DAYAN BIYU

Page 01

by @meenatyandoma

ƊAYAN BIYU

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

Page 01

Tsananin duhun da garin ya yi ne ya saka Shuhuda dafe ƙaton cikinta, ji ta yi ya na motsi tamkar mai neman hanyar fitowa duniya. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon yadda garin ya hade da hadari baƙiƙirin, ga wani iska da aka fara.

"Shuhuda! Kina ina ne? Ba za ki tashi ki kauda kayayyakin nan ba sai ruwa ya sauko?"

Ta tsinkayo muryar sirikarta na fada.

Sunan Allah ta kira tare da dafe cikinta sakamakon ji da ta yi tamkar an kai mata naushi.

"To! Dama kina jina kika barni ina ta ɓaɓatu tamkar ina magana da dutse. Yanzu yarinyar nan shi ne ki ka samu wuri ki Ka tule tamkar dasa falwaya. Me kike nufi da ba za ki tashi ki kauda kayayyaki ba, koko so kike ni uwar mijinki gaki a gidan ni zan fita in hau aiki"

In da sabo ta saba, amma yanzu kam ba zata iya tashi ba domin ji take tamkar an daure mata kafafu.

"Inna don Allah kiyi hakuri. Wallahi ƙafata ce ta rike na kasa mikewa"

"Muna ga Rasulu Manzon tsira. Ni Binta ina ganin ikon Allah. Yanzu tsabar lalacewar zamani don kina da ciki shi ne za ki ce ko aiki ba za ki iya ba? to mu a zamanin mu da ciki wata tara muke surfe hatsi mu dake shi kuma mu yi abincin da shi. Ba kin ce ba ki iya tashi ba, ki zauna har ruwan nan ya iskeki"

Ta karasa maganar cikin sababi irin na masifatattun tsofaffi.

Hawayen da ke tsere a fuskarta ta share. Domin yunkuri babu irin wanda bata yi ba amma sam ta kasa tashi, ta na ji tana gani haka ruwan nan ya safko tana zaune a tsakar gidan wanda ko siminti babu.

Kyarmar sanyi ta ke yi hakoranta na dukan juna. Sai dai duk da ruwan da ke dukanta rumfar ta yi ma cikinta cike da tausayin abin da zai sami abinda ta ke dauke dashi.

"Ka da ki damu! Sarauniya ta na cikin koshin lafiya. Muna tare da ita daga nan har zuwa ranar da zata zo duniya"

Shuhuda ta ji an rada mata a kunne.

Waige-waige ta hau yi amma ko tsinke bata ga ya wulga ba. Walkiyar da aka yi ce mace ta gani tsohuwa tukuf, bakinta ko haƙora babu a cikin mummunar siffa ta na mata murmushi.

Sunan Allah ta kira tare da kara dafe abinda ke a cikinta. Duk da ba yau ba ce rana ta farko da ta fara ganin abubuwa makamantan haka amma yau ta sha banban da kowace rana.

Kaf ruwan da aka sheƙa a kanta ya kare, jar ƙasa duk ta ɓata jikinta ga wata irin kyarmar sanyi da take. Ɗan inna ne ya shigo gidan kasancewar duhun magriba yayi.

"Kan uban can! Wacece nan nake gani ta ke neman tsorata ni. Kai kaga abu kamar an ajiye kayan wanki"

"Mai gida nice. Ka taimakamin in Mike ƙafata ce ta riƙe kaf ruwan nan a kaina ya ƙare"

"Ban gane In taimaka miki ba. To da ni na ajeki ne da zan taimaka miki yau kunga wani matashin iskanci. Ki kwana nan in sai na taimaka miki, inna! Inna!! Kina Ina ne"

Ya yi gaba tare da kwalawa Mahaifiyarsa kira.

Tamkar an zare mata allura haka ta mike ba tare da jin kafarta na ciwo ba. Dakinta ta fada tare da zama a gefen gadon ta da ya ji duniya. Dakin babu komai a ciki sai wannan gado da ya jima da fita a hayyacinsa gefe kuma gana mazgo ce cike da tsummunansu. Kasancewar Shuhuda mace ce mai tsafta talaucin da suke ciki bai hanata gyare dakin tsaf ba.

"Wasan ruwa yayi mata dadi, kinyi belin kanki"

Ta sake tsinkayo wata murya da ta rasa gane daga ina take fitowa ta na fada.

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Ya Allah me ke faruwa da ni haka. Ko dai aljanu ne ke neman shiga jikina? Kai aa ba su bane ni nasan ruwan da ya dokeni ne shi ya sa kunnuwana ke jiyomin sautin da ba daidai ba"

Wata kodaddiyar atamfar ta da ta jima da mutuwa ta saka, ga shi dai ta na so ta fita ta yi sallah amma ta na tsoron kafar ta kara rikewa. Wani irin zazzaɓi ne ta ji ya yi mata dirar mikiya, ba shiri ta ɗan kishingida.

Shigowar Ɗan inna da ita kanta Innar ne ya sakata miƙewa tare da jin gabanta ya yanke ya faɗi. Musamman da ta ga yadda Inna ke sharɓar kuka shi kuma ɗan Inna hannunsa rike da zabgegiyar bulala.

"Inna lafiya! Ko wani abu ya faru ne ban sani ba"

Na karasa maganar cike da tsoron tashin hankalin da zai biyo baya, domin jikina na bani ba banza ba.

"A gaban idonka ka gani ko dan inna? Yanzu ma karyatani take yi. Shuhuda me nayi miki kike son ganin dole sai zuciyata ta buga na mutu na bar miki wannan duniyar"

"Ki barta Inna. Ki barni da ita kawai don jikinta ne zai gaya mata yanzu ba sai an jima ba. Saboda tsabar kin raina Mahaifiyata ta ce miki ki kauda kayayyaki ruwa zai sauko, amma ki budi baki ki ce mata ba za ki iya ba. Hatta miyar tuwon da na dawo zanci kin barta ruwa ya lalata ta"

Wasu yawun wahala naji na hadiye domin na san yau mai kwatata sai Allah.

"Don Allah ka tsaya in maka bayani ka saurareni. Wallahi banyi ma inna rashin kunya ba domin ko ba komai Mahaifiyata ce. Na so tashi in yi abin da ta sakani amma kafata ta rike, hatta ruwan da aka yi kai shaidane nan ka zo ka wuce ni na kasa ta shi"

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Ta sake ƙaryata ni shi kenan! A gaban idanunka ta kuma ƙaryata Mahaifiyarka"

Kafin ka ce me ya ɗaga zabgegiyar bulalar hannunsa tare da sauke ta a jikin Shuhuda ta ko ina. Kuka ta ke ta na rokon suyi mata rai amma ina idanunsa sun rufe jibgarta ya ke tamkar Allah ya aiko shi.

Sai da ya yi mata lilis sannan suka bar dakin. Tun ta ina kuka da hawaye har hawayen suka kare. Da kyar na rarrafa na jingina da gadon tare da jin sabon kuka ya kwacemin.

"Allah na gode da wannan jarabta da kayi mini. Ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawar, na kasa jurewa ji na ke ɗayan biyu dole abu daya ya faru. Ko dai in koma gidanmu ko kuma in San me zanyi Tajo ya daina dukana, ga tsohon ciki amma haka zai kamani ya daka ba tare da kakkarfan bincike ba”

"Ki koma gida fa kika ce? Shin kin manta rayuwar da ki ka baro a gidan naku ne? Kul kika ce za ki kashe aurenki ki koma gida"

Wata zuciyar ta yi gaggawar tunatar da ni.

Zafin dukan da yayi mini ne ya saka wani zazzabin rufe jikina. Da kyar na mike na haye gado tare da janyo hijabin da nake sallah na rufe jikina. Kasancewar ranar ba dakina Tajo ya ke ba ko dakin ban rufe ba a galabaice bacci yayi awon gaba da ni.

Murja da ke laɓe a bayan labule kaf abubuwan da suka faru ta ji dariya ta sheke da ita.

"Da ni kike zancen. Har kin isa ki shigo gidan nan ki ce zaki haihu kamar yadda na haihu. Ki haihu na gani in dai ina raye ba zaki taba haifa cikin can ba, yadda kika zo da shi haka za ki koma da shi"

'yan biyunta ta kalla mace da namiji da a kalla zasu kai shekara biyu, ganin sunyi bacci ya sakata mayar da su dakinsu kafin Tajo ya shigo.

Shuhuda kuwa wani wahalallen bacci ne ya yi awon gaba da ita.

Dare ya tsala baka jiyo sautin komai sai kukan karnuka da sauran halittu.

Labulen dakin ne ya fara kadawa ya tashi sama duk da ce wa ba iska ake ba. Sanye cikin bakaken kaya suka bayyana fuskarsu rufe take, kai tsaye dakin suka shige tare da kewaye Shuhuda da ke kwance ba tare da sanin abinda ke faruwa ba.

Wasu surutai suka fara yi daya daga cikinsu cikin girmamawa ya kama cikin tare da watsa mata wani abu mai kama da jini.

Firgigit na farka daga wannan mummunan mafarkai da suka aureni.

Sai dai wilgin wani abu na gani ta tagar dakina ya wuce. Ban kawo komai a raina ba komawa nayi na kwanta.

Bani na farka ba sai da gari ya waye.

Yunwar da ke cina ce ta saka yi Fara dube-dube cikin dakin, sai yanzu na tuna jiya sam banci abinci ba.

Murja kuwa bayan ta canzawa tuwon miya kowa ta bashi nasa banda Ni. Ba a bani sabuwar miya ba tunda ni nayi sanadiyyar lalacewar ta jiya.

Gayen tuwon na Fara ci, sai dai tunawa da nayi ina da sauran gishiri dauko shi na yi na barbada na hau ci a zalamance.

Ruwan randar dake dakina na sha tare da komawa lakwas na jingina da gado.

"Nima kenan nike rayuwa cikin wannan halin, to abinda zan haifa wace irin rayuwa zai yi a cikin gidan nan"

"Shuhuda! Shuhuda!! "

Na tsinkayo muryar Inna na kwalamin kira. Sanin hali ya sakani zimmar mikewa sai dai abin da nake gudun ne ya faru.

"To basarakiya! Kina nan kin kafa sarautar ta ki ba zaki amsa min kirana ba?"

"Allah ya huci zuciyar ki yanzu nake shirin mikewa"

"Da ma dole ki ce haka. To kayan mijinki da nawa ne za ki wanke inda hali"

"To inna gani nan fitowa"

Ba tare da bata lokaci ba haka ta fita tare da hango tsibirin wankin da suka hada mini.

Ba bata lokaci ta hau yi duk da bayanta da take jin ya rike haka ta ci gaba da aikin.

Murja kuwa haibaice-habaice ta hau yi sai dai in da sabo Shuhuda ta saba bata kulata.

Ganin ya na shirin fita ya sakata yin sauri tana tsayar da shi.

"Me kuma ya faru da ba zaki fada tun dazu ba sai yanzu da kika ga ina shirin fita"

"Dama so nake In je gida in gano Iya in Ka amince"

"Ki je In za ki iya domin kwandala bazan baki ba"

"Yardar taka ma na gode"

Ba ni na gama wankin ba sai bayan azahar jikina ya yi likis. Kamar bazan iya ba sai da na bari anyi la asar nafito. Tare da rike Naira ta ɗari data rage in Sai ma Iya wani abu a kan hanya.

Kancewar a kauye daya muke da kafa na taka duk da kafata da nake jin kamar ta min nauyi. A daidai wata doguwar kwana ta bayan gidanmu na hango wata jigatacciyar tsohuwa ta na Bara.

Kudin hannuna na kalla tare da kallon tsohuwar da ta fini bukatarsu. Ya na iya mikawa suhuwar kudin nayi tare da juyawa zan tafi.

Charaf! Na ji ta rikomin hijabina.

" 'yata tunda kika taimakeni tabbas nima zan taimake ki"

Da mamaki nake kallon tsohuwar

"Ni kam wane taimako zata yi mini, ni dai nasan na taimaketa ne domin Allah"

"Bala'i, masifu, hadi da rikitattun al'amura ne ke bibiyar abin da ke cikinki, ko kuma in ce suke tare da shi. Da kin san abin da zai faru da baki yi gigin baro gida ba, ina mai tabbatar miki wannan cikin ba..."

Maganar tsohuwar ce ta sarke sakamakon keken shanu da ya kwacewa mai shi yayo kanmu. Tamkar an kwasheni haka na ji anyi jifa da ni gefe, a take shanun tare da kekensu suka bi ta kan tsohuwar suka niƙe.

Jinin tsohuwar ne ya feso min a fuska ba shiri na saki ihun daya janyo hankalin mutanen da ke nesa da mu.

A guje suka yo kanmu cikin tashin hankali...

Meenat A 'Yandoma

***