Page 03
ƊAYAN BIYU
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
Page 03
...Mutane da dama sun sulale sun bar gidan kafin wani lokaci. Domin sun fara tunanin anya babu sa hannun jinnu a wannan lamari, ya za a ce Sarkin Rafi ya shiga rijiya shi da a iyakar ittifakin da suka yi akwai amana a tsakaninsa da ruwa.
Nauyin da suka ji igiyar ta yi shi ya tabbatar masu da ce war Sarki ne. Ba su bata lokaci ba suka bada himma wurin janyo shi.
Ganin fuskarsa a bace ga wani gumi da ya ke yarfewa ya saka jama'ar wurin sake shan jinin jikinsu.
Inna Zulai da farfadowarta kenan gabansa ta zube ta na kuka.
"Sarkin Rafi ka taimaki rayuwata, kada ka ce min Tala ta mutu. Ni nasan bata mutu ba doguwar suma ce ta yi, ka fada masu bata mutu ba"
Ta karasa maganar tare da rushewa da kuka.
Sadda kansa ya yi kasa domin gaskiyar da zai fada mata ya san ɗacinta ya fi na mutuwar Tala.
"Kul! Ka fada mata, domin kowa ya sai rariya ya san zata zubda ruwa. Abin da ta shuka shi zata girba"
Wata zuciyar ta yi saurin gargadinsa.
"Sai hakuri! Taka dai ta rigamu gidan gaskiya. Sannan wannan rijiyar daga yau ku tabbatar ko ruwanta kada a sake diba. Ina so samu ne a samu murfi a rufe ta tare da yin kaffa-kaffa da yara kada a bari kowa ya kusanto inda take"
Kururuwa Inna Tala ta ci gaba da yi tare da birgima cikin kasa.
Iya ce bayan ta samu Shuhuda ta farfaɗo ta riko Inna Zulai.
"Zulai hakuri za mu yi, kowa da kika gani a wannan duniyar lokaci ya ke jira. Talatu bata debo da yawa ba, kiyi hakuri kiyi mata addu'a domin ita ta fi buƙata a yanzu"
Tamkar jira ta ke Iya ta rufe baki bangajeta ta yi tare da Fizgo Shuhuda da ke gefe ta na kuka.
Wani wawan mafi ta dauke ta da shi.
"Allah ya isa tsakanina da ku. Ba irin gargadin da banyiwa Malam ba a kan kada ya auri uwarki, amma haka ya kwaso mana mugun iri ga shi nan da kuka ta shi ta kansa ku ka fara. Me Tala ta yi miki za ki kasheta ni ya kamata ki kashe ba ita ba domin ni na hanani waina"
Da kyar aka kwace ta a hannun Inna Zulai.
Mutane ba su yi mamaki ba domin tunda rayuwar Malam mijinsu ba wanda bai san ukubar da Zulai ta ganawa Iya ba.
Da dai Iya ta ga an saki Shuhuda kama hannunta ta yi cikin ƙunar zuciya suka bar gidan.
Tun bayan komawarsu gida an rasa mai rarrashin wani, Shuhuda ce ta yi karfin halin kallon Mahaifiyarta.
"Iya! Ina hadaki da girman Allah ki fadamin gaskiya, shin mu dangin Mayu ne ko kuma matsafa. Iya duk inda na je bani samun hutu gori da wulakanci sune ke bibiyata. Mutum biyu kenan ya mutu wanda jikina na bani duk ta sanadiyyata ne..."
Saurin rufe mata baki iya ta yi ta na girgiza kai.
"Kada zafin ƙaddara ya saka kiyi abin da Allah zai yi fushi da ke. In hankali ya bace hankali ake sakawa ya dawo da shi, Shuhuda sanin kanki ne Uwa da uba duk na rasa su . Mahaifinku shi ne gata na kuma Allah ya dauki abinshi, shin kin taba ganin nayi wani abu mai kama da tsafi ko kuma maita?"
Girgiza kai tayi.
"To kada ki sake fadar haka, komai ya yi tsanani ya na tare da sauki. Duhun dare ya fara ki tashi ki nufi gidan mijinki gobe sai ki dawo a yi jana'izar da ke"
"Iya kina ganin zasu bari mu zauna gidan kuwa? Ki ga da irin abin da ya faru yau"
Murmushin karfin hali iya tayi
"Ko da ba zasu bari ba Tala Yayarki ce Ubanku daya, ke dai ki zo kamar yadda na fada miki"
Har bakin kofa Iya ta rakata.
Tunda ta baro gidan gabanta ke tsananta faduwa. Ga garin ya yi duhu sosai domin gaf ake da yin sallar isha'i.
Kasancewar ana barin wutar Nepa ya saka wasu lungunan In na bi da haske, shi ya sa na ji hankalina ya ɗan kwanta.
Tun daga nesa da na hangota rike da hannun ƙaramin yaro na ji gabana ya yanke ya fadi. Har zan gifta ta na ji ta ce.
"Baiwar Allah sannu! Don Allah tambaya nake"
Jiki a sanyaye na juyo
"Mama! Dariya ta ke mani fa, ba ki gani ba? Don Allah ta bamu ita mu tafi gidanmu ina Sonta"
Jin abin da yaron ya fada ya na kallon cikinta ya saka gaban Shuhuda yanke ya fadi.
"Aa ɗan nan bakomai da aka gani bane ake faɗa. Kul! Na sake jin ka fadi haka, abin da ya ke a mallakinmu mene ne na nuna zalama? Yawwa baiwar Allah share batun yaro. Hayin Sammani za ki nunamin"
Hannu na kyarma ba tare da ta san maganar ta fito ba ta nuna mata can baya inda ta wuto.
"To baiwar Allah! Mun gode! Sai kuma kin haihu muna nan zuwa Barka"
Matar ta fada tare da kama hannun yaron da ke ta faman juyowa suka yi gaba.
Shuhuda kuwa tamkar an dasa ta kwakkwaran motsi ta kasa yi.
"Babu zalama a kan abin da ta ke mallakindu, in na haihu za su zo Barka? To ina ta Sanni me take nufi da kalamanta?"
Juyawar da zata yi nan hankalinta ya kara tashi domin kuwa babu matar bare ɗan ta.
"Ke kuwa ai tsayuwar da kika yi sun isa su shige kwanar"
Wata zuciyar ta yi saurin tunatar da ita.
Jiki a sanyaye ta karasa gida tare da jin kafarta na ɗan rikewa sakamakon tafiyar da ta sha.
Sa'arta ɗaya Inna da Murja duk suna ɗaki, da sauri ta yi alwallah ta shige dakinta.
Bayan tayi sallah wata irin yunwa ce ta taso mata. Dakin Inna ta nufa
Da sallamarta ta shiga dakin sai dai ko amsawa ba tayi ba ta hauta da sababin dadewar da ta yi.
"Allah ya huci zuciyarki! Rasuwa aka yi mana, Tala ce ta faɗa rijiya ta rasu"
Dafe kirji tayi ta zabura ta mike tsaye.
"Wace Talar? Ita yarinya ce da zata faɗa rijiya ta mutu? Kai aa za dai mu ji yadda a ka yi"
Hawayen da ke fuskarta ne suka gangaro domin ta sa ba shakka gobe sai Inna ta bi diddigin abin da ya faru.
"Ki tashi ki je dakinki, Allah ya ji ƙanta"
Karo na farko da na ji Inna ta yi min lafazi mai dadi tun bayan zuwana gidan.
Ɗakin Murja ta nufa domin amsar abincin darenta. Duk da ta ji sallamar amma sam bata amsa ba sai ma faman cin cingam da take.
"Anti Oyoyo! Ina tsarabata? Kin siyo mana ƙanwa. Anti Yaushe za ki siyomini ƙanwar?"
Hussaina ta ƙarasa maganar tare da rungume cikin Shuhuda.
"Kan uban chan!"
Murja ta kunduma ashar tare da fizgo Hussaina.
"Ke wace irin mayya ce, matar nan ƙanwar Uwarki ce ko ta ubanki. Ina rabaki da masifar da kike kokarin jefa kanki amma kina kara shige mata?"
Fashewa da kuka yarinyar tayi ta na kokarin komawa wurin Shuhud, amma rukon da Murja ta yi mata ya hana.
"Haba Murja! Ni ce annoba kuma yau? Murja zaman aure muke ba zaman gaba ba ita yarinya ce ki daina kyararta saboda ni. Ban shigo dakin ki don in bata miki ba shigowa nayi in karbi tuwon dare na"
Ya mutsa fuskar Murja ta yi tare da miko mata wani ɗan kwashin tuwo wanda ko Hussaina aka ba shi ba zai isheta ba.
Daki ta koma duk da ta san tuwon ba zai isheta ba hakan ta ci ta bi da ruwa.
Hankalina ne ya koma ga Iya
"Allah sarki ko ta samu abin da ta ci oho"
Rubabbiyar salularta da ta sha ɗauri da robali ta dauko. Karfe tara da rabi daidai.
Shigowar mai gidan ce ta sakata shan jinin jikinta.
"Iya ta ce Tala ta mutu?"
"Eh! Rijiya ta fada gobe za ai jana'izar ta"
"Rijiya kuma ita ko me ya kaita fadawa rijiya ita ba yarinya ba? Ko da ya ke ba ma wannan ba fito ki dumamamin tuwo bazan iya cinsa da sanyi ba"
Da mamaki ta ke kallonsa
"Ka manta Murja ce da aikai ba ni ba?"
"Ina sane ke nake so ki fito ki Dora in kuma ban isa bane ko kuma ba zaki yi fadamin ina saurarenki"
"Aa ban isa in ce ba ni yi ba, yanzu zan fito in dora in sha Allah"
Ficewa yayi daga dakin fuuu!
Yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ta yi tare da fita tsakar gidan.
Maimakon ta ji miyar da sanyi sai jinta tayi akwai gumi sosai ma.
Haka ta haɗa wuta ta dafa ta kai masa har daki.
Wani irin ciwon kafafu da mara ta ji lokaci daya ga bayanta da ke faman rikewa. Gadonta ta faɗa ta kwanta ba a dauki dogon lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.
Ƙarar wayarta ne ya tayar da ita, hannu ta saka cikin magagin bacci ta na lalubenta. Wata irin Number wadda bata taba ganin irinta ba, kara ta tayi a kunne sai dai bata gane wane irin yare ake mata ba. Katse kiran da ta ji ya yi daidai da katsawar cikinta. Zumbur! Ba shiri Ta mike zaune.
Baya, mara, azababben ciwo suka fara. Wani irin motsi cikinta ya fara tamkar kwarya haka ya dukule wuri ɗaya.
Dirowar da zata yi jini ne ya ɓalle, azabar da ta ke ji a jikinta tamkar ana zuba mata ruwan darma. Ihun da ta kwala shi ya saka duk wani mai rai da ke a gidan tashi a firgice...
Meenat A 'Yandoma
***