Page 16
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 16
FREE PAGE
FREE PAGE
Dukkanin su tsuru su kai kowa a cikin su zuciyarsa sai kai kawo ta ke,tare da sak`a ma sa duk abinda ya zo ma sa a kan sa da tunaninsa,wani daga cikin su ma gani ya ke tamkar mafarki su ke, ko kuma ba gaskiya bane abinda ya faru yanzu a gaban su,ta ya za ai matar da ta shekara sama da Goma da rasuwa wai yau a ce ta bayyana a gabansu ,kuma har ta na ba su umarnin da za su bi domin tsira da rayuwar su,game da halin k`ak`a ni ka yin da su ka fad`a,motse-motse da Yarima Sadauki ke yi ne ya ja hankali su gabad`aya a kan sa,bakin sa sai faman motsi ya ke,sai ka kasa kunnenka da kyau za ka ji abinda ya ke fad`a,"U..Ummm...Ummata....ki na ina,Fulanina ki na ina Giwar Masarautar ?, ki matso kusa da ni,in ji d`umin ki, na ji kamar kin yi min nisa",ya k`are zancen ya na mai mik`a hannunsa da nufin ya lalubota ko ta na ku sa da shi,jin alamun tamkar babu ita a kusa da shi ya sa ya mik`e zunbur tamkar wanda a ka tsikara haka ya zabura gami da mik`ewa baki d`aya,ya na mai watsa idanunsa a cikin filin d`akin da su ke,sai faman wara idanunsa ya ke lungu da sak`on da alama dai wani abun ya ke nema, "Ina Ummata ta ke ?", ita ce tambaya kuma magana ta farko da ta fito daga bakin sa,tambayar ta yi matuk`ar girgiza su domin babu wanda yai zato da tsammanin zuwanta a cikin su,rasa wanda zai iya bud`e baki ya ba shi amsa a kai,wanda hakan ba k`aramin ta da ma sa hankali yai ba.
Da sauri ya kai ma Ja'afar da ke ku sa da shi wata Shak`a tare da sa ke tambayarsa ,"Ina Mahaifiyata ta ke na ce ina ta ke?", har sai da idanun Ja'afar su ka firfito waje ya fara kakari sakamakon tsananin shak`ar da Yarima Haisam yai ma sa ,ganin ba abinda zai sa mu daga gare sa ne ya sa yai wurgi da shi can gefe,ya nufi inda su Habib,Salim,Azim da Ayub su ke tsaye ,hannayensa biyu ya had`e guri guda ya na mai d`an risinawa alamun ya na rok`onsu da cewa," Dan Allah ko kun ga Ummata nemanta na ke,anan nan wurin d`azu-d`azu mu ke tare da ita har na kwanta saman ciyarta ina barci amma na farka ban ganta ba,ku taimake ni in kun ganta ku nuna min rashinta zai illata ni?",Kasa cewa da shi Komi su kai,Ayub kuwa hawaye ne ke shatata saman fuskarsa,da d`an gudunsa ya nufi inda Shahul ya ke ya na mai sharce hawayen saman fuskarsa ya ce da shi,"Ummata na ke tambaya ko ka ganta wata fara doguwa mai d`an kyan-kyan d`in jiki ta na da fara'a ga wishirya a tsakiyar hak`oranta",da sauri Shahul ya bar wurin ya koma bayan su Ayub ya `boye,tashin hankalinsa ya bayyana fili sarari ,dukkaninsu ba wanda ya ta`ba ganin Yarima Sadauki a cikin makamanci ko arin wannan halin.
Kai tsaye inda Jamal ya ke zaune ya nufa ya duk`a da gwuiwowin sa k`asa ya na cewa cikin tausasa lafazi gami da sanyaya muryarsa," Jamal kai d`an'uwana ne na hak`ik`a kuma na san za ka fad`a min gaskiya,za ka taimake ni,ina Mahaifiyata ta ke,ina ta tafi ta bar ni me ya sa ku ka bari ta tafi ta bar ni",ya k`are zancensa ya na mai mai da idanunsa a kan sauran Dakarun, bai wani jira ba ya cigaba da cewa,"Idan su ba sa tausayi na sun kasa tsaida ta kai me ya sa ba ka tsaida min ita ba Kai ko da rok`on ta ne ka yi domin kar ta tafi ta bar ni,domin ka san mawuyacin halin da zan shiga in na tabbatar da ba ta nan",ya k`are zancen hawaye na kwaronyowa daga saman idaniyarsa, rik`o wuyan rigarsa yai ya na mai jijjigasa da iyakar k`arfin sa,"Ka bud`e baki ka yi min magana ta ya za ka mai da ni tamkar shasha,in ta magana kai banza da ni,sai ka ce wani sabon mahaukaci duk kun bi kun juya min baya,"k...kkkk....ka yi hak`uri amma ba mu san kan me ka ke magana ba duk ba mu ga Mahaifiyar ka anan wurin ba, hasalima ba ta zo nan ba, ba wanda ya ganta anan ta ya ma za ai matar da ta mutu tun tsawon shekaru Goma a ce ta zo nan garin da ma k`asar da ba ta ta ba ,ta ya haka zata kasance abun da almara a cikin kuma da kamar wuya gurguwa da Auren nesa..... ",da sauri ya dakatar da shi da cewa
"Kai Dallah Malam dakata mana ka san me ka ke fad`a kuwa Anya kana cikin hankali da natsuwarka kuwa,Mahaifiyar tawa ce za ka ce ba ta zo nan ba, bayan na ganta da idanuwana ,na zauna kusa da ita mu ka yi fira,mu kai zance mai dad`i har ta na yi min alk`awarin zama na har abada a tare da ita, sai yanzu ka ce min wai ba ta zo ba,ko dai ka fara shaye-shaye ne ban sa ni ba?"," Wallahi ko d`aya ban sha komi ba asalin gaskiyar abinda ya faru ne na fad`a ma ka,Mahaifiyar ka ba ta zo nan ba ba wan da ya ganta da alama dai mafarki da ita kai amma ba gaskiya ba ne ba"."......wani wawan bugu ya Kai ma sa a saitin baki wanda da ya same shi ba makawa sai ya zubar ma sa da hak`oran baki.
Da sauri duka sauran mutanen su ka yo kan su su ka shiga tsakaninsu don gudun kar wani munmunan abu ya faru,haki ya ke ya na fizge-fizge ya na cewa,"Ku bar ni in isa garesa ko ba ku ji abinda ya ke fad`a ba,Wai cewa ya ke wai Ummata ba ta zo nan ba wai-wai mafarki na yi da ita","Ka natsu ka kwantar da hankalin ka zan yi ma ka bayanin komi dallah-dallah yanda za ka fahimta",cewar Ayub da ya ke son tausar zuciyar sa."Yauwa ko kai fa dama na san kai ka na so na kuma za kai komi gami da yin duk iya mai yiwuwa wajen ganin na fita daga cikin halin da na ke ciki a yanzu",sai da jikin su ya k`ara mutuwa gami da yin sanyi duba da yanayin da lokaci guda komi na Yarima Sadauki ya canja,tamkar ba shine wannan d`an Sarkinnan ba Babu wanda ya ta`ba tunani haka za ta kasance a garesa yawanci su duk zubar da hawaye su ke,duk ya bi ya rikice ya fita haiyacinsa tamkar sabon mahaukaci haka ya koma.,"Da gaske abinda Jamal ya fad`a ma ka gaskiya ne, ba wacce ta zo nan ,Mahaifiyar ka ba ta zo nan ba da alama dai mafarki ka yi "...." A'a dan Allah kar ka ce haka kai na da zuciyata baza su iya jura gami da d`aukar wannan rikitaccen al'amarin ba,ni fa nan da kai na na ganta kuma mu ka yi zance mai dad`i gami da tsayawa a rai da ita,kai har kuma ina da tabbacin kun ganta,sannan kuma ku ce wai ba haka ba ne ba,Wai duk mafarki ne,ta ya zan yarda da hakan ?","Da gaske ne dukkanin abinda su ka fad`a ma ka ,don haka ka dai na k`ok`arin sanya kan ka cikin wani halin kar ka je ka illata ko cutar da kan ka",cewar Habib
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'una me na ke shirin ji ko dai wata musibar ce ke shirin tunkaro ni ban sa ni ba,ta ya haka za ta kasance,in har ba ha ka ba ne ba to wa ni sabon rainin hankali ne ku ke k`ok`arin zuwar min da shi,Allah ka kawo min d`auki ,ka kawo min maslaha da sassauci abinda ke k`ok`arin riska ta", ya k`are zancen ya na mai kallon Sama ,hakan ba k`aramin k`ara ta da ma su Ayub hankali yai ba,da rashin sanin me kuma me za su yi,har danasanin rashin sanar ma sa da asalin gaskiyar su ka ji, ya fara fara d`arsar ma su arai
Ta kurewa guri guda ya fara yi ya na mai cewa"Ku lullu`be ni sanyi na ke ji,A'a ba sanyi na ke ji ba zafi na ke ji ku yi min fifita,matsa ku ba ni wuri iska ta riske ni",da sauri su ka dare su na mai ba shi fili iska ta Isa gare sa,su na barin wurin ya fara rawar sanyi gami da makyarkyata dole su ka dawo su na yafa mai rigunan da su ke jikin su,kafin ka ce me kuma ya koma jin zafi,nan fa ya tada ma su hankali nan da nan yanayi biyu ya riske shi a lokaci d`aya,