KULSOOM

THIRTEEN

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

  PAGE 13

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

      Bayan sallar Magrib, muna cin abinci ni da khadija yaro ya shiga yace wai ana kiran Ummu-Kulsum a waje. Wani irin Zuuu! Naji hanjin cikina sun murɗa, ji nake tamkar numfashi na zai ɗauke domin babu wanda zai zo nemana in ba Idirisa ba.

Hannuna na tsame daga cikin abincin don nan ta ke naji abincin ya fita raina. Rai na babu daɗi na miƙe na je na wanke hannayena na zura hijabina na fita da nufin yi masa wankin babban bargo. Amma me? Tsayawa nayi ƙiƙam ina ƙare masa kallo, duk da cewa gani ɗaya nayi masa hakan bai hanani shaida sa ba.

Matsawa nayi with surprise nace.

“Why did you send for me? Da bashi ne?”

Murmushi yayi yace.

“Lallai na ƙara tabbatarwa akan abinda ta faɗa min a kan ki, cewa a tsaye ki ke baki shakkar komai...”

Cikin takaici na sa ke cewa.

“Malam why are you here?”

“I'm not Malam,I'm Sadeeq. And because I love you that's why I'm here”

Wani irin malalacin murmushi na saki tare da faɗin.

“You are not serious Sadeeq. Kana saurayin ƙawata daga haɗuwa kawai ka zo ka wani ce kana sona, wannan cin amana ne....”

“Ba batun cin amana Kulsum,Ko cikakken wata ɗaya ba muyi tare ba, saboda haka ina da damar zan sauya akala ta inda ni ke so. da gaske na ke. Tunda na sai ta Fitilun ganina akan ki naji kin kwanta min a rai ke na ke so Ummu Kulsum ba Maimuna ba...”

“You are just cheating your self because I won't allowed that to happen...”

“Then mi zaki yi?”

“I will definitely tell her and I will ask her to stay away from you Kai ba masoyin gaske ba ne. Idan har ace son gaskiya ka  ke mata to ba ni ba, ko wadda tafi ni so million ka gani ba zaka janye zuciyar ka daga gareta ba....”

“Ko mi zaki ce Kulsum now I love only you Ki je ki yi shawara ina jiranki..”

“Ba shawarar da zanyi, kada ka sa ke zuwa inda ni ke, idan ba haka ba I'm going to tell her. Yanzu bamu jima da gama chart ba tace kai ta ke so ta aura”

“I know you can't tell her cewa Wai na zo nace ina sonki, tunda ke ba mahaukaciya ba ce”

“ Sadeeq  I trusted Maimu and she also trusted me, Ina faɗa mata zata yarda. Kuma kada ka yaudari kanka cewa ba zan iya faɗa mata ba, zan iya”

Daga haka na shige na bar shi nan na shige gida abina.

Shi kuma kallona ya ke har sai da na ɓacewa ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya je ya shiga motar sa. Ko a motar sai da ya kwashe almost 30mnt yana saƙawa yana warwarewa sannan at  the end yaja motarsa ya tafi.

A daren ranar har bacci ɓarawo ya sace ni ban daina mamakin Sadeeq ba. Taya ma hakan zata faru, ban san mi yasa wani lokacin samari kwata-kwata basu da lissafi ba. Duk da cewa  ni shahida ce na gani anyi, saurayi ya juya ga ƙawar budurwarsa har suka yi aure. Ni har abada ba zan iya wannan ba musamman ga Maimu.

********

  Duk yadda Ayusha tayi ƙoƙarin hana zuciyarta karye wa wurin rabuwa da mahaifiyarta da kuma 'yan uwanta hakan bai samu.

  Kuka ta ke so sai tamkar wadda aka ce ƙarshen ganin ta da su kenan.

  Da ƙyar aka iya ɓanɓareta daga jikin Ayaa aka kaita ɗakin Khaldun kamar yadda ya bada umarni.

Sa'adu, Meerah da kuma Khaldun su ta tarar a ɗakin.

Kallo ɗaya Khaldun yayi mata yaji zuciyar shi ta karye ganin yadda ta ke ta gunjin kuka kamar wadda za'a kai lahira da ranta.

Cikin ƙarfin hali ya fara magana.

“Ayusha na san cewa ke macce mai matuƙar haƙuri da kawar da kai. Kiyi haƙuri ki zauna lafiya da mijin ki da kuma dangin mijin ki, ki kuma riƙe ibada....”

Waigawa yayi ya kalli Sa'adu wanda ke ta famar danna waya yace.

“And you! You are not a kid, ka kula da amanar yarinyar mutane Sa'adu. Ka barta tayi zumunci mai kyau da 'yan uwanka, kada kuma ka hana ta ziyartar dangin ta. Auren ka kada yasa ka nisanci mahaifiyarka ka kula da ita kuma ka nunawa matarka muhimmancinta a gare ka”

Gyaɗa kai Sa'ad yayi yana kallon yayan nasu yace.

“Thank you so much for being a good brother and also a father to us. Yadda ka ke ɗawainiya da mu muna maka addu'a Ubangiji Allah ya shiga lamarin ka, Allah ya biya maka buƙatunka na alkairi sannan ya baka mata ta gari mai yi maka biyayya tamkar yadda ka ke yi wa mahaifiyarka. Ayusha ƙawata kuma aminiyata ina miki fatan farin ciki a gidan auren ki har abada”

Duk da kukan da ta ke hakan bai hana kalaman Sa'ad na ƙarshe sanya ta murmushi ba.

  Kallon Meerah yayi yace.

“Meerah ki je Ɗan Jarida ya kai ki ya dawo da ke”

Hawayenda suka gangaro mata ta share sannan tace.

“To yayanmu na gode. A fito lafiya”

Suna ficewa ya janyo laptop ɗinsa ya ci gaba da aikin sa.

Ya na cikin aikin bai san lokacin ya zabura ya miƙe tsaye ba, sanadiyyar knocking ɗin ƙofar sa da aka shiga yi tamkar za'a cire ta daga bigirenta.

Cikin sauri ya nufi ƙofa yana mamakin wannan wane irin mutum ne ko dai bai san yadda ake knocking door ba.

A mamakance ya ja baya da sauri yana kallonta.

Murmushi tayi har cikin ranta ta na kallon sa tace.

“abincin ka Hajiya Ayaa tace in kawo maka...”

Cikin tsantsar takaici yace.

“Ke mahaukaciyar ina ce? Sai aka ce idan kika zo ki ɓallamin ƙofa, sannan ba ki san yadda ake sallama a gaisar da mutum ba? Iyeh! Ina magana kin tsaya kina kallona...”

“To ɗakin a buɗe na gansa da zan zo in yi sallama in shigo? An kama ƙofa an rufe kamar gidan yari sai da hannuwana ma suka yi ciwo akan ƙonƙwasa sannan kazzo kabbuɗe, mtsww. Ni dai a ina zan aje maka abincin Malam?....”

Nuna saman kansa yayi cike da ɓacin rai yace.

“Put it on my head stupid girl kawai”

Ajiye abincin tayi nan gabansa ta juya abin ta. Wannan mutumin akwai baƙar zuciya mutum kamar wanda za'a sanya lahira da ransa. Abinda ta ke ta mita akai kenan har ta koma cikin gidan.

Shi kuma rufo ƙofar yayi tare da jan tsaki ya koma ya zauna. Ya daɗe a haka daga ƙarshe ya ci gaba da aikin da ke gabansa.

Knocking yaji, wannan karon a hankali aka yi sau biyu.

“Come in”

Abinda ya ce kenan ba tare da ya ɗago ba.

Jin sallamar Hajiyar sa ya sa yayi saurin saukowa daga kan kujera yana faɗin.

“Sannu da zuwa Hajiya”

Gefen ɗayan couch ɗinsa ta samu ta zauna tace.

“Yawwa sannu. Ya naga abinci a bakin ƙofa?”

“Ni nace ta ajiyemin nan,Kuma sai ban samu dama na tashi na ɗauko ba har kika shigo”

Gyaɗa kai tayi tace.

“Kaga yarinyar ba? Sunanta Karima, ɗiyar Umaima ce...”

“Goggo Umaima kike nufi?”

“Eh Ita. Ba zaka san yarinyar ba saboda tana can hannun yayarta a ƙauyen Mallam Ɓaidu tana riƙonta shiyasa. Ita ce Alhaji Mu'azu yace a aura maka...”

A mugun firgice ya ɗago ya kalleta murya na cracking yace.

“Ha... Hajiya ita wannan ɗin?”

Tunda ta ke da shi bai taɓa katse ta a magana ba, duk yadda zatayi magana ba zai taɓa iya ɗagowa ma ya kalleta ba ballantana ya tsoma bakin sa a zancen ta. Ganin hakan yau yasa ta gane lokaci ɗaya yarinyar bata yi masa ba.

Murmushi tayi tace.

“Eh ita fa. Ba kace mace ka ke so wadda bata waye ba kuma ba tayi karatu ba? Ita ɗin ita ce daidai kai. Bari in je baƙi na jirana.”

“To Hajiya, Allah ya tashe mu lafiya”

“Amin. Gobe idan Allah ya kaimu su Karima za su koma garin su sai ka je ka mayar da su kaga kenan Kaga wuri. Auren kuma nan da wata ɗaya za'a yi shi in sha Allah. Sai ka yi ta haƙuri kowa haƙuri ya ke yi”

Daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin.

Yafi minti goma ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya kasa yi tamkar wanda aka sanyama sasari haka ya ke jin dukkan gaɓɓansa. Yau fa ake yinta, ana dara ga dare yayi. Duk da cewa zaɓi ya basu ai bai zaci abin ya kai haka ba. Wannan ga ƙurciya ga rashin tarbiyya ya zai yi da ransa kenan.

Washe gari ko haka aka yi, yana Office Hajiyar sa ta kira shi wai yazo su Karima sun shirya.  Ba shi da yadda ya iya haka ya zo.

Yana cikin mota bai fito ba ya kalli drivern sa Ɗan jarida yace.

“Kasan ina ne ƙauyen Malam Ɓaidu?”

“Na sa ni yallaɓai. Wani ɗan gari ne ƙarƙashin Talatar Mafara yake, can gefen colony.”

Nodding ɗin kansa yayi yana faɗin.

“Can muka nufa yanzu”

“To ranka ya daɗe”

Kallo ɗaya yayi musu daga ita har mutanen da suke tare su uku ya kauda kai. Sai  ma yanzu  da yasan alaƙa zata haɗa su ya kalleta. Kallon da yayi mata bai yi marmarin sake yin wani ba. Domin yadda ma ta zane fuskar ta zaka rantse da Allah ita ɗin Wata dodanniya ce a zimmar ita Kwalliya tayi.

**********

Bikin Azima aka fara satin nan wanda muke yau rana ta uku Alhamis kenan. Friends Evening ake yau. Shima tunda aka fara ban taɓa tsallake sharaɗin Mama ba. Ganin yadda Azima ta bani matuƙar muhimmanci yasa Mama bata hanani shawagi ba. Tun ƙarfe goma na safe na ke tafiya ƙarfe bakwai dot na yamma na dawo gida.

Tunda Maimu ta faɗamin wannan maganar dangane da Maina na daina ɗaukar kiransa in kiran duniya zai yi mini bana ɗagawa, a what'sapp ma haka bana ma duba chart din shi.

Gefe ɗaya ga Sadeeq ya addabi rayuwata ya dameni. Kiran safe daban na rana daban na dare daban duk da bana ɗagawa, ga text's waɗan da ban taɓa yi mishi reply ba. Duk yadda na so ɓoyewa Maimu dole sai na faɗa mata duk yadda zata ji ba daɗi tunda duk kashe din da nayi masa bai jiya ba.

             OUM AMEER