KULSOOM

FOURTEEN

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

          P14

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

  Kitchen take tana haɗa breakfast ita da Maryama. Wayar ta da ke ringing a farlour yasa ta fito ta zo ta ɗauka.

Cikin girmamawa ta gaishe sa ya amsa daga can ɓangaren sa yace.

“Meerah zanje Kaduna ne shi ne nace ko zaki rakani?”

Murmushi tayi tare da girgiza kai ta ce.

“Yayanmu kaje kawai bana jin daɗi”

“OK.. Allah ya baki lafiya”

“Ameen yayanmu na gode. Safe trip”

“Thank you”

Daga haka ya tsinke wayar. Shiru tayi tana nazari sai daga baya ta juya ta koma taci gaba da abinda take yi.

Khaldun kuwa yana tsinke wayar ya kalli Jodan da ke gefensa yana murmushi ya ce.

“Meerah ta canza”

“And why?”

“Because I stopped her from going back to school. Na ce ta jira har sai tayi aure tukun....”

With surprise Jodan yace.

“To tell you the truth Ko ni ne I will be mad at you gaskiya. Taya mutum ya fara wahala kawai a datse sa....”

“Remember it's my money right? Kuma Jodan I have my reason of doing that. Yanzu Ayusha da ke gidan mijin ta kada kaji yadda hankali na ya kwanta, bani da wata sauran damuwa. To sai naga Meerah a ɗakinta sannan zan ida samun nutsuwar rai. Matan ne yanzu wasu sun zama sai addu'a....”

“Ni zan gaya maka Zurmi, wallahi last week ina kan hanya wata ta tare ni titin can na gada biyu, kasan idan dare yayi ba'a cika samun abun hawa ba ni kuma tunani haka yasa na tsaya. Tana shigowa na tada motar bayan mun fito babban titi na kalleta na ce malama ina muka nufa. Kasan me? Wallahi kai tsaye ta ce min wai duk inda na nufa can ta nufa.....”

Zaro ido Khaldun yayi yana kallon sa. Ganin haka yasa Jodan fashewa da dariya yace.

“Wallahi daren ranar Zurmi Allah ɗai ya ƙwace ni. Nayi-nayi ta fito tace wallahi ita she has no where to go. Ga Madam Sai faman kirana ta ke taga dare yayi nace mata ina hanya amma ta ji ni shiru. Sai da nayi ta haɗa ta da Allah da ƙyar da kuma dubu goma na samu muka rabu...”

Cike da ɓacin rai Khaldun yace.

“Why did you gave her your money? Mi yasa baka tsitstsinka mata mari ba,ka janyo ta da ƙarfin tsiya ka wurgar a waje...”

Murmushi ya yi yana girgiza kai yace.

“Mata akwai Sharri Zurmi idan na taɓata zata iya taramin jama'a ta yi min sharrin da sai ya haddasa min saɓani da iyali na da kuma zubar da mutunci. Kai dai gwanda haka”

Taɓe baki yayi yana ƙara jin tsanar wannan halayyar ta 'yan matan zamani.

********

Tsaye muke cirko cirko ana dakon fitowar amarya daga cikin gida zuwa mota za'a kai ta gidan mijin ta.

Kallon Maimu nayi nace.

“Toh Maimu ni dai zan tafi gida. Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya na riga da na gama yiwa Azima sallama....”

Cikin nuna rashin jin daɗi ta ce.

“Haba Kulsum wai dan  Allah daman da gaske kike da kika ce ba zaki je Zariyar nan ba? Yanzu kina ganin kin kyauta idan ba ki je raka Azima ba? Bata da wasu ƙawaye sama da mu kema kin ga hakan. Tun jiya take roƙona dan Allah in roƙe ki kizo ayi tafiyar nan da ke...”

“Maimu Mama tace ba zanje ba sunyi magana da Baban mu ya hanani tafiya....”

“Kulsum ba fa can za'a kwana ba, yau zamu dawo. Nan da Zaria wani abu ne. Gaskiya idan baki je ba baki kyauta ba”

Shiru na yi ina saurarenta kawai ban sake ce mata alli a gawai ba. Fitowar Azima yasa na je wurinta ina mata raɗa daga jikin mayafinta da ta lulluɓe fuska na ce.

“Azima na wuce, Allah ya kaiku lafiya ya baki zaman lafiya sai mun yi waya...”

Tsananta kukan ta tayi tare da riƙe hannuna gam tace.

“Wallahi ba inda zaki sai kin rakani Kulsum Haba dan Allah! Ya zakiyi min haka. Gaskiya duk ba ki je ba ba zan taɓa yafe miki ba”

Jikina ne yayi sanyi nace.

“Azima gida ba'a barni...”

Wayarta ta dunguromin a hannu tana faɗin.

“Ga wayata ki Kira ta ki bani ita in roƙeta da kaina. Yau fa za'a dawo da wasu kinga sai ki biyo su ki dawo”

Ba musu na saka numbern Mama na kira sai da tayi ringing sau biyu ga na uku sannan ta ɗaga, tana yin sallama nace mama nice. Daga haka wayar ta yanke ina ta kuma gwadawa bata shiga.

Na nufi motar da aka sanyata ina miƙa wayata kawai ta jani ciki. Ga shi sai cewa suke ayi sauri lokaci ya ƙure ga tafiyar.

Ina shiga Maimu ta shigo ta rufe ƙofar.

Haka na haƙura tare da ƙudurta idan na dawo zan yi mata bayani.

Mun ɗan taɓa tafiya kaɗan na kalli Maimu baki na sai mui-mui yake ina son in sanar da ita zancen saurayinta Sadeeq da ke damuna. Kullum abinsa sai ƙara gaba yake kuma gashi a yadda na ga suke alaƙa da Maimu bai nuna alamar cewa yana son rabuwa da ita ba domin kullum suna tare ko a fili ko kuma a waya kuma ita yanzu ba ta da wani zance sai na auren su da zaran mun haɗu. Shi ne nike tsoro kada in faɗa mata tayi fushi har ya kai ga tace ta fasa auren sa hakan zai sa in zama silar rugujewar farin cikin ta. To ba zan so hakan ta faru ba.

Har na haƙura na fasa ƙudurina amma ganin yanzu haka shi ne ke kirana yasa na ƙara matsawa kusa gareta murya ƙasasa na ce.

“Maimu I need to tell you something very important..”

Kallona tayi tamkar mai jirana tace.

“Then I'm all ears...”

“Maimu ina so ki nutsu ki fahimci maganar da zan faɗa miki. Sadeeq...”

Kallon da take min ne yasa na ji shakku kaɗan a raina cikin dakiya nace.

“Sadeeq ba sonki ya ke ba Maimu. Shi ɗin mayaudari ne. Domin a ranar da muka haɗu da shi na farko ƙofar gidan ku a ranar yazo gidan mu ya furta cewa yana sona. Na nuna masa ɓacin raina matuƙa sannan na yi masa ba razanar cewa zan faɗa miki. Hakan bai sa ya janye mummunan ƙudurinsa ba, babu ranar da baya kirana ko kuma ya turomin text message. Ni ina ga ki rabu da shi kawai shi zai fi. Sai ma kinji maganganun da ya furta a kanki. Don Allah ki haƙura da shi in sha Allah Allah zai baki wani”

Wani malalacin murmushi ta riƙa yi wanda ni kaina ban san mi hakan ke nufi ba.

Bayan na gama magana sai da ya ɗau lokaci sannan ta sauke ajiyar zuciya tace.

“Turomin numbern da yake kiran Ki da ita sannan kuma ki turomin da text's ɗin”

Jiki na rawa na tura mata numbern ta What'sapp sannan na shiga gidan message na yi mata forwarding. Wasu ma sharewa nayi domin ba zan iya tura mata ba.

Numbern ta fara dubawa cikin ranta tana mamaki na domin ba numbern da ta san shi da ita bane ita bata san cewa yana da wannan Layin ba.

Messages ɗin ma ta duba kaɗan sannan ta ɗago ta kalleni a raina ina hopping Allah yasa ta yarda da ni.

Murmushi ta sake yi tana gyaɗa kai ta kalleni tace.

“Kulsum Wannan ba Layin Sadeeq ba ne. Ya riga ya sanar da ni komai. Bai kyautu ace wai kamar yadda muke da ke zaki iya zuwa bayan idona Kice kina son saurayina  ba. Rashin mijin aure ba shi zai sa ki nemi rabani da wanda zan aura ba. Tun ranar da kika fara kai masa farmaki ya sanar da  ni. Da ya nuna ƙin amincewar sa shi ne kika ɗaukar masa alƙawarin cewa sai kin raba mu komai rintsi. Kulsum kinyi kuskure Sadeeq yafi ƙarfin ki. Wallahi sai gani sai hange ta Allah ba taki ba....”

Kun san sumewa na kusa yi a  wurin domin a maganganun ta na fahimci cewa Sadeeq ya riga malam masallaci.

Hawaye tuni sun gama wanke min fuska ta A kiɗime na ce.

“Wallahi tallahi Maimu ƙarya yake ba haka aka yi ba ki yarda da ni. How would I do that to you.. Mi ki ka yi min? Kefa ƙawata ce.. Babbar ƙawata Maimu.. Sadeeq na yarda munafiki ne kada ki yarda da shi Maimu...”

Ɗaga min hannu tayi tare da kawar da fuskar ta gefen window alamar ba ta ma son Magana ta.

Hannu na Azima ta riƙe tana faɗin.

“Ki barta kawai Kulsum kada Allah yasa ta yarda. Allah shi yasan zuciyar sa kowa don haka kada ki damar da kanki”

**********

Har muka isa Zaria na kasa daina kukan da nake lokaci ɗaya fuskata ta canja kala. Idanuwa na sunyi suntum tsabar kuka. Azima sai aikin lallashi na take.

Tunda muka je ana gama cin abinci Maimu ta ɗauki jakarta ta bar gidan har yanzu ban sake ganin ta ba.

Duk yadda ake zuzuta kyaun gidan Amarya bai dameni ko abincin kasa  ci nayi. Ganin har ƙarfe biyar ta kusa ba'a yi zancen tafiya ba na miƙe na cewa Azima zan tafi tasha na hau mota ba zan kwana ba.

Muna cikin musu sai gashi an ce masu komawa Gusau su fito.

Sallama nayi mata ina kara yi mata addu'ar fatan zaman lafiya na fito. Ita kuma har ƙofa ta biyo ni tana ƙara bani hak'uri akan abinda Maimu ta yi min.

Ko bayan fitowar mu sai da suka sake tsayawa shiririta bamu bar Zaria ba sai da six ta buge. Yanzu kuma gabadai hankalina ya juye ya koma gida.

  Ina nan ina ta gwada Mama har yanzu baya shiga. Ina tsoron in kira Innani kuma ta zuge su Mama da Yah Naziru.

  Saura kaɗan mu iso 'yan kara na ji an cije burki wai motar zai duba yaji tana wani kuka na daban.

Kallon waje nayi naga har duhu ya gama mamaye ko ina.

Kallon matar da ke gefena nayi nace.

“Mudai don Allah su hanzarta dare na ƙara yi ga wurin nan ance ba shi da kyau....”

Bangama rufe baki na ba naga an fara gudu tamkar ana yaƙi. Kunnuwa na baza na tsinkayi cewa zancen Ɓarayi ake.

Ban san lokacin da na ɓalle murfin motar ba nima na ranci na kare.

Gudu nake duk in da zuciyata ta bani in bi can nike miƙawa. Bayan naci gudu na cikin daji ƙarshe kuma sai gani sa ke faɗowa kan titi. Banyi aune ba sai jina kawai nayi na faɗi ƙasa rijib sanadiyyar mota da ta buge ni.

Cikin tsananin tashin hankali mai motar ya fito ya nufo in da nike yana faɗin.

“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Hasbunallahu wa ni'imal wakil!...”

Abinda yake ta nanatawa kenan har ya zo gareni. Dalle min fuska yayi da fitilar wayar sa cikin tsantsar mamaki da kaɗuwa yace.

“What! You again??... Why always me?..”

Ban san mi yake cewa ba domin tuni na daɗewa da sumewa......

                OUM AMEER