CHAPTER 12
by @nanameera08
***
HASKEN CIKIN DUHU
Chapter 12: “Not Meant for Me”
Nanameera, YOTA/023.
Tuntsirewa da dariya Ahmad ya yi yana kallonsa ya ce“To ka yi zamanka mana, Dole sai ka rakamu?” wani shegen kallo Zayyad ya watsa masa, Ya kalli Mami dake tsaye suna magana da Mommah ya ce “Mami let's go” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Alright” Ta kalli Mommah tana murmushi ta ce“Ki kula sosai Khadijah sai mun sake shigowa” Jinjina kai Mommah ta yi ta ce“Tom Mami, Idan kuma na riga ki zuwa shikenan” murmushi kawai Mami ta yi ta nufi in da Zayyad ya yi parking ride ɗinsa, Tana ƙoƙarin shiga motar General ya fito daga tasa motar. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta tana faɗin
“Barka da dawowa”
Babu yabo babu fallasa ya ce“Kuna lafiya?”
“Alhamdulilah”
Mami replied. Ta shige motar abin ta, Fatiha ce ta kalli Nayla dake riƙe da hannunta ta ce“Sake ni kar Yaya Zayyad ya tafi ya bar ni” langwaɓar da kai Nayla ta yi ta ce“Tom ku gaida gida, Dan Allah kar ki manta ki cewa Salma ina gaidata idan kun je Orange market” Harararta Fatiha ta yi ta ce“You Are mad” Daga haka ta nufi motar. Backseat ta shiga ta zauna kusa da Mami, Zayyad da Ahmad suka shiga front seat, Ya ja motar a nutse Momma da Nayla na daga musu hannu. Sun yi nisa sosai Mami ta kalli Zayyad ta ce“Kana tafiya a hankali mana” ɗan murmushi ya yi yana kallonta ta mirror ya ce“Mami ba fa zan yar dake ba, Ina sauri ne saboda ka da nayi dare” Harararsa ta yi ta ce“Da nufinka a daren nan za ka juyo Abuja?” Gyaɗa mata kai ya yi ta ce“To baka isa ba, Sai dai ka bari sai gobe. Idan kuma baka da wajen zama ne sai naji” numfasawa ya yi a sanyaye ya ce“Inason zan yi magana da Dad ne idan na dawo”
“Koma wace magana ce sai ka bari sai gobe Zayyad”
Mami ta faɗa tana danna wayarta, Shiru Zayyad ya yi amma tabbas ba zai iya kwana a Mararaba. Sai wajejen ƙarfe 8 na dare sannan suka isa gidan, Da idanu Mami ta kalleshi ganin bai fito daga motar ba.
“Sai da safe Mami”
Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi. Girgiza kai kawai ta yi ta ce“Allah ya tashe mu lafiya” Ta yi gaba abin ta dan tasan tun da ya yi haka ba zai taɓa kwanan ba. Kallonsa Ahmad ya yi ya ce“Banza kawai” Fuska a ɗaure Zayyad ya ce“Malam saukar min a mota” ƴar dariya Ahmad ya yi kafin ya ce“Daɗinta dai nima Allah ya hore min ina da mota, Da yau an gama tsinkani” Daga haka ya buɗe motar ya fita. Da harara Zayyad ya bisa sannan ya yi reverse ya bar ƙofar gidan. Har ya dauki hanyar komawa Abuja sai kuma wata zuciyar ta ce masa ya je ya ga Salma, Bai san me yasa ba haka kawai ya ji yana son sanin halin da yarinyar ke ciki. A ƙofar gidansu ya yi parking, Ya ɗauki a ƙalla 2mins kafin ya hango wani yaro yana tafe. Sai da ya bari ya ƙaraso sannan ya fito daga motar yana kallonsa ya ce
“Kira min Salma a gidan nan boy”
To kawai yaron ya ce sannan ya tura ƙofar gidan ya shiga. Babu wani haske a tsakar gidan dan babu wuta, Salma na zauna kan tabarma ta ɗora kanta a cinya yaron ya ce
“Wai ana sallama da Salma”
Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da idanunta wanda suka kumbura tsabar kuka, Murya bata fita ta ce“Ka je ka ce bata nan”
“Da bakya nan kina gidan Ubanki ne hala, Kai je ka ce gata nan zuwa”
Umma data fito daga banɗaki ta yi maganar hannunta riƙe da buta. Juyawa yaron ya yi fita, Ta ƙaraso wajen tana kallonta ta ce“Kin tashi kin fita a gidan nan ko sai ranki ya ɓaci shashasha wadda bata sanmu da arziki” Sake fashewa da kuka Salma ta yi ta tashi ta shige ɗakinta, Hijabi ta ɗauko ta fito ta yi hanyar waje tana tafe tana kuka.
Tsaye ta same shi jikin motarsa yana danna wayarsa a nutse, Tsayawa ta yi tana kallonsa, Cikin shassheƙar kuka ta ce“Gani” Sai a sannan Zayyad ya ɗago kansa ya kalleta. Maida wayar ya yi aljihu ya ƙaraso har gabanta har tana jin hucin numfashinsa, A nutse ya ce
“Meya faru?”
Banza ta yi masa ta ɗauke kanta, Ya sake tambayarta nan ma taki bashi amsa, A ɗan zafafe ya ce
“Keee! Ni nake miki magana ki na ji na? Who are you?” Ya ƙare maganar yana riƙe fuskarta, Fizge hannunsa ta yi daga fuskarta tana harararsa ta ce
“Ina ruwanka dani? Me ka zo yi gidanmu?”
Mamaki ta bashi ya ce“Oh tambayata ki ke me nazo yi gidanku? Ina gidan ya ke?” Salma goge hawayen fuskarta ta yi cike da tsiwa ta ce“Kai ka sani koma ka ganshi ko baka ganshi ba, Ina son na faɗa maka wata magana kar ka sake ƙoƙarin kai hannunka jikina dan ni ba yar iska ba ce, Sannan kar ka sake zuwa gidanmu ka ji na faɗa maka!”
Kasa magana Zayyad ya yi ya tsaya yana kallon ikon Allah, Tun da yake a rayuwarsa babu wata macen data taɓa tsayawa gabansa ta faɗa masa makamanciyar wannan maganar, Ko yar gidan wace ita, Sai ka shi yarinya yar ƙarama ta tsaya tana gasa masa magana. Jin ya yi shiru ya sa ta ɗan saci kallonsa ta ga still ita yake kallo, murguɗa baki ta yi sai kuma ta sake cewa
“Idan ka ji haushi kar ka sake zuwa in da nake, Ballantana ka bawa Ummana kuɗi, Babu ruwanka da rayuwarmu, Kana ji na?”
Tamkar tana magana da dutse haka Zayyad ya yi mata, Sai kawai ta fashe da kuka tana cewa “To ni banason kana zuwa gidanmu, Ummana ta ce sai ta kai ni wajen maza kuma saboda ka zo ne, Kar sake zuwa in da nake dan girman Allah” Taɓe bakinsa ya yi bai ce mata komai ba ya juya ya shige motarsa ya ja ya bar ƙofar gidan, Tamkar yana tafiya da rayuwarta haka Salma ta ji, ta tsurawa motarsa idanu har ta daina hangota. Zubewa ta yi ƙasa ta fashe da wani sabon kukan, Tabbas bata ji tana son daina ganinsa ba, Amma bata san ta bar gidansu a kai ta wani waje, Gara Ummarta ta ga babu wanda yake nemanta ko hakan zai saka ta rabu da ita. A sanyaye ta shigo gidan tana tafiya kamar wata mara gaskiya, Umma Rahmatu dake zaune kan tabarma har sannan ta kalleta ta ce“Zo ki bani abin da ya baki” Wasu sabbin hawaye ne suka fara zubowa kan fuskarta ta kalli Umma ta ce“Ni babu abin da ya bani wallahi” Tafe hannaye Umma ta shiga yi tana cewa“La'iha illalahu Muhammadu Rasulullahi Na shiga uku Ni Rahmahtu, Abin da Jin jin take faɗa min gashi ya fara zama gaskiya” Ta ƙare maganar tana yin kan Salma, Rufeta ta yi da duka tana cewa
“Zaki fito min da abin da aka baki ko kuma sai na kasheki a gidan nan”
Salma ko ban da kuka babu abin da take, ba dan zafin dukan ba, Sai dan zafin maganar da Ummar ke mata. Sai da gaji dan kanta sannan ta rabu da ita, Ta shige ɗaki tana banbamin masifa. Kwanciya Salma ta yi a tsakar gidan tana ci gaba da kukanta kamar ranta Zai fita.
Asokoro, Abuja.
A bakin entrance na gidan ya yi parking ya fito daga motar ya yi cikin gidan yana ɗan tafe a zafafe. Zaune ya samu Daddy a parlon yana karanta news, Ganin yana shirin wucewa ya sanya Daddy ya ce*Zayyad Zo nan” Bai ce komai ba ya dawo ya zauna kan kujera, Kallonsa Daddy ya yi ganin yanda jijiyoyin kansa suka tashi fuskarsa ta yi wani irin jaa, A matuƙar Dame ya ce
“Meya faru? Me aka yi maka?”
Sauke ajiyar zuciya kawai ya yi ba tare da ya bawa Daddy amsa ba, Daddyn ma bai sake tambayarsa ba dan yasan halinsa idan ya yi fushi ba ya magana. Sun ɗauki kusan 5mins a haka kafin Daddy ya ce
“Daman maganar yarinyar General Kabeer ce da ka je ka gani, Inason na sani idan ta yi maka” Tashi ya yi ya ce“Ta yi Daddy, Duk abin da ka yanke shikenan” Murmushi Daddy ya yi ya ce“To Alhamdulillah, Daman mun yi magana dashi, In sha Allah zuwa gobe sai a je a kai kuɗi da kayan saka da rana” Okay kawai Zayyad ya ce sannan ya nufi upstairs abin sa, Daddy ya bisa idanu sai kuma ya sauke ajiyar zuciya.
Yana shiga ɗaki ya zare agogon hannunsa ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi.
“Bana son ka sake zuwa ƙofar gidanmu, Ummata ta ce zata kai ni wajen maza kuma saboda ka zo ne, Dan girman Allah kar ke sake zuwa in da nake”
Ya runtse idanunsa tunawa da kalamanta, Haka kawai ya ji ya damu sosai, Tsaki ya yi ya kashe showern ya saka bathrobe ya fito. Pyjames ya ɗauka white colour ya sanya ya feshe jikinsa da turare ya kwanta.
Washegari
Maitama, Abuja.
Tun da ya fara magana take kallonsa ba tare da ta ce komai ba, Sai da ya kai ƙarshe sannan ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Go straight to the point Faruk ka daina min wannan kwana kwanan” ɗan murmushi ya yi sanin halinta ya ce“Nimrah kenan, yanzu duk wannan bayanin dana yi miki baki gane ba?” Nimra dake haɗa tea ta ce“Ni ban fahimci abin da ka ke nufi bane” Numfasawa ya yi ya ce“As i said before Mama ta saka aka nemi yarinyar, To kuma an riga da an samu matsaya, But yarinyar bata da matsala fa, In sha Allah za ku zauna lafiya” Nimra bata san sanda ta saki mug ɗin hannunta ba, Tea ɗin ciki ya zube a wajen. Tashi ta yi tana kallonsa ta ce“Kana nufin za ka aureta ne ka kawota nan gidan as ur wife?” A nutse ya ce“Eh mana in sha Allah” Girgiza kanta ta yi ba ta ce masa komai ba ta bar wajen, Ya bi ta da idanu yana mamakin shirun nata ya tabbata ba haka kawai ba.
Tana shiga ɗaki ta ɗauki wayarta, Dialing numbern Deeda ta yi, ringing ɗaya ta ɗauka, Nimra da numfashinta ke up and down ta ce
“Ki na ina Dee...?”
Deeda dake zaune parlon gidansu ta ce“Ina gida, Lafiya na ji muryaki haka?”
Nimrah ta ce
“Come to my house please”
“Alright I'm on my way” Nimra ta katse kiran, ta zaune gefen gado tana tunanin irin tashin hankali da za ta yi wa Faruk.
**** Nayla ce tsaye bakin ƙofar ɗakinsa, Ta tura baki ganin har sannan bai buɗe mata ba, Kamar zata yi kuka ta sake cewa
“Yaya Mommah ke kiranka fa”
Zayyad dake zaune kan sofa idanunsa a lumshe hannunsa riƙe da bottle ɗin Red snow wine ya kalli ƙofar, Tun da tafara bugun yake jin ta ya yi mata banza. Gajiya Nayla ta yi ganin tana shirin yin late a school ya sanya ta bar apartment ɗin nasa. A dining area ta samu duk yan gidan, Mommah na ganinta ta ce“Kin zauna magana ko?” kamar za ta yi kuka ta ce“Ko buɗe min ƙofa ma bai yi ba kuma nasan yana ji na wallahi” Daddy dake zaune ya ce“Ku rabu dashi naga kamar ransa a ɓace yake” Kallonsa Mommah ta yi ta ce“Me aka masa?”
“I don't know but tun jiya na fuskanci akwai abin da aka masa, nd kin san halinsa right”
Taɓe baki Momma ta yi ta ce“To Allah ya kyauta". Mommy ta ce“But at least ya kamata a yi magana dashi ko?” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“A'a idan ya gama fushin nasa a yi magana dashi” Murmushi Mommy ta yi ta ce“Allah ya shirya Zayyad” Mommah ta sauke nunfashi ta ce“Ameen ya rabbi”
****
Da idanu kawai Salma ke bin Ummar ganin yanda take ta fama haɗa kaya, Fitowa ta yi riƙe da bakko tana kallon Salman ta ce“Ki tashi ki ɗauko hijabinki zamu shige” a sanyaye ta ce“Umma ina zamu je?” Harararta ta yi ta ce“Sai dake zan yi” Tashi Salma ta yi ta shige ɗakinta. Jakar kayanta ta buɗe ta ɗauko hijabi, wani ɗan ƙaramin hoto ne ya fado daga jikin Hijabin, Ɗaukan hoton ta yi, a hankali ta shiga shafa hoton hawaye na zubowa kan idanunta. She wish Ammina na raye, tasan babu yanda za'a yi irin waɗannan abubuwan su dinga faruwa da ita, Sai dai babu yanda ta iya. Ɗaukan hoton ta yi ta riƙe a hannunta ta sanya hijabi sannan ta fito. Tsaye ta samu Umma, Ta kalleta ta ce“Shige mu je” Gaba Salma tayi Umma na bin ta a baya. Suna fitowa ta sanya kwaɗo ta rufe gidan sannan suka nufi hanyar fita daga Kabayin.
Abacha road, Mararaba.
Girgiza kai Mami ta yi tana kallon Ahmad ta ce“Yanzu shi General ɗin shi ne ya ce zai saka ya auri ƴar abokinsa?” Jinjina kai Ahmad ya yi kana ya ce“Ni Gara haka wallahi Mami, Saboda dama bana son sa da wannan yarinyar Aneeserh, gabaɗaya tarbiyyarta bata min ba” Shiru Mami ta yi sai kuma ta ce“Ikon Allah, a ina yarinyar take?” Gyara zama Ahmad ya yi ya ce“Yar wata minister ce, batada kunya wallahi, But wanda an ce sunan Marigayiya ne da ita Jiddah” Mami ta ce“Tom Allah yasa haka ne mafi Alkhairi, ya basu zaman lafiya” Ameen Ahmad ya ce sannan suka ci gaba da wata hirar.
Murmushi Hajiya Jinjin ta yi tana ci gaba da yankan salak ɗin gabanta ta ce“To shikenan sai kin dawo” Umma dake tsaye tana gyara mayafi ta kalleta ta ce“To Allah ya dawo dani lafiya” Ta kalli Salma dake zaune waje ɗaya gefen kujera ta ce“Ke kuma ki zauna lafiya sai Allah ya dawo dani” A sanyaye Salma ta ce“To Umma, Allah ya dawo dake lafiya” Ameen ta ce sannan ta fice daga ɗakin, Hajiya jinjin ta tashi ta bi bayanta. Da idanu Salma ta bi su sai kuma ta zuba tagumi tana tunane -tunane cikin ranta.
Asokoro, Abuja.
Yammaci ne lokacin, Around 5pm ya tura ƙofar garden ɗin, Zaune ya hangi Daddy kan kujera gabansa a cike da kayan marmari yana ci a hankali, Ƙarasowa Zayyad ya yi ya zauna kujerar dake facing tasa, Murmushi Daddy ya yi yana kallonsa ya ce“Ango” Ɗan murmushi Zayyad ya yi kafin ya ce“Dad!” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“An kai kayan auren sai fatan Allah ya kaimu da rai da lafiya” Ameen kawai Zayyad ya ce sai kuma ya yi shiru. Above 5mins babu wanda ya ce komai a cikinsu, Can Zayyad ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin
“Dad daman Inason zamu yi wata magana da kai”
Gyara zama Daddy ya yi yana kallonsa sosai ya ce“Ina jin ka”
Numfasawa Zayyad ya yi kafin ya ce
“Daman ina son takardun Companyn na Khal B. Idan babu damuwa” Shiru Daddy ya yi for some seconds sai kuma ya ce
“Did something happens?”
Girgiza kai Zayyad ya ce
“Not at all Dad, Kawai ina son amfani dasu ne”
Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Anyway, Zuwa gobe in sha Allah zan saka a kawo sai na miƙa maka”
Murmushi Zayyad ya yi ya ce“Thank U Daddy” Shima Murmushi ya mayar masa yana kai Apple bakinsa.
Miƙewa tsaye ta yi tana girgiza kanta daga ɗaya ɓangaren aka ce
“Yanzu mene abin yi?”
Numfasawa Mommah ta yi ta ce
“Dole a san abin yi, Ba zai taɓa yiwuwa ba! Ki cewa Malam ina nan zuwa in sha Allah”
Murmushi ɗaya matar ta yi ta ce“Daɗina dake kina yin abin da ya kamata, Shikenan sai kin zo”
Katse kiran Mommah ta yi, Ta buɗe press ta ɗauko mayafi ta ɗauki handbag ɗinta ta bar ɗakin dan ba ta ga ta zama ba, Dole ne ta je ta san abin yi.
# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera
***.