ELEVEN
💝 KULSUM 💝
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
FREE BOOK
CHAPTER ELEVEN
Azima cikin mamaki ta kalli Maimu tace.
“To duk wannan da ta tare miki me? I thought ke da Kulsum ƙawance ku ke na amana, duk wanda yaga ɗan uwansa zai cutu sai in da ƙarfin sa ya ƙare....”
Girgiza kai Maimu tayi cike da tsantsar tsana a kalamanta tace.
“I have never love her even once....ƙawancena da Kulsum ya samo asali ne tun lokacin da saurayina wanda zai aureni ya janye daga gare ni ya koma wurinta shekaru uku da suka wuce. Mun shafe tsawon shekara biyu muna tare da shi ya zo gidan mu har kuɗin aure ya kawo...bikinmu baifi saura 3 months ba ya fara janye jikin shi daga gare ni, kwata kwata sai ya daina zuwa kirana ma ya daina, kwatsam sai ga shi bai fi saura sati ba yazo ya kira ni wai ya fasa.... Abin takaici abin baƙin ciki wanda har in mutu ba zan manta ba wai shi ba so na ne baya yi ba, kawai dai yana yin tarbiyata ne bai mi shi ba kuma yayi ta ƙoƙari yana yi min hannun ka mai sanda amma ban ɗau haske ba, kullum ni ce yawon biki, yawon party, ƙawayen banza, shigar banza waye waye, 'yan gidan su ma sunce ban yi musu ba, yayi ta ƙoƙari ya shawo kansu amma sunƙi su amince, to shi yanzu ya samu wata mai tarbiyya..... Ƙarshe wucewa nayi gida abina akan bakin ciki tun daga ranar bai sake zuwa ba, da nayi bincike sai na gano Kulsum ya komawa lokacin tana SS3, da ta yi candy zai aika kayan aure. Ni kuma nan na shiga na san yanda nayi har muka ƙula ƙawance da na gano tana da rawar kai shi kenan abin ya zo min da sauƙi... Ta ke na shige jikin ta cikin ƙanƙanin lokaci na raba tsakanin su. Komai ni ke tsara mana yadda zai kasance duk wanda yake sonta idan naga na ƙwarai ne sai na san yadda na juya komai na lalata shi... Kuma wallahi tun da ta zama silar rugujewar farin ciki har abada ba zata taɓa yin farin kici ba itama sai na lalata rayuwarta...”
Cikin tsananin shock Azima tace.
“Subhanallah! To ita Kulsum miye nata a cikin rabuwarku? Miye laifin ta?”
Wani malalacin murmushi Maimu ta saki sannan tace.
“Azima you won't understand that kind of pain...Wannan yafi komai ciwo...”
Miƙewa Azima tayi tana girgiza kai tace.
“What ever it is, it's nonsense seriously. There's nothing interested a wannan labarin sai ma takaici. You don't have any reason for ruining Kulsum's life. Your Ex ya kamata Ki nemi revenge akan shi ba ita ba. It sound very sweet domin ita Kulsum ɗin duk da tana da rawar kai ta iya kanta sosai da ba haka ba da yanzu abun yayi worst more than expectation. I'm advising you ki yi a hankali domin sharri ɗan aike ne duk inda ka aike shi tabbas sai ya dawo gareka komai daren daɗewa. Kuma remember this... Hassada ga mai rabo taki ce. Na barki lafiya”
Taɓe baki Maimu tayi tare da kyau kanta gefe ɗaya tana mai jin zafin kalaman Azima.
*******
Washe gari da wuri na gama duk abinda nake na shirya, ɗakin Mama na nufa. Ina shiga na durƙusa gabanta na ce.
“Mama na gama duk aikina, zan je gidan su Azima ƙarfe sha ɗaya mu kayi zamu je rabon katin”
Shiru Mama tayi tana kallona kamar ba zata ce komai ba. Sai kuma ta gyaɗa kai tace.
“Kulsum kada ki wuce lokacin da na baki, idan ƙarfe huɗu ta yi na yamma ki dawo ki ɗora mana abincin dare, ki kula”
“In sha Allah Mama”
Har na fice bata daina kallona ba. Abinda yasa ta barni shine ganin duk tsawon lokacin nan da aka hanani fita ban taɓa saɓa doka ba komai yadda ake so haka na ke yinsa.
Ina zuwa na taradda Maimu da kuma wata ƙawar Azima Saudah. Hugging ɗina Maimu tayi kamar zata cinye ni, tana fata kumfar bakin wai she miss me. Nayi kyau sosai saboda ina gida bana fita shiyasa kyau na da haske na ya da ɗa walwali. Nima dai murmushin kawai na mayar mata na samu wuri na zauna. Ba mufi minti goma ba muka fita zuwa rabon iv ɗin. Ƙarfe uku muka gama na wunin ranar domin na riga da na sanar musu cewa da wuri zan koma gida kada Mama tayi min faɗa.
Kwana uku muka jera muna zaryar abu ɗaya. Amma yau kam bai fi gida huɗu ba muka je shiyasa ko da biyu ta buga mun koma gidan su Azima.
Muna cin abinci Maimu ta kalle ni tace.
“Idan ba zaki damu ba wani yana jiran ki a waje please..”
Nan ta ke annurin fuskanta ya ɓace cikin kaushi nace.
“Waye wani? Ni fa yanzu na daina wannan shirmen...”
“Da dai kinyi haƙuri, wallahi yafi wata yana damuna kuma in dai ba magana yayi da ke ba ba zai daina takura mini ba”
Kallo na Azima tayi ta gyaɗa tace.
“Kulsum kiyi haƙuri ki je, idan kika ce kin daina kula samari ai hakan ba mafita ba ce. Sai dai ki kula wurin ganin kin hana kanki tsayuwa da ɓata gari. Allah ya baki miji na gari”
Wani matsiyacin kallo Maimu tayiwa Azima tace.
“Azima mi kike nufi?”
Azima tace.
“Mi ni ke nufi fa! addu'a nayi, ko yin addu'a kuma laifi ne Madam?”
Shiru tayi bata ce mata komai ba taci gaba da danna wayar ta.
Ni kuma hijabina na saka na fita ƙofar gidan.
Tsaye na ganshi bakin mota ya harɗe hannayensa wuri ɗaya yana kallon ƙofar gidan.
“Maina...”
Abinda na furta a raina kenan ina kallonsa. Wani irin haushin shi ne naji ya taso min kamar na shaƙesa haka na ke ji.
Tsayawa nayi ƙiƙam fuska babu sassauci nace.
“Gani ina ji”
Murmushi yayi yace.
“Haba Kulsum. Wai miye laifina dan Allah? mi nayi miki da kika yimin wannan tsanar?”
Kai tsaye na ce.
“Saboda ba son aure ka ke yi mini ba”
Cike da mamaki yace.
“Who told you that ba son Aure ni ke yi miki ba Kulsum?”
Taɓe baki nayi na ce Hmmm! A raina kuma kallon ɗan rainin hankali na ke yi masa, domin tun lokacin da ya ganni ya zo ƙofar gidan mu ya furta kalmar so gare ni, na faɗawa Maimu na kuma kira ta washe gari suka gaisa. Bayan kwana biyu ta zo ta same ni tace tayi ƙwaƙwƙwaran bincike a kansa ta gano tantirin ɗan iska ne, matan da ya yaudara da sunan aure garin Gusau da kewaye sun fi mutum ɗari,saboda haka kada in yarda da shi duk yanda yace zai turo kada in bari domin yaudarata zai yi. Tun daga lokacin na riƙe abin a raina na tsanesa bana son ko ganinsa duk yadda yake bibiyata bana yarda da shi.....
“Kulsum baki amsamin tambaya ta ba”
Taɓe baki nayi nace.
“Wannan kuma kai ta shafa malam, ina da abin yi zan tafi...”
Ƙara kwantar da murya yayi yace.
“Kulsum wallahi gaskiya ɗaya ce ni tsakani da Allah ni ke sonki zan aure ki, duk tsawon lokacin nan da ki ke share ni da kin bani dama da yanzu munyi auren mu”
Dariya nayi nace.
“Allah! Ko ba aure ba. To na gode da ƙaunar ka a gare ni, Sai an jima”
“Dan Allah ki tsaya ki saurareni”
Tsayawa nayi ina kallon sa.
Mota ya buɗe ya ɗauko leda ya bani yace.
“Nan waya ce, ƙawar ki ta faɗamin wayarki ta lalace Sai kuɗin anko, Dan Allah kada ki ce ba zaki karɓa ba, ko kin aure ni ko baki aure ni ba wallahi duk abinda ni ke miki domin Allah ni ke miki”
Karɓar ledar nayi na shige ba tare ko furta cewa na gode ba.
Ina shiga na buɗe ledar daman Allah-Allah na ke in je in ga wace irin waya ce. IPhone ce wadda zata kai ɗari uku, kamar in taka rawa haka na keji akan murna, Sai dubu hamsin daban.
Sama-sama Maimu tayi min murna, domin ba haka ta zata ba. Sai dai a wani gefen hankalin ta kwance don tasan itama ta ta wayar na can ya saya mata kamar yadda yayi mata alƙawari. Ko minti ashirin ban ƙara ba na wuce gida. Cikin zumuɗi na shiga domin nunawa Mama wayar da kuɗi kuma na sawa raina zan bashi dama ya turo iyayen sa inga iya gudun ruwan sa, ko motar sa ba zan yi gigin shiga ba balle ya bani abin sha don cutar dani. Duk matarsa dole ya ganni ya ƙyaleni. Sai dai ina shiga tuni murnata ta koma ciki don Mama tarbata tayi da kwalin waya wai daga Idirisa.
Wani irin tuma nayi na koma gefe ina faɗin.
“Wallahi ni Mama a mayar masa da wayar sa, ga waya wanda zan aura ya kawo min...”
“To bari idan Nazirun ya shigo sai ki faɗa masa ya mayar da wayar don shi ne wanda ya kawo yace daga Idirisan”
Kuka na fasa na nufi ɗakinmu ina faɗin.
“Daman ai Yan Naziru ba ƙaunata ya ke ba na daɗe da gane hakan. To wallahi tun da ba shine ubana ba wallahi ba zan auri Idirisa ba”
Murya Innani na jiyo tana faɗin.
“Idirisa kam ke gama Aure nai in faɗa miki ko ubanki Sulmanu bai isa ya hana wannan auren ba, shegiya mai baƙin hali. Miye aibin yaron nan? yaro ɗan albarka, duk juma'a sai ya zo ya kawomin goro daƙwala-daƙwala, ga ladabi da biyayya”
OUM AMEER