace.
“Gaskiya Hajiya abin da mamaki. Auren nan ƙannen ƙannenka sunyi tun ana bin ka da lalama har aka zo ana nuna maka ɓacin rai ƙarshe dai har muka zura maka ido don mun cire rai shine kuma yanzu zaka zo da wani zance na a nemo maka mata. In dai auren ne ba zaka yi ba kawai ka ce ba zaka yi ba, amma mutum irinka ka shiga gari gari ƙasa ƙasa,ka waye ka san duniya da mutanen cikinta shine zaka ce a zaɓo maka mata”
Ɗan ƙara rusunar da kai nai yayi yace.
“Baba kayi haƙuri ba na nufin komai sai alheri, hakan dai shi na ce ku zaɓo min duk wadda kuka yarda da tarbiyarta”
Ƙure shi da ido baba Mu'azu yayi kamar yadda Hajiya ta ke kallon sa itama, bayan wasu daƙiƙu baba Mu'azun ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Hajiya yace.
“To Hajiya tun da kinji ra'ayinsa, ni ina ganin ayi mai haka ɗin kawai, wata ƙila shi kenan itace silar samun iyalinsa. Saboda haka cikin yaran da kika sani tun daga na maƙota har na abokanan arziki sai ki nemo masa. Allah yasa a dace”
Girgiza kai Hajiya tayi tace.
“Alhaji Mu'azu wallahi ni dai babu wata yau wadda zan ce maka gata, sannan kuma ta hanyar abokantaka bana son irin wannan alaƙa, domin sai kaga anzo anyi aure matsaloli su ta so mutum ba shi da wata mafita, saboda haka na bar maka wannan aikin Alhaji Mu'azu, kai dai ƙanen mahaifinsu ne uwa ɗaya uba ɗaya har yau muna zaune zaman amana tun ubansu na da rai har yau kuma da babu shi, saboda haka na baka dama tunda har haka ya zaɓa ka nemo ko can Zurmi cikin ɗiyan dangi, Allah yasa a dace. Idan an samu ina sauraren ka”
Sa ke kallon Khaldun ɗin yayi yace.
“Khaldun ka ji abinda mahaifiyarka tace, shin still ka amince da hakan aje Zurmi a nemo maka mata?”
Without thinking twice yace.
“Na amince Baba, Allah ya datar mu. Hajiya bari in je ana jirana idan kin bani dama”
“Tashi ka je na baka dama. Allah yayi maka albarka yasa ka dace da mata ta gari”
“Amin Hajiya na gode. Baba a tashi lafiya”
Har fice mahaifiyar ta shi ba ta daina kallon sa ba, har yau ta kasa fahimtar ina ya dosa. Ta ya mutum kamar sa zai ce wai a nemo masa mata. Har cikin ranta tanajin akwai abinda yake shiryawa, tunda an matsa da ya fito da mata bari ya ɓullo da wannan hanyar, to wannan karon ba zata ƙyale shi ba, nemo matar za ayi a aura masa sai ta gudun ruwan sa.
Yana fita ya nufi kitchen, can ya tarar da su harda Sa'adu suna fira sai dariya suke.
Meerah na ganin shi taje tayi hugging ɗin shi tana faɗin.
“Yayanmu I miss you! Mun dawo Kai kuma kayi tafiya”
Murmushi yayi yace.
“Miss you too Yaya's favorite, hope you are fine?”
“Fine and Alhamdulillah. Anty Ayusha ce muke zancen bikin ta ita da Yah Sa'adu”
Cikin mamaki yace.
“And what about you Meerah? Ke bada ke ba kenan?”
Ayusha tace.
“Yayanmu yarinyar nan fa zancen ka ta kunnen dama ya ke shiga yana fita ta hagu, wallahi ni banga ta ɗauki zancen ka serious ba”
Kallon Meerar yayi na ɗan lokaci sannan ya riƙe hannunta cikin tausasa murya yace.
“Meerah would you like to marry my friend Jodan?”
Zaro ido tayi waje tamkar zasu faɗo tana girgiza kai tace.
“Na shiga uku Yayanmu! Yah Jodan ɗin ne zan so mai mata da ɗiya uku? Ƴarsa ta farko fa Jss2 take sanda muka je ɗin nan naji suna fira da Anty Ayusha. Gaskiya ni dai Yayanmu A'a,banyi kwantai har haka ba”
Sa'ad yace.
“To ni akwai abokina da yake sonki kawai dai ban bashi dama ba ne.....”
Tuni har idon ta ya ciko da hawaye, murya a karye tace.
“Yah Sa'adu ni dai banyi kwantai har haka ba, akwai Nasir da muka kai ƙarshe baya nan yana Lagos yaje yin wani course da zaran ya dawo zai turo”
Haye Khaldun ya share mata yace.
“Is ok! No one will force you, Allah ya dawo da shi lafiya. But zan iya samun numbern sa”
Murmushi tayi tace.
“Sure.. Kawo na saka maka”
Daga haka ya wuce shi da Sa'ad ɗin su kuma suka ci gaba da aikinsu suna fira.
*********
Azima tana fitowa ta wuce in da ta baro Maimu.
Tana zuwa ta kalli Maimu tace.
“Maimuna na shawo kanta da ƙyar, kai gaskiya Kulsum akwai baƙar zuciya. Ga yadda ta faɗa min gaskiya baki kyauta ba Maimu.....”
Ɓata rai Maimu tayi tace.
“And so! Ke Khaldun Zurmi fa? Kin san sa kamar yunwar cikin ki Azima wallahi cikin shaguɓe na tura ta wurinsa, na ɗauka zai yi mata mugun wulaƙanci sai gashi tamkar a mafarki ya bata fuska har da yi mata dariya. Ai tuni hankali na ya tashi na shiga neman yadda zanyi in ga sun raba gari, Sai ko idea ta faɗomin na tura ta kuma ta bi sai gashi cikin ruwan sanyi sun rabu ko kwana ɗaya ba'a yi ba, rabuwa kuma ta har abada don wallahi ita da shi sai a lahira. Still daga baya ta dawo ba ta daina son shi ba shiyasa na ce tayi ƙaryar ciki muje gaban mahaifiyar sa, na san ba ita ba har uwar ta da ubanta sai an ɗaure......
OUM AMEER