KULSOOM

TWENTY SIX

by @oumameer2671

💝 KULSUM 💝

            P26

FREE BOOK

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

             BY

AMINA IBRAHIM

     OUM AMEER

Marubuciyar:

ZAYTOONAH

ABARWA RAI

KIBIYAR SO

GUDUN WUCE SA'A

SABABI PAID

Duk zaku same su a wattpad handle ɗina:

@Ummu-ameer

SOPHIE INCENSE

        SOPHIE'S INCENSE

                  SOPHIE INCENSE

Assalamu alaikum mutanen jahar zamfara da kewaye muna farin cikin sanar daku Sophie incense ta sake zo muku da kalolin turarukan wuta masu dadin ƙamshi masu daɗaɗa ran duk wanda ya shaƙa

Ina uwar gida da kuma Amarya? In dai neman ƙamshi kuke magana ta ƙare domin ga Sophie incense ƙarshen ƙamshi

  Muna da turaren wuta kamar haka

💞 Dorot

💞 kajiji

💞 Sandal banger

💞 Gab-gab

💞 Sandal flakes

     Da dai sauran su..

Sai kuma Humrah munada:

💞 Sandal Humrah

💞 White Humrah

💞 Soul malting Humrah

💞 Oil Humrah Da dai sauransu

Akwai kuma

💞 kwalaccar mu ta sirrin rikita mai gida

💞 Turaren mopping

💞  Air freshener

Sophie incense Ƙwararriya ce Kuma gwana wurin kayan ƙamshi. Ta shirya gyara muku gidan auren ku

Iyayen Amare muna yin saitin kayan ƙamshi na kaiwa Amarya gidan aurenta cikin farashi mai rahusa

Muna yin pieces domin rabawa a wurin taron bikin Aure ko kuma suna cikin sauƙi da rahusa

Sai an gwada akan san na ƙwarai ku hanzarta kar abaku labari mata sai da ƙamshi Oga na so ya dawo gida yaji ko ina na tashin Ƙamshi zaku iya samun mu akan number waya kamar haka(*** ko kuma ***). Sophie's incense tana nan a Gangaren Yarima, Titin Sambo Gusau, Zamfara State Nigeria

Delivery Nation Wide 🔮

    Muna aikawa ko ina a faɗin Nigeria da kewaye

Sai kunzo muna maraba da customers   💘💘💘😍😍😍😍😍💕💕💕💕💝💝💝❤️❤️💕💕   muna matuƙar godiya

“Kulsum ƙawata ce ita, duk wani wurin da za muje tare muke tafiya,komai tare muke yi.....”

“Officer, bata shirya bayani ba, inaga ko a nan zaku iya rufe ta ba damuwa idan ta shirya zata faɗa mana gaskiya”

Fitowa duk suka yi tare da making room ɗin being so dark without light yadda ko tafin hannun ta bata iya gani.

Hankalin Maimu yayi matuƙar matuƙar ɗagawa fiye da tunani, tayi kuka kamar ranta zai fita. A iya yadda tasan irin matsayin sa da karfin kuɗin sa tabbas zai iya ɓatar da ita a manta da labarin ta.

Ihu ta dinga yi tana kiran dan Allah a zo a taimaka mata wallahi zata faɗi gaskiyar abinda yake so ya ji.

Sai bayan kusan 30mnt suka shigo har da jodan ma. Kallon ta yayi yadda duk tayi jage jage da majina.

Kamar yadda ta ba wa Azima dalilin da yasa ta ƙulla alaƙa da Kulsum haka suma ta ba su da kuma iya tsawon lokacin da suka ɗauka suna ƙawance har abinda ya haɗa su dangane da saurayinta Sadeeq sai da ta faɗa musu da kuma zuwan su Zaria ba abinda ta rage, da irin yadda suke neman yaran masu kuɗi su yi soyayya da su.

With so much hatred ya kalleta yace.

“Kawai Soyayya da samari babu wata da alaƙa ta sirri....”

Da sauri ta girgiza kai ta hau rantsuwa.

“Wallahi tallahi ko hannunta babu wanda ya taɓa riƙewa da sunan iskanci ni dai a iya sani na da ita, wannan ɗin ma ƙaddara ce kawai......”

“Abu ɗaya na tambaye ki ya isa.....kinga waɗan nan police ɗin?”

Tana sharar hawayen da suka ƙi tsaya mata ta gyaɗa masa kai tace.

“Eh, na gansu”

“I called the presence of them only to be our witness. Za su yi rubutu mu saka hannu da ni da ke. Nazir has told me everything about you, duk abinda 'yar mutane ke yi ke ce sila saboda wani selfish interest na ki, ke kika nemi hanyar lalata musu yarinya. To ki ji da kyau daga yau na datse wannan alaƙar har abada. Babu ke babu matata, kin san ko a hanya? Ko a hanya kuka haɗu kika nuna kin santa i swear you will be jail for the rest of your life. Kada ki sa ke attempting taka mini ƙofar gidana ko gidan iyayen ta ko nawa, daga yau ki sanya a ranki cewa baki taɓa sanin wata Ummu-Kulsum ba a rayuwar ki”

Daga haka ya amshi consent form ɗin yayi signing itama ya bata hannu na rawa ta karɓa ta yi.

Tana gamawa ya sallami police ɗin daga nan ya ce ta tashi ta ɓace mishi da gani.

Tana fita suka koma resting room ɗin shi, ya ɗauko take away da yayi order ya buɗe ya fara cin abinci.

Tunda ya ɗauko abincin Jodan ke kallon sa, sai da ya fara ci sannan ya fara magana.

“Zurmi what's the meaning of this? Tunda kayi Auren nan ka ke cin abincin Eatry, mi ke faruwa?”

Share sa yayi kamar bai ji tambayar da ya ke masa ba sai ma ya ɗauko masa wani zancen da cewa.

“Jodan ya kamata mu sanya idanu akan su waye suke mu'amalantar yaran mu a matsayin abokanan su. Ka ji wannan yarinyar dan Allah! Da bakin ta take faɗin wannan saboda kawai saurayin ki ya guje ki ki nemi hanyar lalata rayuwar wata. Sannan kuma tayi aure ma bata barta ba tsabar mugunta. Ranar mu kayi wasu maganganu da yayanta akan ta saboda na kasa samun nutsuwar zuciya a kanta....”

Cikin mamaki Jodan ya ce.

“Miyasa to?”

“Jodan something I can't tell. Na barwa kaina sani da kuma ubangiji na shine zai yi mini magani, amma yau ta ƙara mini wani haske da ya tafi da wani sashe na damuwata”

Sanin halin sa yasa Jodan bai matsa da tambaya ba kawai ya ce.

“To Allah ya kyauta, ya kiyaye mu daga irin waɗan nan abokan”

“Amin.....is already magrib Sai mu tashi mu tafi sallah daga can zan wuce in yiwa Hajiya sai da safe, Sa'ad ma yana jira na, na aike shi ne nace idan ya dawo jirani a can”

“Ok”

*************

Ya daɗe da dawowa ya shige ɗakinsa yana aiki a system, sallar isha ta fito da shi.

A hanyar sa ta fita nan ya dinga jiyo sautin ta, tana karanto hadisi a cikin kitabu-tauhid tana fassara shi daki-daki. Bayan ta gama bitar in da akayi mata ɗazu ta ɗauko Alƙur'ani cikin nutsuwa shima ta karance shafi biyun ta na satin nan. Ya shagala sosai da sauraron ta har aka gama sallar a masallaci yana nan jikin ƙofar ɗakinta. Sai da yaji shiru sannan ya fita yaje ya yi tasa sallar ya dawo.

Ni kuma ina gamawa nayi sallah na zo na ci abincina sannan na ɗauko sabuwar wayata na zo ɗakinsa na yi knocking, ban jira ya min izini ba na tura ƙofar na shiga.

System ɗinsa ce akan center table ga Kofi a gefe, da alamu yanzu ya ɗaga domin laptop ɗin ma a kunne ya barta.

Zaunawa nayi ina kallon gaban screen ɗin. Heading ɗin na kalla 'Zurmi Store one....'

Ban ƙarasa karantawa ba naji ya ce.

“Ke! What are you doing here? Ni sa'an wasanki ne?”

Miƙewa nayi da sauri na kalle shi muka haɗa ido ganin yanda ya fito yasa ni saurin kauda kaina gefe tare da turo baki ina miƙa mishi wayar na ce.

“To ai ni ban gane kan wannan wayar ba shi yasa”

“And you can't exercise patient ki bari Sai na fito shi ne zaki wani shigo min babu neman izini?”

“To kayi haƙuri....”

“Ke! Wato ni ne To ma?”

Kamar zanyi kuka na sake cewa.

“Yayanmu kayi haƙuri. Kuma ko da na jira ka ba zan ganka ba. Ko da zaka zo ɗauka ta zuwa makaranta lokaci ya tafi ko kuma idan mundawo.....”

“If you dere allow that phone to fall Allah Sai kin biya ta. saboda baki san zafin yanda ake neman kuɗi ba shi ne kike banzarar da duk abinda yazo gabanki”

Ni dai shiru na nayi tare da ƙure ƙasan rough ɗin parlourn da Kallo, a raina kuma ina faɗin, ni dai ina ruwana indai na samu ka koyamin wayar kai ka sani.

Zaunawa yayi ya amshi wayar ya shiga nuna min yadda ake buɗeta ta koma kamar littafi da kuma yadda zan rufeta ta dawo kamar normal android, daga nan ya nuna min gidan kira da message da komai na ta.

Bayan ya gama na karɓa nace.

“Thank you. Allah ya saka da mafificin alkairi...”

Har na juya zan tafi yace.

“Ke!”

Juyowa nayi da sauri na ce.

“Na'am”

“Wacece Maimuna?”

Ban san lokacin da na haɗa ido da shi ba, domin tambayar ta zo min ne a mugun ba zata.

Tura baki nayi ina gunguni ƙasa ƙasa ƙirjina kamar zai faɗo saboda tsoro na ce.

“Ni ban sani ba...”

Juyawa nayi da sauri da nufin ficewa yayi saurin damƙo tsintsiyar hannu na ya ce.

"Ke! Ba da ke nake magana ba”

Ban san lokacin da na fashe masa da kuka ba ina faɗin.

“Ni wallahi ka sa ke min hannuna....”

“Till you tell me who's that bloody basterd in your life”

“To ai ƙawata ce.....”

Shi mutum ne wanda ya tsani kuka a rayuwar sa, ji yake tamkar Meerah ce ke wannan kukan,shiyasa bai san lokacin da ya janyo ta ba zuwa jikin shi. Shi bai ce tayi shiru ba kuma bai hana ta kukan ba.

Ita kuma ta dage bakin gaskiyarta tana ta darza kuka domin bata san irin hukuncin da zai yanke a tsakanin su ba idan yasan wacece Maimu a rayuwar ta. Ko a ina yasan Maimu? Allah masa ni.

Ƙamshinta ya ke shaƙa a hankali, musamman sumar kanta da basu daɗe da zuwa Meerah ta raka ta suka je saloon ba. Jin kukan nata na ƙara sosa masa zuciya yasa a hankali ya furta mata.

“Is ok, ni bana son kuka”

Muƙut! Na haɗiye kuka na jin yadda yayi ƙasa da murya kada in ci gaba har in kai ga fusata sa. Haƙiƙa yau na tsinewa Maimu babu adadi, da ace ban san ta ba, da duk wannan tozarcin ba zai faru da ni ba a yau.....

“Gobe ki shirya da wuri zuwa 10am. I will take you home.....”

Zaro ido nayi tare da juyowa da sauri na cumuimuyesa ina masa magiya da.

“Dan Allah kayi haƙuri, wallahi ni yanzu babu abinda ke tsakanin mu da ita, idan ka kaini gida saboda Maimu Baba da Yah Naziru wallahi kashe ni kawai za su yi, wallahi ni yanzu daman na daɗe da yankewa da ita, ko lokacinda ta zo gidan nan cewa mai gadi nayi ban san taba kada ya barta ta shigo. Duk abinda ya faru ma a baya ƙaddara ce wallahi shine karo na farko kuma na ƙarshe........”

“Malama can you give me an listening ear?”

Shiru nayi tamkar ruwa ya ci ni tare da tattara duk wata nutsuwta na zuba masa idanuwana da suka jiƙe da ruwan hawaye ina kallon sa.

“Za'a kawo kuɗin gaisuwar Khadija gobe idan Allah ya kai muna rai, ki shirya da wuri kada ki ɓata min lokaci. Wanda duk yayi na gari don kansa akwai ƙabari yana nan yana da konsa sai dai idan bai mutu ba, kuma dole sai ya mutu wata rana don ba shi ya halicci kansa ba”

Wata irin kunya ce ta kamani, ban san lokacinda na rufe fuska ta ba a ƙirjinsa, tamkar ya buɗe na shige ciki haka ni ke ji, saboda bana son haɗa ido da shi.

Da alamu shima yanayin ya amshe sa domin bai yi yunƙurin hanani ba.

Mun shafe mintuna a haka sai daga ƙarshe kawai naji muryarsa yana faɗin.

“Malama sai ki ta shi min a jiki ko?”

Miƙewa nayi sum-sum na wuce da sauri kamar wata munafuka.

Shi kuma ƙara gyara zaman sa yayi yaci gaba da abinda yake a laptop.

**********

Maimu ta yi kuka marar iyaka. Duk yadda ta so burinta ya kasa cika akan Kulsum, tabi duk hanyar da tasan zata bi amma abin ya ci tura, ƙarshe ma akan ta abin ya ƙare. Amma ko yanzu ba saduda tayi ba, ta riga ta ɗaukarwa ranta sai tayi duk yadda zatayi ta raba Kulsum da wannan gidan.

Ita daman burinta a aurawa Kulsum Idirisa ita kuma ta auri Sadeeq, shi kenan ita tasan cewa da hakan ta kasance shi kenan ta hau saman Kulsum har abada. To amma yanzu duk da cewa su ma gidansu Sadeeq suna da kuɗi ko kaɗan ba su kamo ƙafar Khaldun ba,domin shi Khaldun kuɗin sa ne gumin sa ne shi ya tara da kansa shi kuwa Sadeeq komai na babansa ne, ya faɗa mata albashin sa iyakar sa dubu saba'in a wata,kenan duk irin ƙarya da fafar da zatayi ba zata taɓa kaiwa ga Kulsum ba.

Kullum kwanan duniya ta tuna cewa Kulsum na can cikin ɗaula ita Kuma tana nan cikin sauro da zahi sai ta fashe da matsanancin kukan baƙin. Saboda haka, she promise her self cewa duk yadda zatayi sai tayi taga Kulsum ta dawo gidan ubanta. Shawarar da ta yanke shi ne kawai ta shiga ta nemo asirinda zata raba su, idan har ba za su rabu ba ai akwai asiri kuma asiri gaskiya ne, saboda haka su tsumayeta.

Gefen soyayyar ta da Sadeeq kuma sai abinda ya ci gaba domin har ya aiko da kayan gaisuwa ya kuma turo iyayen sa kamar yadda yayi mata alƙawari. Yanzu shi ka ɗai ta ke tunawa sai taji Hankalin ta ya kwanta. Shi kuma sai damunta ya ke kullum cewa ina ƙawarta Kulsum tun bata damuwa har ta fahimci yawan tambaya daga ƙarshe tace ai sun rabu da ita shikenan tun daga ranar ya daina tambaya . Bata san cewa har gidan su yaje neman ta ba aka faɗamai tayi aure.

Wata shaiɗaniya ta samu irin ta, bayan ta gama kora mata bayani ita kuma ta bata assurance cewa in dai akwai kuɗi to ba daɗewa buƙatar ta zata biya.

Cike da farin ciki ta je ta kwashe duk kuɗinta na account da ta ke tarawa domin siyayyar aurenta, ta sayar da babbar wayar ta ta siyo ƙarama second hand ta 40k. Ta kawo mata, Sai suka ajiye ranar da za su tafi.

Yau kuma tana cikin baccinta na safe, ƙawarta Rufaida ta yi ta kiranta a waya bata ɗaga ba, tun tana kan mashin ta ke kiranta har ta iso gidan nasu bata ma sani ba.

Wani mugun duka ta ɗana mata a cinya tana faɗin.

“Banza shashasha ta shi ki ga abinda yake faruwa a gari na turo miki a what'sapp baki duba ba”

Firgigit ta miƙe tana tambayar ta mi ya faru. Wayar ta miƙa mata tana faɗin.

“Duba ki gani”

Sai da ta gama ƙwanƙwance abinda ake nuna mata tas! Sannan ta zunduma wani irin ihu tare da faɗuwa ƙasa somammiya.

Hotunan pre-wedding ta gani Na Sadeeq da shi da wata.

Suman da tayi ya kai uku, kuka kamar wadda uwarta ta mutu, kafin kace mi wani mugun zazzaɓi ya kanainaye ta.

Rufaida kuwa sai aikin lallashin ta take, tana tsinewa Sadeeq. Daga ƙarshe ta ce.

“Maimu duk wannan kukan ba shi da wani amfani, ɗaukar waya zakiyi ki Kira Ɗan iskan kiji uwarsa zai faɗa miki ko ubansa....”

Cikin sheshsheka ta ce.

“Kiran me zan yi masa Rufaida? Bayan ya riga da ya gama da rayuwata. Wallahi ji ni ke kamar in tashi in je in kashe kaina na huta....”

“Kai..! Uh uhm Maimu, duk wanda ya kashe kansa fa indai Musulmi ne shi to ya tabbata ɗan wuta. Ke dai ki Kira sa kiji. Ni wannan yarinyar a yadda naji ance 'yar uwarsa ce. Da uwar yarinyar da ubansa uwa ɗaya uba ɗaya suke. Kuma ance sun daɗe tare tun tana ƙasar waje karatu aka yi musu engagement. Sai kwanan nan ta dawo shine za'a yi bikin”

Murya cike da damuwa ta ce.

“Rufaida ke duk a ina kika ji wannan?”

“Wallahi daga majiya mai ƙarfi, duk abinda kika ji na faɗa miki to gaskiya ne...... Kinga Maimu, ni bari in tashi in tafi, na wuni gidan nan tsakani da Allah nasan gida yanzu za'a nemeni yamma tayi. Allah ya sawaƙa”

Rufaida na wucewa ta janyo wayar ta ta kira Sadeeq ɗin, Sai gashi ya yanke kiran ya kira ta back.

“Baby ya ake ciki...”

“Wane baby? Azzalumi, macuci, mayaudari. Wallahi sai Allah ya sakamin ba zan yafe maka ba, na yarda da kai na sakar maka jikina, kayi yadda kaso shine da abinda zaka sakamin kenan kaje kayi pre-wedding zaka yi aure, to ka sani Allah baya bacci....”

“Maimuna wai zaki saurareni ne ko yaya? Ki saurari abinda zan faɗa miki in ya so sai ki yanke duk hukuncin da kika ga yafi miki”

Shiru tayi tana ta ciccika tana sauke ajiyar zuciya.

“Yanzu wane baƙin munafukin ne aka samu ɗan Wuta da ya zo ya ke neman shiga tsakani na da matar da zan aura? Wallahi ni Allah ne shaida ta kin ko san nafi tsoron sa akan ki domin baki da wuta kuma baki da aljannar sakani. Hafsah Mahaifiyata ta yi rantsuwa da cewa sai na aure ta saboda sun san ba son ta ni ke ba, kinga ba zan saɓawa umarnin Mahaifiyata ba, dole zan yi mata biyayya. Ko pictures ɗin da kika gani ba'a son rai na aka yi su ba, babu wata wadda nike so idan ba ke ba, idan naga Hafsah ji nake tamkar in shaƙeta ta mutu akan tsanar ta da nayi, na tsane ta na tsane ta. Ni ke nike so kuma duk gidan mu suma sun san ke nike so hatta ita kanta Mahaifiyata. Saboda haka ki kwantar da hankalinki duk wata tsinannar da zata kawo miki gulma ki gurza mata rashin mutunci ni na ce. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ana gama bikin mu da ita da wata ɗaya za'a yi namu da ke, suma sun sani ita kanta Hafsah ɗin ta san da wannan agenda ɗin. Saboda haka ki saki ranki ki tashi ki shirya zan zo anjima muje mu sha ice cream”

Ji tayi tamkar an zare mata ƙayar da ta addabeta tana yi mata mugun zafi. Wasai taji ranta ya wanke ba sauran wata damuwa. Ita tasan Sadeeq will never do that for her. Shiyasa kafin ka yanke hukunci ya kamata kayi bincike. Tashi tayi taje tayi wanka, kowa a gidan sai mamaki ya ke ganin yadda ta miƙe lokaci ɗaya.

Ƙarfe shida na yamma ya zo kamar yadda yayi mata alƙawari ya ɗauketa suka Lula. Nan yayi ta ƙara kwantar mata da hankali kuma ya bata assurance cewa nan da wata uku za'a yi bikin su da zaran sun cika wata ɗaya shi da Hafsah.

Duk abin nan da ya faru bai sa ta manta da Kulsum ba kullum sai ta nemi matar a waya sai ta ce mata tayi haƙuri bata gari ne, idan ta dawo zata nemeta.

***********

Khadija an kawo kaya har lefe Maina ya kawo. Baba ya saka auren bayan sallar azumi wata huɗu mai zuwa.

Itama dai Meerah an so ayi auren daga baya kuma aka kai shi zuwa bayan Sallar azumi.

Duk na tuna da waɗan nan bukukuwan na mutane guda biyu sai inji tamkar in janyo lokacin ya zo kusa.

Tsakanina da mijina kuma muna nan dai, gaisuwa ce ta ke haɗa mu sai idan zamu fita ya ce min in shirya lokaci kaza zamu fita, kuma Alhamdulillah muddin ya samu lokaci yana kaini ina yin ziyara har Zurmi muka je wurin dangin su muka gaishe su yini guda muka dawo.

Islamiyya ma Ina nan ina zuwa kuma kullum ba fashi, shi yake kaini shi yake dawowa da ni, in kuma baya nan, ya aiko Driver ɗin Ayaa ya zo ya kaini duk da hakan baya masa daɗi sai dai kawai don baya so ina missing classes ɗina.

*********

Yau ma muna fita da sunan zuwa islamiyya sai gamu a wani wurin. Ban san mi za muyi ba shi ma kuma bai faɗamin ba sai daga baya na gane wai passport muka zo yi a office ɗin Imagiration.

Muna nan har kusan Magriba sannan muka koma  gida.

Ko da muka iso gidan har an gama sallah. Ɗakin shi ya wuce nima na wuce nawa na gabatar da sallahr Magriba.

Ina cikin azhkar sai ga waya ya kirani wai nayi baƙuwa tana jirana a main parlour.

Cike da mamaki na fito sai kawai mu kayi ido huɗu da Azima............

               OUM AMEER