Page 15
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 15
"Ku saurare ni da kyau bawai na zo wajennan domin sa ba ne kad`ai a a'a na zo ne domin ku don haka ku saurari duk abinda zance da ku da kunnen basira,sa`banin haka na nufin kai tsaye yankewar rayuwarku".
"Ranki ya dad`e muna cikin rud`u,firgici game da dalilin bayyanar ki a cikin wannan k`asar ta BAIBAH,kuma meye ya ke tafe da ke,wanne k`udirin ne lilli`be a cikin zuciyarki da har ki ka kai ga yin wannan tattakin mai nisan zango,shin mun aikata wani laifi ne koko wani umarni ne ki ke tafe da shi zuwa gare mu ?",Ya k`arasa sauran zancen na sa a d`an tsorace da ita domin Zuciyoyinsu sun kasa yarda da ita domin kai tsaye halin da su ke aciki ya hana bayyanar hakan" Babu ko d`aya daga cikin abubuwan da ka lissafo,Ni na zo ne domin in nusassheku ga hanyar tsira da samun mafita a cikin halin da ku ke aciki","Mafita,tsira a cikin k`asar BAIBAH d`in,ta ya hakan za ta kasance,ko dai ba ki san k`asar BAIBAH ba ne ba,in kuwa kin santa to babu makawa ba shakka kin manta ta,ko kuma kin yi ma ta sanin baya ne,ko kuma na sama-sama,domin a tarihi k`asar BAIBAH na d`aya daga cikin k`asashen da su ka yi shura wajen tara Zakwak`urai kuma Hazik`an Jarumai wad`anda su ke fasa taro a duk sanda su ka tunkari runduna ko gari kai ko da kuwa alk`arya ne",Cewar Ayub,"Ba wai ina nufin ku shirya tak`alar yak`i a tsakanin ku ba ne ba a'a da akwai wata sirrantacciyar hanya da zan d`ora ku a kanta da kuma wasu dokoki ,wanda muddin ku ka bi su za ku samu hanyar tsira da za ta sada ku har zuwa K`asar BIHINAR Ƙasar ku ta Gado",Mu na sauraron ki ya ke shugabarmu,duk da na tari numfashin ki amma dai ina da magana,ta ya haka za ta kasance a ce mu fita da ga cikin Kurkukunnan ba tare da wani Dakare a cikin Dakarun Sarauniya Junayyah ya ganmu ba har mu ratsa cikin Garinnan mu isa ya zuwa ga`bar kogin da zamu hau jirgin ruwa a ce ba wanda zai ganmu ko su ankara cewar bama cikin kurkukun, abun dai da kamar wuya Gurguwa da Auren nesa, duk da dai na ji masu iya magana na cewa abun sa'a ne Wai Matar Falke ta haifi Jaki,akwai tarin d`aure kai a cikin lamarin ", cewar Jamal cikin d`an kwarin gwuiwar da ya fara sa mu sakamakon jin lafazin bakin ta," Ubangiji, zai kare ku daga garesu da ma duk sharrin da su ke nufin ku da shi,Ni dai ba na da wani abu da zan k`ara mu ko na fad`a mu ku face iya abinda aka aiko ni da shi gare ku,sai dai ina da tabbacin idan har ku ka yarda da abinda na gaya ma ku kuma ku ka amince gami da yin biyayya to tabbas ba makawa za ku tsira,Ubangiji zai ka re ku kuma zai ji da lamarin ku gama da ma kome na ku a hannunsa ya ke,Shi kad`ai ne mai yi a sanda ya so kuma ya bari a san da ya ga dama",Gaba ki d`ayansu su ka zube a saman gwuiwowinsa gami da duk`ar da kansu k`asa,su na mai dunk`ule hannayensu duka biyu guri guda tare da d`ora su kan k`irjin su saitin inda zuciyoyinsu su ke,muryar Habib na rawa ya fara cewa,"Mun bi Allah mun bi manzon sa ,mun bi ki ya ke shugabarmu, wallahi mun yi kuskure gami da yin danasanin yin jayayya da ke , dukkanin mu mu na cikin fargaba gami da tunanin ko wani shed'ani ko iblishi ne ke son yi ma na yawo da hankali da mu da Yarimanmu"......ta katse su da cewa,"Kar ku damu Yarana,ai na fahimci hakan tunda fari a ciki kwayar idonku,yanzu abinda na ke so da ku shine daren gobe in Allah ya kaimu shine dare da za ku bar cikin wannan kurkukun, hanyar da za ku kuwa bi,ta na a asalin d`akin kurkukun da a ka fara a jiye ku daga kusurwar gabas da akwai wani sak`o ko lungu a dai-dai wurin rami ne ko kuma ince da ku hanya ce d`od`ar da zata sada ku zuwa wajen Garin BAIBAH da zaran kun fita Kai tsaye, hanyar da ta bi hannunku na dama za ku bi, za ku yi tattaki har zuwa ga`bar kogin Nizla,anan za ku samu wasu fatake ma su Jigilar kaya zuwa K`asar Bazir,kar ku damu har ku Isa nan ba abinda zai same ku ,kai ko wanda zai mu ku kallon zargi ba za ku had`u da shi ba,domin Sirrantacciya kuma `boyayyar hanya ce, daga wannan k`asar ta Bazir sai ku sa ke shiga wani Jirgin ruwan da zai kai ku har zuwa K`asar BIHINAR, in sha Allah za ku isa cikin aminci da tsaro ba tare da kowa ya shaida ku ba,domin mutane k`asar BAIBAH za su bi sahun ku ne ta hanyar da za ta sada ku da asalin K`asar ku ta BIHINAR ne,ku tabbatar kun yi duk abinda za ku kada ku kuskura ku dakata daga abinda na fad`a mu ku ko da hakan zai sa ku bar wani daga cikin ku anan,duk runtsi kar ku tsaya domin ga`bar kogin Nizla a wata sau d`aya ta ke ci hakan ya sa ba sa mai da hankali a kan shige da ficen da ke wakana a wurin ,wannan shine sak`on da na zo mu ku da shi",ta kai k`arshe zancen na ta"Mu na Godiya da taimako tare da karamci da ki ka nuna ma na,da izinin Ubangiji za mu aikata yanda ki ka zayyana",cewar Ayub cikin k`ank`antar da kai.
"Ba damuwa Yaran kirki,yaran albarka,Zan yi kewanka ku sosai,idan Shalelena ya farka ku lallashe sa sannan ku ba sa hak`uri, ku ce da shi karda ya tada hankalinsa ,komi yai zafi maganinsa na hannun Allah, da sannu komi zai warware, kullin da a ka yi a cikin rayursa zai kwance,sirrin da ke lullu`be zai bayyana, za a yaye ma sa shimfid`ar mayafin sharrin da a ka yi ma sa,fitilar alkairi za ta kunnu a cikin bigiren rayuwarsa,zai yi tuntu`be da tushiyar alkairi,haske zai bayyana a cikin dind`ad`d`an duhun da ya mamaye rayuwarsa".....," Ranki ya dad`e wannan wacce irin dunk`ulalliyar magana ce,mun kasa fahimtar komi a ciki ",Cewar Salim," A'a kar ka takura tunaninnika da zimmar son gano abinda ya shallaki hankali da tunaninka, ka tsaya a matsayinka,Komi zai haskaka kan sa da kan sa duk abinda ya ke binne a Ƙasa zai bayyana kan sa,idan ya tashi kar ku biye ma sa duk rigimar da ya zo da ita ku kyale shi,ku bar sa yai duk abinda ya so,ya na da damar da zai yanke ma kan sa hukuncin da ya so,na barku lafiya",tana kaiwa zancen ta matsa saitin inda Yarima Haisam ke shimfid`e tamkar matacce,ya na barcin da bai shiryama sa ba,muryarta ce ta fara rawa a sa'ilin da ta ke saman kansa ta na yi ma sa magana,"Yarona Shalelena zan tafi ka yafe min yaudarar da nai ma ka ,na fad`a ma ka abubuwa da duk ba gaskiya ba ne ba,Na aikata hakan ne domin in samu damar da zan isar da sak`on da aka umarce ni da shi ,ka yi hak`uri na so ace na samu damar da zan yi sallama da kai sai da fitina da rigimarka ba za su bari ba,gashi ban san sanda zan sa ke ganin ka ba,wata k`ilama ko ba zan sa ke ganin na ka ba,Ina son in sa ke had`uwa da kai sai dai ina tsoron faruwar hakan ,domin a duk sanda na ziyarce ka wani abu muhimi ne zai faru ko ya faru da kai,mai dad`i ko akasin haka, wannan karan ban zo da me dad`i ba,sai dai ina rok`on Allah da ya sa idan har zan sa ke dawo ya sa labari me dad`i ne zai kawo ni,ka yi hak`uri da k`addarar da Ubangiji ya jarabce ka da ita,da izininsa komi zai warware za ka dawo tamkar kowanne d`a,za ka samu soyayyar Mahaifinka,Kai ba ma shi ba gabad`aya Ahalinka da mutanen Masarautar ku sai sun so ka sun yi alfari da kai kuma sun yi murna da haihuwarka sai sun shaida cewa kai d`in ka fi kowa ,tuni ka dad`e da ta ka matsayin da ba su yi zato da tsammani ba,ina so ka sa ni ko a cikin rak`uma Allah ke fidda Amale, ka sa hakan a ranka da zuciyar ka,don haka kar ka damu da komi da kowa, zan tafi da tarin kewanka inajin nauyi a k`asan zuciyata,duk da na yi farin cikin ganin ka ,ka girma sosai ka kuma k`ara kyau ,ga hankali da haiba duk sun bayyana a gare ka"....... Sautin muryarta ya fara rawa alamun zuciyarta ta karye ,"Sai wata rana zan koma inda na ke Rayuwa, Zan koma makwanci na ,idan ka tashi kar ka yi hayaniya da yawa,a saboda ba na nan ,ka bi komi a sannu da hankali sai wata rana abun K`aunata zan yi kewar ka shalelena .....",ta na kai wa nan a zancenta ta fara disashewa tamkar hayak`i lokaci k`ank`anin ta `bace `bat tamkar ba ta ta`ba wanzuwa a wurin ba.
*KARAGAR MULKI*