Page 15
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1
*YOTA*
PAGE 15 ❤🔥
"Dan Allah ku kyale ni,ku barni ina so in je in ga `yata da kaina,Zuciyata ta kasa hak`uri, ban san a wanne irin hali take a ciki ba,ina buk`atar in ji d`uminta a kusa da ni", Hibba ta kai zancen cikin yanayin jinya da,kuma marairaicewa.
" Kin ga Hibba dan Allah ki kwantar da hankalin ki,Jadeeda na can ita ma ana dubata kuma ta na samun kulawa ta musanman,don haka ki natsu ki kwantar da hankalin ki,Yarinyar ki zata dawo hannun ki,da izinin Allah.Cewar Ummie Maryam cikin lallashi da ban baki.
Hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanunta, tana mai girgiza kanta alamun bata amince da hakan ba,cikin k`ank`anin lokaci ta birkice musu,"A'a ni ba abinda za ku fad`a min a yanzu in sake yarda da ku,yau kwana nawa wajen kwanana uku da farkawa amma kun hana ni ganin Jadeeda, idan ba za ku bar ni in je inda take ba ku kawota nan in ganta mana, Haba dan Allah",ta kai zancen ta na mai fincike drip d`in dake hannunta har ma da yunk`urin sauke k`afarta da aka d`ageta sama wacce ta samu karaya.
"Hibbah!!!! Ki dakata nace ya isah haka,ko baki da hankali ne,ko kin manta cewa ke muslmace,ya ki ke abu kamar wacce kwakwalwarta ta juye ?"...ya d`an dakata ba tare da ya kai k`arshen abinda yake son cewa ba.
Jikin duk wanda ke wurin sai da yai sanyi,ganin yanda yake mata tsawar kuma hawaye na zuba daga cikin idanunsa,Lura Mama Hadiza tai ya na shirin cewa wani abu tai saurin shan gaban shi gami da fara girgiza masa kai,runtse idanun sa yai Wanda hakan ke tabbatar ma Mama Hadiza ba zai fasa fad`ar abinda yai niya ba.
Tarar numfashin sa tai da cewa," A'a Nasir a kull d`in ka kar ka soma wannan ba shine lokacin da ya dace ba,ka bar komi ya lafa in ba haka ba kuma"......"In ba haka ba kuma me Mama, tsoran me kike ji,me ye ku ke gudun kar ya faru,ita fa Muslmace yarda da k`addara ya zame mata dole, don haka ku gaya mata gaskiya ku fad`a mata cewa Allah ya zartar da hukuncin da yafi dacewa akan ta"....
Duk tsansni da tsafin da take ji a k`afartata,haka ta takata,ba tare da ta yi tunani me hakan zai iya haifar mata da wani abu ba,sai ganin ta su kai a tsaye a gaban su tana mai kama hannun Naseer d`an'uwanta ta na mai cewa,"Dan Allah me ke faruwa shin wani abu ya same ta ne, kar ka ce min da gaske abinda na gani a mafarkina shine ya faru da ita,wai tsaya ina Abbanta yake ban yarda da kuka ce min yana can office aiki ya rik`e shi ba".
Sai da ya kama kafad`arta ya rik`e har da hannun da ta samu tsagewar k`ashi kana ya ce da ita,"Eh ba gaskiya su ka gaya maki ba, Mijin ki na can kwance rai hannun Allah a sanadin hatsarin da kuka samu har k`anwar Mijin ki Cecelia ta mutu"...bige hannun sa da sauri tana mai fara ja da baya daga kusa da shi tana mai cewa, "A'a Yah Naseer kar ka ce min itama Jadeeda ta mutu,kar ka ce min itama na rasata?".
Sai da yak`ara matsawa kusa da ita ,sannan ya bata amsa da cewa,"Ki saurare ni ki kuma natsu Allahn da ya baki ita ya fiki son ta,don haka ya amshi abarsa"....Sai da ta sa hannunta mai lafiya ta hankad`ola shi kafin ta ce "k`arya ka ke Naseer `yata Jadeeda ta na da ranta ba ta mutu ba, domin,ruhina Zuciyata da kuma gangar jikinta suna gaya min ta na raye,kuma bari ka ji yanzu zan fita da kaina in dawo da ita", ta kai zancen ta na mai dosar hanyar da za ta bar room d`in, tangal-tangal ta fara za ta fad`i sakamakon duhun da ya mamaye mata idanunta da sauri su duka Ukun Mama Hadiza, Ummie Maryam da shi kan shi Naseer d`in su kai kanta,jiki na rawa Ummie Maryam ta tafi kiran Doctor bayan sun kwantar da ita .
Ta ma fita Baba Malam da kuma Baba K`arami suka shigo cikin d`akin ganin halin da suke ciki ne ya sa ba su sami zarafin tambayar su me ke faruwa ba.
"Garin ya akai haka ta faru, wannan wanne irin sakaki ne ?",Doctorn ya fad`a a zafafe bayan ya ji abinda ya faru,sosai Doctorn yai fad`a tana mai nuna nasu muhimmancin kulawar da zasu yi da ita,hak`uri suka ba shi har ya gama yi mata duk abinda ya dace yai mata .
A fusace Baba K`arami ya fuskanci shi yana mai cewa," ba ka da hankali ne,ta ya za ka aikata irin wannan d`anyen aikin ko kana hauka ne ?".
"Eh Baba K`arami hauka na ke bani da hankali,idan har gajiya da kallonta a cikin irin wannan yanayin shine hauka to ba shakka na hauka ce,da gaske na haukace,shin ba kwa tunani ko jin tsoran kar yawan sanya ta barcin dole da kuma `boye mata asalin gaskiyar da kuke ya jefata cikin wani mawuyacin halin, shin ko so kuke ta koma sai an kwantar an tayar har k`arsheb rayuwarta,ko kuma so kuke ta koma rayuwar kamar irin wacce Mijin ta ya ke yi a yanzu, na rasa gane wannan tausai ne ko kuma wata sabuwar hanyar cutarwa,ya ci a ce ya zuwa yanzu kun gaya mata gaskiya yau wajen kwana biyar kenan da farkawarta da zaran ta tambaye ku game da Mijinta ko `yarta sai ku `boye mata gaskiya a haka ku ke so ta cigaba da rayuwa,don haka ni dai ma gaji ,Na gaji da ganin `yar'uwata a kwance shar`be kamar gawa ina son in ganta kamar yanda na saba ganinta tun muna yara"... Ya kasa kai k`arshen maganarsa sakamakon rungumar da Baba K`arami ya kai masa,sai da ya tabbatar da ya lallashe shi yanda ya kamata kafin ya raba jikin su ya fuskanci Baba Malam da cewa.
"Maganar Naseer gaskiya ce,ya kamata mu kawo k`arshe komi,mu bar Garin Jingir d`inan haka mu koma can Kano ,za su fi samu kulawa fiye da wacce suke samu anan".
" A'a ni dai ina jin tsoro ta ya zamu bar da su daga cikin Asibiti a irin wannan halin ",Cewar Mama Hadiza.
"Mama ki kwantar da hankalin ku ba gani ba,zan iya ba su duka kulawar da ake so,nima fa Doctor ne,a dukaninsu sun fi buk`atar kulawa ta cikin Gida fiye da ta asibiti, domin ya zuwa yanzu sun d`an samu sauk`i da ciwukan da suka samu na external saura na internal
" To ba matsala amma ya kike gainin za muyi doguwar tafiya irin wannan da marasa lafiya har guda biyu?","Lafiya lau zamu tafi da su ai referring d`in su zuwa wani Hospital d`in zamuyi don haka za su bamu motar mara lafiya a sanya su a ciki har zuwa can Kanon".
"To shikenan sai mu fara Neman Sallamar amma,kafinnan kai K`arami ya ka yi da gawar ita k`anwar Abbakar d`in ?".
" Daganan Asibitin suka had`a ni da wani Pastor nai mishi duk bayanin yanda komi ya faru, ya jimanta mana bayan ya saurari duk abinda ya faru sannan ya amshe ta ban bar wurin ba har sai da su kai mata duk abinda suke yiwa `yan'uwansu in sun mutu sannan suka buzne ta,sun bani tabbacin ko nan da shekara nawa zan zo zasu nuna min kabarinta domin har rubutu a takardar sai da muka yi sannan na taho".
"Masha Allah hakan yayi domin adalcin da zamu yi mata kenan mu sadata da `yan'uwanta su binneta kamar yanda suke ma `yan'uwansu,kun san zamu iya kiran haka a matsayin hak`k`in ta ne a kan mu ,don haka zamu iya tafiyar mu tunda ba wani nauyin ta akan mu".
"Tukunna dai wani hanzari ba gudu ba,shin kun manta a sanda Hibba tai farkawarta ta farko ta ambaci sunan wata ta na mai cewa `yarta na hannunta,to ta ya ke nan idan har hakan ya zama gaskiya, gani na je kamar bai kamata mu bar Garinnan ba har sai mun nemo ta idan mun tabbata ba ta tare da Jadeedan sai my yi tafiyar mu".Cewar Mama Hadiza.
Sai da Baba Malam ya fuskance ta kafin ya ce"Ki natsu ki saurare ni,yanzu haka daga police station d`in da suke gudanar da wannan binciken na ke akwai rikitarwa mai tarin yawa a cikin binciken,sun ce min sun yi iya binciken su su basu ga kowa a wurin ba,kai ko wayar mamaciyar ba a gani ba balle ai amfanin da ita a gano shin da gaske da akwai wata Mace wacce suke tare da ita ko babu,to babu wata takardar ko guda d`aya dake nuni da Cewar akwai wata bayan su uku da kuma `yarsu iya ita Hibban Mijinta da kuma k`anwarsa su ka tarar,babu wata shaida da ka iya tabbatar da wanzuwar ita wannan mai sunan da take ambata,saman wani Mutum Wanda a gaban shi hatsarin ya faru,ya tabbatar mana da cewa ya fi zargin buguwar da tayi ne yasa take ambaton wanna sunan ,kai tsaye dai binciken ya fi tabbatar mana da Jadeeda ta rasu ta k`one a cikin wannan motar".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yanzu Malam kana nufin Yarinyarnan ta rasu ta riga mu Gidan gaskiya da wacce fuska zamu itta tarar Hibba da zancen mutuwar `yarta bayan ga munmuna hademarin da ya fad`a ma Mijinta na juyewar kwakwalwa".Ummie Maryam ce ta matsa kusa da ita tana lallashin ta duk da itama tana zubar da nata hawayen ne.
" Sai hak`uri k`addarar Allah ce,haka ya tsaro mana ita,don haka dole zamu d`auke ta, domin a yanzu in munce zamu nemo me irin wannan sunan nata,ya ma sunan ya ke ?",ya na mai tambayarta su sunan da Hibban take yawan ambata bayan farkawarta.
"Gloria sunan ta",Naseer ya ba shi amsa.
" Yauwa Gloria idan mun tashi nemanta a yanzu ina zamu fara,domin mu ba musan daga ina ta zo ba,ya kamanninta su ke bamu san komi daga gare ta ba,iya Abbakar da k`anwar shi su ne suka santa da kuma inda ta fito, ita waccan Allah yai mata rasuwa,shi kuma wannan ya na kan matakin da shi kan shi bai san ko shi waye ba,kai ko ahalinsu bamu sani ba,in kuma munce muje Jos neman ahalin nasu to ta ina zamu fara da wacce hujja zamu yi amfani ,don haka bamu da wata makama wacce ta wuce muyi hak`uri".
Naseer ne yace,"Ni da cewa nai ko a d`auki hoton ita Ceceliar a sanya a kafafen television ko Allah zaisa ahalin su su gani kun ga shikenan daganan sai mu fara Neman Gloria "," Hmmmmmm Naseer kenan baka ga yanda Allah ya sauyawa Yarinyar nan kamanninta ba, shiyasa har kake fad`in wannan Maganar,zai wahala ko `yan'uwanta su iya gane ta".
"Allah gare ka mu ka zo gare ka muke neman taimako,Allah ka kawo mana mafita a cikin wannan lamarin", Mama Hadiza ta fad`a tana mai share hawayen fuskarta.
" Shikenan kin gama magana Mama Addu'ar mu kawai take so,in sha Allahu indai Jadeeda na da rai a doran duniyarnan to zata kawo kanta gare mu har inda muke duk min daren dad`ewa bi izzatillah,zamu duk`ufa wajen gayama Allah kukan mu,ba zamu gajiya ko min daren daɗewa ba".nan fa suka had`a me kansu kowana k`unshe hawaye da kuma bak`in cikin halin da suke a ciki.
"Masha Allah, Allah yai maku albarka ya zama gatan ku gabad`aya sai abu guda da zan so daga gare ku,daga yau ko da wasa kar wandaya k`ara tada zancen wata Gloria kai hatta ita Jadeedan mu d`auka a ta rasu bata Raye,ko da ita Hibban ta farka kar wani ya bata goyan bayan akan duk abinda zata zo mashi da shi,karma in na son tada wancan zancene,don haka da zaran mun Isa Gida zamu gabatar da Sallahtul ga'ib (Sallahr da ba gawa),da sunan Jadeeda da fatan Allah ya kai rahama da jink`ai cikin kabarinta".
Jikin kowa sai dai ya ƙara sanyi sai dai ba su da yanda zasu yi dole abinda ya kamata suyi kenan su d`au k`addara ta fuskar da ta zo masu,nan Naseer ya fara cuku-cukun sama masu referral zuwa Kano bai huta ba har sai da ya samu a wannan ranar su ka bar Garin Jingir badan sun so ba,Zuciyoyin su d`auke da wani miki ko gyambon da ba zai ta`ba warkewa ba.