SEVENTEEN
💝 KULSUM 💝
P17
FREE BOOK
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
Marubuciyar:
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
KIBIYAR SO
GUDUN WUCE SA'A
SABABI PAID
Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:
@Ummu-ameer
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
Koda muka dawo daga hospital ɗin is already Magrib. Ganin su Baba duk sun wuce masallaci hakan yasa na wuce ɗakin Innani nayi kwanciya ta abina. Abubuwa duk sun bi sun jagule mini. Fata ni ke Allah yasa sanadiyyar lalacewar zancen auren kenan. Wallahi a koda wace daƙiƙa jin ni ke ina tsanar Idirisa ba don yana da baƙar kama ba sai dai kawai ko kaɗan bana ra'ayinsa....
A hankali na ji sautin saukar murya Mama a kunnena wadda ta jima da dishashewa tsabar kuka da damuwa.
“Kulsum yanzu haka yayi miki kenan kiyi ta janyomin magana. Kin san halin Innani sarai bakin ta ba ya iya yin shiru, yanzu har mutanen unguwa babu wanda bai san bakya gida ba..”
“Wallahi Mama ƙaddara ce, banyi niyyar tafiyar nan ba, ƙaddara ce kawai Allah ya rubuto da sai hakan ta faru, kuma duk tare da su Maimuna muka tafi,na kiraki in sanar miki sai naji ta a kashe”
“ko da naji muryarki kin kirani wayar ɗaukewa tayi ba caji,kuma sai khadija ta bar wayar nan gun Injin yara masu kawo niƙa suka ɗauke. Kin saka ni a uku, kin sakani a tashin hankali. Kin san halin Malam sarai, bai cika damuwa da abu ba amma idan ya ɗauki abu da ƙaimi to akwai matsala. Ai har gidansu Maimunar muke tace bata san inda kike ba, sai ita Azimar da Khadija ta kaimu gidansu suka tabbatar mana ɓarayi sun yi kidnapping ɗin wasu en biki kuma har da ke a ciki...”
“Mama kiyi haƙuri in sha hakan ba zata sake faruwa ba....”
“Duk naji. Yanzu ina so ki faɗamin ina amfanin haka? Ina amfani?”
Hawayena na share tare da girgiza kai na nace.
“Ba amfani Mama, amma don girman Allah kiyi haƙuri....”
Juyawa tayi ta fice abinta ta barni. Babu abinda ya ƙara ƙona mini rai irin wai Maimu tace bata san in da na ke ba, alhali duk itace ta kaini ga wannan. Mai yiyuwa kuma tayi haka ne domin ta huce haushin sharrin da saurayinta ya ƙaƙaba mini cewa ina son shi,but dole zan je wurin ta na ji dalilin da yasa ta yi mini haka.
*********
Maimu
A mota suke zaune suna fira da saurayinta Sadeeq. Yardar da tayi da Sadeeq ta ma wuce misali domin irin samarin nan masu shegen zaƙin bakin tsiya. Ga shi ya iya kashe ta da kalamai shiyasa duk samarinta ta rabuda su yanzu bata sauraren kowa sai shi. Ta riga ta gama sakankancewa da shi ne mijin ta da zata aura.
Kullum maganar ɗaya ce yaushe zai turo gidan su ayi magana.
Yanzu ma zancen da suke kenan.
“Babe kwantar da hankalinki, Dad ɗina ni ke jira ya dawo daga Germany,da zaran ya dawo before Rhamadan ɗin nan to ki fara ƙirga kanki a cikin amaren wannan Rhamadan ɗin”
Wani irin mugun daɗi ne taji ya kashe ta, ƙara narke masa tayi tana faɗin.
“Gidana da kace zaka kaini in gani fa?”
“Are you ready now”
Cike da zumuɗi tace.
“Yes dear”
Janyau ta gabas ya kai ta wani ƙatoton mansion wanda ya amsa sunan sa. Yana horn mai gadi ya fito ya buɗe suka shiga. Gate man ɗin tamkar zai durƙushe wurin kwasar gaisuwa a wajen su. Maimu jin kanta take wata sarauniya ta musamman domin bata taɓa tsintar kanta a wannan yanayin ba.
Hannu ya miƙa mata ta sanya nata suna kashe juna da murmushi suka nufi cikin gidan.
Tunda uwarta ta haifeta bata taɓa ganin gida irin wannan ba. Komai na gidan abin burgewa ne. Wani abinma bata taɓa ganin sa ba. Ginin sabo ne hatta fentin ba'a jima da kambala sa ba. Komai an gama furniture's ne kawai babu.
Ta ke taji wani tsoro ya ka mata domin in ta tasan cewa ko da gidan su aka sayar tabbas kuɗin ba za su sayi kayan da zasu tsara gidan nan ba.....
“Babe shirun nan da kika yi I know what you are thinking right now....” murmushin gefen baki yayi sannan yace.
“Don't worry komai na gidan order zanyi in sha Allah, ke nake so saboda haka bana buƙatar komai daga gidanku, ke kaɗai is enough for me”
Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi masa wani farr! Da ido tace.
“Thank you so much love, I appreciate your pure and true love for me. Allah ya bani ikon yi maka biyayya...”
“Haba ke ko duk bana son wannan na sha gaya miki, ina da kuɗi saboda haka babu abinda zai gagare ki muddin kuɗi zasu iya saya. Muje musha ice cream Ki rakani wani gun daga can na ajiye ki”
Har ya fice ta kasa ɗauke idon ta a kansa. Wato wata irin ƙauna ta ke yi masa ta haƙiƙa kai! Ita kaɗai tasan irin yadda take jin Sadeeq a ranta.
*********
Khaldun
Zaune yake a dinning area ɗinsa yana Breakfast. Sashen mahaifinsu ne bayan ya rasu ya baro ɗakin sa ya dawo nan da zama.
Sallama Meerah tayi ta shigo cikin shirinta na zuwa Islamiyya.
Kallonta yayi da murmushi a fuskar sa yace.
“Meerah my favorite, how are you”
Zaunawa tayi ta janyo plate tayi serving kanta tana dariya ta ce.
“Lafiya lau Yayanmu ina kwana”
“Lafiya”
“Ayaa ta faɗamin ka buge wata a hanya Allah ubangiji ya tsare gaba”
“Ameen”
“Daman Yayanmu I want to ask your permission Ina so Idan na taso zan je gidan Yah Sa'adu. Anty Ramlah zatayi tafiya zuwa Kebbi bikin en uwanta shi ne yace na rakata”
“Driver ɗinku ya tafi gida matarshi ta haihu ni kuma zamuyi tafiya da ɗan jarida, da sai in ce Maryama ta rakaki kinga ita ta rakaki no one will excourt her back. So ki bar shi sai na dawo da dare sai in ajiye ki tunda tafiyar ta ku gobe ne”
“ok ba matsala Yayanmu na gode.....”
Daga kallon da ta ke mishi yasan cewa there's something.
Saurin katse ta yayi da faɗin.
“I will transfer 100k for you Sai ki bawa ita matar Sa'ad 50k. Kuma ba zan ƙara daga haka ba don't even waste your time begging”
Dariya ta fashe da shi tace.
“Thank you Yayanmu Allah ya ƙara girma ya ƙara ɗauka ka ya ɗora ka akan maƙiyanka”
Mug ɗin Hannunsa ya ajiye ya juya yana Kallonta da kyau yace.
“Nasiru Lawal mai takalme. Iyayen sa na zaune ne a unguwar Dallatu, Shi ne 3rd born a gidansu yana da ƙanne guda biyar. Yayi karatunsa tun yarinta a nan cikin gusau in da yaje Biu yayo degree a makarantar Sojoji. Wanda yake a matakin second lieutenant a Nigerian army. Ya je course na 3month wanda ya rage some weeks ya gama. Bayan na gama tattaunawa da shi tabbas na ji ya kwanta min a rai. Matuƙar kin amince Hajiya ma ta amince Sa'ad ya amince to nima na gama amincewa ki je ki sanar da su domin da zaran ya dawo zai turo da magabatansa sai mu zauna da su Baba Mu'azu”
Cikin tsantsar mamaki ta ke kallonsa har sai da ya dasa aya, tsabar mamaki har bata san lokacin da tace.
“Yayanmu a ina kasan Nasir haka?”
Miƙewa yayi tare da zura wayoyinsa a aljihu ya nufi ƙofa yana faɗin.
“Naje mun haɗu da shi a Lagos last week. Do fast so that you won't be late, Idan aka dake ki ba ruwana”
Wani Kyakkyawan murmushi ne ya suɓuce mata, kasa ƙarasa cin abincin tayi tsabar farin ciki ta ɗauki jakar littafanta kawai ta fice.
*********
Hajiya Ayaa
Ni sai inga kamar baka farin ciki da auren nan Khaldun iyen! Yarinyar nan fa ko ba komai ita ɗin 'yar uwarka ce. Da uwarta da ubanka uba ɗaya su ke Kaga kenan zumunci bana wasa ba. Kuma auren nan ya riga da ya matso. In sha Allah muddin kayi haƙuri da auren nan wata rana zaka yi farin ciki da hakan.
Shi dai uffan bai ce mata ba kansa na ƙasa kamar ko yaushe. Amma a cikin zuciyar sa bai ma san yadda zai kwatanta yanda yake ji ba. He's dying inside ba zai furta damuwarsa ga kowa ba dangane da wannan auren but Allah ya sani ba wannan aure yake nufi su nemo masa ba. Yarinya ba komai cikin ta sai tsantsar rashin kunya. Ba wadataccen ilimin addini ballantana a kula da yaranka....
“Ka tashi lokaci na tafiya ku tafi. Allah ya tsare yasa a dawo lafiya. Ka tsaya kayi musu sayayya sannan ka bin cike su miye abinda suke so ayi na bukin”
“To Hajiya in sha Allah. Na gode Allah ya ƙara girma”
Daga haka ya tashi ya fice.
Duk duniya ba shi da wani amininda ya wuce masa Jodan amma a wannan karon ya zaɓi ya tafi da Sa'ad da ya je da Jodan domin bai san yadda Jodan zai ɗauki abun ba.
*********
Kulsum
Sama sama naji Khadija tana tashi na domin ko kaina bana iya ɗagawa sanadiyyar matsanancin zazzaɓinda ya taso ya lulluɓe mini. Daman ko can ba gama miƙewa nayi ba ƙarfin hali ne kawai irin na mai rai.
Jin na ƙyaleta ko motsawa banyi ba yasa ta janye hijaabin da na lulluɓa da shi tare da kai hannun ta kan goshi na zuwa kewayen wuyana. Zafi taji ya gauraye dukkan ilahirin jikina.
Ba shiri ta je ta kira Mama. Bayan ta zo ta duba jikin nawa komawa tayi ta ɗauko ledar maganin da likitan nan ya bawa Yah Naziru. Da ƙyar ta samu na ɗan kurɓa ruwan kunu sannan ta bani maganin na sha. Bayan en mintuna na rarrafa hakanan na gabatar da sallar Asuba.
Wuraren sha ɗaya na safe ina duƙunƙune cikin hijabi naji mata na shigowa ana ta famar rangaɗa guɗa. Tamkar saƙon mutuwa haka naji saukar ihun matan nan a dodon kunne na. Tsam na miƙe tsaye ƙyam kamar wata er maye na je na leƙa waje ta cikin labule. Tozali na yi da akwatuna guda uku da ƙarama sai kwalayen minti da lemu a gefe ɗaya mata sunyi dandazo kamar yau ne aka ce musu auren.
Ba zan iya kwatanta halin baƙin cikin da nike ciki ba a halin yanzu. Yanzu da gaske Baba yake ba zai janye zancen auren nan ba kenan. Hijabi na zara cikin sanɗa na sulale na bar gidan ba tare da nazarin inda na dosa ba.
Sai da na iso titi na yanke shawarar zuwa gidan su Maimu. Ko ba komai ita ɗin ƙawata ce wadda ba ni da tamkar ta,wata ƙila ta samo min wata mafita wadda na kasa samarwa kaina.......
OUM AMEER