TUDUN ADAMA

19: Ranar zabe

by @mbello38

Tudun adama ya kasance cikin shirye shiryen takaran zaben sarauniya. Su kwalafara sun hallara a bankadeden zauren zabe, inda ake takaran.
Sarauniya na zaune a high table tareda shugabanni. Kowane kiyashi tudun ya hallara sun mamaye bango da kasa ga zumudin son ganin wazeci takaran yaba yaba a fuskanshi.
Misau tayi kyau tana sheki. Dareja se firfir takeyi da fikafikanta kyawawa yellow. Kwalafara kuwa tayi ta fisu girma, daukan Ido ga tulelen ciki yana turowa ta baya.
Kowa an hallara kawai kwaro daya ake jira. Meya ke daukan lokacine wai haka? Kowa yakosa yaga adeela. Can kofa ta bude se kawai akaga wata katotiwar kwaro, me dogayen kafa, jiki me sheki, antenna me tsawo, tulelen ciki ta bayyana a tsakiyan zauren.
Isowanta keda wuya seta bude fiffikenta firrr! Gasu farare tas, ana ganinta cikinsu. Gasu manta masu tsawo. Tuni kawai ta lashe zaben a idanun jama'an tudun.
In har akwai me kamada adeela a tudun aiba maganan takara. Wannan shine lashe zabe batareda takaraba. Tuni mamaki da bakin ciki ya gauraye sauran 'yan takaran.
"Tunda adeela ta iso, aise a fara takaran!" Dareja ta fadi tana hararan adeela.
"Har kinada bakin cewa a fara bayan ga me nasara bayyane a fili."
"Tunda ta iso ta tsaya gefenmu aita nuna amincewarta da a aiwatar da takaran!" Dareja ta cigaba.
"Me kikace adeela?" Para ta tambaya.
Murmushi adeela tayi don tuni tayi shirinta. Ganin kawai akayi misau ta fadi ta sume. Hisu tayi kanta tareda leburori biyu ta dubata ta girgiza kai.
"In taci abincin gina jiki, suma takeyi." Ta fallasa.
"Mene? To me takeci?" Sarauniya ta tambaya cikeda mamaki.
"Abincin karfi da zaki."
"Wannan be cancanta ta zama sarauniyaba!" Para ta ambato.
Aka dauke misau. Adeela ta kallota ta gefen ido. Inda misau keda rauni kenan. Adeela tasan da an ganta za'a zabeta ba tareda yin takaranba. Shiyasa bata fitowa kwata kwata kuma taji dadin da sarauniya ta btaa daki daban.
Ta barwa pitinau ta cika aikin. Pitinau ta lallaba ta shiga dakin 'yanmatan ta dosa abincin misau. Duk hankalin 'yanmatan na kan situ, namijin da kowa keson ya zama nashi saboda kyau kiranshi da karfin jikinshi wanda duk sukeson kwayakwansu su gada, amma kwalelensu, kwalafara ta kwallafa ranta a kanshi dole su ja baya.
Pitinau ta lura yanata basu labari yana nuna jikinshi yana yanga, ta girgiza kai ta wuce cika aikinta. Inda aka ajiye abincin 'yanmatan daga lungune wanda hakan yayima pitinau dadi.
Tuni ta isa wurin ta kalla bencin ukune. To fah! Yanzu wannene na misau. Tunda adeela ta gaya mata misau bata iya cin abinci me gina jiki to ba shakka bencin gefen hagunnanne nata me cikeda abincin karfi da zaki.
Data lura ba'a kallonta ta, ta amayo abincin gina jiki ta gaurayeshi da dayan ta juya taci karoda wata lebura. Sauri tayi ta wuce leburan nata kallonta canta wuce.
Dareja ta tabe baki tana mamakin lamarin. Ai ita abin ya mata dadi don an kauda 'yar adawa daya.....ji tayi wani mugun ciwon jiki ya taso mata.
Kanta ya harba, kafadunta da hannuwanta suka sage, kafafunta suka mutu, jagwab! Ta rafke a kasa ta kwanta tana wayyo zata mutu jiki ciwo.
Hisu ta kara rugowa ta dubata ta mike tsaye. "Ciwon jikintane ya tashi wanda ke aukuwa idan batayi bacciba na minti goma."
Kai! Kowa yayi mamakin wannan lamarin. Ya za'ayi a zaba sarauniya me bacci? Bazata iya aikintabama kenan.
"Wannan be cancanta ta zama sarauniyaba!" Para ta kara ambatowa.
Taya adeela bazata tona ma dareja asiriba. Ta hantareta itada tashera sun hanata sakat a tudun. Abin yama bata mamaki data gano abinda yake sa dareja ciwon jiki. Rashin bacci na minti goma. Koda tayi na minti biyu beze ishetaba kenan.
Tuni ta tura sintura ta cika aiki. Sintura ta tayi bincike ta gano dareja na jin tsoron gizo aiko ta samo wani abokinta smee tace mishi yaje ya tsorata.
Seda sukayi yarjejeniya na bashi abin armashi. Tace zata bashi dagargazazzen sauraro guda biyu sannan ya amince. Ya kutsa ya shiga dakin 'yanmatan sarauta ya labe karkashin makwancin dareja.
Dareja ta shigo yin baccinta na minti goma kafin zabe don in batayiba a filin zabe ciwon jikinta ze iya tashi. Ta baje kan makwancin ta gyara da kyau ta rintse idanu seme?
Kwarab! Wani abu ya diro.Ta wullo idanu bude ta wurga kallo kewayen daki ba kowa. A wannan lokacinma su kwalafara basu shigoba suna dakin wanka. Tasan zata samu baccinta kafin su dawo.
To wanene yake.......se ganin tayi kafafu na yawo a kasa. Zumbur! Ta mike zaune a razane. Kafa daya, biyu, uku......gizo!!! Tuni jikinta ya hau rawa. Gizo a dakin baccinsu!! Ta shiga uku, Waze koreshi?
Can ta kyallara ido bata ganshiba, haba tsoron ma yafi nada. To ina ya shige? Zaune kan makwancin ta dale sama tanata kallon kasa da lungun katoton dakin.
Can taji motsi kusada lungun bencin abinci, gabanta ya fadi. Bade zeje ya cinye musu abincibane? Aiko shine gashi ya fara hawan bangon dakin.
Haka sukayita guje guje itada gizo. Tana gudu yana binta harta jigata. Ana haka kawai se ganin tayi ya fice ta wani rami a sama. A lokacin kuma su kwalafara suka shigo dole ta manta da bacci don zasuje zauren zabe.
Haka aka kwashe dareja aka tafi da ita. Abin nan yama kwalafara dadi. Dama itace zabin sarauniya hubba da kanta. Tun fil azal ita ta zabeta da hannunta.
Yanzu de ba wanda ya tsaya mata a gaba in banda wannan adeelan da lokaci daya ta canza gabadaya. Duk da haka se tayi nasa.....ruwa me gardi....gardi.....abin yayita raya mata a kai.
Tuni akaga kwalafara ta fara juyi tana zagayen wurin daya tana sambatu.
"Gardiiiiii ruwa me gardiiiii gardiiii!"
Kowa ya sake baki ana kallonta. Hisu ta kara shekowa a guje ta lura da ita taja baya.
"Haukantane ya tashi, ta dalilin shan zumanda tayi."
Shan zuma! Zaki na gyara jikin kwari harde sarauniya. Tana bukatan zaki a jikinta kodayaushe. Inko har zuma na ma wannan  illa har yaja mata wannan gagarumin haukan aida matsala.
"Wannan be cancanta ta zama sarauniyaba!" Para ta kara ambatowa.
Abinma yama adeela saukinwurin kada kwalafara. Inde don zumane tana dashi sosai. Tuni tasa binu ta cika aiki.
Binu taje tasha zuma ta ajiye cikin cikinta wurin ajiyan abinci ta nufo situ, namijin kwalafara.
"Na samo abincin gina jiki situ. Kaje kaba kwalafara yanzunnan."
Ta amayo abincin ta mulmula shi ya zama kwallo ta mike me, ashe gauraye yake da zuma. Situ ya kalla kwallon yaga Yana hade da wani abu yellow me danko kaman.......yayi sauri kallon binu.
"Kwalafara bata shan zuma fa?"
"Kwaine fah, kwan wata kaza daya fashe dazu a gidan kaji."
Yayi murmushi ya karba.
"Meyasa kace bata shan zuma?"
"Ba komai. Tasha zaki dazu, zakin ze mata yawa." Ya wuce ya barta.
Murmushi binu tayi don ta riga ta kwance zaren.A wurinta, abu sananne ne inde zancen kwalafara ne da zaki.
Situ ya kawo ma kwalafara kwallon abinci Yana murna ya mike mata yace ya samo mata abinci me hadi me kyau. Batayi wata wataba ta amshe ta cinye tana jin dadi.
Tuni aka cafke kwalafara akayi gaba da ita.
"A bisaga sakamakon wannan takaran zaben  sarauniya. Adeela ita ta lashe wannan zaben. A yau ta zama sarauniyar tudun adama!"
Akayi ihu akayi shewa akayi murna. Akaci aka sha, akayi kide kide da raye raye domin nuna murnan nada sabon sarauniya.