TUDUN ADAMA

16: Bayyana gaskiya 2

by @mbello38

Shiru akeji malam. Abin yaba adeela mamaki. Ba wai ta gani da idanuntaba lokacinda gumza kecema tashera tasan cikinta ciwo yakeyi inta sha zuma? Ko seya dauka lokacine yakeyi......oh! Ko se tasha da yawane yake mata illa? Kash! Dama ta gaya yawan kokonda zasu sha. Ba komai, ai akwai dayan gwajin.
Lampura ta kalla dumu da jaguwa tace ita bata san menene amfanin wannan gwajin cin abincinnanba. Me adeela takeso ta nuna musune? Dumu tace ita kanta ta rasa dalilin wannan gwajin. Beda ma'ana amma.....
Tashera ta lankwashe ta rike ciki tana wash wash! Kowa akayi shiru anata kallonta. Ciwon ciki takeyi kuma?
"Dan zuman nan da muka shane ya sata ciwon ciki. Zuma nama tashera rauni a jiki. Kunga gaskiyanta na farko!" Adeela ta daga murya don kowa yaji.
Yanzu sun gano muhimmacin wannan gwajin. Zaki na daya daga cikin abinda sojoji sukafi sha kafin fita yaki. Yana kara musu kuzari da karfin jiki da saurin gudu. In soja bata iya shan zuma ana sauya mata aiki ta zama lebura.
Adeela ta cigabada da cewa za kuma ta nuna musu yanda ta samo kafan fara wanda ze nuna musu cewa magananta akan tashera gaskiyane. Adeela ta zura a guje tayi hanyan gonan hatsi. Tashera tabita tana rikeda ciki, akayita kallonta.
Sarauniya ta ware hannayenta seme? 'yanmatan sarauta, su kwalafara suka iso suka bude fikafikansu suka rike hannayenta sukayi fira se saman bushiya inda zasu dinga hango abinda ke faruwa a gonan hatsi. Sauran kwari suka ruga a guje suka bi jikin bushiya don kar a basu labari.
Adeela ta ruga tayi hanyan gonan hatsi inda akafi ganin fara, ta haye saman wani karamin shuka tana kallon gonan. Canta hango fara da yawa suna tacin ganyen hatsi.
Ta kalla taga faranda zata zaba. Duk wadanda ta gani manyane masu karfi, bazata iya dasuba. Canta hango wani fara be kai wadancan girmaba ta murmusa. Sede kuma......
Tashera ta boye tana kallon abinda takeyi seta kallo taga fara nata cin ganye. Haushi ya kamata. Yaya za'ayi yanzu ta iya samo kafan abinda yakejin mugun tsoro.
Tun lokacinda wani fara ya kusa cinyeta tasha da kyar take takatsantsan dasu. Se kawai wannan kwaron tace wai samo kafanshi shine gwajinta.
Muddin aka san tana tsoron fara aita kade. Bari kawai tayi kaman tana fakon fara in adeela ta samo kafarshi tayi abinda ta saba. Ta amshe ba, sede kuma hakan ze yiwu?
Kowa na kallonsu a wannan karon. Sede tayi dibara ta amshe kafan. Ta hango adeela na harin wani madaidaicin fara. Hm, wayon tsiya. Taga tana zuwa wurin faran a boye a hankali kada ya ganta.
Idanu biyu suka hango wata katuwar kiyashi tuni me idanun yaji tsanan kiyashin ya dira cikin ranshi. Ze taketa sannan yayi wasa da fara. Dama kullum se yazo yayi training din kama bera da jangwale tayi amfanida fara,  amma yanzu tunda yaga kiyashi, seya gama ita sannan ya cigabada harkar gabanshi.
Faran mage ta hango illiru yana harin kiyashi ta girgiza kai. Wannan magen wato shide baze bar wannan halin nashiba. Ta kyallara ido se ta hango wani abin ban mamaki.
Wata kwaro tana harin fara! Ta girgiza kai don kara tabbatar ma kanta abinda take gani. Hakadene, to amma meyasa take harin fara? Tade san kiyashi na cin fara me rauni ko wanda ya mutu, amma me rai! Ai hatsarine musu.
Aiko ta samu abin kallo. Tayi mika daga kan simintinda take kwance tana kallonsu ta gyara zama. Kwaron ta matso kusada shukan hatsinda faran kece ta lallaba a hankali ta hau tana boyewa.
Kwaron na isa kusada faran ta daga hannunta se giris! Magenta tashi zaune cikeda mamaki ta kara girgiza kanta. Kai!!! Wannan kwaro fah tana son kashe kantane?!
Tuni fara ya saki ganyenda yake ci a firgice ya kallo kafanshi. Ganin yayi kawai wata kwaro na laftawa a guje tana gangarewa kasan shukan hatsi rikeda kafanshi.
Babban bala'i! Haushi ya turnukeshi yako biyota a guje yana fira. Haka sukayita tsere har faran ya kusa kamota ya mike hannu se ganye ya maujeshi. Ya wuce yabi iska wani pink igiya ya nannadoshi se cikin bakin kwado.
Momo ya fito! Farar magen ta mike tana kallon kwadon. Wani bakin katon kwadone Dake rayuwa kusada pond din dake gefen gidan agwagwa, yana hura habarshi tana kumbura tana sacewa yana wani kara.
Kai amma kwaron ta bala'in burge farar magen. Ta hangota tanata fashi seme? Wannan katuwar kwaronda illiru ke hari ta biyo bayanta a guje ta bigeta, ta fadi kasa  amma kafan faran na nan makale a hannunta.  Farar magen tazo kusa da inda suke don taji me suke cewa.
"Koki bani kafan faran ko in halakaki yanzu nan!"
"Aw, kin ysargune shine kike neman yin halinda kika saba, karbe min wahalanta! To bade yauba!"
Tashera tayi dariyan mamaki tana kallon adeela. Dama ta inda suke ba'a iya hangosu daga bishiyan tudu shiyasa tashera ta zaba wurin ddonta amshe kafan.
Bata taba zaton wannan karamar alhakin zatam iya furta mata wannan kalaminba. Meya bata kwarin gwiwan......
Ji tayi wani irin gurnai ya cika mata antenna kaman se watse. Waigawanta keda wuya seta sankare, wani ash din magene yake kallonta yana gurnani.
Jikintaya hau rawa ta juya zata gudu amma inaaa, ya tarota ya hankadeta, ya harbata a iska take ta bugu da wata shuka ta zube kasa. Magen yayi tsalle don yana bala'in jin dadi in yana harin kiyashi.
Da kyar tashera ta mike tana dingishi ta kallo magen. Taga ya kafa mata ido, bakin cikin idonshi na kara gira yanaso yayi wasa. Wasa! Da ita!! Tabdi, ai kisa kenan!!! Mutus ze kasheta. Tako arta a guje tana neman tsira.
Farar magen ta kalla adeela. "Yau Kuma meya kawoki nan?"
"Takara mukeyi nida wancan kwaron na samo kafan fara don in nuna gaskiyata ita kuma karyanta ya bayyana."
"Karya tayi?"
"Harda kulla shairi tayi min."
Nan fa adeela taba magen labarin tashera da ita da abinda ya wakana tsakaninsu. Magen yace ashe illiru ya taimaketa da yake mata maganin munafukar kwaron.
Ihu sukaji suka waiga sukaga tashera a fili, magen ya matseta da hannunshi Yana mutsussuketa. Tun sunajin ihu ta har suka denaji suka kalla juna.
"Haye bayana in maidaki kusada tudunku."
Abinda be taba faruwaba a tarihin kwarin tudun adama suka gani a ranan. Bayan ganin yanda adeela ta samo kafan fara, sukaga yanda mage ya biyo tashera ya taketa ta mutu sannan sukaga adeela dale a bayan mage ta kawota har bakin tudu ta dire ta wuce abinta tana cewa se tazo feast ranki ya dade!
Haka aka dinga kallon adeela ana mamakin wannan abu daya faru. Ita kuma ta tako tana rikeda kafan fara ta shige rami. Haka kowa yabi bayanta ana murna ana shewa.