Page 17
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
BOOK 1
*YOTA*
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 17
Gabad`aya hankalinsu ya tashi sun rasa madafar da za su kama da ga Yarima Haisam d`in har su kansu sun koma tamkar mahaukata,sai su lullu`be sa lokaci guda kuma su koma yi ma sa fifita,tamkar Aljanu ko kuma wad`anda a ka watso haka su Jamal su ka ga Sarauniya Junayyah a gaban su tare da kuyangarta hannunta d`auke da wani k`ok`o sai bayanta wasu zaratan Dakaru ne biye da ita,ba ta bi ta kan su ba balle su sa ran za ta ce da su wani abu, ta sa wad`annan zaratan Dakaru su ka fara watsa ma su wannan ruwan da ke d`auke a cikin tulun,tun ba a je ko ina ba,duk wanda aka zuba ma wannan ruwan sai ya tsandara ihu mai matuk`ar k`ara tare da sumewa a lokaci guda,duk wanda wannan ruwan ya ta`ba sai ya shiga cikin irin wannan makamancin wannan halin,saukar ruwan a jikinsa wani irin turiri tare da hayak`i ya tashi a jikinsa lokaci guda,take ya fita daga cikin hankalinsa tare da tunaninsa wani irin ihu mai k`arfi Sarauniya Junayyah ta saki gami da fara yi ma kanta kirari,"Sai ni Sarauniya Junayyah `ya gurin Nakil jikar Zafar,tsatson Baidu,yau na cika burina na kamo Jini kuma tsatson k`asar BIHINAR, zan yi duk abinda na so in cika burina na Mulkar wannan duniyar sai na gaji KARAGAR MULKIN uban ka a ta dalilin ka",ta k`are zancen da cewa,"ku d`auke min shi ku mai da min shi `'bangaren da ya fi kowanne `'bangaren tsaro a cikin wannan kurkukun, su kuma wad`annan banzayen ku mai da su wancan asalin d`akin da a ka fara aje su,ta na kaiwa nan ta bar cikin d`akin kurkukun,Kai tsaye ko da isarta d`akinta wurin madubin tsafin ta ta nufa ta sanar da Boka Dürsäås nasarar da su ka sa mu ,tamkar abinda ya ke jira kenan nan ta ke ya sanar da ita gashinan zuwa a yau zai bak`unci cikin K`asar BAIBAH,komin Sulusin dare .Sai da su Ayub su ka kwashe tsawon sa'a biyar sannan su ka farka su ka dawo cikin hankali da natsuwar su,har su ka fara tattaunawa
"Jamal hankalina a tashe ya ke ,ban san me ye dalilin su na zuwa su fidda Yarima Sadauki daga cikin mu ba,tsoro na ke ji kar a ce sun gane ko shi d`in wane ne,ko kuma sun san shirinmu na guduwa "," Haba Habib ta ya zasu gane hakan ,matuk`ar ba wani da daga cikinmu ne zai fad`a masu hakan ba"....."Kai kuwa me ya kawo irin wannan maganar ta ya wani daga cikinmu zai iya tona wannan babban sirrin,to ta ya ma hakan za ta kasance,ta kuma wacce hanyar za a fitar da maganar bayan duk ga mu anan a gark`ame ,kuma babu wani mahaluk`i ko mutum mai rai da ya san da abinda ya faru a jiyan ba,bana tunanin haka gaskiya kai ko da anyima d`aya daga cikin mu barazana da rayuwar sa ba zai aikata hakan ba to ta inama za a fitar da wannan batun ?",Zafar ya faɗa,"To in ko haka ne ,tabbas da akwai wani abu da ke gab da shirin faruwa","Kamar ya Habib ,ta ya za ka rik`a irin wannan zancen ,hakan bai kamata ba,tun wuri ka dakatar da munmunan tunanin da ka ke, kar ka ja ya zama gaskiya, mu bani mu shiga uku","Bawai ina munana fata a kan mu ba ne,a'a kawai dai Ina kallon lamarin ne kamar da akwai lauje cikin nad`i ","Ka kwantar da hankalin ka Habib ka sannan ka kyautata ma su zato,duk da na sani su d`in ba mutanen arzik`i ba ne kuma suna cutar da mu,amma hakan ba zai sa mu d`auki alhakinsu ko mu munana ma su zato ba, idan mu ka aikata hakan ina da tabbacin Ubangijin sammai bakwai da k`assai bakwai zai kubutar da mu ya Cece mu daga cutarwa da azbatarwarsu","To shikenan in sha Allah bazan k`ara kawo makamancin wannan tunanin a cikin Zuciyata ba,ina me tabbatar ma ka in har su ka zo da wani abun na daban tabbas za su sha mamaki,kar ma in su ka yi yunk`urin ta`ba ko kai Yarima Haisam k`arshe"," A'aha ban gane kuma me ka ke nufi ba?","Nufina anan shine ba na fatan su kai ga ta`ba Yarima Sadauki, mudun suka kai ga aikata hakan ,d`unbin danasani ce zata biyo bayan abinda su ka aikata "," Wai Jamal me ya ke samun ka ne ?,ba ka duba da yanayin halin da `yan'uwanmu su ke a ciki ne,kalli Ayub ka gani k`afarsa zubar da jini ta ke,Salim kuwa hannunsa d`aya a karye ya ke,Kai a tak`aice kowa ka kai ganin ka a kansa cikin mawuyacin halin ya ke,da kuma tsakanin rayuwa da mutuwa ya ke,ta ya za ka ishemu da wad`annan banzayen tunanin na ka, ka barmu muji da yunwa,k`ishir ruwa da kuma jinyar da mu ke fama da su.....Ayub ne ya bud`e baki da k`yar ya na mai kar`be zance ta hanyar cewa,"Kabarshi ya fad`i abinda ke kwance a saman harshensa mana ka sa ni ko wata k`ila Allah Subahanallahu wata'ala ne ya haskaka ma sa abinda ke shirin faruwa da mu, don mu shirya ma zuwan haka? "," Aiko in har haka ne muna cikin babbar matsala domin a cikin mu kaf ba mai lafiya ko k`arfin da zai iya yak`ar sama da mutum hamsin balle har mu tunkari Masarauta guda",Cewar Salim.
"Wa ya gaya ma ka haka ,ai mu ke da runduna ,Kai ba ma runduna ba ,mu ke da Mayak`an duk duniya tunda muna tare da Harzan"," Harzan kuma me ya kawo maganarsa anan ?",cewar Abbas a ƙagauce yana d'aga can kwance yana fama da k`afarsa "," Habib ne ya bashi amsa da cewa,"Kai a tunaninka za su yi k`ok`arin cutar da mu ne ba tare da Harzan ko Narshad ya kawo ma Yarima Haisam ziyara ba?","Kai! Kai! Kai! in ko haka ne akwai kallo a k`asar BAIBAH sai dai wani hanzari ba gudu ba,idan har bayyanar Harzan a jikin Yarima Sadauki abun so ne a gare mu to ya ku ke tunani in Narshad,Azla, ko Azeela ne su ka bayyana ?",shiru gaba ki d`ayansu su kai na wani lokaci, Habib da ya fara tak`alo zance ne dai ya amshi zancen da cewa, "Tabbas bayyanar Narshad a cikin wannan k`asar tonan silili ne ga k`asar BIHINAR gabad`aya har ma da mutanen da su ke rayuwa a cikinta,domin na san kai tsaye gidan Gala ko Gidan shaye-shaye can zai nufa,ya nemi mata kuma ya sha Giya,Hakama bayyanar Azla da Azeela Kai tsaye d`abi'un mata zai koma ya na yi,kunga kenan bayyanar hakan abun kunya ne ga kaf `yan k`asar BIHINAR, to meye riba ko amfanin mu a cikin wannan lamarin".
" Gaskiya in dai haka ne Babu wani alfanu da za mu samu a cikin faruwar hakan,Kai har garama rayukanmu su salwanta anan da hakan ta faru","Ka yi magana mai kyau Salim duka-duka mu nawane mu kai saura a da can mu fa Ashirin ne ,bakwai su ka mutu tun muna cikin Jirgin ruwa a sanda ga`bar ruwa ta jawo mu zuwa nan,anan kuma ga mu duk a jinyace to me ye zai sa ba zamu bada rayukanmu fansa a kan mutuncin k`asar mu ba tunda da dama tun farko da niyar haka mu ka baro k`asarta mu,Gidan mu,`yan'uwanmu,matayenmu,abokanmu,`ya`yayenmu har ma da iyayenmu".
"Ka fad`i Gaskiya Jamal don haka mu cire wannan maganar gabad`aya daga rai da zuciyoyin mu,mu tashi mu yi taimama mu gabatar da Sallahr Magriba da alamun lokacin ta ya yi ,kun ga sai muyi amfani da wannan damar mu rok`i Ubangijin da ke `bullo da Rana ta gabas ta kuma fad`i a ta yamma, wanda ya ke fidda rayayye a cikin matacce"," Haka ne amma bari in tari numfaahinku ya za mu yi da maganar barin kurkukunan a wannan daren ,alhalin gashi ba ma tare da Yarima Sadauki ?","Tambayarka ,tambaya ce mai d`auke da babban lamari,tun d`azu ta ke zuwan min arai babu yanda za ai mu tafi mu bar shi a cikin wannan k`asar ,idan har hakan ta faru ba mu san me zai biyo baya ba,kuma idan mun isa k`asar BIHINAR me za mu ce da Madaki da kuma Me Martaba Sarki Abdullah ?","Dole ne za mu tafi in ba haka ba tabbas ba makawa za ai biyu Babu,ko in ce fad`uwar guzuma `ya kwance uwa kwance,ko kun manta abinda Giwar Masarautar BIHINAR tace da mu,dole ne in mu na so mu tsira da rayuwar mu aikata dai-dai da abinda ta ce",Cewar Salim,"Wai ka na nufin mu tafi mu barsa a hannun wad`annan mutanen azzalumai kuma macuta,mujusawa marasa jin tsoran Allah ?",in yi Sahab"Eh mana in ba haka ai ba mu da wata mafita",a harzuk`e Jamal ya nufo inda Salim ya ke ya na mai shak`e ma sa wuya ya na cewa,"Ƙ`arya ka ke d`an talakawa,kai waye,me ka taka da har za ka ce haka,ta ya ma za a ce mu tafi mu bar Yarima Haisam a cikin wannan azzaluma kuma tagaiyararra k`asar¿?"