KULSOOM

TWENTY ONE

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P21

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

      Dan Allah ma su ganin ina musu ba dai-dai su yi haƙuri wallahi matuƙar matuƙar busy na ke a yanzu ko chart bana samun  damar yi, kuyi hak'uri, free book ne duk in da kike so kije ki nema Kulsum free ne, haka ma masu Comment ina gani kuma I really appreciate Allah ya bar tare

“Jodan ban san mi zan ce maka ba. abubuwan nan yadda ka tsince su daga sama dan Allah mu bar su a haka,but I'm Sorry. That's all what I can say now. Yanzu miye abinyi”

“Mu fara zuwa gidan iyayen yarinyar su ganka muyi musu godiya kamar yadda Hajiyarka ta ce. Sannan ka kama hanya ka tafi gidan ka wurin iyalinka kada ka shiga haƙƙinta...”

“Gaskiya banyi niyyar zuwa gidan su yanzu ba, da nufina sai nan irin kwana biyun nan, to amma tunda hajiya tayi umarni dole zan cika. Ka kira Sa'adu muji yana ina shi ne zai kai mu gidan”

Bayan sun dawo ma sun daɗe a mota a suna fira sannan Jodan ya ce.

“Mallam dan Allah ka saukar min a mota ka tafi gun iyalinka nima na je wurin iyalina wallahi ka san halin ta sarai yanzu zata ce ina can na tsaya fira da en mata. Ƙarfe goma fa ake magana..... ”

Hannu Khaldun ya ɗaga masa yace.

“mine ne abin tada jijiyoyin wuya a nan? Relax yanzu zan sauka....”

“Ka ɗauki ledojinka ka wuce please”

Ba musu ya sauka daga motar yana faɗin

“mu kwana lafiya”

Yana shiga ya nufi part ɗinsa direct ya buɗe. Turus yayi yana mai bin ko ina da kallo. Cikin ta kai ci ya ɗaga waya ya kira Sa'adu.

“Sa'ad why is my part empty no furnitures”

“Yayanmu ba ka yi min wannan zancen ba ai, beside ban san ya kake son wurin ya kasance ba tunda we have never talked about it before,only wancan side ɗin ne aka gyara and I'm sure you are going to like it because favorite color ɗin ka su Meerah suka zaɓa...”

Kitt! Ya tsinke wayar. Wata irin muguwar gajiya ya ke ji yau, jiya ya dawo daga tafiya tunda garin Allah ya waye kuma bai zauna ba, mutanen arziki iri-iri da abokan hulɗa dama waɗan da bana hulɗa ba sai zuwa suke da kuma kira a waya suna yi masa fatan alheri. Duk yadda ya tsammaci wannan auren ya kasance ya sha gaban tunanin sa.

Part ɗin ya dumfara tare da yin sallama ya shiga ciki. Sanyin Acn da ƙamshin da  parlourn ke yi suka taru suka bada ma'anar da har ta sanya shi lumshe idanuwa. Ya san duk wasu nau'uka na turaren ɗaki amma wannan ƙamshin kam na daban ne. (ni ko na ce turaren Sophie incense ya fara gigitasa).

Kwance ya hango ta akan cushion ta cure wuri ɗaya tana bacci tamkar wadda aka nannaɗe da igiya.

Matsawa yayi in da take kwancen yazo dab da ita yana ƙare mata kallo. Tun daga ƙafafunta ya fara waɗan da suke cikin takalmi domin babu abinda ta cire, sun sha lalle ja da baki, sai ya haɗe da gyaran da aka yi mata sai walwali yake gwanin sha'awa. Hannayenta ma haka sunsha lalle ga bangles nan da suka sha kuɗi sai ƙyalli su ke. Fuskar nan kuwa tayi suntum duk da tana bacci yana jin yanda take sauke ajiyar zuciya ma'ana tayi kuka har ta gaji.

Ya daɗe a haka yana kallon ta. bacci ta ke amma kai da gani kasan ba na daɗi ba ne sai dai ace don yana ɓarawo bata san lokacin da ya sace ta ba.

Tsintar kansa yayi da rashin jin haushinta kamar yadda ya ke ji a baya bai sani ba ko hakan baya rasa nasaba da faɗan da hajiyarsa tayi masa akan ta ɗazu. Ko bayan shi kuma yasan cewa yanzu tana da haƙƙi akansa bata da  kowa sai Allah sai shi. Saboda haka he will try all his possible best yaga cewa ya kiyaye matuƙar bata riƙa neman tunzira sa ba.

Ledar hannun sa ya ajiye mata nan a gaban ta sannan ya juya ya wuce wurin neman ɗakin da zai shiga kafin gobe.

Yana tsaye yana nazarin ƙofofin sai text ɗin Ayusha ya faɗo masa a rai.

“Yayanmu I have been calling you since but I couldn't reach you. Meerah ta zaɓa maka favorite color ɗinka, ɗakin yana can shi ne na ƙarshe ta can ciki”

Mamaki ne ya kama sa lallai waɗannan yaran sun ƙware a gulma. Yana shiga sai ya ji ƙamshin nan ɗin ya sha bamban da wancan na main parlour ɗin.

Kayan jikin sa ya rage tare da ajiye wayoyinsa ya shige toilet. Komai an gyara an jera kayan amfani kuma komai irin wanda yake amfani da shi ne wanda duk wannan yasan aikin su Ayusha ne.

Bai ƙara tsinkewa da mamaki ba sai da ya buɗe sip ɗin ɗakin yaga kaya, tun daga Kaftan har English wears  of his choice babu abinda babu na amfanin sa a ciki. an jera masa komai yadda ya kamata.

Kayan bacci ya ɗauko ya ajiye gefe ya zura jallabiya ya gabatar da shaf'i da wutri, ya daɗe yana addu'a daga ƙarshe ya kambala ya je ya kwanta bayan ya rage hasken ɗakin.

Ita kuma ba ita ta farka ba sai wuraren Ƙarfe biyu na dare, ko shi ji tayi wurin yayi mata ka ɗan duk ta kasa dogon motsi. Tana duba Agogon da ke manne a bangon ɗakin taga lokaci ya tafi haka bata san sadda wasu sabbin hawaye suka ziraro mata ba. Tana saukar da ƙafarta domin ta miƙe tsaye taji ta ɗora ƙafarta akan abu bata san lokacin da ta ƙwallara wani ihu ba saboda tsoro. Ba shiri ya miƙe bai ma san ya kawo wurin ba, domin ba ƙaramin firgi tasa tayi ba daman shima ba baccin ya ke ba.

Ganin ta a tsaye tana kuka ya kalle ta cike da jin haushi domin bai ga abin ihu a nan ba tunda ga haske yace.

“Ke! Miye haka? Kina hauka ne ba kiga dare yayi ba ne sosai?”

Ai bata ƙara tsoro ta ba sai da taji muryar sa a bayan ta, cikin ruɗewa ta waigo ta kalle sa domin ta bayan ta ya ke.

Ihu ta sake fasawa ta ruga da gudu ta shige ɗakinda aka saka ta lokacinda aka shigo da ita tamkar wadda tayi mugun gamo.

Kuka take tana girgiza kai kamar wata taɓaɓɓiya tana faɗin.

“A'a! Nooo! This is not happening,.... This is not happening Kulsum please wake up.. Tayaya Wai wannan mutumin zai zama mijina? Haba ƙaddara mi yasa zaki yi min haka? Mi yasaaaaa?” Wannan mutumin dai da ya gama ganina a 'ya mace bata hanyar halak ba, shi ne kuma yanzu za'a ce shi aka aura min? To ya kalle ni da wanne ido kenan?..... Wayyo Allah na!” Na shiga uku na... Wannan ita ake kira da mummunar ƙaddara... Ni Kulsum ina zan tsoma rai na in ji sanyi.... Maimu kin dai gama dani kawai kin cuce ni amma ki tsaya ki gani yadda taki ƙaddarar zata kasance...”

Kuka ta ke haiƙan tana sabbatu kamar wata sabuwar mahaukaciya.

Sam bacci ya ƙauracewa idanuwanta a wannan daren. Ƙarshe toilet ta shige tayo alwala ta zo tayi ta nafila tana kuka tana roƙon ubangiji gafara akan duk wasu laifuka nata da saɓawa iyayenta. Daga ƙarshe ta roƙi Allah akan ya bata zaman lafiya da mijinta matuƙar shi ne alkairi a rayuwarta. Bayan ta kambala iya abinda zata iya ta ɗauko ƙur'an ɗinda ta gani tare da hijab ta yi ta tilawa sai da taji an kusa tayar da sallahr asuba ta miƙe ta gabatar da Rak'atanul fajr sannan ta yi sallar asuba ko azkhr bata samu ƙara sawa bacci ya ɗauketa.

Shi kuma yana ganin ta shige ɗaki ya buga tsaki ya koma ya kwanta abinsa bai jima ba bacci ya ɗauke sa.

Ko da ta farka goma har da rabi na safe. Wanka tayo tare da yin alwala ta zo ta gabatar da sallar Duha. Sannan ta koma gefe ta sa ke dulmiyawa duniyar tunani. Shin wai da gaske ne abinda ya faru jiya ko kuma dai mafarki ta ke.

Jin yunwa ta dameta yasa ta miƙe tana mai kallon agogon ɗakin, Ƙarfe sha biyu saura. Zaro ido tayi tare da zura doguwar Abaya maroon colour da mayafinta ta fito. Ido huɗu suka yi da Meerah da wasu mata guda biyu waɗanda bata san ko suwa ba ne, Sai su Khadija suma suna wurin.

Mamaki ne gami da al'ajabi ya gama ka mata.

Rungume ta Meerah ta yi tana dariya tace.

“Gaskiya alamu sun nuna you are very very tired, tun 10 ni ke fa, Sai daga baya su sis khadee suka zo....”

Ɗage gira tayi tana dariya tace.

“Yayanmu is so selfish fa Anty Kulsum shi ne yace wai ba za'a tashe ki ba saboda you need rest. Gidan Yah Sa'adu da gudu yaje ya taso min Anty Ramlatu da naje gidan amma nan kuma naga yadda ake fifiko”

Bata san lokacin da ta fashe da dariya ba sannan tace.

“To we are Sorry....”

“No don't Sorry me anty Kulsum ba laifin ki ba ne ki barni da Yayanmu kawai”

Nan ma dariya suka yi sannan suka je suka zauna suka shiga gaishe da ita one by one. Bayan sun gama gaisa wa Meerah ta kawo mata breakfast ta sanya ta a gaba sai da taga taci sosai sannan ta barta wai ita a dole ta ɗaukar wa yayansu alƙawari zata kula da ita kafin ya dawo.

Bayan sun gama ta faɗa mata mai make up zata zo, masu decoration ma zasu zo za'a shirya wuri a harabar gidan domin za'a gabatar da ƙasaitacciyar walima.

Kafin Ƙarfe huɗu na yamma gidan ya cika cinjim da mutanen arziki.....

     

                OUM AMEER