KULSOOM

SIXTEEN

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P16

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

Khaldun....

     Faɗa Hajiyar sa ta rufe sa da shi tamkar zata cinyesa ɗanye shi kuma sai aikin bata haƙuri yake tamkar ya fashe da kuka haka ya ke ji.

“Tun ranar da ka dawo daga Kaduna na kasa gane kanka baka shigo gidan nan ba sai ƙarfe ɗaya na dare, na tambayeka kace ba komai aiki ne ya tsaida ka bayan damuwa ta bayyana a fuskar ka wadda ba ta aiki ba ce. Tun daga ranar kuma kullum a birkice ka ke. Ina so ka faɗamin gaskiya mi yake damunka”

“Hajiya yarinya na buge a hanyata ta dawo wa daga Kaduna. Shi ne aka kai ta asibiti ni ke zaryar duba lafiyar ta, Alhamdulillah ta samu sauƙi domin ɗazu an sallameta. Iyayen ta sun zo munyi magana na ba haƙuri....”

Cike da kallon mamaki Hajiya Ayaa ta ce.

“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu Khaldun abinda ya faru kenan ka yi shiru da bakinka ka kasa gayamin? Yanzu kuma halin da ka zaɓa kenan?”

“Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, wallahi ba abinda nike nufi kenan ba, na san muddin na sanar da ke zaki dorawa kanki wahalar zuwa ganin ta kullum da yin hidima, ni kuma ganin hidimar da ke gabanki yasa na ce bari in bar maganar kawai....”

“Khaldun a wanne asibiti ka kai 'yar mutane?”

“Hajiya FMC ce, amma har an sallameta iyayenta sun zo sun tafi da ita...”

“Gaskiya baka kyauta min ba, nan da FMC zaka ce abin zai min wahala, shekarun baya da Sa'adu ya buge wani mutum hanyar zuwa Zurmi ba kullum sai munje dubiya tai ba ballantana nan cikin gari...”

Hijabinta ta janyo ta saka ta miƙe ta ci gaba da fadin.

“Na san dai ka amshi lambar wayar Babanta yi maza ka kira shi muji wane unguwa su ke muje in dubo 'yar mutane kada su ce iyayen ka basu da tausayi...”

Wani irin zazzafan zufa ne ya ji yana tsatstsafo masa ta ko ina duk da sanyin ACn da ya mamaye ɗakin nata.

Wayarsa ya ciro ba gardama ya fara dube-dube kamar gaske. Sai da ya dauki mintuna sannan ya kalleta yace.

“Hajiya kin ga ban samu numbern mutumin nan ba, har ta fita daga gidan kira kin san yadda ake kira na a  ko wane lokaci....”

“Ta shi muje asibitin mu tambayi likita muji ai shi ba zai rasa adireshin su ba”

Jiki sanyaye ya miƙe suka nufi haraba. Mukulli ya karɓa daga hannun drivern sa ɗan jarida suka fice.

Addu'a ya ke Allah ubangiji yasa kada a sa meta a wurin. Allah yasa ta tafi kuma ya kasance doctor din bai samu bayanan ta ba.

***********

Kulsum

Ina cikin kuka ina birgima a ƙasa tamkar zan haɗiye zuciya na mutum ni ke ji saboda baƙin ciki. Da in auri Idirisa na gwammace mutuwata ta ɗauke ni a yau.

  Ledar da ke hannuna Yah Naziru ya warce tare da zazzage abinda ya ke ciki.

  Wani kallon takaici ya jefe ni da shi sannan yace.

“ke da mota ta kaɗe ina kika samo waɗan nan kayan harda kayan shafe-shafe?”

“Wallahi tallahi wanda ya kaɗe ni shi ya siyo min su kafin in farfaɗo....”

Wani Marin ya sa ke ɗora min wanda yayi sanadiyyar ɗaukewar jina na wucin gadi, ga gefen baki na sai zubar da jini ya ke.

“Miyasa da za'a sallame ki daga asibitin ba'a baki shaidar sallama ba? sannan shi wanda ya kaɗeki ko likitan miyasa ba su nemi iyayen ki ba kafin su baki sallama...”

Matsowa Baba Ayuba yayi yana kallon Yah Naziru yace.

“Naziru ka barta a bita a hankali mana, wata ƙila gaskiya ta ke faɗa. Yadda kuka karɓeta sam! Bai yi ba ya kamata mu tsaya a  ji ƙorafinta.....”

“Ƙorafin mi za'a ji daga gareta Ayuba? Ta ya zata sanya ƙafa ta fita tsawon kwanaki uku yanzu Kulsum har tayi wannan girman? Mi ta ke nufi? Yawon duniya ta zaɓa, ta zubar mini da mutunci na ko? To cikin biyu dole za'a yi ɗaya. Ko dai ta auri wanda na zaɓa mata ko kuma in sallamawa duniya ita....”

“Malam Salmanu duk wannan bata kai ga haka ba....”

  Waigowa yayi ya kalle ni yace.

“Ummu-Kulsum a wanne asibiti aka kwantar da ke?”

“FMC Baba”

Gyaɗa kai yayi alamar gamsuwa sannan ya ce.

“Zaki iya gane ɗakin?”

“Eh”

“To tashi muje... Kai Naziru ka zo mu tafi da kai. Ku jira mu dawo sai a san miye abinyi na gaba”

Ba musu na tashi muka nufi asibitin. Mai Napep na ajiye mu na miƙa muka shiga ina gaba suna biye da ni.

Ɗakin na amenity ne shiyasa ban sha wahala ba wurin gane sa.

Ido Nurse ɗin ta zuba mini har muka ƙara sa ciki.

Murya a dishashe nace.

“Dan Allah Sister  ina wannan likitan na ɗazu?”

Ficewa tayi tana fadin bari ta duba in yana nan. Hakan yasa na shiga yin addu'a a raina Allah yasa yana nan domin shi ne kaɗai hope ɗina a halin yanzu.

Kamar yadda Nurse ta ke kallona ɗazu shima haka ya zuba min ido da ya shigo. Hannu ya bawa su Yah Naziru suka yi musabaha sannan Cikin mamaki ya kalle ni yace.

“Kin tafi ba tare da izini ba kuma ga ki kin dawo. Yanzun nan Mutumin da ya kaɗe ki ya dawo neman ki tare da mahaifiyar sa ta duba ki, shi ne na faɗa musu kin tafi ba tare da na sani ba. Amma ta roƙi alfarmar dan Allah idan na same ki ko iyayenki in sanar mata”

Cikin mutuntuwa Baba Ayuba yace.

“Likita da gaske ne kenan tana asibitin nan tsawon kwana uku?”

Gyara zaman glasses ɗin sa yayi yace

“Sure. Bana nan aka kawo ta amma a bayananta na file ya nuna an kawo ta ƙarfe tara na dare, kuma bata cikin hayyacinta...”

Nan ya gaya musu duk abinda ya faru har da ƙin bayar da number da na yi don bada kariya ga wanda ya kaɗeni kada su ce yaƙi nuna kulawa gare ni.

Wata uwar harara Yah Naziru ya ɓallamin sannan yace.

“To akan wane dalili kika ƙi bayar da numbern?”

“Ba komai”

“Munafuka kawai”

“To yanzu tunda Allah yasa kun zo bari na kira shi su dawo....”

Da sauri baba Ayuba ya dakatar da shi yana fadin.

“Haba likita ai ba za'a yi haka ba, ga yadda ka faɗa mana ya kula da ita har ta farfaɗo ko wannan ma ya isa. Allah ya saka da alheri ya tsare”

“Gaskiya Baba kuma kuna da karamci Allah ya bata lafiya mungode. Amma duk  da haka zan so kuban lambar kada ta dawo ace na kasa cika mata alƙawari tun da Allah yasa kun dawo”

Lambarsa yah Naziru ya bashi sannan muka amshi discharge letter muka tafi gida.

               OUM AMEER