TUDUN ADAMA

12: Karya me karfi

by @mbello38

Idan zaka kawo karshen makiyinka, ka karya na kusadashi. Suke hura me wutan babbaka. Abinda adeela takeyi kenan. Ta gama da gumza saura tabi 'yan matan tashera ta rabasu da ita.
Zimba ya kalla adeela yaga lallai se kara girman ciki takeyi dana jiki, don tama fishi girma. Hakan ze tabbatar da sata a cikin takaran sarauniya. Tunda yanzu ta warke zata iya takaran gaskiyan.
Suna zaune a dakin maganine tareda da sintura, pitinau da binu. Suna neman mafitane wurin karya tashera kafin takaran gaskiyan.
"Cikin 'yanmatanda tashera tafi yarda dasu akwai bompai, tseela da jera. Idan mukayi nasaran rabata dasu, to lallai adeela zatayi nasara ba tareda wani me ja mata cikas ba." Zimba ya bayyana.
Binu ta matso kusa ta kallo kowa. "In har zamuyi nasara akansu, to se mun rabasu daga junansu munyi harinsu in suna su kadai."
Bompai sojace kuma aikinta gadin dakin ma'adinai ne. Nan ne makwancinta yake tareda sauran sojoji masu gadin dakin. Tana zuwa rage dattin ciki kullum bayan charan zakara. Sintura ta bayyana.
Tseela leburace me tara abincin gina jikin sarauniya. Akwaita da iya dibara da hada tarko me wuyan sha'ani. Tana kadaitane lokacin wanke jiki. An rasa meyasa bata wanke jiki tareda kwari. Pitinau ta bayyana.
Jera kuma aikinta irin na sintura ne, amma ita kula take da yaran kwarin sarauta. Wato wadanda nan gaba zasuyi takaran mulkin tudun adama. Lokacin kadaicinta shine in taje karbanma yara magani. Tana bita boyayyiyar hanya. Sintura ta bayyana.
Boyayyiyar hanya wata hanyace da ma'aikatan kwarin sarauta kebe don yi musu hidima cikin sauri ba tareda bata lokaciba, short cut ce.
"Sintura, kin tabbatar da lokacin kadaicin bompai, ita kadai take?" Adeela ta tambaya cikin kokonto.
Sintura ta tabbatar mata tabita a boye cikin kwanaki biyu dinnan kuma taga kodayaushe, ita kadai ke zuwa ba tareda abokantaba.
"Meya faru da tseela ne pitinau da take boye jikinta?" Adeela ta tambaya tana tunani.
Duk binda pitinau tayi mata, ta kasa gano silan kadaitanda tseela keyi.
"Ki kara jajircewa wurin nemo sirrinta."Adeela tace.
Adeela ta kallo binu. "Kiyi hankali da bompai don tashera tafi yarda da ita duk cikin kawayenta."
Ai binu tasan ta yanda zata bullo mata. Ta tabbatar ma adeela wannan ba damuwa bane.
"Kai kuma zimba, kasa idanu akansu kwalafara da mazansu. Ina kyautata zaton zaka iya wannan!"
Zimba ya kalla adeela yayi murmushi yace mata wannan kaman kurban ruwane. 
Adeela ta waiga ta kallo pitinau. "Pitinau mu fara da kwaronki tseela, sa kokonto a zuciyarta."

Cire kafa kiyashi tayi daga daya daga cikin kafafunta na baya ta ajiye gefe sannan ta cumbula cikin rafin wankan kwari dake cikin tudun adama. Tseela tayi iyo ta juyyuya ta gaba da baya ta wanke jikinta tas sannan ta fito.
Fitowanta daga ruwa bat, kafa yace daukeni. Tabdi! Ya akayi.....waya.....ina kafanta yayi?! Ta dingisa tayita dubawa ba kafa a kusama da rafin.
Haushi ya turnuketa don tasan watace ke wasa da hankalinta. Zatako ci kaniyan koma wacece dake wasa da ita haka!
"Koki fito min da mallakata ko inna nemoki kisha wuya!"
Haba! Haka zaki sakawa wanda keson taimakonki?"
Tseela ta juyo da sauri a tsorace. Taga pitinau zaune kan wani dutse dake bakin rafin rikeda kafan tana wani juyyuyashi tana magana.
"Ke pitinau! Meya hadaki da kafata?!!"
Pitinau ta murmusa ta kalla tseela kallon asirinki ya tono. "Ashe shiyasa baki wanka a gaban kowa. Kafa biyarne dake. Haba shiyasa wani lokaci se in rantse tafiyanki ba daidai bane."
"Bani kafata, koki shiga matsala babba!"
Pitinau ta kalla kafan ta wurgama tseela. Yabi iska tseela ta cafke. Tayi saurin makalawa sannan ta hararo pitinau.
"Me kike nufida kina son taimaka mini? Kinga nayi kamada me neman taimakone?"
"Keko kina son kiyi rayuwa a tudun adama? Ki rike aikinki, ki cigabada kulada jama'an tudun adama? Ko so kike a koreki tareda tashera donkun sabama doka?" Tana zaune tana bada bayani.
"Tashera kanta kawai ta sani. Ita ke fada da adeela bake ba. Kwari an sanmu da hadin kai. Yaushe zaki yarda wata karyayyiyar soja tajaki wuta ki babbake. Ki sani inde tasherace, ta gwammaceki kone ke kadai ita kuma ta cigabada da azabtarda jama'a, duk akan abindama ba fadankiba."
"Kina son inci amanar kawata kenan?"
Pitinau ta tabbatar ma tseela cewa tashera ba kawar arziki bace, ba kawar ajiyewa bace, ba kawarda zata yarda da ita bace. Son kai da mugunta ya mata yawa,
Kuma amfani takeyi da kawayenta badon ta damu dasuba. Tana zama mara amfani wurinta zata rabu da ita batareda wani tunani na biyuba. Kuma duk cikin kawayenta ai tafi jida sauran biyun akan tseela.
Itafa leburace kuma sojoji sun raina leburori dukda su suke samo musu abincin cinsu. Tayi kawane da tseela kawai donta samu abinci a kowane lokaci ta bukata.
Inda tseela zata hanata koda na yini dayane, zataga gaskiyan kulanda tashera take mata.
"Amma idan baki yarda daniba. Kije mahadarku kiga yanda zata nuna miki banbanci tsakaninki da sauran kawayenta biyu." Ta juya ta fara tafiya. "In kika gano gaskiya, kinsan inda zamu hadu." Ta wuce abinta.
Tseela ta kalleta kawai ta wuce abinta.

Abin nata damun tseela a zuci harta isa mahadarsu. Taga tashera na kesa bompai wurin aikin samo mata hadin gwiwa daga sauran sojoji. Yanzu kusan kowane soja yana gefenta.
Ta kesa jera akan tara mata yaran sarauta masu goyon bayanta wurin nuna mata soyayya. Yaran sarauta da yawa suna goyon bayanta.
Seta kallo tseela ta watsar. "Ji wannan leburan se yanzu take zuwa."
Tseela tayi murmushi ta karaso da sauri. Tashera ta tari numfashinta kafinma ta tsaya gabanta.
"Me kika kawo min?"
"Ai abinci shine abu mafi amfani a jikin kwaro saboda yana......."
"Sakarya da sakaran zancenki na abinci. Ba abinda na tambaya kenanba lebura! Me kika kawo min nace!!" Ta rafkama tseela ihu a fuska.
Tseela tayi jim tana tunanin maganan pitinau. Jide yanda tashera ta gama kesa wadancan amma ita sede ta hadata da ihu da rashin mutunci. Ta girgiza kai. Anya, bazata bari pitinau ta rabata da kawarta.....
Tashera ta katse mata tunani. "Aw! Bakima samo min komaiba kika kwaso tarkacen jikinki kikazo nan?!"
Sauran suka fashe da dariya. Tseela taji zafin maganan amma yata iya? Haka nan ta shanye rashin mutuncin.
"Shiyasa nace muku tseela nan batada wani amfanin fari balle baki......"
Tseela ta amayo dagargazazzen masara ta mulmula shi ya zama kwallo tabawa tashera. Fizgewa tashera tayi ta antaya cikin baki ta tauna. "Hm, dayan yafi dadi amma wannan ma zeyi a yanzu."
Tseela ta dan matso kusada tashera. "Dama ina so in miki wata magana....." Aka katseta.
"Uhm?" Tana tauna abincinta.
"Yau bazan iya samo miki na dareba sede kije wurin cin abinci kaman kowa......."
"Sakarya, dama nasan ba wata magana muhimmiya bace zaki min. Wuce kiban wuri!"  Tashera taja kawayenta biyu sukayi gaba.
Tsaye tseela take tana kallon bayansu cikin takaicin abinda tashera ta mata. Bata mata kirki ko kadan. Duk wannan wahalanda take tayi, kusan sau goma a rana take ciyarda tashera amma wannan shine godiyan da take samu! Tuni taji zafi ya cika zuciyarta, taji wani haushi ya mamaye zuciyar. Ta wuce a fusace.