KULSOOM

TWENTY THREE

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P23

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

         Tana isa mai gadin gidan ya hana ta shiga yace sai ta faɗi matsayinta daga ina ta ke. Kallon shi tayi a sheƙe zuciyarta na yi mata uban tururi ta kalle shi tace.

“Idan ka shiga ka gaya mata cewa Maimu ce”

Ko da na fito yau ba motsin komai, yadda na zubar da abinci jiya haka na dawo na tarar da wurin ko cokali ba'a ɗauke ba.

Fillet ɗin na ɗauke tare da kwashe abincin da ya zube har ya fara bushewa na kai Kitchen . Ina shiga naga ba basket ɗin  jiya ba ne hakan ya tabbatar min da cewa wani sabon abincin ne na Breakfast.

Bayan na gama share wurin na goge na sanya turarukan ƙamshi na koma ɗakina na share na wanke toilet na fito na wuto Kitchen na bude foodflask ɗin. Soyayyen dankalin turawa na gani da ƙwa ga soyayyen nama daban sai ruwan Zafi sunsha kayan ƙamshi na haɗa Tea. Tuni naji ya wuna ya tsinke. Ba ɓata lokaci na  ɗauko Fillet na tuttula na zuba ruwan zafi a mug  na haɗa tea Mai kauri na dawo parlor na zauna Ina ci.

Ina cikin cin abincin hankalina kwance kawai naji ana knocking ɗin door, ba shiri na zabura na miƙe tsaye tare da zurawa ƙofar na mujiya ko ina na jiki sai rawa ya ke kamar wadda ta hango abin tsoro.

Tunda ni ke ban taɓa jin anyi knocking na sai yau. Ka yana na tarkata da nufin shigewa da ɗaki domin yau ba zan yarda in yi asara irin ta jiya ba.

Jin abin yayi yawa na ɗan dakata domin idan shi ne ba zai tsaya ba shigowa kawai zai yi.

Matsawa nayi jikin ƙofar murya can ƙasa nace.

“Wane ne a nan?”

Cikin ladabi yace.

“Ranki ya daɗe Mai gadi ne...”

Cikin tsantsar mamaki nace.

“Mai gadi! Mai gadi na ina bawan Allah?”

“Hajiya mai gadi ne, wai baƙuwa kikayi tace in faɗi miki sunan ta Maimu,kin san da ita  za'a Iya barin ta ta shigo?”

Tsayawa nayi ina tantance bayanansa, wato ni ce yau Kulsum ni ke da mai gadi sai ya tambayi izinina kafin ya bari a shigo.

Sunan Maimunar ma da ya kira sai na ji ya na neman ya ɓata min nishaɗin da ni ke ciki, ina tsaka da jindaɗi na tana neman ta ɓata min rai.

Bayan na gama 'yan nazare - nazare na kai tsaye na ce.

“A'a, ban san da zuwanta ba gaskiya kar ka barta ta shigo ni ban ma santa ba”

Daga haka na dawo na zauna na ci gaba da abinda ni ke.

Shi kuma yana buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin tana ƙoƙarin cusa kai.

“Tsaya ko ni baiwar Allah....”

“Dan Allah malam ka barni na wuce baka faɗa mata ba ne? ”

Ƙofar ya datse tare da yin bake-bake ya tare yace.

“Tace ita bata sanki ba, kada in barki ki shiga, saboda haka malama bi nan kawai...”

“Kai ban san renin hankali, ita Kulsum ɗin ce tace bata sanni ba? Ƙarya ka ke malam ka buɗe min na shiga na ce”

“Wallahi in kin fi Aula dubara ba zaki shiga gidan nan, tunda hajiya tace bata sanki ba kawai ki kama hanya don wallahi ba zaki shiga ba....”

“Kai matsiyacin banza rashin kunya ka ke so ka yi min ko ya ya? Kalle ni da kyau Nafi ƙarfin ka wallahi, idan har Kulsum ɗin ta fito ina tabbatar maka sai na saka an kore ka a aiki, banza shashasha....”

“Hajiya ina maganar fin ƙarfi a nan bayan wurin aiki na kika iske ni, kuma doka ni ke bi, wallahi na fiki rashin kunya don sai in tuɓe rigata mu daku billahillazi....”

Ganin da gaske ya ke ya fara cire riga Maimu ta tsorata ta fara ja baya tana dawo rarrashi don kawai ya barta ta shiga amma yaƙi.

Suna tsaye suna musayar yawu wata dalleliyar mota ta iso nan tayi parking. Da gudu ya je ya zuge gate ɗin yana ta famar ɗaga hannu duk da baya ganin kowa ta wajen domin duk tinted ce.

Tsaye tayi tare da saka ran yanzu za'a barta ta shiga ko wanene ya zo, amma wannan irin motar kam ko ba'a faɗa ba kasan cewa mai gidan ne domin motar ta amsa sunan ta.

Ganin mai gadin ya rufe gate akan fuskar ta ya koma ciki abinsa ya sake karye mata zuciya.

Wai da gaske Kulsum tana cikin gidan nan? To wai ko dai ba gidan ba  ne? Ta ya ma za ayi Kulsum tasan ita ce amma ta hana a barta ta shiga? Gaskiya sai dai idan tayi kuskuren gida...kai ba mamaki ma kuskure ta yi. Miƙewa tayi tashiga ƙwanƙwasa gidajen da ke Layin amma sai ce mata ake ba nan ba ne. Sai da ta gaji don kanta ta hau napep zuwa gida.

Tana shiga napep ɗin ta tarar da wasu suna fira suna duba waya,kunnuwanta ta baza domin taji mi suke fira a kai.

Ɗayar ta kusa da ita ta ce.

“Irin waɗannan mutanen fa ba su cika auren 'ya' yan talaka wa ba sai dai masu kuɗi irin su...”

Ɗayar ta cafke ta ce.

“Ni wallahi Guy ɗin nan na zata idan ya tashi aure zai samo wata shegiyar ce masu masifar kuɗi kuma wadda ta waye ta sha boka tayi degree har da digirgir, amma ya ƙare akan wannan. Ance secondary kawai tayi....”

“Ance fa Uwarsa ita ce ta nemo masa auren, amma kuma ai kada kiyi mamaki tunda ƙauyawa ne daga Zurmi fa suka dawo nan, to har yanzu akwai jinin ƙauyanci da yake yawo a jikin ta in ba shi ba ina Khaldun ina wannan Kulsum ɗin dan Allah. Amma shi ma fa ya jima bai yi aure ba, sannan ance ya cika muguwar aƙidar tsiya, kinga duk mahaukatan kuɗin nan nasa? Wallahi uwarsa kaɗai ta isa tayi yadda take so, ƙannensa baya basu kuɗi hatta wannan namijin, aiki ya ke masa duk wata yana biyan sa albashi kamar sauran ma'aikatansa, ƙannensa mata kuma ƙololuwar basu kuɗi dubu hamsin ga doka ta bala'i, kullum cikin zumbula zumbulan kaya kamar wasu matan malamai...”

“Ita ɗayar naji ance yanzu da tayi aure, ya bata takardun gidajen ta da shagunan hayar ta ya kuma saya mata danƙareriyar mota komai nata yanzu yana hannun ta. Kuma wallahi wani wurin ni banga laifin sa ba domin mu mata idan muka samu bamu iya ba....”

Hannun  Maimu na rawa ta warce wayar tana faɗin.

“Mu gansu dan Allah, su wane ne su?”

Baki buɗe mai wayar ta ce.

“Yanzu kina Gusau baki san Khaldun Zurmi ba? Cab! To an sha da ke ba ni wayata....”

Ɗayar ce ta fashe da dariya tace.

“Haba Kubra dan Allah. Ke sister, wani mashahurin, attajirin, ƙatoton ɗan kasuwa ne a nan garin, wanda yayi fice sosai, shi ne yayi aure kwanaki biyar da suka wuce, ya auri wannan, Ummu-Kulsum ɗin, shi ne ake ta martani a kai, kowa yana faɗin albarkacin bakin sa”

Yanzu kam ta gama yarda cewa Kulsum ce, kaiiii! Wannan mummunan al'amari dami yayi kama, wallahi tallahi ba zata saɓuba wai bindiga a ruwa. Ji tayi ma napep ɗin da mutanen cikinta na bata haushi haka dai ta tsayar da shi ta ba shi kuɗin sa ta samu wuri tayi zaman dirshan ta dinga kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu.

**********

Ina nan ina cin abincin  ina  kallo hankali na ya tafi sosai, ban san lokacin da ya shigo ba sai ganin mutum nayi a gabana.

Ban san lokacin da na zabura ba da nufin shafcewa, cikin hanzari ya damƙo tsintsiyar hannuna yace.

“Ke! Ni dodo da idan kika ganni ki dinga ihu kina gudu ko kuma cikin shika shikan iskancin naki ne ki ke nuna min...”

Jikina tuni ya ɗauki mazari, da sauri na girgiza kai na ba tare da na  kallesa ba nace.

“A'a”

Tsaki yaja sannan ya sakar min hannu ya ce.

“Ki shiga ki fito ina jiran ki kada ki ɓata min lokaci na”

Da sauri na shige ciki numfashi na kamar zai ɗauke saboda tsoro, da gudu na shige toilet na yo fitsarin wahala na fito.

Zaunawa nayi a kan  couch Ina nazari. To mi yake  nufi da in shiga in fito yana jirana? Ko me zai faɗamin oho!.

Sai da na ƙara shi zama na daga ƙarshe na miƙe yadda na ke na sake komawa parlourn na yi zamana kan kujera ina kallo. Ni yanzu bani da wata sauran damuwa Allah ya cika mini burina ya bani irin rayuwar da ni ke so, to mi zanyi in ba in yi ta ƙara gode masa. In yi ta ibada ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali idan naji yunwa in fito in ci abinci kuma in morewa idanu wana da kallo, a yanzu duk da cewa bani da waya babu inda hankali na ya ɗagu, Sai dai can ƙasan raina ina kewar 'yan uwana musamman Mama da Innani duk da cewa muna faɗa......

“Ke!”

Miƙewa nayi a tsaye ba shiri na kallesa na ce.

“Na' am”

“Saboda baki da sense a haka zaki fita? Ko kuma nan an faɗa miki wurin da zaki riƙa yin yadda kika ga dama ne?”

Ban san a ina na samo courage ɗin mayar masa da martani ba na zumɓuro baki nace.

“To ai dai duk in da ka ganni baka taɓa ganina ba mayafi ba...”

Ke muguwar tsawa ya dakamin da cewa.

“Ke! Ni sa'an wasan ki ne?”

Da gudu na shige ɗaki domin a yadda naga ya fusata zai iya dukana idan na tsaya.

Wardrobe na buɗe na gama kalle kallena a can na hango wata shadda ready made kawai na ɗauko na zuba tare da hijabi na yaɗi huɗu na fito.

Kallo na yayi sama da ƙasa ya ƙara tamke fuska tamkar soja a bakin daga yayi gaba na bi sa a baya,ko ba komai yaji daɗi a ransa yadda yaga ta suturta jikin ta.

Ni ko a raina na ce oho dai, wallahi ni da wannan gidan mutu kan raba takalmin kaza, ko fashewa zaka yi ka fashe ni ina ruwana da rayuwar ka.

Yadda ya je ya buɗe gaban motar ya zauna mazaunin driver haka nayi Nima na hakimce a gidan gaba ko ɗarɗar. Da alama wannan da ya gaisar da ni shi ne drivernsa don muna fitowa na ga ya hannun ta masa keys ɗin.

Bai ce min uffan ba, ni ma kuma bance masa ina muka nufa ba domin ni har yanzu kunyar sa nike matuƙar ji wallahi, har abada scene ɗin abinda ya faru a tsakanin mu in our first meeting ya kasa barin ƙwaƙwalwata, ko wannan kaɗai aka barni da shi ya ishe ni kunya, ga shi duk inda zamu haɗu haɗuwar ba mai kyau ba ce. Wai yanzu shine a matsayin mijin aure na. Ko me ya ke shiryawa game dani oho. Domin na san indai har da amincewar sa za'a ɗaura mana aure har abada sai dai kada in yi aure.

Ina ganin mun bi hanyar zuwa gidan mu naji wani irin sanyi ya ziyarci zuciya ta.

Muna zuwa na dire ban tsaya bin ta kansa ba na shige gida, ina ihun kiran Innani.

A bayi ta ke ta na wanka, kawai sai gata ta fito duk jikinta ko ina kumfa, tana buga salallami.

“Kursume lafiya dai? Ni yau na shiga Aljannah na maƙale!”

Dariya nayi na ce.

“Lafiya lau, tare muka taho da ni da mijina....”

Galala tayi tana kallona. Ni kuma bakin gaskiyata na faɗi haka domin ina jina a wata duniya ce a halin yanzu.

“OH! Auren kwana nawa dududu da zaki wani tsaya a gabana kina ce min wai ke da mijin ki ke uwar rashin kunya”

Ɗakin Mama na wuce ina faɗin.

“Ke kika sani. Wuce ki ƙara sa wankanki yafi miki, ina khadija..... Salamu alaykum. Mama ina wuni”

Kuɗi take kirgiwa tana ganin na shigo ta ajiye su a gefe ta kalleni tace

“Lafiya ƙalau Ummu-Kulsum da fatan kuna lafiya? Ya gida ya mijin ki?”

“Lafiya lau Mama, yana waje tare muka zo”

“To masha Allah, ki ce ya shigo mana. Khadija na aike ta kasuwa ta siyomin kaya duk sun ƙare kuma ban samu lokaci ba sai yau.”

Miƙewa nayi na nufi waje ina faɗin.

“To sai ko in tayaku ƙullawa tunda na zo”

Ina zuwa waje naga ba kowa na dawo abina.

Mun sha fira sosai da Da Su mama, yawanci duk firar Innani akan bikin ne da gidansu Idirisa. Bayan munyi ta jiran khadija bata dawo ba na tashi na ɗora mana girki muna cikin cin abinci ne Yah Naziru ya shigo, ni wallahi kwata kwata na manta da wani Yah Naziru a cikin rayuwa ta, ban sani ba ko don baƙin halin da ya ke nuna min oho.

Zuwa yayi ya zauna kusa dani yana murmushi ya ce.

“Sister ya gida? Da fatan kina lafiya?”

Ban san lokacin da hawaye suka zubo a kumatu na ba nace.

“But you didn't come? Saboda ka tsaneni ko....”

Hannuna ya riƙe yana girgiza kai yace.

“No! Ba ke na tsana ba Kulsum halayen da kika tsiro ne na tsana. Yanzu kuma ai mun shirya, karki damu in sha Allah zan zo”

“To Allah ya kawo ka”

“Amin. Mama ga mijinta yazo ku gaisa yana ɗakin Innani.”

“To ka ce ya shigo.”

A in da nike zaune ya zo ya zauna babu alamar ƙyama suka gaisa da Mama cikin mutunci sannan ya ce.

“To mu zamu tafi, zamu je can wurin Hajiya in sha Allah”

“To babu laifi, mun gode sosai, Allah ya baku haƙuri da zaman lafiya da fahimtar juna”

“Ameen Ameen”

Ina ganin ya fito, na tashi na wuce ɗakinmu, ka yana na duba na shafe shafe suna nan babu abinda aka taɓa da sauran duk litattafaina da abinda nike buƙata na ɗauko kaya guda na fito mukayi sallama da su.

Ina zuwa ƙofar gida na yi turus ikon Allah ya hanani magana. Khadija ce na gani tare da Maina suna magana. Kuma a yadda na gansu ba shi ne karo na farko ba.

A mamakance nace.

“Maina! Daman ka ne wanda Mama ta faɗa min yana neman khadija zai turo iyayen sa”

Dariya yayi yace.

“Ina wuni Anty Kulsum”

Shiru nayi kawai na wuce mota saboda na ma rasa ta cewa. Ko ya aka yi yasan khadija har ya fara nemanta?

Kallo na yayi sai kuma yace.

“Where are you taking those items?”

“Gida mana, kaya na ne duk ina son su.”

Gyaɗa kai kawai yayi ni kuma na buɗe gidan baya na sanya su.

**********

Ganin ƙofar gate ɗin da yayi parking yana horn yasa naji duk hankali na ya tashi. Ba zan taɓa manta wannan gidan ba, domin shi ne Maimu ta kawo ni ta so a ci zarafi na wanda duk ban gane komai ba sai yanzu, amma da ya ke shi Allah baya zalunci na barta da halinta.

Tun bai gama daidaita parking ba a harabar gidan Meerah ta fito ta dinga ihun murnar gani na.

Ina fitowa ta rungume ni tana faɗin.

“Oyoyo.. Welcome!”

“Thank you Meerah dear, how are you?”

“Fine and Alhamdulillah....Yayanmu ina wuni? Welcome”

“Thank you Meerah. Fatan kin wuni lafiya?”

Daga haka yayi gaba.

Kallona Meerah tayi tana yi min signal tana murmushi ta ce.

“Anty Kulsum yanayin fushi ba? Idan yayi fushi ko, kawai zakiga yana ta ɓata rai, idan kika ɓata masa rai highest ya ce miki. Ke! Ni abokin wasan ki ne...Yayanmu kenan, Ina  matuƙar matuƙar ƙaunarsa,mutum ne marar son hayaniya, amma kinga Yah Sa'adu... Hmmm!”

Dariya nayi nace.

“Meerah Yayanku kika ce baya son hayaniya?”

“Sosai Anty Kulsum,.. Muje ciki zan baki labarin sa. Kinga duk motoci sun cika gidan, yau muna da baƙi ne, Ayaa tayi ta jira Yayanmu ya kawo ki da wuri ku gaisa da mutane shiru sai cewa ya ke kuna hanya kamar waɗan da suka fito daga Abuja. Kin daɗe baki zo ba munsha aiki har mun gaji”......

“Baƙin me aka yi haka?”

“No ba su riga sun iso ba nan duk en uwa ne da abokanan arziki, Anty Ayusha ma tun ɗazu take ta jiran ki, Anty Ramlatu kuma sai gobe zata dawo daga tafiyar da tayi”

“Wacece Anty Ramlatu?”

“Matar Yah Sa'adu fa”

Ko da muka shiga kowa sai kallona ya ke Meerah na aikin ƙara gabatar da ni ga kowa ina gaishe su ɗaya bayan ɗaya.

Daga nan muka wuce sama, Sai kalle kalle na ke tamkar idanuna za su faɗo ƙasa.

             OUM AMEER