JADEEDA

Page 16

by @cwtsumiey19988

*JADEEDAH*

         (It's a story of two love birds who are so different from each other ) 
STORY & WRITTEN BY :
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
        MENE NE ABIN YI ?
        KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1 
PAGE 16❤🔥
After some Months
Zaune take ta rafka tagumi da hannayenta duka biyu,idanunta na kan bed d`in da Abbakar ke kwance amma a zahiri hankali da tunanin ta ba a nan suke ba,hakan ya sa ko shigowar Mama Hadiza ba ta ji ba,har sai da ta kai ga dafa kafad`unta sannan tai firgigit ta farka tun kafin tace komi hawaye suka fara zubowa a saman idonta.
     "Hibba me kike yi haka kar dai kice min har yanzu baki d`auki k`addarar da Ubangiji Allah ya saukar miki ba".
    " Mama ba haka bane ba Zuciyata har yanzu da k`una a cikinta kuma na kasa yarda da Cewar wai Jadeeda ta rasu ta barni,da kaina fa na mik`a ma Cecelia ita ,wannan Gloria ta amsheta,kuma na tuna komi ko da Accident d`in ya faru banga Gloria ko gawarta ba kenan hakan na nufin duk inda Gloria ta ke `yata Jadeeda na tare da ita".
    Sai da Mama Hadiza ta sauke a jiyar Zuciya sannan ta ce da ita,"Ki yarda da Allah ki d`auki k`addarar da ta same ki,ki sani har jana'izar Jadeeda an gabatar to me yai saura da ya wuce ki yarda da Allahn ki kar`bi abinda ya saukar a kan ki,wanda ya baki `yarnan fa yafi ki sonta shine fa ya amsheta to don me za ki tada hankalin ki,ya kamata ki fara k`ok`arin sake sabuwar rayuwa domin ki samu cigaba a cikin rayuwar ki,ba wai ki nemi sake jefa kan ki cikin wata sabuwar matsalar ki kalli fa halin da Mijin ki yake yana buk`atar taimakon ki,idan ki ka cigaba da tafiya a haka ba iya rayuwar ki kad`ai ba harda ta sa rayuwar za ki lalata".
    Tsuru Hibba tai tana mai mai-maita maganganun Mama Hadiza a cikin ranta,"Eh da gaske na ke miki ki tashi tsaye ki tallafi rayuwar ki da ta Mijin ki,kuma ki dage da addu'a ina mai tabbatar miki indai Jadeeda na da rai kuma tana taka doran k`asa sai wata rana ta nemeki ta dawo rayuwa da ke",Mama Hadiza na kaiwa nan ta tashi ta mik`e da niyar barin d`akin,shigowar Ummie Maryam ce ta d`an dakatar da ita.
    "Mama ashe ki na ciki,na shiga sashen ki na iske ba kowa"," Eh inanan na zo na iske ta tana yin sana'ar da ta saba,dan Allah ki rik`a gaya mata gaskiya wala Allah ko ma samu ta dawo cikin hankalin ta ta san abinda ya kamata ta aikata a cikin wannan lamarin "," To Mama amma wallahi inayin iyakar iyawata amma har yanzu ba nasara,hatta da Jaheed ya shiga cikin matsanananciyar damuwa saboda yawan ganinta a cikin irin wannan halin ".
    Sai da Mama Hadiza ta mai da kallonta kan Hibba kafin ta ce da ita"To ai shikenan tunda haka ki ka za`ba ma kan ki",ta na kaiwa nan ta bar masu d`akin.
    Wuri Ummie Maryam ta samu ta zauna kusa da ita tana mai d`ora hannunta akan ta ta ce," Kin gani irin wannan abun nake guje maki tun da farko,Na sani kina cikin damuwa da kuma tashin hankali amma ki sani ba iyake abun ya shafa ba,duk wani na kusa da ke ko kuma mai k`aunar ki yana jin zafi rad`ad`i da kuma damuwa kamar yanda ki ke ji,kar ma Mama domin itama d`in uwace ta kan fi kowa jin zafin abu ko murna idan ya samu d`anta,ina mai tabbatar maki ko ke ba lalle ki kaita shiga cikin tashin hankali da damuwa ba,ki kalli yanda ta rame ta fita hayyacinta ko barcin kirki fa ba ta iya samu,ga yawan cuttuka da ke cikin samunta kuma hakan yasamo asaline da sanya damuwar ki a cikin ranta,ya kamata ki ji tsusayinta,ki rage wannan damuwar,wai ma meye zai sa ba za ki saurari Maganar da ta ke fad`a mi ki ko sau d`aya ne ba,ki tsamota daga cikin yanayin da take a kai , ko hakan kad`ai ka iya sawa Allah ya sassauta ko ya yaye maki halin bak`in cikin da ki ke a ciki".
    Sai da Hibba ta sharce hawayen da ke fitowa daga cikin idanunta kafin tace,"Shikenan Ummie Maryam in sha Allahu daga yau ba za ku sake ganina a cikin irin wannan yanayin ba,zan dan ne duk abinda nake ji in barshi a iya cikin Zuciyata har zuwa sanda Allah zai kar`bi rayuwata in dai har kan ne zai sa ku cikin farin ciki to zan aikata hakan duk da dai"......
    Ta kasa iya k`arasa zancen nata, ita kanta Ummie Maryam hawaye ne ke zuba daga cikin nata idanun har ta bud`e baki zata sake cewa da ita wani abu ta fasa sakamakon ganin da take in har zasu cigaba da yin wannan maganar to ba za su ta`ba daina zubar da hawaye ba ko kuma su samu damar kawo k`arshenta ba,don haka sai ta za`bi yin shirin wala Allah zai zama mafi alkairi a gare su.
 "Ammm Hibba kina da bak`i fa", Ummie Maryam ta fad`a ta na mai kauda idanunta gefe.
    Cikin sabon yanayin da ya zame ma Hibba jiki ta tambayeta," Bak`i kuma ,a wannan lokacin su waye?","Daga Companyn su Abbakar ne,sun sake zuwa ne don su duba jikin shi ","To ba matsala ki sa a shigo da su mana", da to Ummie Maryam ta amsa mata tana mai juyawa har ta kusa fita ta waigo tace da ita," Ki d`an gyara fuskar ta ki kafin su shigo".
   Sai da Ummie Maryam ta sanar da Mama Hadiza zuwan na su,domin ta zo su gaisa ta had`a da saka Jaheed ya je ya sarna da su Baba Malam sannan ta sa a ka shigo da su,bayan sun shigo an gama gaggaisawa sun k`ara yi masu ya mai jiki da fatan Allah ya tashi kafad`unsa,sannan Acountern Companyn Abbas ya ce mu su,"Allah sarki Manager mutumin kirki ne dukkanin mu nan mun shaida haka,a d`an zaman da mu ka yi da shi tun yana matsayin Crista ba a ta`ba samun sa da wani yana musayan miyau da shi balle har ta kai su ga yin fad`a ba,ga gaskiya ga kuma rik`on amana gaskiya ba mu da wani abun fad`a akan shi in har ba yabo da jinjina zamu yi gare shi ba,ba kuma wai a gare mu kad`ai ba hatta manya da kuma k`ananun ma'aikata ,suna ta kuka gami da jajantawa akan abinda ya yafaru da shi ne ".
       " Tabbas Acounter Maganar ka gaskiya ne wanda hakan ne yasa shi asalin mamallakin Companyn ya aiko da wad`annan mutanen wasu likitoci ne guda biyu daga can Abuja suke kawai don su dubasa su bashi kulawar da ta kamata in ta kama a kai ga a fidda shi zuwa k`asar waje ne sai a fidda shi".
   "Kai Bayin Allah, Allah ya saka maku da alkairi, mun gode mun gode,ku Isar da sak`on godiyar mu ga shi Ogan na ku,ni ban ma San da wanne baki ya kamata in nuna muku jin dad`in wannan abun da kuka zo mana da shi ba,Allah ne kad`ai zai iya biyan ku,ya saka maki da alkairi yai maku tukwuici da Gidan Aljannah", Cewar Baba K`arami Wanda hatta a muryasa zaka gane yana cikin farin cikin game da abinda ya saurara.
    "Kar ka damu wannan duk can-cantar da shi Abbakar d`in yayi ne,ba sai ka yi wani Godiya ba, suna son a samu wani yayi masu cikakakken bayanin abinda ya ke faruwa da shi,da kuma irin matakin da ya ke akai a yanzu".
      Nasir ne yai masu cikakakken bayanin asalin da yanda abun ya faru," Ya samu buguwa ne akan shi sakamakon accident d`in da ya gamu da shi Wanda a turance muna kiran wannan cutar da suna Neurological disorder the Conditions affecting the brain, spinal cord, and nervous system (e.g., epilepsy, multiple sclerosis).
    Also Neuro developmental disorder Conditions affecting brain development (such as ADHD, autism spectrum disorder),a ta haka in ka kalle shi zaka iya cewa barci yake ba dan wannan oxygen d`in da aka sanya mashi ba ,wannan shine matsalar da take damun shi".
    "Ammmmm but amma in dai condition d`insa a wannan matakin ya ke bai kamata ace kun na jinyarsa a cikin Gida ba,zai fi samun Good treatment da samun ingantattun magungu ba da kuma nagartattun kayan aiki ya akai haka Doctor Nasir ?".d`aya daga cikin Doctors d`in ya tambaya.
    "Eh haka ne nasan da hakan amma kasan irin wannan problem d`in yana da matuk`ar hatsari da don bin taka tsan-tsan gami da lura dalilin ba d`aya ne da ya sa Na dawo da shi,da zaran wurin da yake,yanzu zai fara shebaring yana shirin fad`owa,yanzu da ace zamu kaure da surutu a cikin wannan d`akin duk da kasancewar sa baya iya ko motsa d`an yatsan shi to da haka ce zata kasance".
    " Okay na fahimci inda matsalar take yanzu za muyi mashi `yan wasu gwaje-gwaje da zamu je muyi amfanin da su,Amma na so ace zamu iya admitting nasa a Hospital yanda zai samu kulawa da shi 24/7,amma hakan ma ba damuwa zan turo Nurses guda biyu da zasu rik`a taimakawa Madam wajen kula da shi, har zuwa sanda zamu kammala namu binciken".
    Godiya Sosai Mama Hadiza,Baba K`arami, Nasir da kuna Ummie Maryam suka rink`a yi ba, don ita Hibba ba bakin magana sai faman zubar da hawayen farin ciki ta ke, a tare su duka suka tafi raka su bayan sun gama duk abinda za suyi har sun kusa fita daga Gidan Abbas Acounter ya dakata yana nai cewa da su yana zuwa yayi mantuwa,"Madam zan iya shigowa ?",Yace da Hibba bayan yayi sallama ta amsa.
    Tsaye take akan Abbakar tana mai motsa mishi wasu daga cikin sashen jikin saboda gudun kar su mutu su daina amfanin,"Am kana neman wani abu ne ko kuwa ka yi mantuwa ne ?",Hibba ta ce da shi.
    "Madam ba mantuwar da nayi,Na zo ne na Isar da sak`on da aka bayar in baki tun kafin yanzu".
    " Sak`o kuma wanne irin sak`o ne wannan haka ?",Hibba ta tambaye shi,bai bata amsa ba sai zura hannunsa yai a cikin aljihunsa ya fiddo wani Embolof daga aljihunsa ya mik`a mata yana mai cewa,"Wannan shine sak`on da yalla`bai ya bani akan sai bayan ya dawo bikin k`anwar shi,in ya tafi seminar d`in da yake shirin tafiya sai in kawo maki,to kafin hakan ta faru wannan tsautsayin ya fad`a akan sa,shine na yanke shawarar in kawo maki ko da abun ciki ba zai amfani ba,ni dai na sauke alk`awarin da na d`auka ".
    Amsa Hibba tai idanuwanta na fara k`ok`arin zubda hawaye, ta amsa tana mai yi mashi Godiya.
    Jikin Hibba na rawa ta fara bud`e Embolof d`in abinda ta gani ne yasa numfashi da kuma jikinta tsayawa cak,sai da ta d`auki wani dogon lokaci kafin ta dawo cikin hayyacinta,hannunsa guda ta kama ta rik`e kam tana mai d`ora kanta a saman gadon da yake kwance tare da fashewa da kuka cikin mad`aukakiyar murya tana mai cewa "Me idanuwana ke gani,wacce irin cutarwa ce na aikata ma kaina,Na cutar da kai na zama silar salwantar mana da `ya d`aya tilo da muke da ita kai kuma ga ka kwance cikin halin mutuwa da rayuwa,duk don saboda tsananin fushi da son kaina da ban hassala ka ba da idanuwanka basu rufe daga ganin motar da ta tunkarowa mu ba,da yanzu ina tare da kai da kuma ƴata ɗaya tilo da na ke da itanikam wacce irin Mata na zama,wacce irin uwa ce ni mai salwantar ta ran `yarta da kuma ta Mijin ta,bayan kai ka kasance mutum mafi adalci kyautatawa a gare ni,kullum buri da fatan ka ka ga na zama abar kwatance,Na cika buri da duk wani fata da nake da shi,da wacce irin fuska zan kalle ka aduk ranar da ka warke ka tambaye ni ina Jadeeda ta ke, da wanne baki zan iya gode maka irin tarin alkairan da ka yi min a iya d`an zaman da muka yi tare da kai?"......
   Da sauri Ummie Maryam ya k`arasa iso kusa da ita tana mai tambayar," Lafiya me kuma ya k`ara faruwa ?".kasa iya cewa komi tai sai nuna mata Peppers guda biyu da ke zube a k`asa ,d`auka tayi ta fara dubawa,d`aya admission na shiga jami'a ne a matsayin d`alibar jinya,sai na biyun kuma dogon bayanin ne akan yanda yake sonta da kuma murnar samun admission da yake taya ta,daga k`arshe ya ke cema ta ta kula da kanta da kuma Jadeeda har zuwa ran da zai dawo.
    "Mene ne abin tashin hankali a cikin wannan lamarin naga kamar takardar cigaba da karatu a university ce waye ya samo ta?"," Shine ya samo min tun kafin faruwar wannan a'lamarin ya bari ne yai surprised d`ina sai kuma hakan ta faru ".
   Sai da Ummie Maryam ta samu guri ta zauna tana fuskantar Hibba sosai da sosai kana ta fara cewa da ita,"Hibba ki natsu wannan babban dama ce kika samu, bai kamata ki yi wasa da ita ba,a da idan kin d`auki wannan karatun a matsayin buri ko fatan ki,to a yanzu ki canza ki d`auka Cewar za ki yi karatu dan Mijin ki,za ki rayu dan shi ki yi karatu dan shi,ki manta da komi da ya faru,ki farfad`o da rayuwar ki da tashi a lokaci guda,kar ki wasa da wannan damar".
    Shiru Hibba tayi na wani lokaci kafin ta bud`e baki tace,"Ummie na yi miki alk`awari zan yi amfani da wannan damar da kuma shawarar da ki ka bani,zan yi karatu ko dan Mijina,zan zama Malamar jinya ko dan shi ya cigaba da rayuwa ya samu kulawa ta, zan yi iya yi na don ganin haka ta faru".
    Sosai Ummie Maryam ta ji dad`in wannan lafazin na Hibba har sai da ta kai ga ta rungumeta.
Wannan kenan
    After 5yrs 
    A guje ta fito tana mai kwalama Ummie Maryam kira ta na mai d`oki da murna,"Mun samu damar ganin Likitan kwakwalwa a can U.s.a,Ummie muna cikin alkairan Allah ".
    Cikin zumud`i Ummie Maryam ta ce," Kai Alhmdllh Masha Allah gaskiya muna cikin alkairi yanzu bayan Schoolarship d`in da ki ka samu ,kuma sai ga wannan babban alkairin ya zo ?".
    "Ke dai bari Ummie ga Mama can ta tafi ta sanar da Baba Malam ,nasan shima zai yi farin ciki, har Baba K`arami da kuma Yayah Nasir na Kira a waya na sanar da su, yanzu haka na san Baba K`arami ya kusa isowa domi mu fara tsara yarda zamu yi tafiyar,kin San fa tare da Yarona zamu tafi", ta kai zancen tana mai fad`ad`a fuskarta da murmushi.
    " To ai dama nasan da haka Jaheed ai d`anki ne in ki ka tafi ki ka bar ni da shi, ai ba zan iya ji da rigimar shi ba,dan haka addu'a ce tsakani na da ku,yanda kuka sanya mashi rai a wannan tafiyar ai in baku tafi da shi ba ba zaman Lafiya kaf Gidannan don haka Allah ya ba Abbakar lafiya ya sa wannan shine k`arshe wahalarsa,ku kuma Allah ya sa albarka a cikin karatun da za ku yi".
    Haka dai suka cigaba da murnar su har sanda su,Baba Malam, Baba K`arami da kuma Yayah Nasir su ka zo,suka cigaba da tsara yanda komi zai tafi game da da tafiyar su Hibba, lokacin da mutanen Gidan suka samu labarin wasu sun yi murna wasu kuma a fili suka rik`a bayyanar da hassadar su a fili,amma a cikin su ba wanda ya kula su,sai ma k`ara k`aimi da suka yi game da shirin su.