KULSOOM

TWENTY FIVE

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P25

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

Da safe ƙarfe takwas na fito zuwa Kitchen domin na tashi da wata muguwar yunwa.

Nama na fara soyawa sannan na dafa indomie na saka ƙwai har guda uku saboda baƙin zari. Na kuma haɗa tea sannan na fito Farlour. Leda na gani kan Cushion na ɗauka na buɗe, Uniform na gani riga da wando da hijab na 4yrd, sai kwalin waya itama daban a Leda. Sai wata ƙatuwar School Bag daban. Jin tayi nauyi yasa na buɗe inga miye a ciki. Litattafan Islamiyya ne a ciki sababbi.

Jujjuya jakar na shiga yi ina mamaki, ita wannan jakar zuwa islamiyya ce sai kace wadda zata je University.

Kan wayar na koma na ciro ta a kwali, kallon ta kawai na ke ina jujjuyawa domin na rasa ta yadda zanyi in yi operating na ta. Ga simcard daban na MTN. Da naga ban iya ba na mayar a kwali na kai na ajiye tare da kayan,na zauna na cinye abincina sannan na fita naje nayi share share na da goge. Ɗakin da ke kallon nawa na ce bari na buɗe domin shi wancan na kusa ga nawa ya ke ciki to shi wannan miye a ciki? Ina murɗa handle ɗin kawai na ji ta buɗe. A hankali na sanya kaina ciki kamar wata ɓarauniya ina leƙe. Farlour na gani da kujeru komai na ɗakin Maroon and milk colour ne.

Cike da mamaki na shiga ciki ina ƙara buɗe idanuwa na da kyau, parlourn yayi matuƙar tafiya da imani na, wata ƙofar na hango kawai na bita ba tare da wani tunani ba,ashe bedroom ne da toilet shima kayan Gado Iri ɗaya sak da na parlourn, kan gadon na faɗa wanda ya sha ƙura sosai ina ta ƙyaƙyata dariya kamar wata mahaukaciya ina mamaki a raina ina faɗin to wai waɗan da suka kawo ni ne ke da laifi ko ni? Taya za'a yi ni da gidana ace ban san ina da waɗan nan ɗaku na ba, ga shi yana kallon ɗakin da na ke, ni wallahi na zata wani ɗaki ne kawai ko wani toilet ashe room and Farlour ne.

Bayan na gama tunane tunane na ta tashi na je na ɗauko tsintsiya da mopper na zo na zage na gyara komai fes ya dawo sai tashin ƙamshi ya ke sannan na fito.

Ɗakin da ya ke nayi ƙarere na buɗe. Komai iri ɗaya sak da wanda na gama gyarawa sai dai wannan kujerun Ash and black color ne komai na ɗakin.

Zaro ido nayi ganin yadda ya tara tarkace, ga datti duk ta ɓata ko ina, ga kofuna waɗan da yake amfani yana barin su nan. Ga kayan wanki nan an an wanke an goge amma ya bar su a parlourn. A raina nace su dai wasu mazan wallahi sun shiga uku, haka wannan ya ke shima kamar Yah Naziru, duk zai dawo sai ko ni ko khadija wata ta mishi shara amma da ya gama ya tafi kina shiga ɗakin zaki tarar tamkar anyi yaƙin badar a ciki. Haba! Ji wannan abin dan Allah, mtsww!

Bedroom ɗin na wuce shi ma dai same colour da Farlourn, ga kaya nan ko ina da takalmi babu tsari. Ina leƙa toilet shi kam tsaf. Nan na gane ƙeta ce kawai ya ke yiwa kansa tunda har yana iya kulawa da tsabtar toilet.

Shima dai tsayawa nayi na gyara masa komai na ɗauko kayan wankin na kai na jera masa, na fitar da Boxers da vest na wanke na kai baya na shanyo sannan na je na ɗauko bedsheet sabo na zo na canza masa na gyara na dawo parlour shima na gyara, na je na ɗauko turarukana na baza su a burner na feshe ko ina da Air fresherner na sophie incense. Lokaci ɗaya Ko ina na gidan ya game da ƙamshi mai sanya nishaɗi.

Ko da na duba biyu saura, wata irin muguwar gajiya na ji ta dirar min ga yunwa itama tace salamu alaykum.

Cornflakes na haɗa na sha na je nayi sallah ko wanka ban samu damar yi ba, bacci ɓarawo ya sace ni.

Ƙarfe biyu da mintuna goma ya shigo gidan, ɗakin da ya sanni a baya ya buɗe ya shiga, yaga bana nan ya je ƙofar toilet yayi knocking Nan ma ba amsa, Sai ya fito ya shiga kitchen mamaki ne ya kama sa, domin har bayan gida ya je bai ganni ba amma yaga kayansa a igiya. Shiru yayi ya tsaya yana nazari sai daga baya ya koma ciki ya buɗe ɓangaren sa, nan yaji wani masifaffen ƙamshi ya ziyarci ƙofofin hancin sa wanda ya sanya shi lumshe ido ba tare da ya shirya ba. Nan ma shiru yayi yana mai ƙarewa Farlourn kallo sannan ya wuce bedroom, shima komai an gyara, tsintar kansa yayi da jin ya gode mata a yau.

Ganin bata nan yasa shi fitowa da sauri ya tambayi mai gadi ko ta fita yace, ba wanda ya shigo ba wanda ya fita.

Komawa yayi ya buɗe dayan ɗakin mai single bedroom Kamar wancan bana nan daga nan ya buɗe ɗaya.

Kwance na ke akan 3seater ina ta shara bacci na hankali kwance ga cup and spoon a gabana.

Tsayawa yayi ya ƙare min kallo. 3quater ne a jikina black colour sai red vest Mai hannu ɗaya kai na lulluɓe da hula baƙa.

Instead of ya kirani da ke ɗin da ya saɓa bai yi haka ba, hannu yasa ya bubbuga gefen in da nayi resting kaina.

A hankali na buɗe idona, muna yin four eyes na miƙe ba shiri domin na tsorata wata ƙila zai tuhume ni akan miyasa na shigo nan ɗin shiyasa ya shigo.

Bai yi min wata magana ba kawai zuba min ido yayi yana kallo na, ni kuma duk na ruɗe ban san laifin da na masa ba kawai na zube ƙasa na ce.

“Sannu da zuwa Yayanmu....”

Yau dai yarinyar nan ta gama kashe sa. A ina kuma ta aro irin wannan ladabin yau? Kuma dai mai gadi yace ba wanda ya shigo ballantana ace faɗa aka mata.

Basarwa yayi ya ce.

“Are you not checking on time? Ba Ki ga na ajiye miki kaya ba? Oya go and change quickly lokaci ya tafi, you supposed to be there by 2:00,almost 3 know...”

Ya idar maganar yana duba agogon hannun sa.

Waje ya nufa yana faɗin.

“I'm waiting for you at the car, please hurry up”

Cike da mamakin sa na miƙe na koma wancan ɗakin na shiga toilet na yo alwala quickly tunda ya ce jirana yake, na zuba uniform ɗin na tsaya gaban mirror na ɗaura liƙab ɗin, Sai naga ya yi min wani mugun kyau. Ina murmushi na ɗauko jakar na fito.

Tun da na fito ya ke kallona ya kasa kauda idonsa a kaina har na iso na shiga muka fita.

Mun iso bakin makarantar zan sauka kenan naji muryarsa yana faɗin.

“at 4:00pm I will be back and take you home, take care”

Kai tsaye na ce.

“I will, thank you. Allah ya tsare ka”

“Ameen”

Daga haka na sauka na shiga gate ɗin makarantar, na san dai kalar uniform ɗin kuma na san makarantar a nan ta ke amma ban san sunan ta ba.

Wata nayiwa bayanin cewa ni new commer ce kuma ban san inda zanje ba.

Da wata malama ta haɗani muka aji daya ta ce in zauna kafin malam ya zo.

Ina nan sai ga shi ya shigo ya zauna yace in zo.

“Assalamu Alaikum Malam”

“Wa'alaikissalam, Hajiya barka da zuwa. Ina form ɗin da yace zaki dawo da shi?”

Shiru nayi domin ni bai bani wani form ba.....

“Ya ce zaki fara da nan ajin ne amma duk da haka zamu yi miki bincike in sha Allah, Sai muji wanne kalar salon karatu zamu bi da ke, saboda haka samu wuri ki zauna ki fiddo da Litattafan ki”

Zaunawa nayi na fiddo da littafan, dariya ta so ƙwace min domin in da ba dan liƙab ɗin nan ba da malamin ya fahimci haka. Ƙur'ani hizib biyu ne mai haruffa a ciki, sai su tajweedi, Sira ta ɗaya, arba'una hadith, Akhdari...

“Zaki iya karanta surarinda suke ciki?”

Gyaɗa kai na nayi nace.

“Malam na sauke Alƙur'ani in sha Allah...”

“Masha Allah. To litattafai fa?”

Suma haka na jejjero masa waɗan da na sauke da kuma waɗanda nike kai.

ƙarshe yasa aka kawo littafan waɗan da ni ke da su kuma na ɗauko aka bani Alƙur'ani 60hizib ya dinga buɗomin duk inda ransa ya ke so, ni kuma cikin nutsuwa nike rera masa tare da kiyaye ƙa'idoji. Bayan ya gama ta fannin Alƙur'ani ya ɗauko Sauran littafan yayi ta bincika ta. Daga ƙarshe muka dawo fannin alwala, sallah wanka. Ban san lokacin da idanuwana suka ciko da hawaye ba saboda takaici, wai shi mutumin ɗaukar jahila yake min ko ya ya? Ya ɗauko ko bihim ban sani ba kenan.....

“To hajiya bisa ga wannan binciken da muka gabatar in sha Allah zaki tafi aji biyar, Sai ki ɗora daga in suke, in da suka wuce ki kuma sai kiyi ƙoƙari ki samu cike gurbin. Sannan sai ki yi magana wa mai gidan domin a canja miki littafan da alkur'ani. Kina harda?”

“Eh,Inayi, nai kai hizib arba'in amma yanzu na san gaskiya akwai gyara domin na kwana biyu ban yi rihazal ba kuma na daina zuwa karɓa da bayarwa”

“To masha Allah. Ba bu damuwa malam zai bincike ki sai ku ɗora daga inda kika tsaya, Allah ya taimaka

“Amin. Na gode malam, Allah ya saka da alheri”

“Amin.......Malama sai ku tafi ki nuna mata ajin ta in sha Allah”

Ko da aka tashi na fito yana nan yana jirana, cikin mamaki na tambayi wata da muka fito tare na ce mata dan Allah karfe nawa ne yanzu, ta faɗamin huɗu da minti sha biyar.

Gyaɗa kai nayi tare da ce mata na gode.

Ina zuwa na buɗe na shiga muka tafi,bai ce min ba nima ban ce masa ba, kuma idan har gaskiya ake bi ni ce ya kamata na gaishe sa amma banyi ba.

Ina shiga gidan na wuce sabon ɗakina na kai jakar na zo na canza kaya na wuce na ɗora girkin Macaroni, Sai da na tsaya ta yi na sauke sannan na ɗauki lemun freshyo a fridge na shanye sannan naje na kwaso kayansa da na shanya a baya na kai masa ɗaki sannan na je nayi wanka. gaba ɗaya yinin yau banyi wanka ba duk aikin da na sha.

Bayan na gama har sallar Isha na je naci abinci, na zo na yita jido ka yana ina dawowa da su nan, bayan na gama na haɗa littafan islamiyya ta na zuba a jaka ta sannan nayi shaf'i da wutri na je na kwanta ko kallo ban tsaya yi ba saboda gajiyar da ke jikina.

Kusan sati biyu kenan muna haka. idan na wayi, gari zanyi aikace aikace na in ci abinci in yi wanka kafin biyu ta cika na gama komai yana, Sai a lokacin zan sanya shi a ido idan ya zo kaini daga ya dawo dani kuma shi kenan ni da sake ganin sa sai kuma gobe.

Wata ƙila ko zuwa kai ni ɗin da yake Hajiya Ayaa ta ce shi zai riƙa kaini da ɗauko ni, amma idan ba haka ba mi zai sa ya riƙa baro duk abinda ya ke yana zuwa don kawai kaini makaranta,bayan akwai drivers da yawa,sannan kuma akwai keke napep a gari.

Yau ma da wuri na shirya na zauna zaman jira, ina yi ina duba agogon parlourn har uku ma ta gota.

Ina ganin haka na tashi na shige parlour na na kunna kallo na kwanta akan kujera.

*********

Khaldun kuwa baƙi yayi tun safe yana tare da su a office. Duk yadda ya so ya samu time ya zille abin yaƙi yiyuwa. Ga shi baya son ko wane driver wai da sunan tuƙa matarsa a mota shi bai ga amfanin hakan ba. Ganin yau ba shi da wata mafita ya sa shi kamo Layin ta yayi dialing a mamakin sa sai ya jisa a rufe.

Meerah tayi complain akan layinta baya tafiya, Ayaa ma haka, to ya ɗauka network ne. Innani ma ta faɗa mishi har yau ba su samu kursume a waya ba ita ma bata neme su ba.

Ya yi ta kira har ya gaji amma amsa ɗaya ya ke samu cewa a kashe ta ke.

Sai karfe tara na dare ya samu ya iso gidan.

Parlournta ya same ta zaune tana kallon Arewa24.

Miƙewa na yi ina raba ido na ce.

“Sannu da zuwa Yayanmu”

“Ke! Ina wayar da na kawo miki?”

“Tana ɗaki, in ɗauko maka ne?”

Shi mamaki ma ya hana sa magana. Ganin bai ce komai ba yasa ta wuce ta ɗauko ledar wayar ta miƙa masa.

Yadda ya kawo mata ita haka ta ke. Kallon ta ya sake yi yace.

“Mine ne amfanin waya a cikin rayuwar ɗan Adam?”

“Ya kira kuma a kira sa....”

“Why did you keft it baki ɗauka kinyi amfani ba? Kinga hakan ya janyo yau kin rasa makarantar ki. So nayi in faɗa maki Ɗan jarida zai zo ya sauke ki saboda ayyuka sun yi min yawa a office..... ”

Zumɓuro baki nayi ina faɗin.

“To ai da ka sani kace yazo sai in fita muje, ko kuma ka bani kuɗin napep in riƙa tafiya kaima sai ka huta....”

“An gaya miki ni ɗan iska ne?”

“To mi kuma ya kawo wannan maganar?”

“Maganar da kika yi ita ta kawo wannan maganar. Kawai sai in aiko driver yazo ya ce ki fito ku tafi, ko kuma in baki kuɗi ki hau ƙarfe a waje....”

“To su waɗanda suke hawa fa....”

“Zan yi maganin wannan bakin mai rashin kunya. Waɗanda suke hawa iya ƙarfin da Allah yayi musu kenan ni kuma da ya bani irin wannan ba don na fisu ba, idan har na barki kika hau ƙarfe na kuɗi ban godewa Allah ba kenan. Miyasa baki kunna wayar ba?”

“Toh me I don't know how to operate it”

Karɓar wayar yayi ya buɗe ya saka simcard ɗin sannan ya kunna sai ga shi ya buɗe ta kamar littafi. Baki buɗe na bi wayar da kallo.

“Lalalahh! Wai daman wannan wayar ce? Wallahi sau ɗaya na taɓa ganin irin ta ko shi a film ne. Kai gaskiya Yayanmu na gode na gode sosai, Allah ya ƙara buɗi ya kare ka daga dukkan sharri”

Farin ciki na ya kasa ɓoyuwa, naji daɗin wannan wayar ba kaɗan ba, ni ko mi zanyi wa wannan mutumin domin na saka masa shima?

Ganin na kafe sa da ido sai kallon sa ni ke ina murmushi ji nake tamkar na je na rungume sa tsabar farin ciki.

Wucewa yayi ya barni nan, ina ganin ya fita na ɗauki wayar ina ƙara dubawa.

***********

Maimu.

Tunda ta gano cewa tabbas nayi aure kuma Khaldun na aura shi kenan ta ƙara haukace wa. Duk ta bi ta yamutse ta hana kanta sukuni ko baccin kirki bata samu. Tayi duk yadda zata yi ta samu zuwa gidana hakan ya faskara. Taje gidan mu Yah Naziru ya yi kashedi kada ta sake zuwa. Gidana Kuma tun ranar mai gadi ya hana mata shiga. Har gidan su walida ta koma akan su zo tare sai tayi rashin sa'a domin Walidar ma bata ƙasar. 

   Tayi tayi bata samu nasara ba dole ta haƙura. Yanzu kuma plan ɗinta ta je ta gayawa mahaifiyarsa wacece Kulsum, Sai daga baya tayi nazari cewa idan har tajewa Hajiya Ayaa da zancen ba zata saurare ta ba domin ta dalilinta Kulsum ke zaune a gidan. Sai dai ta je ta samu Khaldun ɗin ta fayyace masa komai, idan ma ya manta ta tuna masa Kulsum ce dai wadda ta shirya ba shi kanta ba ta halattaciyar hanya ba.

Wannan shawarar nayi Register a brain ɗinta ta shiga fafutukar yadda zata yi ta samu ganin Khaldun. Da ƙyar ta samu address ɗin office ɗin sa.

Kullum Sai ta je saboda ɗaukar wa rai wahala ba ta samun ganin sa tafi sati tana zarya sai yau wani daga cikin ma'aikatan yaji tausayinta sannan yayi wa sectary ɗin sa magana domin shi duk a zatonsa neman taimako ta zo.

Tun sha biyu take wurin bata samu shiga ba sai bayan ƙarfe huɗu da ya dawo daga ɗauko Kulsum.

Kallon ta yake har ta samu wuri ta zauna.

Kamar munafuka sai wani sissinne kai ta ke, murya na rawa ta ce.

“Ina wuni?”

“Ban san in da ya ke ba. Who are you?”

Daram taji ƙirjinta ya amsa tamkar wadda taji ƙarar harbin bindiga....

“I'm asking. Who are you?”

“I'm.... I'm... Ni ƙawar Kulsum ce, Aminiyarta ta ƙut da ƙut”

“So what are you here for?”

“Na zo in faɗa maka Wata magana ne..”

Gyaɗa kai yayi yace.

“OK! Your name”

“I'm Maimuna...”

Sa ke gyaɗa kansa yayi tare da ɗaukar waya yana dannawa.

Fita yayi tare da neman excuse kusan 30 minute tana zaune sai gashi ya shigo tare da police.

Wani ɗaki ya shiga sai gashi an tasa ƙeyarta zuwa can. Sai raba ido ta ke Hankalinta yayi mugun ta shi.

Kallon ta yayi ba hayaniya ya ce.

“Maimu ko? Ina iya rufe ki a nan babu wanda ya sani har numfashinki ya ɗauke in kuma ɗauke ki in yasar a bola. To ba zan yi hakan ba, yanzu ina so ki faɗamin wacece Ummu-Kulsum? Gaskiya ɗaya ni ke so daga gareki idan ba haka ba, zan saya a kulle ki babu wanda zai tuna da ke har abada”

Hawayen nadama ta fara zubarwa murya a raunane tace............

              OUM AMEER