TWENTY FOUR
💝 KULSUM 💝
P24
FREE BOOK
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
BY
AMINA IBRAHIM
OUM AMEER
Marubuciyar:
ZAYTOONAH
ABARWA RAI
KIBIYAR SO
GUDUN WUCE SA'A
SABABI PAID
Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:
@Ummu-ameer
SOPHIE INCENSE
SOPHIE'S INCENSE
SOPHIE INCENSE
Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa
Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi
Muna da turaren wuta kamar haka
💞 Dorot
💞 kajiji
💞 Sandal banger
💞 Gab-gab
💞 Sandal flakes
Da dai sauran su..
Sai kuma Humrah munada:
💞 Sandal Humrah
💞 White Humrah
💞 Soul malting Humrah
💞 Oil Humrah Da dai sauransu
Akwai kuma
💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida
💞 Turaren mopping
💞 Air freshener
Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku
Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa
Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa
Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria
Delivery Nation Wide 🔮
Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye
Sai kunzo muna maraba da customers 💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕 muna matuƙar godiya
“Ummu-Kulsum, sannu da zuwa...”
Faɗuwa nayi gabanta tare da faɗin.
“Ayaa ina wuni”
Kamar yadda Meerah ta faɗamin in kira ta da sunan.
Murmushi tayi ta ce.
“Lafiya lau Ummu-Kulsum fatan kina lafiya? Ya gida? Fatan komai lafiya?”
Nima sai wani blushing ni ke zuciyata cike da farin ciki na ce.
“Lafiya lau Alhamdulillah...”
Ina juyawa muka haɗa ido sai wani harara ta yake ƙasa ƙasa wanda ni ban san dalili ba.
“Tun ɗazu ina ta saka ido ki zo da wuri ashe kin ce ya kai ki ki duba iyayen ki hakan ma yayi, Allah yayi albarka.”
Kallon shi na yi cike da mamaki mutumin da aka ce wai ba ya son hayaniya amma ya iya zura ƙarya har haka, ni inama na san in da za muje ba sai da naga mun kai gida ba......
“Kayan Lefen Meerah da na baiko duk za'a haɗa a kawo yau, ga shi har angama gama ayyuka bakya nan Ramlatu ma bata nan...”
Wayar ta da aka kira yasa ta yi shiru tare da yin picking ta fita waje.
“Ai akwai abinda naji Ayusha tace ba'a ƙarasa ba sai ta wuce ta ƙarasa”
Ayusha da fitowar ta daga toilet Kenan tace.
“Angama komai fa yayanmu, wanke wanke ne ya rage Su Maryama suna can suna yi.....”
“Wanke wanken shi ba aiki ba ne? Ko kuma su su Maryama ɗin ba mutane ba ne ba rayuwa ke gare su ba?”
Miƙewa nayi ko kaɗan banji wai raina ya ɓaci ba, ina murmushi na ce.
“Aunty Ayusha bari naje na yi ba komai, ai na saba babu aikin da bana iya yi....”
“Ke! Wacece Auntyn?”
Ido na zuba mishi kawai domin mutumin nan ya kai ɗan renin hankali, to ina ruwan sa da rayuwa ta ne wai...
Dariya Ayusha tayi tare da riƙe kunnuwa alamar ban haƙuri tace.
“Tuba na ke Yayanmu, wallahi na faɗa mata kada ta kira ni haka amma ta ƙi ji”
Pressing wayar sa ya shiga yi tamkar ba shi ne ya ƙalubalen ce mu ba.
Sa ke kallon ta nayi nace.
“Aunty Ayusha Mu tafi...”
Sake kallon na yayi cike da mamaki ya ce.
“Ke! Ni sa'an wasan ki ne ko....?”
Gaba nayi suka tsaya magana Ayusha sai daga baya ta fito tana dariya ta ce mini.
“Please tunda baya so dan Allah ki daina, ai girman ki ne, dole yaji haushi domin ni jaririya a hannun sa matar sa ta riƙa kirana da Aunty dole zai ji haushi....”
Murmushi nayi ina jin kalmar matarsa da ta kirani ta ƙara min ƙaton kai. Sai yanzu ma na fahimci abinda yake nufi, wato baya so ni matarsa ƙanwar sa tana kirana Aunty ya yarda ni matarsa ce kenan?.
Kitchen muka je duk yadda ta hanani sai da na zage muka yi wanke komai tare da masu aikin sannan muka kwashi komai muka kai muka ajiye inda ake buƙata.
*********
Tun da ta fita daga parlorn da aka kira ta sai yanzu ta dawo, yadda ta bar shi haka ta dawo ta same shi.
“Wai daman baka tafi ba? Ba wanda yace min kana nan”
“Eh hajiya daman jiranki na ke muyi magana”
Zaunawa tayi tana faɗin.
“To ai sai kayi magana, tun ɗazu ina wurin su Hajiya Rahinatou ban sani ba,ina jinka”
“Hajiya daman cewa nayi, ina so a saka furnitures a ɗayan part ɗin nawa, tunda ba'a samu damar sakawa ba....”
“A'a Khaldun, ai ni tun ranar ni na hana Sa'adu ya saka kaya a can. Daga kai sai matarka babu yara babu kowa amma kace duk girman wannan part ɗin ba zai ishe ku rayuwa ba ku biyu kaɗai. To gaskiya ban amince ba,ban hana in Allah ya nufe ka da ƙara wani auren ba wata rana amma dai yanzu ba zaka bar ƴar mutane ba ita kaɗai”
“To Hajiya ba matsala, Allah yasa hakan shi ne mafi alheri”
“Amin amin. Da wata maganar ne? Kuma Ina fata babu wata matsala daga yarinyar?”
“A'a Hajiya shi kenan in sha Allah, babu wata matsala ina godiya, Allah ya ƙara lafiya da tsawon rai mai albarka”
“Amin amin. To naji daɗin jin hakan, Allah ya ƙara baku zaman lafiya. Ayi ta haƙuri, yadda kayi haƙuri ka kula da ƙanwar wa su kaima haka za'a yi haƙuri da ƙannenka a kula maka da su. Yanzu matarka ka tuna ita ce rufin asirinka, idan ka kula da haƙƙoƙanta sai Allah ya ci gaba da dafa maka akan dukkan al'amuranka. Ni har ga Allah da niyya ta mai kyau na nemo maka wannan auren, domin mahaifiyar yarinyar ta bani tausayi matuƙa, akwai ciwo a sanya ranar ɗaura aure har an zo ranar kuma a ce an fasa, dole Uwa zata damu, ta sanya kanta a tunani. To gaskiya shi ne yasa na gamsu na amince musu da zuciya ɗaya. Allah yayi muku albarka, ya baku zuri'a ɗayyaba”
“Amin Hajiya, na gode na gode. Zan tafi sai idan anyi sallar Isha zan zo na ɗauketa”
“To babu laifi Allah ya nuna mana”
“Amin.”
Yana zuwa mota ya zauna yayi shiru, Sai yanzu ya ƙara samun relief tun da aka yi auren nan, shi ya kama kasa gane wani kalar tunani zai yi akan yarinyar nan, Hajiya ta sarƙafeshi ta ɗaureshi gam akan wannan auren. A duk lokacin da ya tuna yanayinda suka kasance shi da ita a ranar haɗuwar su ta farko sai yaji yana ƙara tsanar ta, da hajiya ta nemi izininsa kafin auren nan ko bindiga za'a ɗora masa a ƙoƙon kansa ba zai amince ba, saboda gwanda Karima sau dubu da wannan, duk abinda ya gujewa bai tsere masa ba sai da ya zo ya iske shi har gadon baccinsa. Wannan wace iriyar ƙaddara kenan?
Maganganun Hajiya ba ƙaramin tasiri suka yi a zuciyar sa ba, tunda har ya riga da ya aure ta dole yayi haƙuri. Ko ba komai shi ma yana da ƙanne mata guda biyu ba zai so abinda zai sanya su baƙin ciki da damuwa ba a gidan auren su.
Ganin wankin hula na neman ya kai sa dare yasa ya buga motar sa ya wuce.
**********
Muna nan aka kawo kaya abinda a kaya komai yayi masha Allah, ni kuma nace masu kuɗi sunji daɗin su komai baya musu wahala, wani ɓangaren na zuciyata na faɗamin amma kuma wani lokacin daga zuciya ne domin wani talaka har ma yafi wani mai kuɗin zuciyar yin abu, wasu ƙaton gidan ne kawai ba komai ciki sai ƙunci wani kuma a ƙaramin gida ya ke amma matarsa kullum a farin ciki ta ke.
Tunda muka shige ɗaki Meerah ta ke zuba min Fira wani abin Aunty Ayusha ta saka baki wani abin kuma ta share damu.
Bayan an watse muka ƙara kimtsa wuri, na je nayi Sallar Isha. Ina kan sallaya Sa'adu ya shigo.
Da gudu Meerah ta je ta rungume sa tana ihun murnar ganin sa. Ita dai haka rayuwarta ta ke so simple bata da wani damuwa, ko da yaushe ranta a sa ke.....
“Yah Sa'adu kayi kuɗi fa...”
“Ke Meerah bana son sharri”
“Wallahi ya Sa'adu kayi wahalar gani, tun safe da ka shigo baka sake shigowa ba, kuma gashi Aunty Ramla bata nan ballanta in ce ita ce ta ke ɓoyeka,....ni har fari ma naga ka ƙara I swear...”
Tsaki ya ja sannan ya ce
“To abun ya koma na cin zarafi kenan....”
Tahowa yayi har inda na ke yana murmushi ya ɗaga hannu alamar gaisuwa ya ce.
“Allah ya taimaki matar mai taimako, da girman kujerar ki, Aunty Kulsum Ina wuni”
Zaro ido nayi dukkan mu muka saka dariya na ce.
“Dan Allah Yah Sa'adu ka daina bana so, wane irin Aunty....”
“Ni kuma so ki ke ki katsemin hanyar abincina ko?”
“Saboda me?”
“Ah to, mai gida yaji kina cewa Yaron gidan sa Yayah ai hukuncin na kora ne”
Dariya muka sake fashewa da ita sannan Ayusha ta ce.
“kada ma ka Yarda da daɗin bakin ta Yah Sa'adu ɗazu da kirani da Aunty mijinta tamkar zai cinye ni ɗanye nama”
“To kinji ba? Dan Allah ki rufa min asiri ki kirani da Sa'adu na, haka suna na ya ke”
Gyaɗa kai nayi ina dariya na ce.
"To shike nan, zan yi tunanin sunan da zan sanya maka ni ko”
“Aunty ya gida, ya hak'uri? In sha Allah idan Madam ta dawo zamu zo, kin san Meerah ta fesa min cewa baki fara girki ba, ni kuma duk inda babu girki tsakani da Allah ba wurin zuwa na ha ne”
“Kai Yah Sa'adu...”
“Shin kin faɗa ko baki faɗa ba?”
“Eh na faɗa amma ai you are the one that ask me that”
Miƙewa yayi ya nufi hanyar fita kamar bai ji mi tace ba yana faɗin.
“Sadaƙallahul Azimm! Matar Yayanmu sai mun zo, Sai da safe kuma Allah ya bamu alheri”
Ayusha kallon meerah tayi wadda tayi kicin kicin da rai tana dariya ta ce.
“Kema dai kin san sarai Wane ne Yah Sa'adu zaki tsaya kina ɓata ranki a banza”
Janyota nayi kusa da ni nima ina dariya nace.
"Don't worry your self, nima na fahimta ai. Yaushe zaki zo?”
" In sha Allah cikin week ɗin nan da zamu shiga, amma sai zuwa friday ranar da ba Islamiyya”
"OK ba damuwa Allah ya kaimu”
Cikin raina kuma mamaki ni ke da ta ce wai idan ba islamiyya. Yanzu ita nan islamiyya ta ke zuwa? Lallai yau na tabbatar kuɗi kala kala ne,wa su ai ko malami aka kawo musu cikin gida ba su cika zuwa ba, ballantana su fita su gauraya da sauran mutane.
Ina tsaka da tunani Maryama ta leƙo ta ce.
"Aunty Yayanmu yace yana jira a waje”
Miƙewa nayi lokaci ɗaya naji kewar su ta cika zuciyata ji nake tamkar kar na tafi gida na bar su.
Sallama nayowa Ayaa na fito, ita ma Ayusha ta ce ya wuce da ita saboda barrister baya garin.
Muna shiga gida na buɗe baya ina wuwwugar idanu na marairaice murya nace.
“To ni ina kayana?”
Ƙala bai ce mini ba ya wuce ya barni nan.
Ganin ban gansu ba da gaske bani da kuma mai bani amsa yasa na bi bayan sa kawai.
Ina shiga har ya wuce ciki, kan cushion na tarar da kayan, yadda na ajiye su haka su ke babu abinda aka taɓa.
Na kwashe na shige ɗaki na.
**********
Tun daga ranar ban sa ke sanya shi a idona ba, ni kaɗai ce a gida sai idan Meerah ta zo ko khadija. Haka zan zage in yi gyaran gidan ko wace kusurwa in baza turarukan ƙamshin Sophie incense masu sanya nishaɗi da riƙe martabar gida. Lokacin da naga an daina ajiyemin abinci lokacin na ge na daina shan banza. Haka zan tsaya in tsara abincin da nike so in ci. Daga baya haka zan tsaya in buɗe network ɗin wayata in ɗauko kalolin girki in riƙa yi, idan taste ɗin ya min daɗi in ci idan kuma bai yi ma'ana ba in zuba shara, idan na ƙoshi inje in yi kallo domin ni dai kullum naga akwai nepa,ko ta ɗauka bai fin minti goma zan ga ta dawo, in kuma lokacin Sallah yayi in shige in yi sallah in sha bacci na.
Ga kayan gyaran jiki na waɗanda ni ke saya daga wurin Reedart Organic skin care da ke Mortgage Gusau.
Ko ni idan na kalli kaina ganin nike ina ƙara kyau har da fari, da kuma ƙiba hankali na kwance.
*********
Yau ma dai wani abu na ɗauko wanda ake yi da fulawa da ƙwai da su carrot da nama har ma da shinkafa fara, to nidai bani da farar shinkafa amma akwai ta buhu, saboda haka na bi duk yadda suka yi nima nayi, ƙarshe dai wasting ɗin energy na nayi da ingredient domin kwata kwata bai bayar da ma'ana ba. Haka na bar su a nan, na haɗa goldenmoon na sha na je na yi sallahr zuhr na hau baccin rana.
Shi kuma yana office zai shiga meeting ya tuna da file ɗin bayanan sa a gida dole ya dawo a gaggauce ya shiga ya ɗauko.
Kitchen yayiwa tsinke domin ya sha ruwa, kawai ya ga komai ga shi nan a barkace, ga ɓarnar da tayi nan ta bari a buɗe ga wani nan a fillet.
Tsaye yayi Mamaki ya hana shi motsi. Yanzu abinda kawai ta ke yi kenan, ranar ma yazo ya samu wani shirmen tayi ta zuba a shara gudan himili. Haka ta ke ɓanna mi shi kayan abinci wato. Ruwan ya ɗauka ya wuce abin shi.
Ni kuma sai yamma Lilis na taso na yi sallar La'asar na zauna na ci gaba da kallo saboda bana jin yunwa.
Sai gab magariba na ta shi na je na ɗora jallof ɗin suphagetti na shige wurin sallah.
Ana gama sallah ya yi shaf-shaf ya zo gidan, domin Jodan yace yau ko yana nan ko baya nan sai sun zo gidan. So baya so su zo su tarar da wata haukar shiyasa ya gaggauta ya zo da wuri.
Duk irin ƙamshin da ke tashi a parlorn bai hana mi shi jin ƙauri ba wanda ya gama gauraye ko ina na gidan.
Da sauri ya wuce Kitchen ya yi ƙoƙari ya kashe gas ɗin. Ransa ya kai ƙololuwa wurin ɓaci direct ya wuce ɗakina. Ina zaune ina azhkar ya shigo.
“Ke! Ke mahaukaciya ce ko? Kina so ki yi min gobara da gida saboda ba ke kika sha wahala kika nemo kuɗi kika gina ba ko? Idan kika ƙara bari abinci ya kama a gidan nan sai na saɓa miki”
Tsakani da Allah na tsorota da yadda ya shigo yana jidalin nan, ga shi ina ga nafi wata ban sanyashi a ido na ba. Ta ke naji wani sabon tsoron sa ya sake mamaye zuciya ta. Murya na rawa na ce.
“Kayi hakuri,in sha Allah ba zan sa ke ba”
“Ta shi kije ki tabbatar duk wannan ƙaurin nan ya bar cikin gidan nan, kuma ki shirya baƙi za su zo idan aka gama Isha”
"To..!”
Da sauri na wuce Kitchen nima ƙaurin duk ya dame ni ya kwashe abinci na kai can bayan gida, na dawo na tuttula air freshner, na kunna turarukan wuta na ƙara gudun ACn. Sallar Isha na gabatar sannan na je na shirya cikin doguwar Abaya da mayafinta na zo Farlour na zauna.
Banyi minti goma da zaunawa ba, ya shigo suma baƙin suna bayan sa.
Murmushi nayi na miƙe tsaye ina faɗin. Sannunku da zuwa.
Wuri na nuna wa matar na ce ga wuri ta zauna, ga yara waɗan da da alama yaran ta ne su uku.
“Sannu da zuwa Aunty”
“Yawwa Amaryar Zurmi, ga shi dai Allah ya nufa...”
Mijinta shima yana dariya ya ce.
“Ga ta nan fa Ummu-Kulsum 'yar Aljanna, ta rufawa abokina asiri...”
Yaran ne suka shiga gaishe ni, nima na amsa su cikin saka fuska, Sai dariya na ke bance komai ba su kaɗai suke firarsu.
Daga nan na wuce Kitchen na kawo musu lemu da ruwa.' ƴar ƙaramar cikin su na janyo wadda zatayi 6years ina mata magana tana bani amsa......
“I'm Aminu Ko kuma ki ce Jodan,... Wannan mata ta ce Saudah, waɗan nan yaran mu ne, Khadija, Ahmad, and Yusrah”
Murmushi na yi nace.
“Allah sarki. Na yi farin cikin haɗuwa da ku, Allah ya bamu haƙurin zama”
Kallo na Khaldun yayi sai kuma ya kawar da kai gefe yaci gaba da magana da Ahmad, yawancin firar duk Jodan da matarsa ne ni sai dai nayi murmushi.
“Kawai sai kikaji mutumin nan zai yi tafiya ko? To ya kika yi da ya tafi ya barki? Ni wallahi mamaki ne ya kama ni da Abbahn Ahmad ya ce wai Zurmi yayi tafiya kusan 3weeks”
Dariya nayi na ce.
“Haƙuri na yi ta yi Aunty har Allah ya da shi lafiya”
Mamakina ya ke yadda ni ke mayar da zance kamar gaske, ni kuma mamaki ni ke wai har yayi tafiya bani da labari muna gida ɗaya.
Sai da muka sha fira kusan ƙarfe goma sannan suka tafi.
A bakin kofa tace mini.
“Hajiya Kulsum yaushe zaki zo mana ziyara?”
Kallon shi nayi kamar mata da miji na gaske na ce.
“Ga shi nan tsaye a gaban ki, duk ranar da ya amince yace mu zo in sha Allah zan zo”
Kallon shi ta yi tace.
“To Zurmi ina zuba ido”
Murmushi yayi ya ce.
“Idan na samu time I promise zamu zo”
"To na gode”
Suna tafiya na shige ɗakina don ma kada in sa ke haɗuwa da shi na rufe na yi shaf'i da wutri na kwanta ko abinci ban ci ba.
OUM AMEER