KULSOOM

TWENTY TWO

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P22

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

     Walimar ta ƙayatar ainun, domin ko ni da bana jin abin a kaina ba ƙaramin burgeni yayi ba. Sai nan-nan  kowa ya ke dani tamkar wata zinariya. Yadda aka tsantsaramin kwalliya da kayan da ke jikina kawai ya isa ya tabbatar maka cewa bukin na musamman ne. Haka ni ke jin kai na a wata duniya ta daban.

An ci an sha komai ya tafi yadda aka tsara.

Kafin takwas na dare kowa ya kama gabansa ya rage daga su Khadija sai su Meerah.

Itama Ayusha tana gama sallar isha ta jani cikin bedroom ɗina tana murmushi ta ce.

“Yayanmu ya jima bai samu wadda yake so ba sai ke, to  ina roƙarki dan Allah ki zauna da shi lafiya, mutum ne marar hayaniya. Allah ya bada hak'uri ya bada zaman lafiya na tafi, Allah ya bamu alkairi”

“Na gode Anty Ayusha....”

“No! Please stop calling Aunty it's not even sound sweet. Please call me Ayusha...”

Nima girgiza kai na nayi nace.

“Gaskiya I can't, because kina da wata kima ce da daraja a idona wallahi ba zan iya kiranki ba”

Murmushi Ayusha tayi tana ƙara  jin ƙaunar ta a rai tace.

“Shi kenan, let's be calling each other's Aunty since haka kika zaɓa. Allah ya bamu alheri”

Kallon ta nike da ɗan cikin ta wanda ya fara showing kaɗan har ta fice daga ɗakin. Ban san yadda lokaci ɗaya naji ina ƙaunar ƙannen nasa ba, ko don sun nuna matuƙar kauna a gare ni ne ban sani ba. Musamman Meerah ta shiga raina daga jiya zuwa yau.....

“Anty Kulsum muma fa zamu tafi Yah Naziru sai kiran waya yake”

Ajiyar zuciya na sauke na ce.

“Haba Khadija ba zaku kwana ba ku bari sai gobe...”

“Cab! Kinga ma waɗan da  suka tsaidani can suna wurin santin kallon gidan da yanzu mun tafi, Sai da safe”

“Khadija nifa wallahi har yanzu a duhu ni ke, wai da gaske yayan su Meerah aka ɗaura min auren da shi ba Idirisa ba? Yah aka yi wannan abin ya kasance a haka? Dan Allah ki fitar da ni a duhu domin wannan abin akwai  rikitarwa ina ruwan biri da gada”

Dariya khadija ta dinga yi har sai da naji haushin ta sannan ta tsagaita tace.

“Anty ikon Allah ne kawai shi ne wanda yake yadda ya so. Ana cikin shirin yadda za'a gudanar da ɗaurin aure har Yah Naziru ya tafi kasuwa cefane kwatsam sai ga Hajiya Kulu kinsan ta ai? Ƙanwar Hajiyar Idirisa ce. To hau bakin ta sai abinda ta manta wai ɗan su ba zai auri mai kawon bariki ba waya mutu waya dawo, ke maganganu babu daɗi Mama tayi ta kuka tamkar zata haɗiye zuciya ta mutu akan baƙin ciki, Anty Kulsum wai kinga tijarar da matar nan tayi sai da ta gaji don kanta ta fita ta bar gidan. Innani ta fita itama wai taje sayen daudawa da girishin kayan da za ta haɗa miki ko da ta dawo ta iske Mama na ta darza kuka shine fa da taji ba'a si ta fita ta nemo almajirai ta sakani a gaba muka kwashi kaya muka je gidan itama tayi ta surfa musu ruwan bala'i tun daga uwarsa har ubansa babu wanda ta ragawa,sai da ta gaji dan kanta tayi shiru.....”

“To shi baban su fa mi ya ce?”

“Ya fita tare da Baba Ayuba Mama ta kira shi tana sanar mai halin da ake ciki, wallahi kasa dawo ma gidan yayi daga can ya ce wa Baba ayuba ya dawo shi ya wuce kasuwa. Shi ne fa Innani da sauran mutane suka taru aka yi ta bawa Mama baki sannan ta sassautawa kanta ta buɗe bakinta tayi addu'a mafi alkairi a cikin rayuwar ki damu baki ɗaya. Kawai na fita shago ina dawowa na iske mahaifiyar Su Meerah a ɗakin Mama....”

“Toh ya aka yi tasan cewa an fasa ɗaurin aurena?”

“Haba Anty Kulsum har tambaya ki ke bayan kin san akwai redio mai jini a gida, ai Mama na kaita ɗakin Innani su gaisa kawai ta hau zuba tamkar tsinkakkiyar jigida ta bata labarin komai. Shi kenan in gaya miki matar nan ta ce a bawa ɗanta auren ki...”

“Tare suka zo da shi?”

“A'a, ita kaɗai ta zo tace shi yayi tafiya ne da tare za su zo duba ki. Mama ƙin amincewa tayi fa. Wallahi sai da Innani tayi ta yi mata faɗa tana cewa ta kwantar da hankalinta, duk da cewa Baba ya san wannan ƙanen babansu ne ko Wan babansu ɗin nan hakan bai sa ta kwantar da hankalinta ba, musamman da taji ko ina ya ɗauka cewa don sun  ga kuɗi ne zasu bayar da ke....”

“Ita hajiyar Ruwan kuɗi tayiwa Innani ne?”

“Ko ɗaya fa. Wallahi babu ma wanda yasan ko su waye su domin ita kanta da zata zo gidan a napep ta zo, kuma har aka yi komai babu wanda yasan wai su masu kuɗi ne sai da sukaga an kawo kayan lefen nan, sannan wa sunsu har nan gidan suka zo saboda kawai su yi gulma, to shi ne fa ganin haka unguwa ta ɗauka wai kuɗi aka bi aka bayar da ke waye-waye. Ke ko yau ma maganar da nike miki har yanzu hankalin Mama ba'a kwance ya ke ba, don ko ɗazu na kirata ina gayamata yadda wurin nan ya ƙawatu ta ce ita hankalinta ba'a kwance ya ke ba domin wannan auren bai kwanta mata ba, Sai da nayita bata baki sannan”

Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama jin wannan kwamacalar nace.

“Ki ce mata na ce ta kwantar da hankalinta ina cikin ƙoshin lafiya kuma in sha Allah zan ci gaba da kasancewa lafiya babu abinda zai same ni, kawai abinda nike so daga gare su shine addu'a, suyi min addu'ar zaman lafiya kawai. Allah ya bamu alheri, wa zai kai ku gida?”

“Drivern su mana”

“To amma na ji Anty Ayusha tayi ta jiran sa tun ɗazu ance bai dawo ba yaje kai wasu baƙin”

“Eh... Am.. An ce ya dawo”

“Khadija gayamin gaskiya who will take you home?”

“To mijin ki ne, yana waje yana jiran mu”

Daga haka ta wuce ni ko na sake baki domin mamaki ma ya hanani magana.

Suna kan hanyar su zuwa gate ɗin, ma'arufa ta kalli khadija tace.

“Ke dai Khadija ki faɗa mata gaskiyar waye zai kai mu, ni fa kin san ina da tsoro bana son abin magana”

“Ni dai ki zo mu tafi idan kuma tsayawa zakiyi to, ke kika sani”

**************

Maimu

Tana kwance akan yaloluwar katifar ta tana chart kawai a Twitter taga Meerah ta wallafa hotunan Kulsum da Khaldun a shafinta tace.

“What ever has a beginning must surely have an end one day. Alhamdulillah! it's my happiest day ever, my Yayanmu ya zama angon anty Kulsum. I pray for many blessings and barakat to stay at your door always and for ever. Allah ya bada zaman lafiya. Please say a prayer to them”

Wata irin muguwar zabura ta yi kamar wadda aka tsikara tana ƙara ƙurawa wayar ido tamkar za su cire su faɗa kan wayar, sai ƙara zooming ta ke jikin ta ta ke ya ɗauki mazari kamar wadda akewa kiɗan gangi.

  Wani murmushi ta saki tare da yiwa kanta wawan mintsini domin taga idan ma bacci ta ke ta yi gaggawar farkawa amma still babu abinda ya canza.

Jiki na rawa ta janyo mayafinta ta saka ta fice sai gidan su Kulsum.

Gidan duk an fara watsewa, sauran mutanen da suka rage kuma har sun je sun kwanta, Mama na ɗakin ta tare da baƙi. Innani kuma na tsakar gida ita da Babanmu da Baba Shu'aibu suna magana.

Kwatsam ta faɗo tamkar wadda aka jeho ɗauke da sallama a bakinta.

Dukkan su babu wanda ya shaida ta sai Innani kaɗai ta watsa mata kallon tuhuma tana mamakin miye kawo ta cikin wannan tsohon daren. Sai wiƙi-wiƙi da ido take kamar wadda tayiwa sarki Ƙarya.

“Ke wai lafiya kika zo kika tsaya mana kina walima da ido kamar wadda bawan gidan su ya ɓata”

“Kulsum ni ke nema, tana ina?”

Wata taslima Innani ta buga kamar wadda aka cewa an saki Kulsum tace.

“Ni yau na shiga uku ban lalace ba! Tun lokacin da ake auren baki zo ba sai yanzu yarinya na gidan aurenta ki zo kina figar namanta don munafurci? Tukunna ma Uwar me kika nema ga Kursume ɗin da kika zo nemanta cikin talatainin daren nan? ”

Ji tayi tamkar Innani ta kwaɗa mata guduma a tsakar kai da ta ce wai Kulsum na gidan aurenta. Aure? Aure dai! To wai Kulsum ɗin ce ta yi aure kuma da Khaldun Zurmi ko kuma ta fara shaye shaye ne bata da masaniya?......

“Tambayarki na ke uwar me ki ke nema gareta?”

Murmushin da ya fi kuka ciwo ta ƙirƙiro ta ɗora akan fuskar ta tace.

“Ba fa komai Innani, kawai dai na zo yi mata Allah ya sanya alheri ne...”

“Da can ba ki zo ba sai yanzu?....”

“Mun ɗan samu saɓani ne sai yanzu na sauko shiyasa na zo....”

“To ai yanzu duk ta haƙuri kuma ta ƙare domin Allah ya sauƙaƙa mata ta ta rayuwar ta yi aurenta ta huta da gantaliliya ,Saura ke kuma, kema ina miki fatan Allah ya gwadawa iyayenki sun kai ki gidan mijin ki lafiya.....wuce mun gode”

Hanya Innani ta nuna mata akan ta fi ce. Ba musu ta juya ta fice zuciyar ta kamar zatayi bindiga ta mutu saboda takaici da baƙin ciki,ita tana can ta sakankance akan Kulsum na hannun bandits ashe tana can an ɗaura mata aure da Khaldun wannan wane irin mummunan mafarki ne?

Wayarta ta ciro ta shiga kiran ƙawayensu one by one tana bincikar su ko sun san Kulsum tayi aure, amma kuma abu zat mamaki kowa sai ce mata yake ba gaskiya ba ne. Marin ƙwarai ta shiga ɗirkawa kanta wai ta gani idan ma mafarki ta ke amma kuma babu abinda ya canza ita ce dai a kan hanya zata je gida bayan ta dawo daga gidan su Kulsum.

*********

Bayan kowa ya watse komawa nayi ɗakin da nasan mallaki na ne domin su Khadija sun jera min komai nawa a ɗakin tun daga kayan sawa har zuwa kayan shafe shafe. Sauran kaya kuma wai an kaiwa mai ɗinki.

Wanka nayo na zo nayi sallar isha na koma Kitchen na ɗebo abincin da Meerah ta ce an kawo mana yana Kitchen, Sai da na ɗebo wanda nasan zai ishe ni na ciko nama sannan na ɗauko wani lemu wanda ni kaina ban yada ganinai ba na zo na zauna.

Ina tsaka da cin abincin kawai na jiyo muryar an yo sallama, ina ɗagowa muka haɗa ido ban san lokacin da na watsar da pillet ɗin hannuna ba na zunduma na gudu na shige ɗaki jikina sai ƙyarma yake na rasa dalili. Wai mutumin nan tsoron sa na ke ko ya ya? Ko kuma dai tsananin kunyar sa ce nikeji take sa har ban iya tsayawa in da yake?”

Lock na je na sanyawa door ɗin na zo na kwanta kawai ko Shaf'i da wutri ban  samu damar yi ba sai da na farka kusan ƙarfe ɗaya na dare.

Shi kuwa Khaldun gaba ɗaya yinin ranar yana office, daman gashi kwana biyu baya nan ko da ya dawo kuma abubuwa sun tarar masa.

Ko yau a mugun gajiye ya dawo gidan. Yana shigowa ganin haukar da Kulsum ta buga mishi tasa shi sanƙamewa a in da ya ke tsaye,sai da ya kwashe kusan minti biyar a wurin nan sannan ya ja ƙwafafuwansa ya wuce zuwa ɗakinsa, jira yake daman a gama ya nutsu ya samu lokaci a siyo kaya a sanyawa part ɗinsa ya daina ganin wannan haukar.

*********

Maimu

Yanda taga rana haka taga dare, duk yadda bacci ya kai ga iya sata a wannan daren bai samu galaba a kanta ba. Kwana tayi tana ba idonta abinci domin hotunan Kulsum da Khaldun sun zame mata tamkar madubin dubawa.

Ƙarfe goma a ƙofar gidan su Walida  tayi mata, maƙotansu Khaldun. Sai da tayi kusan tsayin minti talatin sannan aka barta ta shiga gidan.

Ko a main farlour ta daɗe zaune sannan Walidar ta leƙo, cikin tsantsar mamaki tace.

“Maimuna! Hope all is well?”

Murmushi Maimu tayi tare ɗan muskutowa gaba daga kan kujera ta ce.

“Wallahi lafiya, kawai dai na zo ne in tambaye ki akan wani abu very important?”

“Owk! You can come in”

Ɗakinta ta koma suka shiga tare. Toilet ta wuce ta jima sannan ta fito, ta kira aka kawo musu Breakfast ta zauna karyawa tare da yiwa Maimu Bismillahi.

Ita kwata kwata ba wannan ne a gabanta ba yau, ta ƙagu taji gaskiyar magana ita kuma Walidar sai wulaƙanci ta ke tamkar ba jiranta take ba.

Sai da ta kambala sannan ta ce.

“Maimunice! What Is that very important da kike son tambayata?”

Ajiyar zuciya ta sauke with serious attention ta kalleta tace.

“Wai da gaske Khaldun Zurmi yayi aure? Da gaske wata Kulsum na nan ita ya aura?”

Dariya Walida tayi tace.

“Ke ko wai miye yake tsakanin ki da guy ɗin nan ne? Haka ma last time kika yi. Kuma shi ba gwanin 'yan mata ba ballantana in ce soyayya ku ke....”

“Dan Allah Walida just ke dai answer my question”

Kai tsaye walidar tace.

“He got married 5days ago. ya auri Ummul-Kulsum Salman aka ce sunanta...”

“Daga wace unguwa ta ke?”

“I don't know. Familyn ta ba sanannu ba ne gaskiya yadda aka ce, because nima banje ba su hajiyar mu ne suka je walima jiya. Amma dai gulma nata yawo cewa iyayenta kuɗi suka bi suka aura masa 'yar su. Su kuma nan cewa aka yi ƙungiyar asiri ya shiga wadda a sharaɗinta babu aure shi yasa duk yadda iyayen sa suka so yayi aure ke tun mahaifinsa na da rai  suka so yayi aure ya ƙi, mahaifiyar sa tayi faɗa tayi rarrashi amma duk a banza, to ana ta cewa ko aljana ce ta aure shi ta hana mishi aure sai kuma aka ce ƙungiyar asiri ya shiga. Sai gashi kwatsam da rana tsaka duniya sai ɗaurin auren sa taji, babu labarin neman auren babu ba lefe ba komai, komai sai daga baya aka yi. Kuma ita Hajiyar sa itace ta nemo masa ita tunda yaƙi ya nemo da kansa. Ba ki ganta ba 'yar yarinya da ita aka ce ni wallahi tayi matuƙar bani tausayi kuma iyayenta ba su kyauta ba, wurin son abin duniya sun ɗauki' yar su sun bawa tsoho......”

“Dan Allah ina ne gidan nata ita Amaryar?”

“Gaskiya ban sani ba, amma ance Gada biyu ne”

“Dan Allah ko zaki kwatanta min ne?”

“Bari in tambaya miki Ikhlas tare suka je jiya”

Wayarta ta ɗauka ta kira ƙanwarta Ikhlas ta tambayeta nan ta saka hands-free ta hau yi mata bayani tiryan-tiryan.

Tana gamawa ta ɗauki Jakarta tare da yi mata godiya ta wuce.

Tana fitowa ta samu napep ta shige. Suna tafiya bata ankara ba sai dai taji hawaye shar! Kamar an buɗe famfo, kafin ka ce mi! Kuka ta ke haiƙan wanda ta rasa dalilin yinsa har suka isa ƙofar gidan Kulsum ɗin wanda take tunanin shi ne........

               OUM AMEER