TAEESH

CHAPTER THIRTEEN

by @zinariya0102

____Tunda Jazuli ya tafi, sarkin farauta malam Ibrahim ya cika da mamakin abin da wannan saurayi zai yi da makahon Damo, matarsa da ke jin duk tattaunawar da suka yi da Jazuli, ta tare Malam Ibrahim ta ce" amma da jin buƙatar wannan yaro akwai wani babban al'amari da zai yi da wannan Damon" sarkin Farauta ya ce" tabbas ko shakka babu maganarki gaskiya ce, amma duk abin da zai yi da shi, ni tunda ya biya, zamu samo masa shi" ta ce" to Allah ya kyauta" ya ce" yanzu ni bari na shiga kasuwa na samo mana ɗan abin taɓawa" matar tasa mai suna Huwaila ta yi dariya tana faɗin " hahhh haka yake ai gara a shiga a samo mana mai ɗan maiƙo-maiƙo" ya na tafiya yana ta ƙara gwada kiran ɗansa Adamu, cikin sa'a kuwa ya same shi, cikin zumuɗi ya fara magana " alo-alo(hello-hello) Adamu kana ji na?" wayar aka amsa da "eh ina jinka Baba" sarkin farauta ya ce" ka nausa dawa ka farauto min makahon Damo, kana ji na ko" Adamu ya kuma amsawa " makaho kuma Baba, me za a yi da shi?" sarkin Farauta ya ce" duk yadda za a yi kar ka dawo sai da wannan Damon, Allah ya ba da sa'a" ya kashe wayarsa, tsaki ya ja, jin tana yi masa low battery, sai ya ba yar an sa masa caji, dake a cikin kasuwa kaɗai ake cajin waya, kaf garin babu wuta,fura da nono kindirmo mai kyau ƙwarya guda ya siyo, ya haɗo da naman ƴan shila, kasan cewar sa mafarauci ya saba da cin naman dabbobin dawa.

Har tsahon kwana biyu ana sauya girki a gidan malam Ibrahim, a rana ta uku kuwa ya yi ta kiran wayar Adamu amma a kashe tun safe yake sa ran dawowarsu daga farauta har yamma babu su babu alamar su, hakama yake ta zuba idon ganin Jazuli ya zo, amma shima shiru, don a ranar ne aka tashi da rashin lafiyar Ciroma Ubaid, sanin uwar ɗakin nasa ba a nutse take ba, yasa bai je ba.

GARIN DUMAMA

Ganin Kawunsu Baba Tanimu ne ya sa ta yi shiru, ta na kallonsa. "Ko za ki rama ne, na ce ko zaki rama ne, mara kunya fitsararriya ko shi uban naku Ahamadu bai isa ina ce ga yadda za a yi ya sauya min ko ya musa min ba, duk da shine gaba da ni" Sahura ta ce" Kawu wallahi ba za a siyar da gonar nan ba" ta juya a fusace ta fice daga gidan. "La'ila ma salli ila, kunga ƴa da rahin mutunci, kai Allah wadaran naka ya lalace" ce war Inna Uwa.

Kawu ya ce" barni da su, da ni suke zancen" ya shige ɗakinsa, sannan ya fito hannunsa ɗauke da buta, banɗaki ya shiga.

"Uhum ina ruwan kallo da gajiya, mu dai namu ido ne" matar Isma'il ce ta ce" wannan fa duk rahin (rashin) rabo ne, da ta kwantar da hankalinta da bata sha mari ba" "hmmm ta maru kuwa hahh hahh" ce war Abida suna kyakkyalewa da dariya.

Ko gani Yaya Sahura bata yi tsananin ɓacin rai, jefa ƙafa kawai take ta ko ina, ikon Allah ne kawai ya kaita gidanta.

gararam ta daki ƙyauren gidan, mijinta malam Kabiru ne ya ce" waye nan?" ganin Sahura ce a hauka ce, ya ajiye daron da ke hannunsa na awaki, " Sahura lafiya?" kuka ta fashe da shi, ta kwance zani, tasa gefensa ta share hawaye sannan ta nemi guri a ƙasa ta zauna, ta ci gaba da kuka, "wai mutuwa aka yi ko kuwa, ki yi magana mana Sahura" ce war Malam Kabiru.

"Dan an ga iyayenmu sun kwanta dama, shiyasa ake yi mana ɗiban albarka, wai ni Kawu ya mara, Kabiru kalli kunci na, a kan suna so su zalunci marayan Allah ya mare ni" Malam Kabiru ya ce" subhanallahi shi Kawun?" ta ce" shi dai, ina gonar Ali ta can kwari" ya ce" eh na ji dai" to ita Kawu yasa a kasuwa zai siyar" Malam Kabiru ya ce" zai siyar to shi Alin ne ya ce a siyar?" ta ce" ina fa, kawai son zuciya irin nasu ne, gobe in Allah ya kaimu sammako zan yi, in je in sanar da shi, idan ma zai buɗe baki ya yi magana ya yi, idan ba zai iya ba, ni kaɗai zan iya ƙwatar masa ƴancin sa alkur'an.

Ɗanta ne ya shigo, mai suna Mudan, hannunsa ɗauke da kayan gwan-gwan cike a buhu, ya yi fututu. Saurayi ne sosai don an kai kuɗin aurensa, ganin iyayen nasa cikin wani hali yasa ya dire kayan, ya ce" Iyarmu waye ya mutu?" Mahaifinsa Malam Kabiru ne ya ce" babu wanda ya mutu, kawai ƴar hatsaniya suka samu da can gidan nasu" Mudan ya ce" kutmar uba waye ya sa ka ta kuka?" ya faɗa cikin jin haushin abin da ke faruwa, labarin abin da ya faru ta ba shi, ya ce" abin da ba zai yuwu ba kenan, don an ga Baba Ali'n baya magana kuma ba shi ɗan da zai yi magana, to nima nan ɗansa ne kuma babu mahaluƙin da ya isa ya siyar masa da gona ba tare da amincewarsa ba" Yaya Sahura ta ce" Allah ya yi maka albarka, ai gobe zan je gidan nasa na sanar da shi duk abin da ke wakana anan" Mudan ya ce "hakan ya yi idan kinga da cutarwa kar ki bari a siyar masa da gonar nan, don nasan halin Baba Ali zai iya ce wa to a siyar, ko da a ransa baya so" Malam Kabiru ya ce" gaskiya ne wannan" da haka zuciyar Sahura ta ɗan yi sanyi.

A ranar dai yaya Sahura ba ta yi bacci ba, Allah- Allah take gari ya waye ta kama hanyar zuwa garin Ɗan Kada, duk da ƴaƴanta na ɗaki (waɗan da suka yi aure Rashida da Dije) yau za su zo su wuni don ba su samu daman haɗuwa a lokacin bikin sallah babba ba.

Asubar fari ta daka sammako zuwa tasha, sai dai kash! Motar da take son hawa har ta cika, waɗan da suka zo cin kasuwa dare ya yi musu a garin suka kwana, dole sai haƙura ta yi, ta zauna zaman jiran mota ta gaba ta cika, sai kusan goma na safe sannan motar ta cika, suka ɗauki hanya, tafiyar awa uku ke kai mutum garin Ɗan kada daga nan garin na Dumama........

Zinariya ce✍🏻