TUDUN ADAMA

14: Karya me karfi 3

by @mbello38

"Ki saurareni kiji, bompai." Ta kalla bayanta taga ba kowa ta maida kallonta ma bompai.
Wohoho! Wannan bazata barta taje tayi abinda zatayiba seta saurari wani magananta! To shikenan! "Menene wai?!"
Su kananan sojojine a tudun adama......
Kaman bata san wannan ba, bompai tayi mata kallon seme?
Amma suna yin aiki me muhimmancine a tudun. Kirga kwarin fita da kwarin shiga abune dake tabbatar da yawa da lafiyan kwarin tudun adama.
Idan an samu kari suna sani, in an samu ragi suna sani. In karine dama na leburorine amma in ragine, sesu tura wasu sojojin suje waje neman kwarin, ko a raye ko a mace se sun dawo dasu.
"Waime kikeso kicene?" Ta tambaya cikin matsuwa don yanzu abin harya kaiga bompai matseshi takeyi karya watso waje, shi kashinba.
Sati uku da suka wuce an samu ragi da dama harya kaiga abin ya fara basu tsoro don suna tunanin ko wani dabbane babba kaman jangwale ke cinyesu.
"Uhm?"
Se suka tura binturai da sojojinta suje su binciko meke kawo bala'in raguwar kwarine haka. A binciken su suka gano tasherace ke tura sojoji da leburori zuwa wurin katanga har jangwale yake samun daman cinyesu.
Daga baya wani labari me girgizawa yazo musu daga kwaro daga tudun mitsili wai tasherace tayi yarjejeniyada wani bakin jangwale kada ya cinyeta inya ganta ita kuma zata dinga turame abinci batareda ya wahalaba.
Aise kashin yabar turowa cikin bompai yayi wani irin kara seda akaji. Binu ta kalla cikin, bompai ta kalla cikinta se suka hada idanu.
"Gwara kije kiyi abinda zakiyi." Binu tayi gaba.
Kan bompai ya buga tana komawa wurin aikinta tana tunani. Tashera tayi yarjejeniyada jangwale don a halaka jama'anta don ita ta samu saukinshi!
Kai! Abinda da wuyan yarda.......seko ta hango tashera tareda wasu sojojin tudun suna tattaunawa. Taso tazo wurinta se kuma taga ta wuce tabi wani hanya a boye.
Bompai tabi bayanta taga ta shiga wani dakinda inda bata bitaba, bazata gane akwai kofaba a wurin. Tako bita ta hango tashera da dareja suna tattaunawa ta labe.
"Yanzu ya ake ciki da adeela? Kinsan ita ke kawo min cikas a takaran nan."
Tashera ta tabbatar mata cewa komai na tafiya daidai da yanda tsarinsu yake. Amma tambayan shine, ya za'ayi da kwalafara? Dareja ta tabbatar mata da cewa kwalafara bazata zamo mata cikas a takaran sarauniya ba.
Tashera tace sede in za'a farka ne aga kwalafara ta rage girma da kulada yara da lafiya shine dareja takeda daman cin takaran. Dareja tai dariya tace ai in kwalafara zata nuna mata girman jiki da iya kulada yara, bazata nuna mata hankalinba..
"Me hakan ke nufi?"
"Zan gaya miki wani abu gameda kwalafara. In tasha zuma hauka takeyi. Waze nada mahaukaciyar sarauniya?"
Kan bompai ya buga. Hauka Kuma? Ita kwalafaran? Kuma ma wai tashera ba mutuniyarta bace? Dama bada zuciya daya yake tareda kwalafara ba? Meke faruwane? Abinda tashera takeyi ya kaucema doka da tsarin tudun adama. Dole ta tsaida.......
Ganin kawai tayi idanun tashera kanta. Tofah! Wannan babban sirrinda taji, aiko tunda taji shirinsu ba barinta zasuyi ta kubuce musuba. Ta kawo kanta gidan kashe kanta.
Daukan wani sanda tashera tayi tana kallon idanun bompai. "To fito bompai tunda kinyi labe kinji duk shirinmu." Tace tana buga sanda a tafin hannunta.
Bompai ta fito a hankali tana kallonsu cikeda mamaki. Kenan binu gaskiya take gaya mata. Amma.....kenan da gaske karyayyiyar soja ce! Kenan.....bata son cigaban tudun adama tunda tana kashe jama'anta. Kuma amma dareja tasan abinda wannan muguwan takeyi kuwa?
"Kawarkice?" Dareja ta kalleta kasa da sama ta lura ita sojace me mukami. Ana gane mukaminsu bisaga suffar jikinsu. Tanada kakkauran kafafu.
"A zatontaba." Tashera tace tana kallo tana nazarin wane wurin zata fara jigatawa a jikin bompai.
Bompai ta girgiza da jin haka donko a zaton nata batada kawa daya wuce tashera. Zatayi komai saboda ita amma yanzu se zuciyarta ya karye dajin wannan kalamin daga bakinta.
"Magance matsalan nan." Dareja tace tayi gaba abinta.
Fitanta keda wuya se tashera tayi cikin bompai da iccen ta daga zata buga mata a kai ta doje ta mulmula tayi gefe. Ta kallo idanun tashera ta gama bata gane wa take kalloba.
Idanunta sun canza, cikeda son kasheta. Aiko tasan bazata iyada tasheraba ta ruga a guje tabi hanyan waje. Inaaa, iccen tashera ya harbo kafanta. Kas! Ta kalla kafanta ya karye ta zuba ihu.
"Waye wurin?!" Akace daga waje.
Nan take tashera ta ruga tabi bango ta fice ta wani rami a sama. Bompai na rikeda kafa tana kallon inda tashera tabi. Sega binu ta shigo. Hamdala ya sauka a fuskan bompai.
"Ashe kin fadi gaskiya, binu. Nayi nadaman zama kawar tashera. Ta bani mamaki. Meke damuntane?"
"Karki damu bompai. Muje in kaiki wurin hisu."

Kash! Abin yaba tashera haushi. Yanzu dole setaje a yau dinnan ta kashe bompai inba hakaba ta tona mata asiri. Tana tsaye bakin kofan dakin baccin sojoji ta juya taga jera gefenta.
"Kin kirani?"
"Eh jera, bompai taci amanarmu. Dolene mu kaudata....."
"Tsaya! Mu kaudata na nufin......?"
"Kinga in don samun nasarane a zaben sarauniya dake zuwa da cigaban tudun adama komai zan iyayi don ganin na cimma burina!"
Ganin yanda jera ta taro maganan yasa tashera canza magana.
Um, harda tsorata kananan yaraba! Jera ta aiyana a ranta tana jin takaici tashera. "Ba seki kyaletaba da halinta. Yaushe kikeda lokacinta bayan gobene zakiyi takaran gaskiya."
"Hakane amma in bamu kaudataba, zata jawo muna babban rigima."
"Kaman me?"
"Ke jera! Ban kirakiba donki cikani da tambayoyi. Kiyi kawai abinda na umurta!!"
"Tashera kina mancewa ke kawatace ba shugabataba ba kuma sarauniyataba. Babu umurni tsakaninmu se kyautatawa........"
Nan fa ta tari numfashin jera tace ai tana neman taimakontane ta rike bompai a dakin tsaro harse bayan takaran gaskiya, sannan ita zata san yanda zatayi da ita.
"Kina nufin zaki kamo bompai ki garkame, ni kuma in zauna a wurin insa mata don karta gudu? Wane irin laifine tayi haka?"
"Wanda ze iya kawo karshena a tudun adama. Bansan yaushe ta zama munafukaba. Kila adeelace ta hure mata kunne."
Kallon kokonto ne barara a fuskan jera.
"Kiyi abinda nace, zan miki bayani daga baya!" Tashera ta wuce.
Jera tayi jim tana tunani. Lallai akwai makarkashiya a wannan zance ne tashera. Wai meke faruwane?