EIGHTEEN
💝 KULSUM 💝
P18
FREE BOOK
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
Marubuciyar:
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
KIBIYAR SO
GUDUN WUCE SA'A
SABABI PAID
NUUDARR
BAHIYYA PAID
KRRAKNNKRM PAID
Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:
@Ummu-ameer
Ko Arewabooks:
Aminatu Ibrahim
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
“Mi ya kawo ki gidan mu?”
Tambayar da Maimu ta jefa mini kenan bayan mun haɗa ido da ita.
“Duk cin kashin da kika yi min bai ishe ki ba yanzu ma sai kin sa ke yi min wulakanci. Remember you are my best friend, Kada Ki bari wani ƙaton banza ya haɗani da ke, wallahi duk abinda ya faɗa miki ƙarya yake so kawai yake ya haɗa mu faɗa....”
Kalamaina ba ƙaramin ƙara tunzura Maimu suka yi ba. Cikin ɓacin rai ta miƙe tsaye tana faɗin.
“Ke ce ƙatuwar banza ba Sadeeq ba. Wallahi kin bani mamaki Kulsum ko in ce ma kina tsakiyar bani mamaki domin har yanzu ban gama farfado wa daga shock ɗin da kika bani ba....”
Roƙonta na fara yi ina magiya ina kuka akan dan Allah ta tsaya ta saurareni.
“Maimu please give me a listening ear, Wallahi Ina cikin damuwa. Yanzu ba lokacin wannan ba ne ki taimake ni Su Baba zasu aura min Idirisa kuma kin san cewa bana son shi.....”
“Bakya son shi saboda Sadeeq ya tsone miki ido shi kike so kike muradi...”
“Wallahi tallahi I don't have any interest on Sadeeq please ki daina kawo min ma maganar Sadeeq....”
“Then go and marry your parent choice Idan har ba shi kike targeting ba”
A yadda Maimu ta ke mayar min da martani cikin kakkausar murya ina ganin tsantsar tsana ta a cikin rinannun idawunta.
Ban iya sa ke furta mata ko kalma ɗaya ba kawai na juya na fice daga gidan na su ba tare da sanin ina na nufa ba.
*********
Hajiya Ayaa.
Zaune ta ke a ɗakin Mama.
Bayan sun gama gaisawa cikin mutuntawa mama dai tayi shiru tana mai nazari wacece wannan matar domin a iya saninta bata taɓa sanin wannan matar ba.....
“Hajiya na san ba zaki shaida ni ba. Ni ce Mahaifiyar wanda ya kaɗe yarinya a hanya. Bai samu sanar da ni ba har Allah yasa aka bata sallama daga asibiti to kuma bayan na zo sai aka ce har kun tafi da ita bamu samu haduwa ba, Sai yau likitan ya kirani yanzu ya ba ni adireshin ku.....”
Murmushi mama tayi tace.
“Allah sarki! Ai babu komai mungode Sosai Allah ubangiji ya saka da alheri ya kare gaba”
“Amin amin. To ina ita mai jikin? ina fatar ta samu sauƙi?”
“Alhamdulillah! Ta samu sauƙi har na ɗan aiketa”
“To babu laifi Allah ya ƙara lafiya”
Shiru ne ya ratsa tsakanin su sannan daga ƙarshe mama ta miƙe tana faɗin.
“Babansu ya fita sai dai muje ku gaisa da Innani”
“To babu laifi mu tafi”
Zaune suka isketa a tsakiyar ɗakinta tana famar fige zogale.
“Innani baƙuwa mukayi shi ne na kawo ta ku gaisa..”
“Ah to to Sannunta da zuwa..”
Tabarma ta ɗauko ta baza mata ta zauna ita kuma mama ta fita taci gaba da aikin da take.
Ido Innani ta zuba mata ta na ƙare mata kallo babu ko ƙeftawa sannan daga ƙarshe tace.
“Baiwar Allah ban shaida ki ba fa”
Murmushi Ayaa tayi sannan ta kora mata irin bayanin da tayiwa Mama.
Numfashi Innani ta sauke sannan ta girgiza kai tace.
“Wannan Yarinya wannan yarinya ta zama 'yar jakar uba. To Hajiya ka zaɓarwa kanka bijire wa iyaye ba dole ka riƙa ganin ba daidai ba a rayuwarka. Wallahi in faɗa miki yarinya ce mai hankali da nutsuwa ga ilmi kamar ruwa amma tunda ta haɗu da wata tsinanninyar yarinya shi kenan ta birki ta ta. Ke ko hajiya ka kama hanya ka je kai amarya babu izinin uwayenka ai dole kayi haɗuwa da tsautsayi domin hakkin iyaye ba wasa ba....”
Innani duk irin rayuwar da Kulsum ta keyi ita da Maimu babu abinda ta ɓoye mata har wannan abin da ya faru da kayan aurenta da aka kawo ɗazu sai da ta bata labari ƙarshe ta ce.
“To kinga dai duk abinda uban yayi ya tashi a banza da kuma rantsuwar da yayi na ɗaura mata aure yanzu sai dai a fitar mai da kono tunda uwar yaron ta rantse da abinda zai kasheta tace ba zai aure ta ba tunda yawon ta take zuwa tayi kwanaki bata nan. Bayan nan ta zo ta tsuguna tana roƙar mu a ba shi auren Kursume ɗin shine yanzu zata zo da wani bakin ta mai wari tace ba zata bar shi ya aure ta ba. To kuma abinki da harakar maƙota ga gida ga gida hmmm! Sai dai Allah ya sawaƙa”
Murmushi Ayaa tayi tace.
“To mi yasa suka fasa, haraka irin wannan ai haƙuri ake.......”
“Ke ko hajiya in an ce miki abu akwai 'yan hassada da ɓakin ciki, ai mutane en gulma a unguwa sun bani sun lalace ba za su ga annabi ba. Kinga duk mai neman hana sunnar ma'aiki! Duk mai neman hana wannan albarka wallahi ba zai ga daidai ba a rayuwar sa. Nan na kafe kai da fata na ce sai ta auri Idirisa amma da yake shi ma ɗin ba ɗan halak ba ne har da shi a watsa mana ƙasa a ido. To yayi wa kansa wallahi. Yanzun nan dawowa ta kenan daga gidan su na ƙare musu zance na saka Hadiza gaba da almajirai muka kai musu tsiyar kayan da suka kawo. kuma in sha Allahu sai ta samu wanda ya fi sa matsiyaci kawai mai baƙar fuska. Duk unguwar nan kowa ya san Sulmanu ba shi da abokin faɗa haka ma uwar ta Habiba ba ruwanta da kowa ko yawon maƙota bata zuwa kullum tana cikin gidanta tana neman na kanta, Sai kuma Allah ya shiryar mata da yaran nan uku da Allah ya bata.”
“Iya ban san ku ba haka kuma baku sanni ba. Shin zaku iya ba wa ɗana auren 'yar ku?”
Zaro ido Innani tayi tamkar taga wani bala'i tace.
“Hajiya daga haɗuwar farko, ba mu san juna....”
“Iya komai kika gani a rayuwa yana da dalili da sanadi, wata ƙila ita ɗin rabon ɗana ce shiyasa duk abubuwa suka zo a haka. Dan Allah ku bamu dama ni idan kun amince yau ma ɗin sai a ɗaura auren”
Kuka Innani ta saka har da sharce majina ta ce.
“Ai kuwa da kin rufa mana asiri Hajiya. Haka Sulmanu ya fita kamar wani mahauci domin ya gama sakankancewa akan auren nan yau amma sai suka zo suka watsa mana ƙasa a ido, wallahi na san yana can kasuwa amma hankalinsa baya jikin sa. Ita ma baiwar Allah Habiba tasha kuka kamar ranta zai fita daga ƙarshe dole ta bawa zuciyar ta magana ta fawwalawa Allah al'amarin. Sai ga shi yayi mana mafita tun ba'a je ko ina. Amma kuma bani ce na haifi Kursume ba banida hurumi akanta bari in kira ubanta yazo muji ra'ayinsa da uwar ta”
“Ba laifi Iya bari nima in kira iyayen sa da yake shi kuma yaron da zai yi wata tafiya nan zuwa mafara to sai gashi tafiyar gaggawa ta taso masa sai ya wuce zuwa Abuja, to amma ba damuwa ba ne in sha Allahu matuƙar kuka amince”
Magana kamar da wasa bayan Baba ya dawo suka tattauna ta faɗa musu asalinsu daga karshe ta koma suka yi magana da Alhaji Mu'azu suka koma dawowa tare gidan. Aka yi sa'a kuma Baba yasan Alhaji Mu'azun sosai domin a kasuwa wurin kasuwancin su ɗaya suna kusa da juna shi kenan sai faɗuwa ta zo dai-dai da zama.
Haka suka shirya komai aka ɗaura auren Ummu Kulsum Salman da Abdul Rahim Umar farouk Zurmi. Da misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma.
**********
Da ƙafa na sharto tun daga unguwar su Maimu har na kawo wata makarantar primary ciki na shiga na samu bakin wani iccen bedi na zaune na jingina a jikin sa. Kuka na ke ta rusawa tamkar mai ɗanyar takaba ina ta addu'a a raina Allah ya sassauta min ya zaɓa duk abinda yake alheri a rayuwata.
Wai akace bacci ɓarawo. Na ɗau tsawon lokaci ina karanta wasiƙar jaki daga nan ban ƙara sani ina kaina yake ba. Ni ka ɗai na san yadda nike ji a jikina ga kuma rashin ishashshen baccin da ban samu ba. ban san cewa na share dogon lokaci ina bacci ba sai da naji murya sama sama ana tashi na.
“Baiwar Allah.... Baiwar Allah”
A hankali na buɗe idona ina bin mutumin da ke tsaye a kaina da kallo tun daga ƙasa har sama.
Zaunawa nayi da kyau tare da amsawa murya can ƙasa nace na'am.
“Baiwar Allah tun wuraren ƙarfe biyu kika zaune a wurin nan gashi yanzu har magariba ta gabato, kina macce ya kamata ace kin tafi gida domin nan wurin ba shi da tsaro a gareki....”
Girgiza kaina nayi wasu sabbin hawayen na ƙara wanke fuskata nace.
“Baba ba zan iya komawa gidanmu ba domin ahlina nema suke su sanya rayuwata a baƙin ciki da kuma damuwa ta har abada....”
Tsohon hankali tashe ya shiga furta.
“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Yake wannan yarinya ma'abociya siffa da kamala irin ta yaran kirki masu tarbiyya ina mai baki shawara da kuma umartarki da kada ki bari kururuwar shaiɗan tayi tasiri a cikin ruhi da gangar jikin ki. Wallahi iyayen ki sune ginshiƙinki sune bangon jinginar ki kuma a yanzu da yi musu biyayya ne kawai za ki iya samun hanyar tsira. Iyaye ba abin wasa ba ne. Kiyi hakuri kiyi biyayya ga abinda suka zaɓa miki in sha Allahu zaki ga ribar wannan biyayyar da za kiyi wata rana....”
Ganin yadda zuciyata da dukkan gaɓɓaina suka bada haɗin kai wurin sauraren sa yasa ya dage yayi ta zuba min nasiha har da ta auren ma da za'a ɗauramin da Idirisan.
Tabbas maganganunsa ba ƙaramin tasiri suka yi ba a cikin zuciyata,sun janyo ni daga makauniyar hanyar da na faɗa wadda ta yi kusan halakar da ni.
Daga ƙarshe ya ce.
“Ki je kiyi hakuri, in sha Allah zaki ga sakayya. Allah ubangiji ya yi miki albarka, Allah ya zaunar da ke lafiya da mijin ki ya baku zuriya ɗayyaba. Kuma ina so ki ɗaukarwa Allah alƙawari daga kin fita daga nan ba zaki tsaya ko ina ba sai gida”
Share hawayena nayi na miƙe nace.
“In sha Allah na ɗauka. Kuma duk abinda ka faɗamin shima na ɗauka Baba, na gode sosai”
Ina isowa ƙofar gidanmu mukayi ido huɗu da Maina yana tsaye ya jingina a jikin motar sa.
Matsowa nayi kusa da shi yau cikin ruwan sanyi na mi shi magana na ce.
“Ina wuni”
“Lafiya ƙalau Kulsum. Hankali na ya tashi ina ta kiran wayarki bata shiga da na nemi Maimuna sai ta ce min anyi kidnapping naki hanyar ku ta dawo wa daga Zaria. Kuma sai da nace mata inzo in dawo da ku ta ce a'a akwai wanda zai dawo da ku. Kullum sai na kira ta tace min babu labarin ki ɗazu around five na Kira ta tace taji labari kindawo gida an yi miki aure. Tunda na zo na aika aka aiko min yarinya a faɗamin cewa ke yanzu matar aure ce kada na sake dawo wa”
Wani irin Dum! Naji zuciyata tayi tare da tsinkewa. Wasu hawayen ne suka sake wanke min fuskata wadanda ban ko nami ba ne. Daga karshe sai na sakar masa wani guntun murmushin da yafi kuka ciwo na ce.
“Ka ji ko? Hakan ya tabbatar maka da cewa you are late...”
“Kulsum ke ce kika janyo mana duk wannan, Allah ya sani So ɗaya na yi miki na haƙiƙa amma sai kika ce kin zaɓi rayuwar bariki da aure, duk abin da kike babu abinda Maimuna bata sanar da ni ba. Nayi nayi ki amince min tun tuni ki manta da wannan rayuwar kika ƙi...”
“To saurari ni abinda ta faɗamin a kanka , tace bada aure kake nema na ba kowa ya sanka kai fasiƙi ne, tayi bincike a kanka da ma dangin ka baki ɗaya.....”
Duk abinda ta dinga faɗamin ga me da shi babu abinda na ɓoye masa.
Daga yadda naga yana ta nanata Innalilahi wa inna ilaihi raji'un! Ya tabbatar min da tsantsar mamaki da tsoron da ya kama shi.. Bai jira komai ba kawai ya juya ya shiga motar sa.
Ina sanya ƙafata cikin gida naji gabana ya tsananta bugawa tamkar ana yimin lugude a samansa.....
***
OUM AMEER