FIFTEEN
💝 KULSUM 💝
P15
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
Jin ɗamshin da nayi a cikin kunnuwana na sanyin ruwa shi ya tabbatar min da cewa na dawo hayyacina domin hawaye ne ke ta kwaranya daga idanuwana bana wasa ba. Kukan ne kawai abinyi a gare ni yanzu domin na rasa ma wanne kalar tunanin zanyi.
Sautin ƙarar tafiya na ji hakan yasa na gaggauta tsayar da hawaye na tare da ƙara runtse idanuwana na nutsu tsab ina jira in ji wane kalar hukunci iyayen na za su yanke zuwa gare ni....
“Doctor I have already done what I can,all I can say Allah ya tashi kafaɗunta,but idan ta farka dan Allah ka sanar da ni i have gave you my digits already, saboda a san yadda za ayi a samu iyayen ta tunda babu waya a tare da ita”
Gyaɗa kai likitan ya shiga yi yana ƙara rusuna masa tamkar zai durƙushe saboda ladabi. Bayan Khaldun ya kai ƙarshe ne yace.
“Ranka ya daɗe ai samun irin ka kam wallahi sai an tona, saboda babban mutum irin ka ace saboda ya buge mutum ya tsaya zarya asibiti har tsawon kwana ki uku, Allah dai ya saka maka da mafificin alkairi”
Ƙayataccen murmushin sa ya saki sannan yace.
“Doctor wurin maganar ran ɗan adam babu zancen girma, na gode Allah da abin ya tsaya a haka, na gode ni zan tafi...”
Maganar su da ta daki masarrafar jina ta sanya ni gigitar da ban san lokacin da na wuntsilo daga kan gadon asibitin ba tare da sakin wata irin razananniyar ƙarar da ta kusa sanya su zubawa a guje. Sabbatu na shiga yi tare da ɗora hannuwana a kaina ina faɗin.
“Na shiga uku na lalace! ni yau naga baƙar rana a cikin tarihin rayuwa ta. Kwana uku a asibiti su Mama ba su san a ina ni ke ba... Wayyo Allah na! Kai co naahh...”
“Ke dan Allah rufe mana baki kinji ko? Ke da kika saba yawon barikin ki zaki zo nan kina mana wani ihun banza, am very sure ma yanzu haka daga wurin barikin kika fito...”
Girgiza kai na nayi tamkar wani ubana ya tsare ni na hau rantsuwa ina faɗin.
“Wallahi ba daga wurin yawo na ke ba, bukin ƙawata aka yi shi ne muka tafi kai ta Zaria akan hanyar mu ta dawo ɓarayi suka rutsa mu shi ne wurin gudun ceton rai a ka bige ni da mota...”
Cikin tsananin ɓacin rai ya katse ni da faɗin.
“Would you shut up Ko Sai na ɓaɓɓalaki a wurin? Marar kunyar ƙarya kawai....”
“Sir please calm down. Remember she just wake up now, so please ka bari mubi abin a hankali”
Abinda likitan ya cewa Khaldun kenan yana mai sassauta murya. Sai kuma ya ƙara kallon sa da mamaki yace.
“But yallaɓai kalamanka sun nuna kamar you know her, Kuma ga shi ka faɗamin cewa it's your first time da ka taɓa ganin ta”
Wani irin ƙugi ciki na yayi domin idan bai gane ni a lokacin da bana hayyaci na ba yanzu kam dole ya shaida ni.....
“Doctor irin waɗan nan yaran ko baka taɓa ganin su ba yanayin su kaɗai sometimes ya na iya nuna maka halin su. Daga yadda ta ke ta wannan ihun kaɗai ya tabbatar cewa daga yawon ta ta fito”
Hankalina ne naji ya ɗan kwanta ko ba komai a karo na biyu ya kare ni.
Miƙewa nayi tsaye still ina tsiyayar hawayen baƙin ciki na nufi hanyar da ke nuna alamun nan ake shigowa.
Da sauri Doctor ɗin yayi azamar damƙar hannuna wanda yasa na ƙara gigicewa na hau fisge-fisge ina faɗin.
“Wallahi ni gida zan tafi Mama ta na can na jira na, ban san ma yanzu a wane irin tashin hankali na bar su a ciki ba...”
“Malama ki nutsu hannun ki yana zubar da jini sakamakon cannula ɗin da kika fisge...”
“Bana jin zafin komai ka bar ni in je gida please..”
Wata irin muguwar tsawa Khaldun ya buga min wadda tayi sanadiyyar sanya min wata nutsuwa ta musamman ba tare da na sani ba.
Gefen gadon na koma na zauna, likitan ya shiga gyara min hannun nawa tare da faɗamin kalamai masu sanyi na cewa in kwantar da hankali na yanzu zan tafi gida kuma za su yiwa iyayena bayani yadda za su fahimta.
Sai yanzu na ji hankalina ya ɗan kwanta. Da fe kaina nayi da ɗayan hannuna sakamakon wani irin azababben ciwon da ya ke yi min.
Bayan ya gama na kalli gefen da Khaldun ya ke tsaye wanda ni duk a zato na shima ɗin likita ne.
Ganin irin kallon da ya ke min ne yasa na yi saurin kawar da kaina gefe ina mai dana sanin kallon sa da na yi.
Matsowa yayi in da na ke zaune ya miƙo min ƙaramar wayar sa fuska a tamke yace.
“Ki sanya min numbern Mahaifin ki ko mahaifiyarki, kuma idan kika yi kuskuren bani numbern wani banza wallahi i promise you sai na baki mamaki”
Ba musu na miƙa hannuna da nufin karɓa in sanya mai numbern Baban mu sai kuma lokaci ɗaya wani tunani ya ɗarsu cikin zuciya ta wanda ya katangeni daga karɓar wayar ta sa na janye hannuna tare da sa ke kawar da kaina gefe ɗaya.
“Ke! I'm not talking to you? Ko ni abokin wasan ki ne?”
Ban iya yi wa harshe na linzami ba kai tsaye na furta.
“Bani da numbern kowa a kaina ga shi kuma wayata ta faɗi. Allowed me I can take my self home”
“ƙarya ki ke yi. Karɓi wayar nan ki saka min layin iyayen ki, i want to talk to them...”
“Ni ban haddace numbern kowa b....”
Ihu ya hau yi min akan dole sai na ba shi numbern iyaye na, ni kuma daman tun ɗazu ni ke hasashen cewa so ya ke ya faɗa musu abinda ya faru tsakanin mu kwanakin baya, shi yasa na fasa ba shi numbern domin ko giya na ke sha ba zan yi wannan gigin ba, yana faɗa musu Baba na san zai tsine min kai tsaye ita kuma Mama zuciyar ta ce zata buga ta mutu lokaci ɗaya saboda haka idan sama da ƙasa za su haɗe wallahi ba zan ba shi ba.
“Yallaɓai kasan fa wani bai damu da haddace number ba ko ta shi ce, ka bar ta kawai...”
“Doctor I want to talk to her parent domin su san irin matakin da za su ɗauka a kanta, su tsare ta har sai ta faɗa musu inda ta fito because ni Sam ban yarda da duk ƙaryar da ta shirya mana ba....”
“Yallaɓai don't stress yourself too much, Kai fa ka faɗa da bakinka irin waɗan nan yaran akwai su da yawa. Wata ƙila gaskiyar ta faɗa domin a hanya ka bige ta kasan harakar bandits ɗin nan da gaske ne a wannan yankin namu. Idan ma ƙarya tayi ta yiwa kanta. Ka barta ta tafi, Allah ubangiji ya shiryar da ita ya shiryar mana da zuria baki ɗaya. Ka manta da ita ka barta ta tafi tunda bata son taimakon”
Wani irin sanyi ne na ji ya ratsa ƙahon zuciyata, tabbas wannan likitan ya huta da duniya domin yana cikin mutane masu fahimta da uzuri.
Wayarsa da ke ruri ya ɗaga cikin ladabi na ji yana faɗin.
“Hajiya Allah ya huci zuciyar ki, a yi haƙuri ina hanya yanzu in sha Allah”
Cikin sauri ya ciro kudi ya ba likitan, sannan ya ajiye min wasu a gefen da na ke zaune,daga nan ya sa kai kawai ya yi ficewar shi ba tare da ya sa ke kallon in da ni ke ba.
Sai yanzu ya ke nadamar tsayawa wurin wannan marar kunyar yarinyar saboda abinda ya ke tunkarar gaban sa kawai idan ya tuna shi ya ishe shi.
Wata Nurse ce likitan ya kira yace ta haɗamin kayana.
Sororo nayi Ina kallon ikon Allah domin idan zan iya tunawa ko dankwali babu a kaina ballantana aje ga mayafi ko takalmi amma sai ga shi tana miƙo min Leda wai in canza kaya tare da ajiye min takalmi a ƙasa. Ledar na karɓa ba musu na buɗe, abaya na gani da kuma hijabi ga cream ga toothbrush da sauran su.
Hijabin kawai na ciro na saka da takalmi na yi wucewa ta kafin ma likitan ya zo.
**********
Zuciyata ce ta ƙara tsinkewa yayin da na yi arba da ƙofar gidanmu. Duk addu'ar da ta zo baki na ita nike furtawa har na tura ƙofar gidan na shiga cike da karyewar zuciya na yi sallama. Tsaye na cimma dukkan ilahirin mutanen gidan har da ƙannen mahaifina ma.
Mama na fara haɗa ido da ita wadda ta yi zurun-zurun duk ta ƙare tamkar wadda tayi ciwon shekara, idanu sun yi mata suntum sunyi ja tsabar kuka da damuwa, Baba ma duk ya birki ce. Ko Yah Naziru da ni ke yiwa ɗaukar ma ƙiyi na kallo ɗaya da nayi masa ya tabbatar min da irin damuwar da yake ciki, khadija ma ta sha kuka kamar wadda aka cewa na mutu ba zan dawo ba.
Wata irin taslima Innani ta doka tana mai kafe ne da ido ta ce.
“Ke ɗiyagga ina kika shiga tsawon kwana uku. Ki sanya mu a bila'i da tashin hankali”
Kuka na fashe da shi tare da durƙushewa kan ƙafafuwana na ce.
“Na tuba Baba dan Allah ku yafe min, na tafi Zaria wurin kai Azima ba da izinin ku ba, kan hanyar mu ta dawo wa muka haɗu da ɓarayi kowa ya yanki daji wurin gudun ceton rai, shi ne mota ta kaɗe ni a ka kai ni asibiti wallahi sai yanzu na farfaɗo..”
“Ke Kursume kiji tsoron ubangijin da ya shaya miki awazzai. Kina nufin suma kika yi har kwana uku?”
“Wallahi tallahi ban san in da ni ke ba tun ranar sai yanzu....”
Ita dai Mama ta zuba min ido kawai tana kallona yayin da Baba yayo kaina yana faɗin.
“Wallahi ko kin ƙi ko kin so sai na ɗaura miki aure da Idirisa yau-yau ɗin nan ba sai gobe ba, in ya so ki mutu in mutuwa zaki yi. Mi ma zanyi da ke, mi zanyi da ganin ki, haihuwar ki sam bata min rana ba Ummu-Kulsum. A gidana zaki saka ƙafa ki fita tsawon kwana uku saboda baki ɗauke ni bakin komai ba, ai munje har gidan su shaiɗaniyar ƙawar taki....”
“A'a Sulmanu kada fa ka yi mata baki, ko wannan ka barta da shi kawai ya ishe ta da anyi auren ai magana ta ƙare...”
Ihu na saki tare da ƙara Sautin kuka ina roƙon Baba.
“Dan Allah Baba kada ka aura min Idirisa, wallahi idan aka aura min shi mutuwa zanyi....”
Wani irin azababben mari ya sauke min wanda yayi sanadiyyar zubewa ta a ƙasa ban shiryawa yana faɗin.
“Wallahi tallahi ko zaki mutu sai na aura miki shi, muddin kika ga baki aure sa ba to sai idan ɗayan ku ne ya mutu.........
OUM AMEER