TWELVE
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
💝 KULSUM 💝
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
CHAPTER TWELVE
Ɓangaren gidan su Khaldun kuwa; Bikin Ayusha da Sa'adu ya kankama wanda ya rage ɗaurin aure saura kwana biyu sai shirye shirye ake. Yau kamu za su yi wanda an riga da an gama tsara komai yadda ya kamata.
Bayan motoci sunzo an ɗauki amarya zuwa MARYAM-HALL in da can ne bikin zai gudana Meerah ta fito wadda ita ce last. Khaldun kawai ta tarar wanda yake zaune akan mota shi kuma Jodan yana tsaye gefen sa suna duba abu a waya. Ta san ba komai ba ne face harakar kasuwanci.
Yau kuma sai ta tsinci kanta da jin haushin Jodan ɗin wanda ta rasa dalili.
“Yayanmu kowa ya tafi I'm the only one left, kuma gashi ka hanani fita ni kaɗai ka hanani fita da ƙawaye, now what should I do? Ko kuma ba zan je kamun ba...”
Hawayen da ta ke ƙoƙarin riƙewa ne suka zubo.
Ranshi ne yaji ya baci domin ya tsani rashin tarbiyya a rayuwar shi.
Fuske a tamke ya kalleta yace.
“And sai aka ce ki zo mana haka kawai babu sallama babu komai, ga Jodan baki gaida sa ba ki hau karanta mini shirme, huh! Is that right?”
Da sauri ta girgiza kanta tana share hawayenta ta kalli Jodan tace.
“Good evening Yah Jodan”
Murmushi yayi yace.
“Evening dear, how are you?”
“I'm fine”
Mayar da kallonta tayi wurin Khaldun murya a sanyaye tace.
“I'm sorry Yayanmu....”
Murmushi yayi yace.
“Is okay dear. Je ki kira Maryama ta rakaki...”
Juyawa tayi taje ta kira Maryama mai aikinsu kamar yadda yace, shi da kansa ya kai su har bakin hall ɗin,bayan Maryama ta fita ta kalli yayan nata tace.
“Yayanmu we are resuming back to school next month, and I have talked to Ayaa cewa ina son wasu 'ƴan kuɗaɗe but tace in dakata, jiya ma na sake mata magana tace in jira”
Hannun shi ya sanya cikin nata yace.
“Meerah you are not going back to India har sai kinyi aure. That's my final decision. Kada ki damu i have already cleared everything da naje last month....”
Cikin mamaki tace.
“But Yayanmu an fa kashe kuɗi sosai, Is only one year I spend....”
“It's my money Meerah not yours. Sauka kije lokaci na tafiya”
Daga haka ta fice daga motar, da ba dan ta riga ta iso hall dinba da sai ta fashe da kukan baƙin ciki, amma dole tayi haƙuri ta bari komai ta ke ji har sai ta koma gida.
**********
Tunda muka gama rabon katin auren Azima na kama kaina ban sake fita ko ina ba. Na ɗaya ina duk wannan ne don kawai a ga tausayina a bar maganar auren mu da Idirisa na biyu kuma ina so ko FCET ɗin ce a barni in je in yi NCE.
Tun da Maina ya bani waya na share sa, duk kiran da yake min ina gani bana ɗagawa. Daga shi har Idirisan wani irin haushin su na ke ji.
Ina kwance bayan na gama sallar azahar ina danna wayata na jiyo sallamar Maimu.
Da Innani suka yi karo ina jin tana faɗin.
“Oh ni 'ƴasu! Wannan yarinya duk a gama ta kin haɗa dangi da Mayu. Yanzu mun samu Allah ya rufa mana asiri kursume ta nutsu wuri ɗaya muna batun aurawa Idirisa ita, shi ne zaki dawo ki zo don ki birki ta mata lissafi...”
Yah Naziru na jiyo shima yana faɗin.
“Tashi ki fice daga gidan nan malama”
Miƙewa Maimu tayi ba musu ta fice. Ni ma duk da muna faɗa naji ba daɗi yan da suka yi mata domin ba kyau wulaƙanci.
Washegari da tambayi Mama da sunan zan dubo wata 'ƴar ajin mu ta islamiyya da bata da lafiya daga can na sace hanya na wuce gidan su Maimu.
A mota na cimmata da wani suna fira. Tana ganina ta zuge glass ɗin motar zuwa ƙasa tana murmushi ta ce.
“Meet my new boy friend Sadeeq..”
Murmushi nayi ina kallon sa na ce.
“Hi!”
Shima dai murmushin yayi yace.
“Hlo!”
Daga haka na shige gidan su, bayan mun gaisa da mamansu da sauran mutanen gidan su na samu wuri gun inuwar bishiya na zauna, domin yanda zafin nan yayi yawa na tabbata ɗakin su ba zai yi daɗin zama ba akan yawanda suke da shi a ɗakin.
Bata fi minti goma ba sai gashi ta shigo.
“Sorry na bar ki kina jirana”
“No ba komai. I just came to apologize for what Innani and Yah Naziru did to you...”
Dariya tayi kamar abin bai yi mata zafi ba tace.
“kai Haba Kulsum, wallahi kina da abin dariya, miye abin bada haƙuri akan ɗan wannan abin. Ni fa na ɗaukeki tamkar 'ƴar uwa ta ne, iyayenki kamar iyayena ne ya yanki nima yayane a wurina, ba komai kada ki damu. Daman Maina ne ya dameni wai baki ɗaga wayar sa shi yasa nayi masa alƙawarin zuwa naji dalili...”
Tsaki na ja nace.
“Ban ga damar ɗaga wayar ba. Kin san ma wai miye ɗan rainin hankalin yake gayamin ranar? Wai shi wallahi so na yake da na bani shi dama tun tuni da yanzu mun daɗe da yin aure,ni kuma bai san na riga da nasan niyyar da ke cikin zuciyar sa ba”
Cikin nuna alhini tace.
“Kada ma ki yarda da shi Kulsum , jiya jiya abinda yake faɗamin wai wayar da ya baki ba a banza ba sai yasan yadda yayi ya cire ta a jikin ki...”
Cikin tsoro na ce.
“What?”
Saurin riƙe hannuna tayi tana girgiza kai tace.
“Ki kwantar da hankalinki Kulsum babu abinda ya isa yayi miki, ba wai ina faɗa miki haka bane don in ɗaga miki hankali, kawai ina faɗa miki gaskiya ne domin babu cuta tsakanin mu. Ki iya takon ki kawai shine”
Miƙewa nayi kaina har yana sarawa na ce mata.
“Maimu zan tafi ban faɗawa Mama cewa zan zo nan ba, Sai an jima”
Rako ni tayi muka fito waje nayi mamakin ganin saurayinta bai tafi ba wanda itama abinda yake ranta kenan.
Kai tsaye yace ta zo su rage mini hanya. Duk yadda na so dojewa hakan bai samu ba saida yasan yadda yayi yaja ra'ayina har na shiga motar. Ban bari suka ƙara sa dani ƙofar gida ba, daga nesa ba sauka ina musu godiya na shige gida.
OUM AMEER