KULSOOM

NINETEEN

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P19

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

NUUDARR

BAHIYYA PAID

KRRAKNNKRM PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

Ko Arewabooks:

Aminatu Ibrahim

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

 

Khaldun

Yana office ɗinsa yana jiran Sa'adu ya zo su tafi Mafara sai ga kiran gaggawa ya sa me sa zuwa Abuja. Cikin farin ciki ya kira Hajiyar sa ya sanar da ita tafiyar uzuri ta kama sa zuwa Abuja yana so tayi haƙuri a jingine wannan tafiyar a barta har ya dawo idan tayi masa izini.

Idan dai harakar kasuwancinsa ce bata wasa da ita shiyasa ba musu amince.

Haamdala yayi tare da godewa ubangiji akan wannan ɗaukin da ya kawo masa.

Shi kam ya zai yi da ransa akan wannan auren da Hajiya ke nema ta ƙaƙaba masa?

Ko minti ashirin bai ƙara ba ya tattara kayansa suka nufi Sokoto tare da Sa'adu.

Tunda ya sauka ya je ya haɗu da wasu baƙi bai dawo gidansa ba sai ƙarfe uku da mintuna na rana.

Wanka kawai yayi yaci abincin da ya zo da shi daga waje ya ɗan kwanta bacci ya ɗaukesa bai farka ba sai da aka gama sallar Magriba har duhu ya mamaye.

Cikin gaggawa ya miƙe ya je yayo alwala ya zo ya gabatar da Sallahr Magriba. Yana gama azkhr ya jiyo kiran sallar Isha sai kuma ya fita masallaci.

Bayan ya dawo ya ɗauko wayoyinsa waɗan da ya manta bai cire  a silent ba tun da ya fito daga meeting.

48miss calls ya tarar. Zaro ido yayi ya shiga call log. Kusan babu wanda bai kira sa ba a makusantan sa. Mamaki ne da tsoro suka taru lokaci ɗaya suka dabaibaye masa zuciya.

Hajiyar sa ya fara kira domin,da addu'ar Allah yasa lafiya.

“Haba Khaldun sabida Allah ina ka shiga haka?”..

“Hajiya ayi haƙuri wallahi bacci ne ya sace ni bayan na dawo daga meeting kuma sai aka yi rashin sa'a ban cire wayar a silent ba. Allah yasa lafiya?”

Washe baki tayi tamkar yana a gaban ta tace.

“Lafiya ƙalau Alkairi ne. Daman tun da rana nike kiranka in sanar da kai Baban ka ya nema maka auren yarinyar nan wadda ka kaɗe a hanya, Kaga ashe rabo ne a tsakanin ku shiyasa wannan ƙaddarar ta haɗa ku,to sai gashi baka ɗauki wayar ba. Yanzu Kuma an riga da an ɗaura sai fatan zaman lafiya”

Mamaki, tsoro, fargaba ne da al'ajabi suka hana mi shi ma yin magana.....

“Hello Khaldun kana jina kuwa?”

Numfashi ya sauke a hankali yana mai kokawa da harshen sa wurin neman haɗin kansa domin ya samu furta mata magana.

“Hajiya na gode Allah ubangiji ya saka da alkairi”

“Amin. Amin. Yaushe ne zaka dawo?”

“Hajiya sai zuwa jibi in sha Allahu....”

“A'a, ba batun jibi duk abinda zaka yi kayi shi ka gama ranar Alhamis ka dawo gida. Wannan karon kayi min afuwa na shiga cikin aikin ka amma kuma wani abin ya sha gaban wani”

“Hajiya ba komai in sha Allah zan dawo a ranar, Allah ya kai mu”

Yana katse kiran ya koma bakin gado ya zauna tare da rabka uban tagumi. Kamar wani ƙaramin yaro haka ya mintsini kansa domin ya tabbatar idan ma bacci yake ya farka domin wannan mafarki ne marar daɗin sauraro amma sai dai kash! Wannan ba mafarki ba ne zahiri.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!...”

Abinda ya ke ta nanatawa kenan har sai da yaji ransa ya ɗan yi masa sanyi kaɗan.

Wayarsa da ke ruri a gefen sa ya janyo ya duba, ganin sunan Sa'ad yasa yayi picking da sauri yace.

“Allah yasa wannan maganar da naji gun hajiya mafarki ni ke Sa'adu”

“Yayanmu Ango congratulations. Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya. Oga Jodan ma da shi aka yi komai...”

Cikin tsananin takaici da hargagi ya ce

“Ubanwa ya ce ka sanar ma Jodan ɗin?”

“Yayanmu mafi aka sari wasu abokan hulɗarmu fa an sanar musu sun zo, duk da abin yazo a ƙurarren lokaci wallahi baka ga yadda aka cika ba....”

Ƙitt! Sa'ad yaji ya tsinke wayar. Daga ƙarshe ma kashe wayar tasa yayi baki ɗaya.

***********

Turus nayi ina raba ido ganin matan Baba Shu'aibu da su Inna Mai jidda ƙanwar Mama, ga 'yan Uwa kowa yana nan tamkar biki. Wasu daga cikin abokan wasa na suna yin arba da ni suka fara guɗa suna ihu suna kiran min amarya. Tun ina yaƙe har na kai ga fashewa da kuka.

Ɗaki Goggo Rabi ta jani tana faɗin a ina naje na daɗe haka daga aika shi kenan na maida wuri na zauna. Ni dai  na san Mama bata aike ni ba kawai ta faɗa musu haka  ne kada a sake cewa nayi wani  laifin.

  Muna shiga na kalle ta nace Goggo banyi sallah ko ɗaya ba gashi har Magriba tana neman shige wa itama.

Buta ta miƙo min na karɓa kamar wata baƙuwa na nufi toilet.

Har ƙarfe goma ina ɗakin Innani kwance babu wanda yace mini ci kanki kowa sai sha'anin gaban sa yake.

Mutanen unguwa kuma sai shigowa suke kamar tururuwa suna ta wani Alkah ya sanya alheri yasa ɗakinta ne.

Ganin abin su ya ƙi ƙarewa yasa na kira  khadija tazo. Janyota nayi ta faɗo gefena ta zauna sannan na ce.

“Khadija da gaske wai an ɗauramin aure?”

Dariya tayi wadda ta sanya rai na ɓaci, cikin jin haushi na ce.

“Miye haka da iskanci ni abokiyar wasan ki ce?”

“To anty Kulsum tambayar ce taki ta bani dariya ai. An ɗaura ɗazu da ƙarfe biyar na yamma in sha Allah. Wallahi baki ga taron  nan ba tamkar an shekara ana shela an taru....”

“Tashi ki tafi dan Allah”

.

Salin Alin khadija ta fice ta barni ina mai dasa sabon kuka. Ko ta kan abinci ban bi ba haka ma su Mama ba wanda  ya zo inda nike haka na sha kuka na har na gode Allah sannan na yi bacci.

*********

Washe gari ina kuka ina komai haka Inna Mai jidda ta saka ni a gaba sai muje gyaran kai daga can muje lalle. Ina kuka ina komai haka ta sakani  gaba muka je tudun wada.

Bamu dawo ba sai kusan ƙarfe biyar na yamma. Ko minti goma ba muyi da dawowa aka shiga jido kaya daga waje ana kawo wa, kayan akwatuna ne da kayan saka rana da kayan sa lalle kai babu abinda babu. Komai munafurcinka sai dai ka gaji ka bar su. Domin naira ta ko ka tasha kashi.

Ni dai na zubawa sarautar Allah ido sai yadda aka yi dani bani da wani sauran kataɓus. Duk na fige na zabge lokaci ɗaya har ɓakin wahala nayi domin jiki baya samun gyara kamar yadda aka saba, gani nan dai kamar ba Kulsum ba.

*************

Ƙanwar Hajiya Ayaa ce Safiyya ta rufe ta da masifa kamar zata cinye ta akan miyasa zata aikata wannan ɓaranɓarama, daga zuwa ganin yarinya shikenan a laƙaba wa yaro.

“Safiyya in sha Allahu babu abinda zai faru sai alheri....”

“A'a anty, wannan fa ganganci ne kawai..”

“Ke dan Allah kada ki dameni fa a'a! Ke uwa ta ce da zaki tsaya kina yi mini faɗa sai faman baki haƙuri nike tamkar na saɓawa mahallicci na. Kiyi fatan alheri kamar yadda kowa yayi Safiyya muddin kina so mu shirya. Duk yadda ta lalace ina kyautata zaton wannan sai ta fi Karima domin tayi karatu iya secondary school ta tsaya daman kuma haka shi Khaldun din  ya ke sa. Na daɗe da sanin baya maraba da auren karima, kuma na ɗauki alƙawari sai yayi aure to kuma ga shi Allah ya cika mini buri na. Sai kuma addu'a da fatan zaman lafiya”

Safiyya bata da yadda zata yi dole ta ja bakinta ta tsuke. Ayusha ma hannu biyu ta karɓi zancen, Meerah kaɗai ce take ɗan ɗari-ɗari kuma ko ita don ance mata yayan nata bai san cewa za'a ɗaura mishi aure yau ba.

  Sa'adu ta Saka a gaba shi da su Ayusha suka je kasuwa suka haɗa komai da ake buƙata daga can suka kai mata ta gani tace Sa'adu ya nemi jodan suje su kai kayan yanzu yanzu da dubu ɗari.

***

            OUM AMEER