FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
FATALWA BAƘAR TAFIYA SAKACI SALMA RAZANI WANI ƘARNI RUWA BIYU ƘULLALLIYA
Sample · Page 01
ƊAYAN BIYU©️MEENAT A 'YANDOMAWattpad: Meenat_A_YandomaArewaBooks: MeenatyandomaMANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONMASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***Page 01Tsananin duhun da garin ya yi ne ya saka Shuhuda dafe ƙaton cikinta, ji ta yi ya na motsi tamkar mai neman hanyar fitowa duniya. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon yadda garin ya hade da hadari baƙiƙirin, ga wani iska da aka fara."Shuhuda! Kina ina ne? Ba za ki tashi ki kauda kayayyakin nan ba sai ruwa ya sauko?"Ta tsinkayo muryar sirikarta na fada.Sunan Allah ta kira tare da dafe cikinta sakamakon ji da ta yi tamkar an kai mata naushi."To! Dama kina jina kika barni ina ta ɓaɓatu tamkar ina magana da dutse. Yanzu yarinyar nan shi ne ki ka samu wuri ki Ka tule tamkar dasa falwaya. Me kike nufi da ba za ki tashi ki kauda kayayyaki ba, koko so kike ni uwar mijinki gaki a gidan ni zan fit...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.