TWENTY
💝 KULSUM 💝
P20
FREE BOOK
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
Marubuciyar:
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
KIBIYAR SO
GUDUN WUCE SA'A
SABABI PAID
Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:
@Ummu-ameer
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
Maina
Tunda ya baro gidan su Kulsum ya rasa abinda ya ke masa daɗi, sai yanzu ya gane cewa Maimu makirci ne ta ke ta haɗawa a tsakanin su. Lallai ko sai yayi mata abinda ko wani aka ce ta sake ɓatawa suna ba zata yi ba.
Sai da gari ya waye sannan ya zo musu da zuugar motar police guda yayi parking ƙofar gidan su.
Duk 'yan gidan sai da suka shiga gigita da aka ce ga motar police a ƙofar gidansu ana neman Maimuna wadda ta ke zaune ta gama cancara kwalliya zasu yi tafiya da Sadeeq zata rakasa Kaduna.
Da full confidence ɗinta ta fito domin ita bata san ta taɓa kayan kowa ba. Lokacin da Maina ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari bata san lokacin da ta kife ba har ɗankwalin kanta yana zamewa.
Ba don police ɗin ya dakatar da shi ba so yayi ya naɗa mata shegen duka kafin ma a kai ga sauraren bayanan ta.
“Ni zaki ɓatawa suna Maimuna? Mi nayi miki? Ban taɓa saninki ba sai ta dalilin ƙawar ki da ni ke so, shi ne kika ɓatamin suna kika ce kinyi bincike a kai na ni da Ahlina ba mutanen kirki ba ne. Wallahi sai na ɗaure ki akan ɓata suna na da na iyaye na da kika yi kuma kaf dangin ki sai naga Uganda zai iya fitowa da ke. Duk gusau Familyn Mai Taya guda ɗaya ne, ke kuma Wacece ke duk faɗin Gusau da kewayenta?....”
Duk wanda ke wurin sai da cikinsa ya ɗuri ruwa domin sun san gidan da yake magana ba ɓoyayye ba ne a gusau.
Cikin tashin hankali Mamanta ta zo ta fara roƙonsa.
“Ɗan nan ka yiwa Allah da darajar iyayen ka kayi haƙuri ka yafe mata, wallahi ita ɗin ba kowa ba ce dan Allah Kay.......”
“Wallahi Wallahi Mama abinda tayi min har na rasa wadda ni ke da ƙudurin aura da ɓata sunan iyaye na ba zan yafe mata ba, sai ta je gidan yari”
Maimu ganin da gaske yake hankali tashe ta fasa kuka ta fara roƙonshi akan sharrin shaiɗan ne Ya yafe mata.
“Ai kece shaiɗaniyar yarinya na tare da ke da zuciya ɗaya kina binta da sharri. Kuma abinda baki sani ba ko yanzu ɗin ta fiki kuma har abada ba zaki kamo ta ba.... Officer please ku tafi da ita.”
Duk irin roƙon da suka yi masa bai tsaya ya saurare su ba ana sakata mota ya ja tashi motar ya bar wurin.
Sai da ta kwana gari ya waye sannan ya zo misalin ƙarfe goma sha biyu na rana, kwana ɗaya da tayi kawai duk ta fita a hayyacinta. Ga shi Sadeeq bai turo iyayen sa ba ballantana gidan su a san da zaman shi har su iya neman taimako daga gare sa. Yayi ta kiran wayar ta yaji ta a kashe yazo kuma ƙofar gidan su ya aika yaro ance bata nan. Hakan yasa yayi tafiyar sa.
Wani kallon wulakanci ya jefa mata sannan yace.
“Ke ƙaramar marar kunya ce ai da har kika yi la'asar da wuri haka. Wallahi ko yanzu kinci darajar Mahaifiyata da ta ce in zo in saka a sake ki wallahi da sai munyi shari'a da ke kin tafi gidan yari”
Hawayenta ta share tare da faɗin.
“Na gode, Allah ya baka haƙuri”
Ko saurarar ta baiyi ba ya kai ƙarshe da police ɗin ya tafi.
**********
Khaldun
Tunda Hajiyar sa ta faɗa masa zancen auren nan nasa ko sau ɗaya bai bawa ƙwaƙwalwarsa damar samun hutu ba. Wannan yarinyar? Wannan yarinyar da ta zaɓi bariki a matsayin sana'ar ta, ta kwashe kayan ta daga gaban ma'aiki, yarinyar da ko a mafarki bai taba tunanin haɗa hanya da ita ba, wai yau ita ce matar aurensa, shin wai ko dai bai ji ta da kyau ba ne? To miye ya kai hajiya gidan har zancen aure ya shigo har kuma wai akace har an ɗaura musu aure.
Yadda ya ga dare haka ya ga safiya, tun yana tunanin abu mai ma'ana har ya kai ga rasa mi ma zai yi tunani a kai. Abu ɗaya ya sani shi ne Hajiya bata yi masa adalci ba shi ya zaiyi da auren wannan yarinyar.
Duk jiransa da ake ba shi ya tafi wurin Conference ɗin ba sai wuraren sha biyu na rana.
Yana kan hanya hajiyar sa ta kira sa. Bayan sun gaisa ta ce.
“Yi maza ka turowa Sa'adu 'yan kudaɗe yanzu ina jira...”
“To Hajiya kamar nawa kenan za su isa?”
“Million biyar Ina ga zasu isa in sha Allah”
“Toh Hajiya yanzu za'a tura in sha Allah”
“Yawwa Allah ya tsare ya bada sa'a”
“Amin Hajiya na gode”
Gefen hanya ya samu yayi parking cikin mamakin mi za'a yi har na million biyar ya kira Sa'adu.
“Yayanmu tun jiya ni ke ta neman ka bana samu su Ayusha ma haka, Oga Jodan ma yace ya kasa samun ka...”
“Sa'adu mi za'a yi har na 5 million?”
“Ayaa ta faɗamin tana neman 5million na ce mata kuɗin yayi yawa sai an nemi izininka. Da ta nemi iyayen Anty Kulsum ɗin akan ba sai sun kawo mata komai ba,to sai mahaifinta ya kafe akan haƙƙinta ne dole sai ya bata, shine ya bayar da dubu ɗari bakwai da hamsin ta ke so ta haɗa”
“To ba damuwa ka bata”
“OK Yayanmu. Na ce yaushe zaka dawo ne?”
“Gobe in sha Allah”
“To Allah ya dawo da kai lafiya. Ammm! Yayanmu gidan Barakallahu Ayaa ta sa aka buɗe....”
“Why?”
“Ta ce saboda shi ne sabo ba'a daɗe da gama sa ba, nan ya fi dacewa domin ya fi kowanne girma..... ”
Kashe wayar sa yayi domin ji yayi maganar Sa'adun ma ta gunduresa.
*********
Tare da Goggo Rahana da tazo ɗazu da Inna mai jidda suka tafi kantin daji wurin saya mini kayan ɗaki.
Ni fa har yanzu ban yarda wai an ɗaura mini aure ba duk da cewar naga an taru sosai musamman yau an ƙara cika gidan mu. Ga mutane en unguwa sai shigowa suke group group wai sun zo ganina wadanda ban san daga ina suke ba.
Sai amarya suke kira min ni kuma duk lokacin da na yi to zali da madubi gani nake ina ƙara haukacewa ina yamutse wa kamar ba ni ba.
Wankan lallen da nayi jiya shi Innani tazo ta sake tasa ƙeyata gaba na sake yin sannan Goggo Rabi ta zo ta ta shiga yi min turaren jiki kamar jiya. Muna gamawa ta bani turaruka daban ta ce in mulke jiki na sannan in nemi wurin da na kwanta idan na ci abinci. Da to kawai na amsa amma ba don wai abincin yana mini daɗi a harshe ba.
Ina cikin yi Mama ta shigo riƙe da pillet a hannunta ta miƙomin tace.
“Yi maza ki cinye abincin ina jiranki muyi magana”
Ba musu na karɓa naci abincin duk da ban cinye ba na ɗan ci da yawa.
“Kulsum kinga in da kika fito ko? Ni ma kinga irin halin da kika riƙa sanya ni a ciki. Dan Allah dan girman Allah Kulsum ki rufamin asiri, ki rufawa kanki ki rufawa mahaifinki ki zauna gidan auren ki. Kin ga mutane har sun fara faɗin kuɗi muka bi muka yi miki wannan auren, duk da bamu san halin sa ba ina kyautata masa zato in sha Allahu daga yadda ya tsaya a kanka asibiti har aka sallameki da kuma karamcin iyayen sa...”
Kuka na ke kamar raina zai fita. Duk wata nasiha da uwa ya kamata tayiwa 'yar ta Mama tayi min ita ta sauke haƙƙinta ni ya rage in ɗauka ko in bari.
“Na gode Mama in sha Allahu zanyi amfani da duk abinda kika faɗamin. Dan Allah ki yafemin duk abinda nayi miki dan Allah ki cewa Baba ya yafemin...”
“Ba komai duk mun yafe miki. Share hawayen ki kije ki kwanta, Allah ya tashe mu lafiya”
Sama sama na dinga jin firar su khadija ita da su Ma'arufa tun ina sauraren su har bacci ya sace ni.
*********
Khaldun
Ko da ya shigo gida ƙarfe sha biyu na dare ta buga.
Yayi mamaki yadda yaga mutane sun cika gidan nasu kamar ana wata hidima.
Yana dumfarar part ɗin hajiyar ta su yaji surutu sosai hakan yasa ya wuce part ɗin sa kawai ya kira Meerah a waya ta zo.
“Yayanmu welcome!”
“Thank you Meerah. How are you?”
“Lafiya Lau Yayanmu. Me I'm not Happy with this your marriage..”
Zaro ido yayi cikin mamaki ya kalle ta ya ce.
“Why are you not happy Meerah?”..
Turo baki tayi tace.
“Because I heard it from Aunt Safiyya cewa you don't like it too. Ba ka san da auren ba, so na san baka son yarinyar.... ”
“No it's not so Meerah, I love her so much. Da amincewa ta Hajiya ta nemomin auren, ai na ga yarinyar kafin ma kowa ya ganta. So, Ki so ta ki ƙaunaci Mata ta tamkar yadda kike ƙaunar Ayusha da Sa'adu.”
Murmushi tayi har cikin zuciyarta ta amshi zantukansa. Riƙe hannun sa tayi tace.
“I rest my case Yayanmu ango. Allah ya bayar da zaman lafiya da kai da Anty Kulsum”
"Me ne?”
“Yayanmu cewa nayi Allah ya baku zaman lafiya kai da anty Kulsum”
A ransa ya ke tambayar kansa daman sunanta kenan?.....
“Yayanmu a kawo abinci ne?”
“A'a Meerah. Ba kuyi tafiyar ba ke da Ramlah?”
“Cewa nayi tayi tafiyar ta. Ga buki a gidan mu zanje buki gidan wa su. Yayanmu ka bani kudi please ina so in yi siyayya Yah Sa'adu 50k kawai ya bani”
“Meerah 50k bai isa ba, ba na baki 50k ba ranar? Ki je ki haɗa 100k kenan, na gayawa Haroon ya ɗinko miki Sababbin kaya ya kawo miki yau da veil ɗin su da shoes. To sai me zakiyi”
Maraire ce fuska tayi tace.
“Thank you Yayanmu amma dan Allah ka ɗan ƙaramin mana dan Allah...”
“Dan Allah ki je Meerah har kin fara sakamin ciwon kai, I will talk to Sa'ad ya ƙara miki 50 shi kenan.”
“Thank you Yayanmu good Night”
*********
Washe gari ƙarfe biyar na yamma aka jera motoci a ƙofar gidan mu.
Mata en gayu ne suka shiga shigowa gidan mu.
Rungumar da aka yi min ne yasa na yaye lulluɓin fuska ta ba shiri.
Cike da farin ciki Meerah ta kalle ni tace.
“Wow.... You are so Masha Allah sis in-law. You look beautiful and parfect. Yah Allah ya albarkace ku ya sanya ku zamo Sanyi da farin ciki wa junan ku. I'm Meerah Zurmi, the Yayanmu's favorite....”
Ƙwaƙwalwata na shiga yaƙi da ita akan ta bani haɗin kai wurin ganin na haɗa tunani wuri ɗaya domin in samu damar fahimtar mi ke faruwa....
“I'm the last born ga Kuma Anty Ayush....”
“Meerah please! Ki barta mana dan Allah. Surutunki yayi yawa”
Dariya tayi tace.
“Shikenan Anty Ayusha shiru amma Anty Kulsum ina matuƙar matuƙar ƙaunar ki”
Bin su kawai na ke yi da idanuwa amma ban san mi ke faruwa ba. Ya naga waɗan nan a nan? Su waye su mi suka haɗa da Idirisa ko en uwansa ne?
Hannu na yiwa khadija da na hango tazo, a kunnen ta na raɗa mata.
“Su waye waɗan nan khadija?”
“ƙannen mijinki ne mana. Ko jiya sun zo, anty Meerah da Anty Ayusha”
A birki ce na ce.
“Idirisa wai?”
“Wane Idirisa kuma Anty Kulsum? Abdul Rahim dai....”
Goggo Rabi ce ta zo ta ja hannuna muka fita. Ban ƙara tsinkewa ba sai da naga mun shiga mota wai an tafi a kai ni gidan mijina......
OUM AMEER